20
by @oumfatima33
💓MATAR MANYA💓
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 20
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
......... Kamar yanda Abba ya faÉ—a washe gari daya fita wurin aiki ya biya Ofishin Alhaji Murtala dala ya same shi da maganar abinda ya faru. "Barka da zuwa, Bismillah ga wuri zauna." Alhaji Murtala dala ya faÉ—a yana nunawa Abba wurin zama.
Zama yayi suka fara gaisawa da alamun sanayya a tsakaninsu. "A'a Alhaji Tahir kaine a ofishin nawa, kwana da yawa ba'a haÉ—uba." Alhaji Murtala dala ya faÉ—a yana murmushi.
"Alhaji Murtala dama kaine surukin nawa ban sani ba?." Da mamaki ya kalleshi yace "Suruki kuma? Ta ina? Ko dai kana da Babban yaro ne da yake neman ɗaya daga cikin yarana?." Ya masa tambayar cike da mamaki da yake dama mua'amalar kasuwanci ne ya taɓa haɗasu ba wata doguwar alaƙa ba da kowa zai iya sanin iyalin kowa.
"A'a ko ɗaya, Matarka Salma ai ƴar wajen Yayar mai ɗakina ce kuma yanzu haka tana can gida tare da iyalin nawa." Lokaci ɗaya fara'ar dake saman fuskar Alhaji Murtala dala ta ɓace ɓat ya shiga mazurai.
Alhaji Tahir bai damu da canjin yanayinsa ba yaci gaba da magana "Dama taje mana ne da wata magana wacce muka kasa gane me take nufi shi yasa nace bari inzo da kaina in sameka mu tattauna." Ya ƙare maganar yana kallon sa. Maimakon Alhaji Murtala dala ya bashi amsa sai kawai yasa hannu a aljihunsa ya zaro farar takarda ya miƙa masa sannan yace. "Dama ina shirin zuwa can gidan nasu in bata wannan saƙon, amma tunda gashi kazo shikenan sai ka amsar mata."
Amsar takardar Abba yayi yana juj-juyata kafin ya kalli Alhajin yace. "Ta micece wannan É—in?."
"Ka duba zaka gani." Ya bashi amsa a taƙaice. Bai musa ba ya shiga ware takardar ya duba. Da sauri ya ɗago yana kallon Alhajin ganin takardar saki ce ya rubuta wa Salma, saki kuma har uku.
"Subhanallah! Alhaji me yayi zafi haka? Ina ganin bai kamata ka yanke wannan hukuncin cikin gaggawa ba, kamata yayi ace kayi tunani sosai ka yake hukuncin wata ƙila ku samu masalaha da iyalinka tunda gaugawar sakin bata da amfani."
"Kayi haƙuri Alhaji Tahir na riga na yanke hukunci, sannan maganar ciki kuma na faɗa mata bana buƙatarsa, idan ta shirya zubarwa tayi min magana zan kashe ko nawa ake buƙata wurin aikin." Da tsan-tsar mamaki Alhaji Tahir yake kallonsa yana mamakin wannan wane irin jahilci ne haka.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "To shikenan tunda ka riga ka yanke hukunci Allah yasa haka yafi alkairi, sai dai maganar zubar da ciki babuta idan kai baka buƙatarsa to ita tana son abinta, muma kuma muna son duk abinda ya fito daga gare ta koda kuwa ace ba ta hanyar aure ta same shi ba bare ɗan sunnah. Gargaɗin da zanyi maka shine ba ruwanka da cikinta idan kuma kai ko matarka kukayi yunƙurin cutar da ita to ba zamu bari ba, zamu ɗauki matakin Shari'a, na barka lafiya!". Ya ƙare maganar a fusace ya miƙe ya fice ba tare daya jira cewarsa ba.
Kai Alhaji Murtala dala ya dafe yana dukan table É—in gabansa yama rasa abinda ke masa daÉ—i, lokacin daya fara ganin yarinyar a kallo É—aya yaji ya rasa control É—insa saboda irin zubin hallitar da Allah ya mata wacce a nan take yaji wata irin sha'awarta mai tsanani ta kamashi, yaji zai iya bata komai idan har zata amince masa.
Ya tareta da maganar soyayya da aure tamkar yanda yake yiwa ko wace yarinya idan ya ganta ta masa, cikin sa'a kuwa yayi dace yarinyar nada rawar kai da son jin daɗi da rayuwar hutu, wanda yayi amfani da haka ya rinƙa kashe mata manyan kuɗaɗe har ta gamsu dashi ɗari bisa ɗari ta kuma amince masa. Sai dai kuma da yaje neman aurenta tamkar yanda ya tsara sai Mahaifinta yace ya bada ita, da yaga zai rasata ne da gaske ba tare daya samu abinda yake so ba shine ya kirata da sunan zai bata gudunmuwar aure yayi amfani da damar ya saka mata ƙwaya a abin sha ya yaudareta da kalaman ƙarya yayi abinda yakeso.
Koda yaga tana shirin masa bore sai ya lallaɓata akan wannan abinda suka yi shine kaɗai mafitar da zasu mallaki juna, ta amince da hakan suka rabu da niyar ko an ɗaura auren Mijin zai sake ta idan ya san abinda ya faru sai ta dawo ya aureta. Ya dai a lokacin ya faɗa mata ne kawai amma ba da gaske yake ba saboda ganin ya riga ya samu abinda yake kwaɗayin samun dama, sai dai kuma bayan nan ya kasa natsuwa yaji duk duniya tamkar bai taɓa haɗuwa da Macen data kaita ba. Wannan shine dalilin da yasa yaji ba zai iya rabuwa da ita ba ya shiga nemanta a waya bai sameta ba.
Koda ya sametan kuwa cikin sa'a aurenta ya mutu shine ya dawo ya aureta da nufin idan ya gama morewa ya saketa kamar yanda ya saba ya kuma yiwa matarsa alƙawari. Sai dai a halin yanzu ya kamu da soyayyarta ta gaskiya gashi kuma ba yanda ya iya dole ya sake ta bisa umarnin Matarsa da baya iya mata musu, sai dai yana cikin nadama da dana sani.
Abba kuwa koda ya koma gida ya sanar da Aunty Zali yanda sukayi da Alhaji Murtala dala saliti tayi ta salamce sannan tace. "Amma dai Alhaji wannan mutumin anyi mutumin banza."
"Hm ki bari kawai Zaliha, aini abin nasa ma tsoro ya fara bani."
"To Allah ya kyauta, Allah kuma yasa haka shi yafi alkairi, ai ni gara ma daya sakata cikin sauƙi. Domin kuwa da bai saketa ba da kaina zan kaishi kotu ya saketa, yo wannan ai ba mijin aure bane, Allah dai yasa mu dace."
"Ameen." Abba ya faÉ—a.
"Ina ganin gobe idan Allah ya kaimu zanje in yiwa su Yayar bayani, amma Salma kam anan zataci gaba da zama har Allah ya sauketa lafiya ta samu wani Mijin ɗan arziƙi tayi aurenta, ɗa kuma ko me ta haifa ni zan riƙe in sha Allah domin kuwa dama nema nake!". Ta ƙare maganar cikin sanyi murya.
"In sha Allah mu zamu riƙe ko menene ta haifa kar ki wani damu." Cewar Abba. Ni dai da nake zaune ban san ina zubar da hawayen farin ciki da tausayin Aunty da Abba ba. Ƙaunarsu ce mai girma ta ƙara mamaye zuciyata saboda irin soyayya da ƙaunar da suke nuna min. A cikin zuciyata na shiga yi musu addu'ar Allah ya basu haihuwa mai albarka, yayinda naji a raina cewar zan iya mallaka musu abinda na haifa halak malak.
★★★ Washe gari Aunty ta shirya ta nufi gidan Yayarta domin sanar dasu halin da yarinsu take ciki, sai dai taje ta samu gidan ba daɗi domin kuwa ya tabbata dai Zainab cikine da ita wanda Baba da kansa ya kaita asibiti aka aunata aka tabbatar masa da abinda ake zargi. Wanda anan Baba ya yanke jiki ya faɗi shima sai gado aka bashi.
Bayan yasha laidojin ruwa aka sallame shi suka koma gida, gaba ɗaya gidan ya rikice domin kuwa Baba Mari ma dai kukan data kwana yi zazzaɓi ya zuba mata a kwance take rijib. Yau dai ga irin ƙaddarar data samu wata ta rinƙa izgili tana cika baki sai gashi itama abin yazo kanta.
Dawowar su Mama daga asibiti kenanan Aunty Zali ta iso ta tarar da abinda ke faruwa. Ya jiki tayiwa Baba kafin suka shiga É—akin Mama. "Wai Yaya lafiya mike faruwa a gidan ne? Me ya samu Malam É—in da ita waccen Matar?". Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta shiga bawa Aunty labarin abinda ya faru.
"Hm ai dama ba'a yiwa al'amarin Allah shishi-shigi, gashi nan itama ta gani a ƙwoƙwonta. Wallahi ko sannu ba zan mata ba bare Allah kyauta abinda ta shuka take girbewa."
"A'a Zaliha ba'a haka, ai ba'a biya ta mutum, ki shiga ki dubata kiyi mata Allah kyauta."
"Shike nan Yaya tunda kince zan je, yanzu dai ba wannan ba muyi maganar data kawo ni."
"To ina jinki." Duk abinda ya faru Aunty Zali ta faɗawa Mama. Ajiyar zuciya Mama tayi tace "Allah yasa haka shi yafi alkairi!." Ta ƙare maganar fuskarta na bayyanar da damuwa.
"Ki kwantar da hankalinki Yaya ba abinda zai faru in sha Allah ke dai kici gaba da mata addu'a, sannan kuma zataci gaba da zama a can har ta sauka lafiya ta samu Miji tayi aurenta."
"Haka ne Zaliha hakan yayi dai-dai, Allah ya saka muku da alkairi, amma yarinyar nan tana ganin jarabawa da ƙananan shekarunta."
"Zata cinye ta in sha Allah, ƙarshen ko wace jarabawa nasara ke biyo baya, matuƙar mutum ya dogara da Allah kuma ya amsheta da hannu biyu." Aunty Zali ta faɗa cikin son kwantarwa ƴar'uwarta hankali.
"Amma yanzu ba zan fadawa Malam ba kar abin ya masa yawa zuciyarsa ta buga, idan yaji sauƙi sai a sanar da shi. Haka suka ci gaba da tattaunawa har Aunty ta tashi tafiya sannan ta shiga tayiwa Baba Mari ya jiki hadi da jajanta mata abinda ya faru duk da rabin jajen magana ce ta faɗa mata a kai-kaice.
Rakata zaure Mama tayi tana cewa in sha Allah zataje can gidan Iyayensu ta amso mata addu'oin abawa Salama ta riƙa amfani dasu, kuma ta dage da azukar saboda neman kariya daga sharrin masharranci. Da haka suka yi sallama ta wuce gidan saboda Salma data baro ita kaɗai a gidan kuma ba lafiya gareata ba.
Koda ta koma a kwance ta sameta kasancewar jikin nata ba kwari har yanzu, saboda yanayin laulayin nata irin na wancan cikinne mai takurawa.
"Sannu da zuwa Aunty kin dawo, ya kika baro su Mamar?." Na faÉ—a ina tashi daga kwancen da nake saman kujera. Zama Aunty tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da cewa. "Ai ki bari kawai gidan naku yau a ruÉ—e yake." A firgice na dubi Aunty nace.
"Subhanallah! Aunty meke faruwa a gidan? Mama dasu Sagir duk suna lafiya ko?!".
"Kinga ki kwantar da hankalinki lafiyarsu ƙalau ba abinda ya same su." Aunty ta faɗa cikin son kwantar min da hankali. Ganin hankalin nawa yaƙi kwanciya ta shiga sanar min abinda ya faru, na shiga firgici jin abinda ya faru da kuma rashin jin daɗin rashin lafiyar Baba. "Allah ya kyauta ya bawa Baba lafiya."
"Ameen, ai dama bai kamata dan Allah ya yiwa bawansa wata jarabawa ba ka riƙa cika baki kana nuna kai kafi ƙarfin haka, ni na godewa Allah daya nunawa Mari iyakarta." Aunty ta faɗa, ni dai ban ƙara maga ba saboda jikina da yayi sanyi.
Bayan watanni tara
Dukkanninsu tsai-tsaye suke a bakin ƙofar ɗakin theatre cikin zullumi da jiran tsammani, fuskokinsu kaɗai zaka kalla su shaida maka cewar basa cikin natsuwa. Ba mai cewa kowa komai sai addu'a da kowa yake iya abinda ya sani a zuciyarsa.
Bayan dogon jiran da suka yi cikin ƙaguwa aka buɗe kofar ɗakin, Nurse ce ta fara fitowa ɗauke da jariri naɗe a cikin farin shawul na jarirai. Gaba ɗaya mutanen wurin nufarta suka yi cikin sauri suna fatan ganin abinda aka samu, jiki na rawa Aunty Zali ta miƙa hannu ta amshi jaririn tana kallon fuskarsa. Baki ta buɗe zata yi magana wata Nurse ɗin ta fito ɗauke da wata jaririyar ta miƙa musu tana murmushi tace "Masha Allah kun samu ƙaruwar yara biyu mace dana Miji."
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!". Aunty Zali ta shiga mai-maitawa tana tsarkake sunan Ubangiji daya basu kyautar yara har biyu bayan irin gwagwarmayar da aka sha yayin rainon cikinsu, Allah ne yayi sai sun shaƙi iskan duniya amma sosai akaso salwantar dasu tun basu zama tsoka ba a cikin Mahaifiyarsu.
"Yaya kin ga ikon Ubangiji ko? Yara har biyu gasu sun shaƙi iskan duniya, zakaran da Allah ya nufa da yin cara ko ana mazuru ana shaho sai yayi." Aunty Zali ta ƙare maganar hawayen farin ciki na zuba saman fuskar ta.
"Haka ne Zaliha wannan kaɗan daga ikon Allah ne ya nuna wani bai isa hana a haifi wanda Allah ya tsara zai zo duniyar ba duk irin ƙoƙarin da zai yi wurin ganin ya hana faruwar hakan."
"Wannan haka yake Yaya ko yanzu Hajiya Fatsuma taga iyakarta, Allah ƙadirun alaan yasha'u." Aunty ta faɗa tana sake rungume kyakykyawan jaririn ɗaya ɗebo kamannin yan'uwansa sak wato yaran Hajiya Fatsuma.
Abinda ya faru shine lokacin da Hajiya Fatsuma ta kafe akan sai ta zubar da cikin dake jikin Salma don kar a haifawa yaranta kishiya. Babu irin shige da ficen da batayi ba wurin Malamai tana sakar musu kuɗi akan a salwantar da cikin, ba ƙaramar wahala Salma tasha a wancan lokacin ba Allah ne kawai ya ƙaddara tana da sauran kwana a gaba, sannan kuma dole sai an haifi Yaran da rabon haihuwarsu ya rantse, wanda a sanadiyar yawon gidan bokaye Hajiya Fatsuma ta haɗu da mummunan hatsari yanzu haka tana kwance bata iya ko motsawa domin kuwa lakar bayanta ce ta stinke koda yaushe tana kwance sai dai ido, kuka kuwa tayi shi tamkar hawayenta zasu ƙare. Hakan kuma baisa tayi nadama ta tuba bisa laifukanta ba, sai ma tsananin baƙin cikin rashin zubewar cikin da yake sakata zubar da hawaye ba dare ba rana na takaicin faɗuwar da tayi a karo na farko a tarihin rayuwarta.
(Dama haka Allah yake yiwa mushrikai ya ara musublokaci suyi ta shuka tsiyarsu suna ganin wayo da dabararsu ce ta kaisu. Basu san É—aurin talala ya musu ba, lokaci É—aya kuma idan ya tashi kama mutum sai ya masa kamun kazar kuku ta yanda zai nuna masa shi ba komai bane, Allah ka hane mu aikata shirka amin)........