PAGE 3
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
Free-book
PAGE 3
"Amma Ammie wannan da kike ta kallo haka kin san shine?"
Girgiza kanta ta yi a hankali ta maido kallonta zuwa gareni ta ce.
"Ban san shi ba Beenafah, kawai dai ya bani tausayi ne."
Cike da mamaki na ce.
"To amma kuma miye na kuka?"
"Ke yarinya ce Beenafah. Duk wani mahaluƙin da yake cikin irin wannan halin ina matuƙar matuƙar tausaya masa da yi masa addu'ar samun waraka daga wurin Ubangiji mai Rahma. Nasan cewa mikinda yake zuciyata har na kwanta damata ba zai warke ba Beenafah..."
Yatsun hannuna na saƙala a cikin nata ina mai bata kalaman ƙwarara gwiwa na ce.
" Babu wani abin sarari dana ɓoye wanda ya gagari Ubangiji Ammie. In Sha Allah watarana wannan mikin zai warke ya zamto kamar ba'a yi ba."
Daga haka na dawo da ita inda nake zaune na koma jikin window ɗin na zauna, daman can ni ce yakamata ace na zauna wurin tun farko ban san miye abin da ya ɗauke min hankali ba har ta fara wuce ni ta zauna.
Tun da muka kamo hanya babu abin da nake tunani da mafarki a cikin Ƙwaƙwalwata sai hasaso warkewar Ammie, shi ka ɗai ne abin da ya tsaya a tunanina, domin magana ta gaskiya muna cikin wani halin ƙangin maraici da wahala wanda ko ba Uban a tare damu atleast mahaifiyarmu ta zamto inuwa kuma mafaka a garemu.
Ina nan a haka muna ta tafiya sai da muka iso Bunguɗu lokaci ɗaya na ji hankalina ya yi tashin gwauron Zabo tuna cewa ko ƙwarar hatsi na kaiwa a bakin salati bamu da shi a gidanmu.
Kuɗinda Dr. Basheer ya damƙawa Bahrain bayan ya biya mana kuɗin mota ya ce wai ya siya chocolate Idan mun koma gida na ciro daga cikin ledar maganinda take hannuna. Ko da na ƙirga su naira dubu talatin ne cif. Wata irin sassanyar Ajiyar zuciya na sauke tare da yin hamdala na sake ninke kuɗin na mayar bayan na cire dubu biyu na riƙe a hannuna wanda bayan mun sauka da su muka hau abun hawa zuwa gida.
Da mu da babu mu a gidan duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, shiyasa duk yunƙurinda Ammie ta yi na son shiga ɓangaren su Mummy Zaliha na hanata, domin babu wata gudummawar da suke bayarwa wurin kulawa da lafiyarta fa ce ma ƙarin damuwa da sa ciwon nata ya ƙara tsananta sakamakon baƙaƙen maganganu da habaice-habaicen da Mummy Zaliha ke jifar ta dasu a kai-kai ce.
Bayan mun yi salla na ɗauko mana sauran abincinda aka bamu daga gidan Dr. Basheer muka cinye sannan na kalli Ammie na ce mata zan fita kasuwa.
"Yanzu Beenafah duk shagunanda suke a kusa da mu basu isa ba har sai kin je kasuwa?"
Zaunawa na yi tare da nuna mata takardar hannuna na ce.
"Wannan shi ne sabon jadawalin tsarin abincin da zaki riƙa ci shiyasa nake so in je kasuwa domin a can ne zan samu duk abin da nake buƙata."
Lumshe idanunta kawai tayi ta ɗan kishingiɗa jikin katifarta wanda na tabbatar akwai maganganu da yawa a zuciyarta yawan magana ne bata so a yanzu.
"Aunty Beenafah ki sawomin kayan school kin ji dan Allah, kin san dai kin yi alƙawari ko?"
Jinjina kai na yi ina murmushi na ce.
"Na ji Bahrain, amma sai idan zaka tashi yanzu ka shirya kamar yanda na ce ka wuce islamiyya..."
"Kai Aunty Beenafah dan Allah ki bar shi gobe mana, wallahi duk na bi na gaji dan Allah."
"To ni kuma ba zan siyo ba.."
Miƙewa ya yi yana cuna baki ya ɗauko uniform ɗinsa ya saka ya ɗauki jakarsa ya rataya ya yi wa Ammie sallama ya fi ce.
A bakin gate ya haɗu da Biba wacce tana ganin shi ta tarbeshi da dariya ta ce.
"Bahrain! Bahrain ɗan Ammie. Yaushe kuka dawo? Ya jikin Ammien ka?"
Shi ma murmushin ya mayar mata ya ce.
"Sannu Aunty Biba. Ɗa zu ne muka dawo, kuma shine Yayata ta dage wai dole sai naje makaranta yau."
Murmushi ta yi tare da dafa kansa ta ce.
"Haba Bahrain! Auntynka so take ka yi karatu sosai ka sauke alƙur'ani ka zamto babban malami wanda duniyar musulunci zata yi alfahari da kai. Kuma kaga idan kana so ka cim ma buri irin wannan to dole sai ka jajirce sosai ka yi karatu..."
Jin kamar alamar buɗe ƙofa daga ɓangaren Mummy Zaliha ya sanyata yin gaba cikin sauri tana gudun kada wani ya ganta tana magana da Bahrain tunda Mummy Zaliha already ta yi mata zazzafan jan kunne cewa kada ta sake shiga ɓangaren Ammie ko magana wannan ta fatar baki kada ta sake yinta da su, domin idan tana shiga wurinsu yau da gobe sai an wayi gari Ammie ta ji mata mummunar rauni kuma wallahi babu ruwanta ko sisinta ba zata kashe wurin yi mata magani ba tunda ba ita ta aike ta ba.
To amma abin da yake ƙara daurewa Biba kai shi ne, har yau ta kasa gane miyasa hatta wannan magana ta fatar baki ta hanata yi da su sai ka ce ba mutane ba.
***
Bayan na dawo daga kasuwa tare da Ammie muka yi girki inda na ajiye mata kujera a farfajiyar harabarmu ɗan nesa kaɗan daga in da nake yin girki, magi ta ƙanƙare mini da dai sauran abin da bai taka kara ya karya ba, domin har yanzu dole in yi taka tsan-tsan da wuƙa da kuma wuta ko rijiya da sauran su. Muna nan ina yi mata fira har muka kambala wanda sai da mukayi sallar Isha sannan na sanyo mana abincin muka ci mu uku. Bayan mun kambala na ɗauko mata maganinta na bata na gyara mata shimfiɗa da wuri ta kwanta sannan na kalli Bahrain da ke bitar litattafansa na ce ya ci gaba zan je na dawo idan kuma ya kambala yana iya kwanciya.
Yau kam a bakin motar sa na taradda shi da alama yau bai dawo da wuri ba.
Hmm! ɗan Adam kenan mai abin mamaki! Wai yau Daddy ne muka dawo banza wofi a wurinsa. Daddy wanda yake rasa ina zai aza damu a faɗin duniyar nan wai shine shugaba wurin ci mana fuska da wulaƙanta mu. Yanzu gashi mun share tsawon sati shida bama nan amma ko dai ya nuna ya damu da al'amarinmu.....Kai ko waya ce ya ci ace ya kira tunda yana da numbern doctor Basheer amma bai yi hakan ba, tamkar ma ya ga wata sabuwar fuska haka ya tarbeni a yau.
Haƙiƙa ina da zafin rai, ina da matuƙar ɗaukar zafi da rashin jure wulaƙanci a ko ina na tsinci kaina, hatta Mummy Zaliha da ta ƙware wurin iya kai ni maƙura wacce tasan cewa bana iya mayar mata da magana idan ta yi min abu ji nake tamkar na haɗiye zuciyata na mutu. Na tsane ta, na tsani duk wani wanda ya fito daga gefenta, cewa da ta yi babu ruwanta da al'amarinmu ko kallo bamu isheta ba a yanzu, hakan ba ƙaramin gode mata na yi ba, domin tun da ta yi wannan furucin shikenan muka samu sauƙin ta wanda taurin rai da na nuna mata ne har yasa tayi mummunan fushi ta yanke wannan hukuncin. Daddy ma haka, a yanzu bana jin komai a zuciyata na kasancewar sa Uba a garemu fa ce zallar tsana da mummunar ƙiyayya ta har abada.
"Ni fa so nake in shiga ciki Beenafah, kuma kin zo kin tsaya ƙiƙam ke baki ce komai ba."
Cike da fargaba na rusuna na ce.
"Ka yi haƙuri. Daman zuwa na yi na faɗa maka cewar mun dawo.."
"To.. To..Masha Allah! Ya jikin ita Mulaifar?"
"Jiki Alhamdulillah! Ta samu sauƙi sosai. Daman cewa na yi zancen kuɗin maganin watan nan da muke ciki a yanzu, to daga can asibitinma an biyomu kuɗi wanda idan zamu koma zamu bayar..."
"Ke Beenafah bana son Ƙaryar banza da wofi! Uban waye zai bi ku bashi a asibitin tunda ba ku ne kuka kafa musu ita ba...wait! Kina nufin duk tsawon lokacin nan da kuka ɗauka a asibiti duk a bashi kuke zaune?"
Gyaɗa kaina na yi kamar da gaske na ce.
"Eh Daddy. Zaka ma iya bincika wa da kanka ka ji."
Wayarshi ya ciro daga cikin babbar rigar sa ya kira Dr. Basheer wanda a raina ba abin da nake sai addu'a da fatan Allah yasa Dr. Basheer ɗin ya ɗauki haske ya fahimci manufata. Ba komai yasa naƙi faɗa masa cewa mun samu tallafi ba sai domin idan ya bamu kuɗin mu riƙa siyen abinci da kuma korewa kanmu sauran buƙatun rayuwa na yau da kullum.
Ban fahimci komai ba domin wayar ba a handsfree take ba, sai da ya kambala sannan ya kalle ni ya ce.
"Na ji, amma ki sani Wata ya riga ya yi nisa bani da kuɗinda zan baku a yanzu sai dai kuma ki jira ƙarshen wata."
Daga haka ya rufe motar sa ya shige gida ya barni nan ina ta famar share hawaye. Tun a nan na fara lissafin yanda zamu rayu tsawon sati biyu ko fiye ma da hakan kafin wasu kuɗi su sake shigomu domin yau da gobe ta wuce wasa.
Na jima tsawon lokaci a inda nake tsugunne ina karanta wasiƙar Jaki wacce idan kwana zan yi nasan ba za ta tsinana mini komai ba fa ce ƙarin tarin damuwoyi da baƙin ciki.
Bayan tsawon lokaci na lallaɓa na koma sashenmu wanda na shafe tsawon lokaci ban samu bacci ya ɗaukeni ba sai cikin talatainin dare. A yanzu na ƙara tabbatarwa cewa ikon Allah ne kawai da ƙarfin addu'a yasa nake tsaye da lafiyata ba tare da wani ciwon ya kamani ba,domin matsalolin da na fuskanta ko nake fuskanta a yanzu sun fi ƙarfina.
****
Haka dai muka yi ta gurgura rayuwa. Katsar-watsar muka ga sati biyun nan sun zo sun wuce cike da fatan Daddy ya tura mana kuɗin domin ba ƙaramin jigata muka yi ba. A raina ina ta hamdala da tunanin cewa wahalar wannan watan ta riga ta ƙare sai dai kuma idan wata ta zo. Ashe ban san cewa akwai wata babbar jarabawa da ke tunkararmu ba wacce tafi ta baya muni da tsananin tashin hankali.......
✍️ OUM-AMEER ✍️