MATAR MANYA

22

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 22

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Suhail......

Cike da farin ciki ya dawo masaukinsa ɗauke da satificate ɗinsa na shaidar kammala degree ɗinsa na biyu wato master's a babbar jami'ar dake babban birnin Andra Pradesh dake ƙasar Indiya. Gaba ɗaya Suhail ɗin ya canza ya ƙara zama cikakken mutum mai cikar halitta da kwarjini da kamala.

Ga tarin nastuwa da take bayyana kanta a gare shi, ya ƙara zama miskili fiye da yanda yake a baya, don yanzu magana ma wahala take masa. Sai ka share mintuna kana masa magana ya baka amsa a dunƙule cikin taƙaitattun kalmomi.

Haka abokanan karatunsa suke fama da shi, don da farko kafin su fahimce shi sun ɗauka tsabar girman kai da wulaƙanci ne sai a hankali suka fahimci halinsa ne a haka ba wai wulaƙanci ba, saboda yana da kyakykyawar mu'amala da waɗanda ke tare da shi. Tun dama can Suhail mutum ne mai farin jini sosai musanman a wurin ƴanmata, a nan ɗinma bata canza zani ba domin kuwa yanda ƴanmatan ke shishshige masa harda ƴanmatan Indiyawan suna son yin mu'amala da shi.

Sai dai rashin fuska da baya basu tun suna nacin wasu har su gaji su haƙura, a cikin tarin ƴanmatan dake nacin kulasa harda wata yarinyar mai suna Hanifah ƴar wani hamshaƙin ɗan kasuwa a garin Kano. Itace guda ɗaya data kasa rabuwa da shi take masa naci har yanzu, masifar nacin nata ne yasa ya ɗan fara amsa gaisuwarta da amsa mata hirar da take nacin masa sama-sama.

Ita hakanma yayi mata zataci gaba da dagewa har ta samu shawo kansa, a yanzu daya kammala karatunsa yana shirin wucewa gida yayin da ita kuma take a shekara ta biyu. Ba ƙaramar damuwa take ciki ba don haka take saka shi gaba ta rinƙa masa kukan cewa zatayi missing ɗinsa.

A yau ya gama kammala komai nasa gobe jirginsu zai tashi zuwa Nigeria, don haka yana cikin farin cikin komawa ga ahalinsa. Sai dai a ƙarƙashin farin cikin nasa tarin damuwa ce da tunda yazo bai rabu da ita ba, sai dai yayi matuƙar ƙoƙarin dannewa ta yanda ba kowa zai fahimci halin da yake ciki ba, musanman ma daya kasance ba mai sakin fuska ba.

Ya gama duk wani abin da zai yi don haka ya fita waje domin ya sha iska, wurin hutawar dake can bayan apartment ɗinsu yaje ya zauna ya ciro wayarsa ya shiga dubawa. Bai jima da zama a wurin ba wata kyakykyawar budurwa tayi masa sallama, a naste ya dago kai ya dubeta yana amsa sallamar da tayi masa a saman laɓɓansa.

"Zan iya zama?." Ta faɗa a shagwaɓe tana marai-raice fuska.

"Bismillah." Ya faÉ—a ya maida kansa ga abinda yake yi."

"Thank you." Ta faÉ—a tana zama kusa da shi.

"Noor yanzu shike nan tafiya zaka yi ka barni a nan ni kaɗai, gaskiya ni dai zan faɗawa Dady ya mayar dani gida in ƙarasa karatun a can. Don gaskiya hankalina ba zai kwanta ba kana can ina nan!". Ta ƙare maganar da iya gaskiyarta. Idanu ya zuba mata yana kallonta, yama rasa da wani yaren zai mata bayani ta fahimta ta fita a rayuwarsa don bata da gurbi a cikinta, amma sai dai yarinyar nacin masifa ne da ita ta kasa fahimtar ɗaga mata ƙafar da yake yi.

Cikin natsuwa ya fara mata magana cikin tausasawa saboda koba komai masoyi yafi maƙiyi.

"Kefa ba yarinya bace amma kina yin abu irin na yara, kar kiyi haka kin ji ko. Ki zauna ki kammala karatunki kamar gobe ne zaki kammala kema ki koma gida." Ya ƙare maganar fuskarsa da ƴar sakewa da alamun kulawa.

Sanyi sosai taji a ranta ganin yanda yayi mata magana da Æ´ar kulawar da bata taka kara ta karya ba. Amma hakan ba kaÉ—an ba ya tsaye mata a rai saboda bai saba ba, lokuta da yawa har tayi surutunta ta gama ko kalma É—aya baya furtawa.

"Shike nan tunda haka ka buƙata, amma don Allah ka rinƙa amsa kirana idan na kira ka, idan kuma ba haka ba zaka ganni ne kawai a duk inda kake." Kallonta kawai yayi baice komai ba saboda ba wata shaƙuwa a tsakaninsu ba itace mai nacin neman shaƙuwar.

Iya haka hirar ta tsaya har lokacin sallah yayi ya miƙe ya mata sallama ya wuce, itama tafiyar tayi tana jin tamkar ta bishi su tafi tare. "Akwai lokacin da zan kasance tare da kai har abada Moor." Ta faɗa lokacin daya ɓacewa ganinta.

★★★

Washe gari jirgin daya ɗauko su ya dira a Nigeria, a Lagos ya sauka don haka daga nan jirgin ƙasa suka biyo zuwa Kano.

Ahalinsa sunyi matuƙar farin cikin dawowar tasa inda labari ya baza ko ina cewar Suhail ya dawo daga Indiya, labarin har kunne Salma don ƙawarta Raliya dake unguwar su Suhail ɗin ita ta kirata ta faɗa mata.

"Masha Allah, Allah yasa an samo abinda akaje nema yayi albarka." Shine abinda na faɗa ba tare dana bata damar da zata gane halin da nake ciki ba kamar yanda na san gulma ce ta sakata kiran nawa ta faɗa min. Ranar haka na yini ba wani kuzari sosai har aka tashi daga makaranta na koma gida, har Aunty sai da ta tambaye ni abinda ke damuna mace mata kaina ke ɗan min ciwo. Allah ya sauwaƙe tayi min tace in sha magani.

A ɓangaren Suhail ma ko hutawa bai yi ba aka zayyane masa halin da Salma take ciki da wanda ta shiga a baya, bai ce komai ba saboda babu abinda bai sani ba a game da ita tun bayan tafiyarsa duk yanda yaso yakice al'amarinta kasawa yayi. Haka ya riƙa bibiyar halin da take ciki ta hanyar wani abokinsa dake sanar da shi komai.

Ya shiga matuƙar tashin hankali lokacin daya samu labarin wahalar da tasha a rainon cikin su Ameerah wanda har aka haƙura da ita amma Allah ya tsallakar da ita. A wancan lokacin damuwar da yake ciki har sai da ta shafi karatunsa, bashi da yanda zai taimake ta sai dai yana mata addu'a ba dare ba rana har Allah ya bata lafiya sannan shima ya samu natsuwar ci gaba da abinda ya kai shi har ya kammala ya dawo.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya gama wannan tunanin ya kalli Mahaifiyarsa da itace ke bashi labarin halin da Salmar ta shiga ci gaba tayi da cewa. "Ai dama na san Allah ba zai barta haka ba, sai ya rama maka abinda ta maka, donma naji ance wai Uban yaran ya dawo yana son ya amshe su, sai dai tace bashi basu har abada domin ta mallaka wa Iyayen riƙonta yaran. Amma duk da haka kar kaga yanda uban yake hidima dasu. Ni ji nayi ance ma har yanzu yana son yarinyar don dai saki ukkune a tsakaninsu babu yanda zai yi ne ya maida ta, yarinya sai kace mayya in ta kama zuciyar mutum bata saki ta sauƙi." Baba da bata rula da halin da ɗan nata yake ciki akan zancen da take ta zuba waba ta ƙare maganar tana zuba masa abinci.

Sai da ta kammala ta ɗago ta kalle shi ya lumshe ido ya faɗa tunani, taɓa shi tayi tana cewa "Kai miye haka? Ka tashi kaci abincin ka samu ka huta, ka san ya kamata gobe kaje ku gana da Aliya tunda bikin nan ya kusa."

A hankali ya buɗe idonsa daya kaɗa yayi ja tsabar damuwa ya miƙe yana cewa. "A kai min ɗaki, sai nayi wanka tukun na." Yana gama faɗa ya wuce saboda baya son taga halin da yake ciki. Baba kuwa baki buɗe ta bishi da kallon tana cewa "To fa, ba dai yaron nan har yanzu yana son waccen fitsararriyar yarinyar ba? Ai kuwa sai dai bayan raina zai kuma aurenta." Ta faɗa tana miƙewa.

"Ai kuwa zaki mutun idan Allah yayi da rabo a tsakaninsu." Mahaifin Suhail da shigowarsa kenan ya faÉ—a.

"Malam ke nan kai yanzu sai ka bari ya ƙara komawa wurin yarinyar daba ƙaunarsa take ba?."

"Kwarai kuwa idan Allah ya hukunta hakan me zai sa in yi jayayya." Ya bata amsa.

"Ai kuwa hakan ma ba zata faru ba, domin kuwa yaro ya samu matarsa ƴar mutunci zai aura me zai yi da wacce ta gama lalacewa a titi taje gidansa da cikin wani, sannan ta fito ta aure shi saboda dukiya, har yara biyu fa fa ta haifa Malam!". Ta ƙare maganar tana jin ciwon abinda ya faru.

"Ko wane bawa ai baya tsallake ƙaddararsa, ki dai bi a hankali don baki san abinda ke zuciyar yaron naki a game da ita ba, kuma shida aka yiwa laifin ma ya yafe sai kece zaki ɗorawa kanki kiyi ta dakon abu a zuciyarki yana damunki."

"Hm Malam kenan, a bar maganar kawai." Baba ta faÉ—a.

******* Basu daɗe da dawowa ba ya samu kira daga wani babban Company gine gine inda suka buƙaci ganin takardunsa, bai musa ba ya kai saboda aikin yake buƙata. Ai kuwa cikin sa'a suka ɗaukeshi aiki da babban matsayi aka bashi babban Office saboda manyan takardunsa da kuma ƙwarewarsa da basirarsa a fannin saboda abinda ya karanta kenan.

Cikin ƙanƙanin lokaci rayuwar Suhaila ta fara canzawa inda yake aikinsa cike da ƙwarewa da shaukin abin dan da nan Companyn ya fara samun manyan nasarori wanda hakan yake ƙara masa matsayi a wurin mai Companyn dattijon arziƙi. A yanzu haka shine Manager a Companyn.

Sosai rayuwarsa data Iyayensa ta sauya don kai bazaki taɓa cewa wancan Suhail ɗin bane na baya da bashi da komai sai rufin asirin Allah. A yanzu haka ya gama gina ƙaton gidansa wanda a ciki amaryarsa zata tare, sannan ya rushe gidan Iyayensa ya saye kangon dake kusa dasu ya haɗa ya kantama musu ƙaton gida ginin zamani da babu irinsa a unguwar.

Bai watsar da sana'arsa ta baya ba saima ƙara ingantata da yayi don yanzu haka yana da manyan shagunan waya guda biyu da babu abinda ba zaka samu ba na kayan waya.

Ana haka kuma gwanma ya bawa waɗanda ya fitar karatun muƙami a gwamnati don haka yanzu Suhail ɗin da ƙafafunsa yake tsaye.

Baba ta dage ta matsa sai da aka yi bikinsa da Aliya ƴar wajen ƙanwarta da suke Uwa ɗaya Uba ɗaya. Wanda Mahaifiyar Aliyar ce ta dage ta matsa sai da ta saka Baba tilasta masa ya amshi auren duk da baya so, saboda yanda Allah ya ɗaukaka Suhail ɗin basa so ya kuɓuce musu.

Haka dai aka yi auren daya amsa ne kawai bada son ransa ba, don dai kawai ba zai iya jayayya da Mahaifiyarsa ba. Amarya ta tare a ƙaton gidansa daya gina mai part biyu wanda ya bawa amarya ɗaya na ɓangaren hagu, ganin yanayin tsarin ginin da yayi na zaman mace biyu ne hakan ba ƙaramin ɗagawa Aliya da mahaifiyarta hankali yayi ba saboda da kar yace zai mata kishiya.

Kasa haƙuri suka yi sai da Mahaifiyar Aliya ta tambayi ƴar'uwarta tace mata ta kwantar da hankalinta ba abinda zai faru kawai haka yake ra'ayin ginin nasa. Itama Aliyar sai da ta tambaye shi, sai dai ita bata samu amsa ba saboda babu wannan shaƙuwar a tsakaninsu kawai dai yana ƙoƙarin ganin ya sauke haƙƙinta daya rataya a kansa.

Bayan wani lokaci......

Sosai na maida hankali na kammala karatuna cikin natsuwa na tattare duk wani abu da na san zai dame ni na aje a gefe, hatta maganar bikin Suhail da akayi ba abinda ban sani ba. Saboda da gayya ake zuwa a kawo min labari amma na shanye komai saboda na san na riga da nayi wasa da damar da Allah ya bani a baya, a kan me zan damu kaina da rayuwar da yake ciki a yanzu.

Babban burina a yanzu shine in kammala karatuna in tsaya da ƙafafuna domin in taimakawa Iyayena. Ta ɓangaren yarana bani da matsala saboda duk inda ake neman gata da kulawa sun same ta linki biyu ma, a ɓangare ɗaya Mahaifinsu da yake ƙoƙarin ganin ya gyara rayuwarsa inda ya auri wata babbar Mace mai hankali suke zamansu tana kula masa da yaransa saboda Mahaifiyarsu har yanzu tana kwance ba abinda take iya yiwa kanta sai an mata. A ɗayan ɓangaren kuma Iyayensu wato Aunty Zali da Abba da suke jin zasu iya musu kyautar rayuwarsu ma saboda soyayyar da suke musu.

Rayuwar farin ciki muke gudanarwa a gidan bazaka taɓa cewa nice na haife su ba saboda jikina bai nuna hakan ba, ba kuma ma kammani dasu a fuska saboda yan'uwansu suka biyo da suka ɗauki kamar Mahaifinsu baki ɗaya. Sai abinda ba za'a rasa ba nawa da suka ɗauka, kuma sannan da unty suke kirana Aunty Zali itace Mamynsu haka suka tashi suka gani.

Koda wasa zuciyata bata taɓa sakani naji nadamar kyautarsu da nayi ba wa mutane masu karamci a gareni ba, sai dai hakan bai hana ni jinsu a zuciyata ba, ina musu soyayya irin wacce ko wace uwa kewa ƴaƴanta.

Alhamdulillah na kammala karatuna na fita da sakamako mai kyau inda Abba ya shiga nema min aiki. Sosai rayuwata ta sauya da sauyi mai tazara tsakanina da rayuwar da nayi a baya, na gama cika cikakkiyar Mace mai aji da tarin natsuwa. Yayin da kyawuna da kyawun halittar jikina ke sawa mutane da yawa soyayyata mai girma.

Sai dai ba wanda na taɓa bawa damar shiga rayuwata kamar yanda suke buƙata.

Koda can Salma ƴar gayuce akwai son wanka bare yanzu dana san kaina na ƙara gogewa da wayewa ta fannin ado da kwalliya. Saboda haka idan nayi kwalliya na fita ba mai cewa na taɓa yin aure bare haihuwar yara biyu da ba inda basa zuwa yanzu domin har makaranta an saka su.

Ba wai ina nufin kwalliya ta zane fuska ba, a'a kwalliya ta iya saka suturar data dace da jikina nake nufi, sannan bana wasa da gyaran jikina akoda yaushe wanda Aunty Zali da yanzu muke kira Mamy saboda yara dake faÉ—a ta É—ora ni a kai.

Alhamdulillah Abba ya sama min gurbin aiki a wani Company har sun buƙaci na kai takarduna ranar Monday zasu tantance ni, don haka nake cike da farin ciki har Mama na kira nace tayi min addu'a zanje jarabawar ɗaukar aiki......