PAGE 1
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
Note: Wannan Labarin ƙagaggen labari ne wanda yake mallakina, banyi shi don cin zarafin wani ko wata ba, nayi shi ne domin faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa, idan kuma yayi daidai da rayuwar wani to arashi ne.
SHIMFIƊA..........
Akwai lokuta da dama a rayuwa da duniya ke ba mu labarurruka masu kama da almara amma kuma a zahirin gaskiya su ne HAƘIƘANIN labarin rayuwar da mafi yawan mutane suke gudunarwa a doron duniya......Labarina zai motsa muku zuciya, sannan zai sa ku kasance cikin tunani da kuma tuhumar kawunanku akan haƙƙoƙan da suka rataya akan wuyanku na cewa shin kuna sauke su yanda yakamata ko kuwa akwai buƙatar gyara a cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Haƙiƙa komai a rayuwa yana da haƙoƙansa kuma yana da iyakokinsa.........
PAGE 1
G.R.A,
Gusau,Zamfara State.
Nigeria.
Tun da na farka ƙarfe uku na dare ban sake samun damar runtsa idanuwana ba ko na second ɗaya, sakamakon gigitaccen ihun da Ammie ta farka da shi tamkar za ta tada ɗakinda muke kwance a ciki. Da ƙyar na samu na yi nasarar lallaɓa ta ta nutsu sannan na bata ragowar maganin ta da ya rage na wannan watan sannu a hankali ina karanta mata addu'o'i har ta koma bacci.
Kallon inda Bahrain yake kwance na yi idanuna tab da ruwan hawaye waɗanda suka zame mini jiki. Matsawa na yi dab da shi na sake gyara mishi zanin lulluɓin shi sannan na ja gefe ina mai fashewa da kuka cikin sauti marar tashi sosai. Tabbas ba don kada in zamto cikin gafalallu ba da na ce na cire rai da tunanin samun warakar ciwon Ammienmu har abada, sai dai kuma, tuna cewa Ubangijin da ya hallicemu shi keda iko akanmu ga komai, ya rubuta mana dukkan abin da zai samemu tun daga farkon rayuwarmu har zuwa lokacin mutuwarmu, sannan idan har mun kasance masu imani to kada mu taɓa yanke ƙauna daga rahamarsa domin shi ne wanda yake da iko akan komai.
Duk irin yanda bacci ya kai ga ƙwarewa a iya sata bai samu ya yi galaba a kaina ba a wannan lokacin, sanadiyyar duniyar tunanin da na zurma marar amfani da kuma rashin mafita a gare ni kamar koyaushe. Ina nan a haka ban yi aune ba sai kiran Salla da na ji lokaci ɗaya ya shiga karaɗe dodon kunnena. Sai da na yi Salla sannan na fita na hura wuta na ɗora girkin jallof ɗin spaghetti, bayan na kambala na ɗora ruwan wanka suka yi zafi sannan na je na taso Bahrain na haɗa mi shi ruwan na ce yaje ya yi wanka sannan na koma ɗakin cikin faɗuwar gaba na shiga tashin Ammie a hankali wanda ina fata ta farka ba tare da wata doguwar matsala ba,sai dai kamar yanda aka saba wasu lokutan idan ta farka in yi maganar duniya amma ba za ta buɗe baki ko da sau ɗaya ne ta yi mini magana ba.
Kallon ta nake da idanuwana waɗanda suka kumbura suka yi mini nauyi sosai tsabar kuka murya a ƙasa na saƙala hannayena a cikin na ta na ce.
"Ammie kin farka? Ga ruwa na zuba miki a toilet ko za ki yi wanka?"
Yan da ta shiga kalle-kallen ɗakin ne yasa da sauri na gyaɗa mata kaina na ce.
"Bahrain yana bayin waje yana wanka Ammie, yanzu za ki ga ya fito ba jimawa."
Wani irin kallo ne ta bini da shi wanda a duk lokacin da ta ƙureni da ido tana mini wannan kallon, hakan yana mini ciwo sosai a raina, sai na riƙa jin tamkar tana mini kallon wata baƙuwa ce wacce ta fara gani a karon farko.
Idanuna na lumshe sosai waɗanda suka jiƙe da ruwan hawaye sannan na buɗe a hankali na ce.
"Ammie ki tashi ki yi wanka, ki wanke baki ki zo ki ci abinci."
Ganin na yi ta sakar mini murmushin ta tare da jinjina kai sai kuma ta miƙe ta nufi toilet ɗinda yake cikin ɗakin.
Basket ɗin Bahrain na ɗauko na zuba mi shi spaghetti tare da bottle water sannan na zuba mi shi ruwan lipton ɗinda na dafa a cup na kawo tsakiyar ɗakin na ajiye masa.
Gaishe dani ya yi bayan ya kambala salla da cewa.
"Aunty Beenafah ina kwana."
Jinjina kaina na yi ina mai sakar masa murmushi, na ce.
"Lafiya lau Bahrain da fatan ka tashi lafiya?"
Jikin Ammie ya je ya kwanta wacce ta jingina jikinta ga bangon ɗakin tayi shiru kurum ba tare da ta ce komai ba tsawon lokaci.
Tray ɗinda ke hannuna na dire a gabanta ina mai kallon Bahrain na ce.
"Bahrain ka tashi ka sha tea ɗinnan ka zo ka tafi ƙarfe takwas ake magana."
Daga haka ya zamo daga jikinta ya zauna tare da jan cup ɗin zuwa gabansa da bread ya fara ci.
Bayan ya kambala ya ɗauki school bag ɗin shi ya kalle ta ya ce.
"Ammie na tafi makaranta."
Jinjina kai ta yi tare da ɗaga mishi hannu kawai alamar Allah ya tsare take masa sai ya dawo.
"Ammie zan raka Bahrain yanzu zan dawo."
Na faɗa ina mai tsatstsare ta da ido domin in ga reaction ɗinta, sai dai komai bata ce min ba har muka fice.
Muna fitowa na saka key a hankali na rufe ɗakin gudun kada bayan na fita ta fito. Sai da mukaci rabin hanya sosai domin makarantar gwamnati ce yake zuwa kuma tana da nisa sosai da gidanmu na kalle sa, na ce.
"Allah ya tsare. Please kada ka tsaya wasa daga zaran an tashi kasa kai ka yi sauri ka dawo gida."
Basket ɗin shi ya ƙarewa kallo sannan ya ɗago ya kalleni ya ce.
"Aunty Beena banga kin saka mini komai ba fa, naga sai food flask da bottle water only."
Hannun shi na kama tare da kallon shi, cike da ƙwarin gwiwa na ce.
"Amma Bahrain na faɗa maka cewa komai ya ƙare sai idan mun siyo wani ko ba haka ba?"
Jinjina kai ya yi ya ce.
"To ki yi haƙuri na manta ne."
Murmushi na yi na ce.
"Ba komai, Allah ya tsare ya bada sa'a."
Daga haka yasa kai ya nufi makaranta ni kuma na juya na koma gida. Ina shiga gate ɗin gidan na nufi sashen Daddy a hankali na tura ƙofar parlourn na shiga, a dining area na tarar da shi yana zaune tare da Mummy Zaliha da kuma autar ta Humaida cikin shirin ta na makaranta itama.
Har ƙasa na duƙa tare da sadda kaina sosai, na ce.
"Daddy ina kwanan ku?"
Fuska ba yabo ba fallasa suka amsa sannan Daddy ya sake cewa.
"Beenafah ya jikin Maman ta ku?"
Sai yanzu na ɗago na kalle shi ina mai ƙara yin ƙasa sosai da sautin muryata na ce.
"Jikin Ammie da sauƙi Daddy, sai dai kuma maganin ta ya ƙare sannan kuma lokacin komawa asibiti ya yi tun jiya.."
Lokaci ɗaya yanayin fuskar sa da sautin muryar sa suka sauya wanda hakan sai ya sakar mini mummunan faɗuwar gaba, idan ban manta ba ko last month haka mukayi da shi sai da ya gama yi mini mita kamar ba zai saurare ni ba.
" Beenafah! Ni fa ki sani, magana ta gaskiya an fara ƙure manejin haƙurina..."
Cike da tsantsar mamaki da tashin hankali na ƙara zuba rinannun idanuwana akan sa cikin muryar magiya na ce.
"Don Allah Daddy ka yi haƙuri kada ka gaji... Likita ya tabbatar mini cewa har da rashin shan maganinta bisa kan ƙa'ida yake ƙara tsananta ciwon na ta. Ammie tana cikin zafin ciwo sosai..."
Ɗan ƙara muskutowa ya yi zuwa gaba kaɗan muna fuskantar juna da shi ya ce.
"Idan fa ba ki yaba mini a kan ciwon Mulaifa ba to bai kamata ki ga laifina ba Beenafah....Ko ba haka ba Hajiya Zaliha?"
Ya ƙarashe zancen yana mai kallon Matarsa Hajiya Zaliha.
Taɓe baki tayi tare da dire spoon ɗin hannun ta ta ce.
"Uhm! Ciwon dai in kai ne ka ɗora mata ai sai ka ɗauke mata mu gani. Abu yaƙi ci yaƙi cinye wa sai kace cin ƙwan makauniya! Kullum cikin narka dukiya ake wurin neman magani amma kamar wacce ake ƙara turarawa turaren sabuwar hauka! Mace sai kace ba musulma ba, kin kasa haƙuri da jarabawar da Allah ya ɗora miki, haba! Dama ace ke ɗin wata ce mai cikakkkiyar nasaba."
Wayar sa naga ya janyo da ke gefe ya shiga dannawa tsawon mintuna sannan daga ƙarshe ya mayarda kallon sa a kai na wanda tuni na gama rikicewa da kuka ya ce.
" Kukan nan ya isa haka Beenafah, ni kawai na wa taimako ne, kuma abin da zan iya shi zan yi. Na tura miki kuɗi sai ki je ki ɗauki ATM card ki ciro kuɗin, sannan kuma ku yi haƙuri da abin da kuka gani, nauyin ne ya yi mini yawa."
Daga haka ya miƙe ya nufi ƙofa Humaida dake zaune itama ta miƙe ta bi bayan sa, sai mai aikin su Biba da itama ta bisu ɗauke da kayan makarantar Humaidar za ta kai mota.
Muryar Mummy Zaliha na ji a kai na tana faɗin.
" Yanzu Beenafah godiyar ma ba za ki iya yi wa Alhaji ba? Kin san irin wahalar da yake sha wurin neman kuɗin nan amma kuma ya tura muku zunzurutun kuɗi ba za ki buɗe baki ki iya yi masa godiya ba?"
Gwiwa a sanyaye na ɗago kaina na kalle ta na ce.
"Ki yi haƙuri Mummy. Mun gode sosai Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi."
Daga haka na miƙe na koma ɓangarenmu inda na tarar da Ammie har yanzu tana nan a wurin da na barta. Ruwan lipton ɗin kawai ta shanye, spaghetti ɗin kuma ta kwaɓa ta tare da bread ɗin ta cakuɗe wuri ɗaya.
" Beenafah! Ina kika je kika bar ni tun ɗa zu? I'm scared.."
Zaunawa na yi gefenta ina kallon ta na ce.
"Ki yi haƙuri Ammie na, na je wurin Daddy ne. Yanzu ma zan ƙara fita na je wurin mai P.O.S muna da buƙatar kuɗi. Babu komai a nan, babu abinda zai same ki, yanzu zan dawo. "
Jinjina kai ta yi da murmushi ta ce.
"Allah ya tsare."
"Amin Ammie."
Ina fitowa na sake rufe ta a ciki kamar ko yaushe na fito na je shagonda na saba zuwa can nesa da unguwar tamu sosai, bayan mun gaisa na miƙa mi shi ATM card ɗin na ce ya fara checking balance ko na wa ya gani ya cire mini.
"Dubu tamanin ne a ciki, su za'a cire?"
Mutuwar tsaye na yi jin kalaman Baba mai shago na cewa wai dubu tamanin ne a account ɗin. Tamanin fa? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ni Beenafah ta ina zan fara? Kuɗin maganin Ammie kawai na wata ɗaya dubu sittin da biyar ne, ga kuɗin mota da zamu hau zuwa da dawowa ya kai dubu talatin, ga shi abincinmu ya ƙare.
"Ke nake saurare Beenafah kin ga mutane na kan layi suna jirana."
Hawayena na share ina mai jinjina kaina na ce.
"Ka cire kuɗin gaba ɗaya ka bani."
Haka ya ciro kuɗin ya bani har na chargies suka kama dubu saba'in da tara da ɗari biyar.
Tafiya nake akan hanya kuka nake har na iso gidan na buɗe ƙofa na shiga.
Ban san lokacinda na yi watsi da kuɗinda yake hannuna ba na nufe ta da gudu cikin tsananin tashin hankali ganin yanda duk ta ji wa kanta ciwo ga glass ɗin window duk ya farfashe ya tarwatse a ƙasa.
✍️ OUM-AMEER ✍️