19
by @oumfatima33
💓MATAR MANYA💓
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 19
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
******** Washe gari kamar yanda nasa kaina haka na ƙwarara kaina na shirya na nufi gidan Aunty Zali duk da yanda zazzaɓi ya rufeni ban fasa kudurina ba saboda so nake in ceci rayuwar ɗana kota wane hali, na san kuma muddin naci gaba da zama a nan sai Alhaji ya zubar min dashi ko azzalumar Matarsa tayi min irin abinda ta yiwa Habasiyar Baba Attine.
Ban baro gidanba sai da na tabbatar na tattara duk wasu abubuwa nawa masu muhimmanci da taimakon Baba Attine, hatta takardun gidan da Alhaji ya nuna min ya saye shi da sunana sai da na É—auka ban bari ba don na tafi kenan ba dawowa.
Mun tsara da Baba Attine cewar koda Alhaji yazo nemana zata ce bata san lokacin dana fita ba.
Da ƙyar na kai kaina gidan Aunty Zali ina zuwa na zube a tsakar gida ina sauke numfashi. "Subhanallah! Lafiyarki kuwa Salma?." Aunty Zali da fitowarta kenan daga ɗaki ta ganni kwace a ƙasa ta faɗa tana nufo inda nake. Da ƙyar na iya ɗaga kai na kalleta nace "Aunty bani da lafiya ki kaini Asibiti."
"Subhanallah, yo ina mai gidan naki?." Kai kawai na girgiza mata na koma na kwanta ina yunƙurin aman da yake murɗa mun tun ina cikin adai-daita sahu.
Cikin tashin hankali Aunty ta ɗauki wayarta ta kira Mijinta tace yazo gida ba lafiya. Bai ɓata lokaci ba kuwa sai gashi ya dawo a rikice yana tambayar "miya faru?."
"Ka ganta yanzu ta shigo ta zube min wai bata da lafiya in kaita asibiti!." Ta faÉ—a cikin damuwa.
"To jiran me ake? Kamata maza muje." Abba ya faÉ—a. Da sauri Aunty ta koma É—aki ta sako hijabi ta fito ta kamata suka fita ta sakata a cikin mota suka wuce wani private hospital da suke ganin likita a can.
Suna isa aka amsheta aka jona mata drip ganin yanda jikinta yayi laushi, a can Abba ya barosu ya koma wurin aikinsa. Sai yamma ya dawo ya É—auke mu da Aunty ta kira shi ta sanar dashi an gama, gida ya mayar damu bayan nasha laidojin ruwa da yawa na samu karfin jikina.
______________★
A can gida kuwa Salma na tafiya ba daɗewa Alhaji ya iso gidan a fusace ya haura sama yana ƙwala kiran sunan Salma ko Bebyn babu. Saukowa ƙasa yayi bayan ya gama duba ko ina a saman bai gantaba.
"Attine! Attine!! Attine!!!". Haka ya shiga ƙwalawa Baba Attine kira. Da gudu ta fito daga kiching tana gyara ɗaurin zaninta dake ƙoƙarin kwancewa saboda saurin da take.
"Gani Alhaji, ina kwana." Bai kula gaisuwar da take masa ba yace "Ina wannan yarinyar ta shiga?."
"Ai ranka ya daÉ—e tun jiya data dawo ta hau sama bata saukoba inaga bata da lafiya ne."
"Ban gane bata sauko ba, to ina ta shige tunda na duba ko ina a saman ban ganta ba!". Ya ƙare maganar ransa na ɓaci da wannan rainin wayon.
"To ina Hajiya ta tafi kuwa?." Ta faÉ—a cikin damuwa tamkar gaske. Tsoki ya saki ya wuce ya fita wurin mai gadi ya tambaye shi ko yaga fitar ta.
"Eh ranka ya daÉ—e tunda safe naga ta fita É—auke da jaka."
"Are you mad? Uban wa yace ka buɗe mata ƙofar?!". Ya ƙare maganar a matuƙar fusace.
"Ayi haƙuri ranka ya daɗe baka ce kar a barta ta fita ba shi yasa." Bai ko kulashi ba ya koma ciki ya shiga zazzagawa Baba Attine masifa yace da saninta ta tafi baki suka haɗa tunda ba yanda za'a yi ta fita bata ji motsinta ba. Ita dai haƙuri ta riƙa bashi har yayi ya gaji ya fice direbansa ya jashi zuwa gidanshi.
Yana wucewa Baba Attine itama ta tattara nata ya nata tayi gaba abinta tana yiwa Salma addu'a da fatan samun nasara. Koda taje Hajiya ta tambayeta me yasa ta dawo cewa tayi "Hajiyar ce ta gudu shine itama ta dawo.
"Allah ya kyauta." Shine abinda ta faɗa kawai. Daga haka itama Baba Attine bata ƙara komai ba taja bakinta tayi shiru.
******** Alhaji kuwa suna zuwa gidan ya fita a motar ya shige ciki, a palonsa ya samu Hajiya Fatsuma tana ta kai-kawo. Tana gani shi ta nufo shi da sauri tana cewa "Ina munafukar take? Kai nifa banma yarda cewar bada sanin ka ba ta samu cikin nan. Na lurafa dama can ƙaunar yarinyar nan kake, to bari kaji wallahi sai ka saketa yanzun nan kuma koda uwarta take yawo sai an zubar da cikin nan ko kuma ta nema masa wani Uban ba dai kai ba!." Ta ƙare maganar cikin masifa da bala'i.
Zama kawai yayi saman kujera ya dafe kansa masifar tata na hawar masa kai. "Magana fa nake maka Alhaji!". Ta kuma faÉ—a a fusace.
"Ki kwantar da hankalinki mana za'a yi yanda kike so, yanzu dai bata gidan inaga gidansu ta tafi saboda na lura taurin kai ne da ita domin tun a can naso a cire cikin taƙi yarda." Ya ƙare maganar cikin kwantar da murya wanda duk mai hankali idan ya kalleshi ya san ba haka kawai ta barshi ba yake mata wannan biyayyar.
Ciki ta shiga ta ɗauko biro da takarda ta miƙa masa tace "Amshi nan maza rubuta mata saki uku, kuma daga yau ka gama auren wata ƴa Mace in dai ina raye kuma ina amsa sunana." Ba musu ya amsa ya rubuta mata saki uku ya miƙa mata.
"Yayi kyau, riƙe ka kai mata sannan maganar ciki kuma na san matakin da zan ɗauka." Tana gama faɗa ta fice fuuu tamkar kububuwa.
Kansa ya dafe yana sauke ajiyar zuciya yana jin wata irin nadamar sakin daya mata tana kamashi, sai dai ba yanda ya iya dole yayi abinda take so É—in. Ya jima a zaune kafin ya linke takardar ya saka aljihu ya fice a gidan direba ya jashi suka nufi Ofishinsa.
Lokacin da ake wannan gwaramar a nan a can gidan Malam Shehu ma rikicin ne ya ɓalle domin kuwa Sajida da aka samu aka mayar gidanta da ƙyar shine yau Mijin ya mata saki uku bayan ya ƙara lakaɗa mata mugun duka ya korota. Dalilin rigimar tasu shine Mijin ke neman Mata ita kuma tayi ta masa tijara, shi kuma ya sameta ya naɗi jaka ya kuma ce ta tafi gidan Ubanta inda ta saba cin tsanwar miya.
Kullum tazo haka Baba Mari zata lulluɓe ainahin abinda ya faru taƙi faɗawa ko Babansu ne a ɗauki mataki saboda gudun kar a mata dariya. Haka zata lallaɓa Sajida ta bata haƙuri harda kuɗi take bata na toshiyar baki don ta koma, shi ma Mijin ta kira shi ta bashi haƙuri su koma.
To yau dai tura ta kai bango domin kuwa Sajida na fita asibiti antinatal Mijin ya kawo mata karuwa har cikin gida, a cikin É—akinta saman gadonta ta dawo ta kama su shine fa tayi ta kururuwa ta tara masa mutane, shine yaji haushi ya lakaÉ—a mata duka ya kuma mata saki uku take ga tsohon ciki.
Koda taje gida da kuka da ihu tana faɗar ta bani ta lalace, da gudu Baba Mari ta hankaɗe kayan abincin da take zubawa tana masifar Zainab taƙi ta shirya tazo ta fita sai kwanciya take wai bata da lafiya. Shine fa Sajidar ta shigo tana wannan ihun.
"Ke lafiya, meya sameki kike wannan ihun haka?." Ta faɗa tana riƙeta.
"Ya sakeni Baba, Shikenan Tukur ya sakeni saki uku Baba!." Sajida ta faÉ—a tana rushewa da kuka.
Baki ta toshe mata ta jata ɗaki tana cewa. "Ke dallah rufewa mutane baki zaki tona mana asiri a gaban maƙiya." Ta faɗa tana makawa Mama da taji kururwar ta fito harara. Ana haka Zainab ta fito daga ɗaki tana yunƙurin amai kafin ta shiga kelaya shi kore shar ba kyan gani.
Sakin Sajida Baba Mari tayi ta nufi Zainab tana cewa "Ke kuma aman uban me kike? Tashi mu gani." Ta ƙare maganar tana miƙar da ita ta shiga duba idanunta da bakinta da yake ta jima tana kwanciya da ƴan ƙananun ciwace-ciwace da take fama dasu, da farko Baba Mari ta zaci shawara ce ke damun Zainab ɗin. Ashe dai shawara ce mai lasisi.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, wace iriyar lukutar masifa nake shirin gani da rana tsaka ni Mariya?." Ta ƙare maganar tana ɗora hannu a ka tana zunduma ihu ama manta da a tsakar gidan take tonawa kanta asiri.
Juyowar da zata yi suka haɗa ido da Mama ta ƙara maka mata harara ta shiga zaginta da kiranta da munafuka, cewa take yi "Azzaluma muguwa asiri kika yiwa ƴaƴana saboda taki ƴar ta gama lalacewa shine kika yiwa nawa ƴaƴan asiri to wallahi baki isaba." Tana ƙare maganar ta nufi Mama da nufin kamata da kokawa ta riƙe mata hannu tace "Kar ki soma, koda wasa kar kice zaki taɓa jikina da sunan duka wannan ne kuma baki isaba. Duk abinda zaki faɗa kije kiyi ta faɗa ba zan kulaki ba, ai Allah ba azzalumi bane yana ji kuma yana ganin abinda kowa ke aikatawa. Mugun alkaba'in da kike ɗorawa yarinya akan ƙaddarar data faɗa mata shine kika fara ganin sakamakon a cikin ɗakinki." Tana gama faɗa ta yarfar da hannunta ta shige ɗaki abinta.
Kuka kawai Baba Mari ta fashe dashi ta shiga sabbatu tana korar maƙota da yara da suka cika gidan ganin ƙwam.
(Haka Allah yake al'amarinsa, hausawa suka ce wai idan kaga gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta to ka shafawa naka ruwa don baka san abinda zai iya faruwa a gaba ba, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyarmu).
ÆŠaki Baba Mari taja Zainab tama manta da kayan abincinta da yara suka dakawa wawaso suka yi waje da gudu, dukanta ta shiga yi tana tambayarta wanda yayi mata ciki, kuka take tana kururuwa tana neman ceto sai dai ba wanda ya shiga saboda sanin halin Baba Mari da akayi. Sai da ta daku sosai taji zata mutu sannan tace. "To ba Audu bane abokin Yaya Habu da yake bani kuÉ—i da yawa ina kawo maki ba."
Salati suka saki Baba Mari da Sajida wacce wannan tashin hankalin yasa ta manta da tata matsalar. "Shike nan kin kashe mu Zainab." Sajida ta faÉ—a.
Wayarta ta ciro ta kira lambar Karima tace tazo gida babu lafiya.
A haka Malam Shehu ya dawo daga yawon neman abinda zai rufawa kansa asiri ya tarar da wannan tashin hankalin da yasa shi kusan faÉ—uwa.
______________★
Da dare bayan Abba ya dawo daga wurin aiki suka zaunar dani shida Aunty Zali suka tambayeni abinda ke faruwa. Ban ɓoye musu komai ba na faɗa musu har labarin da Baba Attine ta bani na jikarta. Sosai hankalin Aunty Zali ya tashi, ko shi kanshi Abba sai da ya girgiza da jin wannan batun.
"Wasu irin mutane ne waɗannan masu tsananin son zuciya da rashin tsoron Allah?, in banda butulcewa ni'imar Ubangiji, haihuwar da wasu ke nema ido rufe amma kai Allah ya baka ka riƙa salwantar dasu a banza saboda son zuciyar wata!." Abba ya ƙare maganar a sanyaye da alamar abin ya taba shi ba kaɗan ba.
"Bari kawai Alhaji, ai kuwa akan wannan basu isaba,don zan iya shari'a dako waye akan wannan cikin babu ubanda isa a zubar da shi. Aure kuma kin gama aurensa, dole ya sake ki tunda ba mutumin arziƙi bane!." Aunty Zali ta ƙare maganar a fusace.
Ni dai na kasa cewa komai kuka kawai nake ina jin cewar alhakin Suhail ne yake bibiyata, dama Æ´an magana sunce idan baka godewa ni'imar Allah ba ka godewa azabar
'ko ina yake yanzu? Oho'. Nayiwa kaina tambayar na kuma bawa kaina amsa duka a zuciyata.
Maganar Aunty Zali ce ta katse min tunanina da naji tana cewa. "Yanzu ta ina ya kamata mu fara Alhaji?."
"Daughter bani address ɗin da zan same shi sai muyi maganata masalaha muga in zai fahimta tukun. Idan kuma yaƙi to sai mu ɗauki matakin Shari'a."
"Haka ya kamata ayi kam." Cewar Aunty Zali. Address ɗin office ɗinsa daya taɓa kaini lokacin da muna soyayya na faɗawa Abba kafin suka sallameni na tafi ɗakina na barsu suna tattaunawa akan ya kamata Aunty Zali taje ta sanar da Mama da Baba don su san halin da ake ciki ko addu'a sa taya da ita.
"Haka ne Alhaji gobe sai in je in sanar dasu."
To Allah ya kaimu."
********** A ɓangaren Hajiya Fatsuma kuwa ta gaza tsaye ta gaza zaune tunanin duk wata hanyar da zata bi ta salwantar da cikin nan take yi. Babban tashin hankalinta shine a haifawa yaranta kishiya, ya zamana cewa akwai wasu da zasu ci gadon Alhaji bayan su.
Lambar aminiyarta ta kira ta sanar da ita duka halin da ake ciki, shawara ta bata akan su kai sunanta gidan teacher ya aika mata mugan aljanu su zuƙe cikin kowama ya huta. Da wannan shawarar suka rabu sannan ta samu natsuwar yin wanka taci abincin data kasa ci tunda Alhaji ya sameta da maganar cikin......