MATAR MANYA

21

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 21

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

.......... Mai jego da yaranta sunci gaba da amsar kulawa a wurin likitoci tare da kulawar Iyayenta dake bata kulawa tako ina ta juya kulawa suke bata.

Satinsu ɗaya a asibiti aka sallameta suka koma gida, inda kai tsaye gidan Aunty Zali aka wuce da ita tunda dama a can take da zama kamar yanda su Aunty Zali suka buƙata.

A can gidan Malam Shehu kuwa shima abubuwa sun faru ciki akwai haihuwar da Sajida tayi a gidan taci gaba da kula da jaririn data samu wanda Mijin ya saka masa sunan Kakansa Dauda, ba ƙaramin rikici aka kwasa ba tsakanin Sajida da mijin nata akan sunan daya saka saboda tace bai isa ba bazata kira ɗanta da Dauda ba.

Inda shi kuma yayi rantsar ba wanda ya isa canzawa ɗansa suna haka yaga dama, ƙarshe dai dole aka haƙura aka tsawatar musu amma duk da hakan Amir take kiransa dashi.

Zainab ma dai ta haifi yarinyar ta bakwaini da tazo ba rai, hakan sosai yayiwa Baba Mari daɗi don a gaban kowa ta duƙa tayi sujada tana yiwa Allah godiya akan ƴar da tazo ba rai domin ya taƙaita musu wahala.

Domin kuwa ba ƙaramar rigima da aka kwasa da Audu ba domin cewa yayi shi ba zai amshi cikin ba tunda ba shi kaɗai yake mu'amala da ita ba, rigima sune har police station sai da ƙyar aka kashe rigimar akan idan ta haihu za'a je ayi gwajin DNA test. Cikin ikon Allah kuma sai aka haifi ƴar ba rai.

A ɓangaren Yaya Habu shima bai daddara ba ya bari aka ƙara kama shi da mugan ƙwayoyiyi wanda duk irin shige da ficen da Baba Mari tayi don ganin an sake shi hakan bai samu ba domin kuwa sai da aka miƙa shi prison wanda fitowarsa sai Allah domin ba ƙaramin laifi bane fataucin miyagun ƙwayoyiyi.

Duk wani ɗan jarin da Baba Mari take juyawa sai da ya faru ya ƙare ta dawo bata da komai ta zauna sai abinda Malam Shehu ya kawo aka sarrafa aka bata. Gaba ɗaya tabi ta lalace ta ƙare ta fita hayyacinta tamkar ba Baba Mari ba, duk wannan baisa ta saduda ta zubar da komai ba akan ƙiyayyar da take yiwa Mama ba sai ma abinda ya ƙaru.

Duk inda ta tsuguna bata da aiki sai zagin Mama ta riƙa faɗar cewa tayi mata asiri ta tarwatsa mata kan ƴaƴa duk sun tambaɗe, ai itama gashi nan Allah ya nuna mata ishara tunda an sako ƴar gwal ɗin kuma mijin yaƙi amsar cikin yace ba nasa bane.

Sharri da ƙazafi babu wanda bata faɗa amma Mama taƙi kulata ta tura mata aniyarta, Karima dake gidan Miji ita ke ɗan taimakawa uwar da abinda zasu ci wata ran duk da cewa itama ba wata wadatar take ciki ba. A halin da ake ciki yanzu Mama tafi Baba Mari rufin asiri domin kuwa tana ci gaba da sana'arta ta ƙulle-ƙulle, a ɓangare ɗaya kuma ƴar'uwarta naci gaba da taimaka mata tamkar yanda ta saba.

Da yake zuciyarta mai kyauce duk irin sharrin da Baba Mari ke mata baya hanawa in ta dafa abinci ta ɗebi wadatacce ta miƙawa Yaran Baba Mari, wanda zatayi ta masifa idan suka amsa amma ba mai kulata suke cinyewa har Sajida da Zainab ɗin.

Gaba ɗaya Malam Shehu ya ƙara zama abinda ya zama domin tun daga wancan lokacin baya da isashshiyar lafiya, don ma Allah yayi shi mutum mai ƙarfin zuciya da son sauke haƙmin da Allah ya ɗora masa. A hakan in yaji dama yake fita ya lalubo abinda zai basu su sarrafa.

******* Sati na biyu da yiwa Salma CS aka shirya shagalin suna wanda iyayen riƙonta suka ɗauki nauyin komai har ragunan da za'a yanka. Wanda jikin Salma Alhamdulillah ta warke sai abinda ba za'a rasa ba, bata da bakin da zata yiwa iyayen riƙonta godiya sai dai tayi musu addu'ar Allah ya cika musu burikansu na alkairi domin kuwa sun mata komai sun tsaya tsayin daka wurin bata kariya ita da abinda ke cikinta tun yana ƙarami ba tare da gajiyawa ba.

Wannan dalilin ne yasa lokacin da aka sallame su suka koma gida a gaban Iyayenta Mama da Baba da suka zo dubata tace ta mallaka wa Aunty Zali da mijinta yaran halak malak har abada domin kuwa sun can-canci wannan sadaukarwar.

Babu wanda bai zubar da hawaye a lokacin ba saboda tsabar farin cikin dasu Auntyn suka nuna domin kuwa kuka suka yi da idanunsu suna godiya da kyautar da Salma tayi musu wacce kuÉ—i basu isa su basu ba.

Saura kwana ɗaya suna ana ta shirye-shirye da yamma aka aiko kiran Abba wai wani mutum yana son ganinsa. Cike da mamaki Abba ya fita ƙofar gida don ganin mai kiran nasa a wannan lokacin.

Wanda ya gani ne tsaye a jikin mota sai direbansa daya fito shima yana jiran umarnimsa ya bashi mamaki domin bai yi zaton ganinsa ba, mamaki sosai ya kama Abba ganin Alhaji Murtala dala ne mai son ganin nasa. Shanye mamakinsa yayi ya nufeshi ba yabo babu fallasa ya masa sallama, da sauri ya ɗago daga duba wayar da yake yi ya miƙa masa hannu yana cewa "Barka da fitowa Alhaji Tahir."

" Barka dai." Abba ya faɗa yana miƙa masa hannu saboda sanin mahimmancin yin musabiha a musulunci. Alhaji bai wani tsaya ɓoye ɓoye ba ya shiga bada haƙuri akan abinda ya faru a baya, a ƙarshe ya ƙare da cewa "Wallahi sharrin shaiɗan ne da kuma sharrin mace, amma ba da son raina na saketa ba saboda da ina matuƙar ƙaunarta. Don Allah ayi haƙuri na janye maganar da nayi akan yaran data haifa, wallahi ina matuƙar ƙaunarsu har cikin raina tunda jinina ne su ɗin!". Ya ƙare maganar cikin damuwa.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan yace "Maganar nan bata nan bace, Bismillah mu shiga ciki." Ya faɗa yana nuna masa ƙofar sitting room ɗin sa. Bai yi musu ba ya bishi ciki ya zauna.

Cikin gida Abba ya shiga yayiwa Aunty da Salma magana yace suzo sitting room akwai baƙo, basu tsaya tambaya ba suka amsa masa da to. Shigowarsu kenan cikin sitting room ɗin Salma taci birki saboda wanda ta gani zaune a parlon ya zubawa mata ido yana kallonta tamkar zai cinyeta dasu.

"Bismillah ku shigo mana." Abba ya faɗa wanda hakan ne ya yanke kallon juna da muke yi nida Alhaji, a ɓangarena kallon tsana da tsananin mamakin abinda ya kawo shi nake masa. Yayinda shi kuma yake mata kallon tsananin kewa da bege.

Bayan sun gama gaishe-gaishensu wanda ko buÉ—e baki ban yi ba bare in gaishe shi, sai shine yake bina da kallon dana tsana. Gyaran murya Abba yayi ya shiga mana bayanin dalilin zuwan Alhaji, ajiyar zuciya Aunty ta sauke kafin ta fara magana.

"Yara dai nasa ne duk da yace baya buƙatar su, hakan ba zai sauya su daga jininsa b..."

Katse Aunty Zali nayi ta hanyar cewa "A'a Aunty waɗannan yaran basu da wata alaƙa dashi ko a shari'a, saboda shi ya buɗi baki yace baya buƙatar su tunma kafin a san meke ɗauke a cikina. Don haka yanzu bashi da damar da zai zo neman sulhu dasu, yara naku ne halak malak na tabbatar da hakan a gaban shaidu, ina roƙon daku ce masa ya gaggauta barin gidan nan. Sannan har abada kar ya kuskura yaje kusa da yarana idan kuma yayi wannan kuskuren to Shari'a ce zata raba mu."

Ina gama faɗin hakan na miƙe nayi ficewata ina jin yanda yake ƙwala min kira na juyo na watsa masa wani kakkausan kallo mai ɗauke da gargaɗi. Kai ya dafe bayan wucewarta yama rasa ta inda zai fara.

Aunty Zali ma tashi tayi tabi bayanta don bata da lokacin saurarensa, haƙuri Abba ya bashi ya kuma tunatar dashi cewar saki uku ke tsakaninsu saboda haka yama dai na maganar komawarta gidansa. Shiru yayi tamkar zai fasa kuka. Tashi Abba yayi ya shiga ciki ya amso yaran ya kawo masa su ya saka musu Albarka.

Kyawawan yaran ya zubawa ido yana kallonsu soyayyarsu mai zafi na ratsa zuciyarsa, rungume su ya ƙara yi a jikinsa yana jin tamkar mamansu ta fito suyi tafiyarsu gida suyi rainomsu tare.

Ba don yaso ba ya bawa Abba yaran ya mayar cikin gida ya fito suyi sallama, bayan motar direba ya buɗe aka shiga fitowa da sayayyar kayan jarirai masu kyau da tsada ana kaiwa cikin gidan. Ɗayar motar ɗaukar kaya da Abba bai san tare suke da Alhaji ba yaga an fara sauke kayan abinci masu tarin yawa da manyan raguna guda biyu da ƙaton sa.

Kusa da Abba ɗaya saki baki yana kallon ikon Allah ya matsa yana cewa "Ga wannan ayi hidimar suna na roƙeka da Allah kada kuƙi karɓa haƙƙin dake kaina ne na sauke." Ya ƙare maganar yana zaro kuɗi a emblop ya miƙa masa. Kasa magana Abba yayi sai hannu daya sa ya amsa, godiya Alhajin yayi masa ya shiga mota direba yaja suka wuce.

Koda Abba ya shiga gidansa sanar da Aunty Zali da Salma abinda ke faruwa kasa cewa komai sukayi saboda mamaki. "Lallai Alhaji Murtala dala ya canza, Allah ya ƙwatoshi daga sharrin mace. Koda yake ai itama taga sakamakonta tun anan duniya." Aunty Zali ta faɗa.

"Allah ya kyauta." Abba ya faÉ—a, ni dai komai bance ba na shige É—aki.

Nan da nan zancen haihuwar Salma dana abinda ya faru na dawowar mijinta da abinda ya kawo ya bazu a can unguwarsu domin wasu daga ciki suna nan abin ya faru, suna zuwa suka fara yaɗawa masu tayata murna nayi masu hassada na nuna baƙin ciki. Duka ba wanda ya isa ya sauya abinda Allah ya tsara.

★ Washe gari aka gudanar da bikin suna wanda ya ƙayatu sosai, anci ansha an yi walima. An raɗawa yara ainahin sunansu Hasan da Usaina za'a kirasu da Ameer da Ameerah.

Daga can gidanmu ma su Sajida da Karima duk sunzo wurin sunan inda itama Karima ta haifi ƴarta mace yanzu haka ma wani cikin ne da ita. Wasu daga cikin ƙawayena ma sunzo harda Bestie wanda a wurinsu ne nake jin labarin cewar an saka ranar auren Suhail da ƴar'uwarsa da Babarsa ta zaɓa masa daya dawo za'a ɗaura auren.

Wani irin tsits-tsinkewa naji zuciyata nayi amma na daure ban nuna ko a fuskata ba. "Ya dai?." Na faɗa ina kallon Bestie data tsareni da ido tana son karantar yanayina amma naƙi bata damar hakan. Ajiyar zuciya ta sauke kawai ta ɗauke kanta ba tare da tace komai ba.

Bayan shekara biyu.....

A cikin shekaru biyu da suka wuce abubuwa sun faru, ciki harda yaye yarana da nayi a shekara ɗaya da wata biyar na miƙawa Aunty su ni kuma Abba ya nema min makaranta naci gaba da karatu. Sosai yaran suka girma suka yi wayo a shekaru biyun da suka yi kai kace sun kai shekara uku ba biyu ba saboda wani irin girma da suke yi. Cikakkiyar kulawa suke samu wurin Aunty da Abba, wani irin gata akewa yaran wanda komai nasu na musamman ne kuma a killace yake, ga Babansu a ɓangare ɗaya da gajiya da saya musu abubuwan buƙata tun daga kan abincin da ake basu suturu da sauransu. Abbama bai taɓa gajiyawa da saya musu komai ba duk da cewar Babansu na kawo wa, a ɓangaren Aunty Zali manhajar abin yake musanman Macen da kullum cikin saya mata kayan kwalliya take yi, tako wani ɓangare bani da matsala sai dai ince Alhamdulillah, sai kuma rayuwar gidanmu da nake fatan Allah ya bani ikon sauyata.

Duk yanda naso yanke alaƙa tsakaninsu da mahaifinsu abin ya gagara domin kuwa wata irin matsananciyar soyayya yake musu da baya iya jimawa bai zo ya gamsu ba. Tun ina mita ina faɗa har na gaji na ƙyale su tunda Abba da kanshi yake kai masa su idan yazo, wasu lokutan m har da ƙananan yaransa yake zuwa.

******* Karatu nake yi ba wasa na tattara komai na aje a gefe domin so nake na sauya rayuwata da sauyi mai nisan tazara tsakanina da rayuwar da nayi a baya.

Alhamdulillah kuma sauyin na samuwa domin kuwa idan ka ganni a yanzu baka isa cewar waccen Salmar bace data gudanar da rayuwa cikin tsananin shirme da ƙuruciya ba. Wannan Salmar cikakkiyar mace ce mai aji da tarin natsuwa da ba ruwanta da shiga harkar da bata shafeta ba, ko a cikin makaranta na kame kaina bana shiga mutane, abinda ya kaini shi kawai nake yi.

Na hana samarin dake son mu'amala dani ko wace irin dama da zasu kusance ni da wani shirme wai soyayya, domin tuni nayi wuri na ajiye ta a can bayan da bana son wai-wayenta bare tunawa da ita. Toma wai da nayi soyayyar a baya me na cinta a cikinta bayan tarin ƙalubalen daya kusan gigita rayuwata.

A yanzu burina shine in kammala karatuna in tsaya da ƙafafuna domin in taimakawa Iyayena in cire su a ƙuncin rayuwar da suke fama......