GANIN IDO

PAGE 2

by @oumameer2671

GANIN IDO 🥀🥀

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

      OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa

PAGE 2

Ƙanƙameta na yi gam a jikina ina mai fashewa da kuka tare da girgiza kaina na ce.

"Ammie dan Allah ki daina! Ki daina cutar da kanki haka na roƙe ki, ki yi Haƙuri...."

Wani ɗankwalina dake gefe na ɗauko cikin hanzari na yage shi na ɗaure mata yatsun hannunta na dama dake ta famar zubar da jini wanda ina yi ina kuka. Bayan na kambala na koma na ɗauko tsumma da ruwa na zo na goge wurin, sannan na tattara broken glasses ɗin na kwashe na dawo inda ta kwanta nima sai na kwanta a gefenta zuciyata cunkushe da ƙunci da damuwa har bacci ya yi nasarar ɗauke ta.

Tashi na yi na tattara kuɗin na kai na ajiye sannan na dawo na shiga shirya mana kayan tafiyarmu zuwa asibiti gobe.

Bayan na kambala na ɗauka cikin kuɗinnan na siyo mana shinkafa gwangwani huɗu da mai da yaji dakakke da gawayi na zo na ɗora a wuta. Ba don kowa nake wannan ba sai don Bahrain kada ya dawo ya taras cewa ban ajiye masa komai ba ba zai ji daɗi ba.

Ina kan aikin ya dawo ƙarfe biyu na rana ya taddani, bayan ya cire kayansa ya yi salla ya fito ya tanyani muka kambala. Muna yi yana damuna da tambayoyinda ya saba a kullum kamar wani sabon ɗan Jarida har ya gama ci ya yi wanka ya wuce Islamiyya.

Ina nan har ƙarfe uku na rana Ammie bata farka ba, hakan yasa na je na shiga tashinta, sai dai kuma hankalina ne ya ƙara tashi sosai jin yanda jikinta ya gashe da zafi sosai alamar zazzaɓi.

Ban yi ƙasa a gwiwa ba na shiga karanta mata addu'o'i ina tofa mata sannan daga baya na ɗauko ƙyalle ina tsomawa a ruwa ina goge mata jikin domin in samu zafin jikin na ta ya rage saboda ƙa'idar likita na cewa kada a taɓa bata ko wane irin magani matuƙar ba daga gare su bane, hakan yasa na yi amfani da wannan hanyar don rage mata zafin jikin kafin gobe.

Bayan na gama kambala sallar Asr na ɗebo abincin a plate na zauna da kaina ina ba ta wanda bata wani ci sosai ba ta ɗauke kai.

Muna nan Bahrain ya dawo muka zauna muna ta tattaɓa fira wanda yawanci duk shi ne yake tambayata ina ba shi amsa kamar abin dole, Ammie babu abin da take idan ba aikin bin mu da kallo ba.

Misalin ƙarfe tara saura na dare na tashi bayan na kambala sallar Isha na cewa Bahrain ya kula da Ammie zan je sashensu Mummy Zaliha na dawo wanda a lokacin na tabbatar Daddy ya dawo gida yana parlourn sa tare da iyalansa suna nishaɗi.

A hankali na yi sallama tare da tura ƙofar lokaci ɗaya na shiga ciki.

Idona ne ya sauka akan Daddy dake zaune akan 3seater, Hassana da Husaina a gefensa wanda da alama dawowar su kenan garin domin ɗazu da na zo da safe ban taradda su ba. Sai kuma Humaida dake gefen Mummy riƙe da babbar robar ice-cream yayinda su ma kowannensu ke riƙe da abin ci da sha na more rayuwa suna ci suna fira cikin nishaɗi.

Tsayawa na yi daga can nesa da su na durƙusa kamar ko yaushe na sadda kai na a ƙasa na gaishe su ɗaya bayan ɗaya.

Aunty Husaina ce kawai ta kalleni ta ce.

"Beenafah ya jikin Ammie?"

Jinjina kaina na yi na ce.

"Jiki da sauƙi Aunty Husaina sannunku da zuwa."

"Yauwa sannu! Ina Bahrain?"

"Bahrain yana ciki Aunty Husaina na gode."

"Ya akayi kuma Beenafah?"

Cewar Daddy yana mai tsatstsareni da ido tamkar wanda ya kama mai laifi.

Kallonsa na yi murya a ƙasa sosai na ce.

"Daddy gobe ne zamu tafi asibiti, shine na ce bari na zo na yi muku sallama..."

"To ba na riga na tura muku da maƙudan kuɗi ba? Mi kuma kike nema?"

Girgiza kaina na yi na ce.

"Ba komai Daddy, sallama na zo na yi muku saboda na san koda za ku tashi da safe mun riga mun tafi."

"OK. Ki je ki yi wa Biba bayani tun yanzu cewa za ki bar Bahrain kada ta manta da shi."

Sake yin ƙasa da idona  na yi  na ce.

"Ai Daddy da shi zamu tafi wannan karon?"

"Tow! Lallai Beenafah."

Cewar Mummy tana mai jinjina kai tamkar wacce aka cewa na aikata wani zunubi.

Shima dai Daddyn shiru ya yi na wasu daƙiƙu sannan daga ƙarshe ya sake kallona ya ce.

"But why do you want to go with him? Ko ya ce miki ana mi shi wani abun ne idan kun tafi?"

Da sauri na girgiza kaina na ce.

"A'a Daddy, bai faɗa mini komai ba kawai dai ji nayi hankalina bai kwanta da na bar shi ba a wannan karon."

Wani irin kallon mamaki Mummy ta jefa mini tareda faɗin.

"Hankalinki bai kwanta da ki bar shi ba? Kamar ya?"

Kallon ta Daddy ya yi ya ce.

"A'a Hajiya Zaliha, ai duk wanda ya ce zai haɗiye gatari to sakar mishi ɓota."

"Ai abokin munafurcin Beenafah ya mutu ya barta a duniya Alhaji. Da Bahrain za ki je asibiti ko? To Allah ya tsare hanya."

Miƙewa nayi a raina ina cewa Amin, na juya da nufin ficewa sai na ji muryar Aunty Husaina ta kira sunana.

Waigowa na yi kawai ba tare da na motsa ba nace.

" Na'am Aunty Husaina"

"Zo ki ɗauki wannan ledar ki kaiwa Bahrain."

Ba musu na zo na ɗauka ina mai yi musu godiya tamkar zan kifa gudun kada kuma Mummy Zaliha taga laifina akan cewa ban yi godiya ba, ga shi sai wani hararata suke sai ka ce ni ce na roƙe su.

Ina fitowa na zo wurin da suke zuba shara zuciyata na wata irin tafarfasa na kifa ledar a ciki gaba ɗaya ina mai ƙara jin wata irin sabuwar tsanar su na daɗa ninkuwa a zuciyata.

Bahrain ma daga rana irin ta yau muddin ina raye da raina da lafiya ta ba zan sake barin shi hannunsu ba har abada.

Sai da na tsaya na darji kukana son raina sannan na koma ciki na gyarawa Bahrain shimfiɗa ya kwanta sannan na gyarawa Ammie wuri itama wadda ke zaune da littafi a hannunta wanda ba zance ga abin da take yi dashi ba, karantawa take ko kuma kallon littafin kawai take ban sani ba.

Takardun zuwa asibitin na ɗauko na haɗa wuri ɗaya tare da tulin emptyn kwalayen magungunan na haɗe a leda ɗaya na ƙulle su.

Washegari tun ƙarfe shida na Asuba muka kambala shiryawa muka fito mu uku, sai da muka iso babban titinda da yake daura da makarantar Maryam Qur'an sannan muka samu keke napep ɗinda ta kai mu tashar mota muka hau motar Sokoto.

***

Psychiatric Hospital Kware,

Illela Road, Sokoto State.

Nigeria.

Psychiatry unit muka nufa kai tsaye. Wani Office dake gefen hagu wanda aka rubutawa 'Dr. Bashir Sani Consultant Psychiatrist' da manyan haruffa kai tsaye muka shiga bayan an yi mana izini.

Dr. Bashir shi ne mutumin da muka yi matuƙar sabawa da shi a halin yanzu domin tun ban san ma miye ciwon hauka yake nufi ba muke zuwa wurin nan har na zo ta ƙarfin tsiya tsabar wahala da rashin mai tsaya mana yasa na fahimci mine ne matsalar mahaifiyata.

Cike da girmamawa na gaishe sa Bahrain ma haka sannan ya yi mana izinin zama, sai da na zaunar da Ammie kujerar da aka tanada domin ta sannan muma muka zauna akan kujerun da ke jere gefe ɗaya.

Cikin sakin fuska kamar ko yaushe ya kalli Ammie ya ce.

"Hajiya Mulaifa, ina wuni."

Shiru kawai ta yi tana mai kallon ƙasa tamkar mai nazarin wani abu, hakan yasa ya ƙara kallonta ya ce.

"Madam Mulaifa good Afternoon...."

Still ba ta yi responding ba. Ƙarshe dai duk  wa su hanyoyinda yake bi ya bi amma kuma ko kallon shi bata yi ba ballantana ma ta nuna da ita yake magana.

Kukanda nake riƙewa ne ya suɓuce mini, jiki sanyaye na kalli Dr. Basheer na ce.

"Likita! Sosai yanayin Ammie ya sake rikirkicewa,komai ya sake lalacewa a 'ƴan kwanakin nan. Da farko munji kwanciyar hankali sosai ganin yanda ta dawo yin al'amuranta kamar kowa, za ta zauna mu yi fira, Sallah ma bata wuce ta da duk wasu ibadunda ta saba amma kuma yanzu komai ya dawo sabo tamkar ma yanzu ne ciwon ya same ta"

Jinjina kai ya yi cikin jimami yana ƙara nazartar yanayinta sosai sannan ya ce.

"Kamar yanda na faɗa miki a baya Beenafah, magani baya so a riƙa shansa yanda aka ga dama,ƙetare lokaci da akeyi idan tasha wata ɗaya ko biyu sai bayan wata ɗaya kuma a sake siye wannan matsala ce musamman ga irin matsalar mahaifiyarki. Magana ta gaskiya ga yanda aka ɗauko hanyar magance ciwonta da ace an ɗore da wannan hanyar da yanzu ta warke baki ɗaya, domin kamar yanda na faɗa miki tun farko cewa ciwon ta ana warke shi baki ɗaya idan har an kula yanda yakamata tun daga kan maganinta da kuma kulawa ta musamman. Ƙetare lokaci da ake yana sa cutar ta dawo wanda muke kira (relapse) wanda halin da ta tsinci kanta a ciki tun karon farko zai iya dawowa har ma yafi na baya muni da hatsari. Sannan tsallake lokaci da ake yana ƙara tsananta cutar, sannan shi karan kanshi jiki janyewa daga magunguna da ake yana sa a samu withdrawal symptoms wanda yake sa yawan zazzaɓi, ciwon kai, mummunar firgici, ko rikicewar barci..."

Cikin hawayenda suka kasa tsaya mini na girgiza kaina cike da baƙin ciki na ce.

" Wallahi likita! Da ace ina da iko ko wani zarafi da mahaifiyata bata kasance a cikin halin da take ciki ba a yanzu. Da akwai yanda zanyi ciwon ta ya dawo gareni da na yi domin ta samu sauƙi, azabar da take ciki ta yi mata yawa..."

Cike da mamaki Dr. Basheer ya kalleni ya ce.

"To amma nasan cewa kuna da zarafi da hanyoyin kulawa da ita kamar yanda aka faro, miyasa kike cewa haka a yanzu?"

Cike da jin wani sabon abu da ya taso ya tokare mini zuciyata na ce.

"Duniya ta shayar da ni mamakin da har yau ban gama farfaɗowa ba Likita..."

"Ina Daddynku Alhaji Mudassir Wazeer?"

Wani guntun murmushin ƙarfin hali na saki wanda yafi kuka ciwo na ce.

"Shine mutumin da yafi kowanne ban mamaki ma likita. Ba zan ɓoye maka ba domin abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa. Jiya gaba ɗai abin da ya bamu Eighty thausand ne wai har kuɗin motar tahowarmu nan da kuma kuɗin maganin wata ɗaya duk a ciki...."

Ƙasa na zamo ina mai harɗe hannayena wuri ɗaya murya cike da kuka na ce.

" A yanzu muna cikin tsananin halin neman taimako, bamu da kowa bamu da komai, bamu da wani gata mu ukun nan da ka gani sai Allah. Ba zan iya jure ganin halinda Mahaifiyata take ciki ba,ina tsananin ƙaunarta da kuma wannan ƙanin nawa, don Allah don girman Allah ka taimakamana kamar yanda Allah ya taimakeka, koda taimako ne ka nema mana don Allah ka ce ci Mahaifiyata daga wannan ƙanginda take ciki."

Jiki sanyaye ya jinjina kai sannan ya ce.

" Ina dangin mahaifiyar ta ku to?"

Nan ma girgiza kaina na yi cike da jin wani sabon ƙuncin na ce.

" Likita ka yi haƙuri, amma ba zan iya sanar da kai komai ba dangane da dangin Mahaifiyata."

Sai da ya ɗauki tsawon lokaci tamkar ba zai furta komai ba sannan daga ƙarshe ya sauke ajiyar zuciya ya kallemu ɗaya bayan ɗaya cike da tausayi ya ce.

"Shikenan! In sha Allah zan yi iya abin da zan iya Beenafah. Allah ubangiji ya bata lafiya yasa a da ce."

Cikin farin ciki na shiga yi masa godiya wanda har can ƙasan raina na ji daɗi sosai, kuma hakan sai ya ƙara fahimtar dani cewa har abada mutanen kirki ba su ƙarewa a duniya amma kuma marasa kirkin sun fi su ya wa.

Nurses ya kira guda biyu suka zo da case folder ɗinta ya yi duk wasu rubuce-rubucenda zai yi sannan daga baya ya yi musu umarnin tafiya da ita kamar yanda aka saba tare da shi zuwa can ainahin ɗakin jinya da gwaje-gwaje.

Hannunta ya kalla wanda na ɗaure mata shi tun jiya sannan kuma ya dawo da kallon sa a kaina yace.

"Amma miye abin da ya same ta a hannu haka? Ina ce sai da aka yi miki kashedi akan ajiye duk wani abin da zai sa ta cutar da kanta ko ba haka ba? Kuma duk kin san da waɗannan ƙa'idojin miyasa kike wasa haka? Kin san fa abu ne mafi sauƙi ta illata kanta."

Ajiyar zuciya na sauke cikin rashin jin daɗin abun da ya faru na ce.

"Wallahi babu komai a cikin ɗakinmu likita, daga katifa sai litattafai da kuma kayan sakawarmu. Fita na yi na je shago koda na dawo ta ɗauki dutsen da muke tare ƙofa da shi ta fasa window."

"Ki ƙara kiyaye wa."

"In Sha Allah."

                        ***

Dr. Basheer ya yi mana taimakonda har na mutu ba zan manta da shi ba, domin ya tsaya mana a lokacinda duniyar ta yi mana ƙunci. Ya taimaka mana daga aljihunsa sannan ya nemo mana taimako daga ƙungiyoyi masu bada tallafi wanda Alhamdulillah! A yanzu ta yi jinya mai kyau sannan mun samu tallafin kusan kuɗin maganin wata shida da kuma ɗaukar nauyinmu na zuwa follow-up ko wane wata kamar yanda aka saba. Sannan dangane da Bahrain ma hankalina kwance domin gidansa ya kaimu ni da Bahrain wanda matarsa ta kula da mu tamkar wacce tayi shekaru da saninmu har muka gama zaman asibiti wanda ya ɗaukemu tsawon sati shida duk da cewa ni bacci kawai ke dawowa da ni gidan har muka kambala.

Muna zaune a Office ɗinsa bayan ya kambala duk rubuce-rubucensa na sallamarmu ya kalli Ammie wacce ke riƙe da hannun Bahrain ya ce.

"Hajiya Mulaifa akwai wata damuwa? Ciwo? Ko wani abu dai koma miye"

Girgiza kanta ta yi cikin sanyin halinta ta ce.

"Ba wata damuwa likita, sai dai kuma...Sometimes I used to hear people talking..and I...."

Hannunta na jimƙe sosai a nawa, cikin sigar lallashi na ce.

"Kada ki damu Ammie, in sha Allah shima wannan a hankali zai daina."

Bayan mun kambala a motar sa ya kai mu tashar Mota yana mai ƙara yi min jan kunne akan kulawa da ita sannan ya juya ya koma.

Bayan mun shiga motar mun zauna na shiga yi mata kalamai ma su kwantar da hankali, sai dai kuma koda na leƙa fuskar ta, ta juya kanta tana kallon Window tamkar idanuwanta za su zazzago wanda ko kaɗan hankalinta baya tare dani. Cikin tsantsar mamaki nima na miƙa kaina sosai domin ganewa idona abin da take kallo a waje da har yasa ta bubbuɗe ido haka, ƙirjina ne ya doka sosai ganin mutuminda take kallo a tsakiyar tashar motar wanda kallo ɗaya zaka yi masa ya tabbatar maka da cewa mahaukaci ne. Na shiga ukuna! Kar dai ace wannan.....

           ✍️ OUM-AMEER ✍️