Matar khalees 16
by @nusybee143
*****MATAR KHALEES*****
✍️Nusy bee
Kwanan nan fa sai ana min uzuri 😅 saboda ciwo na da yake yawan tashi yana buƙatar hutu,still ayyuka sunyi yawa,gashi nan dai gashi nan dai,duk da haka ina godiya kuma at the same time Ina neman afuwa 🙏
Page 16
Sai dai bata samun damar,hakan, saboda Deeja bata taɓa barin Kofar dakin ta a buɗe matuƙar ba fitowa zatayi ba,kuma indai zata fita goya shi takeyi ko ta datse ɗakin
Kwanan ta tara da dawowa da yamma bayan tayi sallar la'asar tana zaune tana gyara kayan Affan a taji ƙaurin miyar da ta ɗora,da sauri ta miƙe ta fito ta gyara miyar sannan ta koma ɗakin ta
Tun kafin ta ƙarasa ɗakin taji Affan ya canyare da kuka,da gudu ta ƙarasa don ta san bacci ta fita ta bar shi yanayi
Abinda ta gani ne yayi matuƙar gigita ta, Nadiya ce take shafawa Affan niƙaƙƙen barkono a fuska,wani ihu Deejan ta saki sannan tayi kan Nadiya, Nadiya ta firgita da zuwan ta amma tayi saurin watso mata ragowar yajin, Deeja ta goce sannan ta hankaɗe Nadiyan ta ɗauke ɗan ta
Kai tsaye banɗaki ta nufa da yaron tayi masa wanka sosai,amma har lokacin bai daina kuka ba,ta fito duk jikin ta rawa yakeyi,a lokacin Nadiya bata ɗakin,ta cire zanin gadon ta sanya wani ta kwantar da yaron tana kallon yadda fuskar shi tayi ja yana ta tsanyara ihu,kamar wadda aka tsikara tayi maza ta ɗauke shi da nufin shayar dashi amma yaƙi kamawa,sai kawai ta fashe da kuka mai motsa rai, hankalin ta ya kai ƙololuwa wajen tashi,tana tunanin mafita amma ta rasa dabara
Wayar ta ta soma ruri,a firgice ta ɗauka ko ganin sunan batayi ba ta ɗaga
Muryar ƙawa ta safeena taji tana faɗin"Hello! Deeja bakya ji na ne?"
Sabon kuka Deeja ta saki, safeena tace"subhanallahi!ina hanya gani nan zuwa"
A harabar gidan ta samu Deeja tsaye tana jiran ta,ko daidaita parking batayi ba ta fito tana faɗin"lafiya dai?"
Deeja bata iya magana ba illa nuno mata Affan da zuwa yanzu ya fara rage kuka,da sauri safina ta amshe shi suka faɗa mota suka nufi asibitin doctor su'ad
Tayi masa abinda ya dace,ya samu bacci,sai a lokacin Deeja ta samu nutsuwa,tayi musu cikakken bayanin abinda ya faru
Salati suka sanya suna tafa hannaye, doctor su'ad tace"lallai matar nan bata da ko ɗigon iymani, jariri yaron da bazai iya aikatawa kanshi komai ba ballantana ya aikatawa wani me yayi zafi haka za'a yanke masa ɗanyen hukuncin da ko babba bazai jura ba?"
"Wanne laifi kuwa?bakin hali ne fa kawai,ke dai Deeja ki ƙara kula da yaron ki kawai"a cewar safeena cikin ɓacin rai
"Ina kula dashi sosai, duk da cewa Allah ne mai tsarewa,yanzun ma Allah ne kaɗai yasan abinda zai faru ya taƙaita mana wahala"a cewar Deeja
Doctor su'ad tace"hakane kam,yanzu dai gashi nan an magance matsalar,a shawarce Kar ki nuna mata damuwa,ki rabu da ita,ki bar ta da halin ta kawai"
Deeja ta girgiza kai tace"Ni dama ko kallo bata ishe ni ba,ko me zatayi bata gaba na,idan tayi min na rabu daita ai idan tayiwa wani bazai ƙyale ta ba ko?"
"Hakane kam, to Allah yasa mu dace"a cewar safeena
Doctor su'ad ta amsa da"ameen
Sun daɗe suna hira har maghriba,sukayi sallah sannan safeena ta mayar da Deeja gida
Har parlour suka shigo suna hira da dariya, Nadiya ta fito da sauri,ganin su Deeja a haka ya tabbatar mata da babu matsala,nan da nan ranta ya ƙara ɓaci,Deeja na kula da ita,amma sai ta nuna tamkar bata ganta ba
Deeja ta cigaba da gudanar da rayuwar ta yanda ya kamata,har zuwa sanda su Aunty Bintu zasu tafi ƙasar Syria,tafiyar ta kama ranar Lahadi,don haka ranar ta kama babu aiki,don haka Deeja taje yi musu sallama
A can ta yini,itace ta kai su airport,a gaban ta akayi komai ƙarfe biyar na yamma jirgin su ya tashi,itama ta juya zuwa gida
A falo ta samu Nadiya da umaima da ƙawar su siyama zaune suna hira,da farko ƙin shiga tayi ta tsaya daga bakin ƙofa don jin mei zasu ce
Umaima taji tana faɗin"ai tunda kin ce aikin baya cin ta na samu wani boka ya bani wani magani tace ayi haƙa a ƙofar ɗakin ta a binne,to tabbas zata gamu da hauka idan ta tsallaka,kinga tana can tana hauka,ga miji ya dawo naki ke kaɗai,yaron kuma zai dawo ƙarƙashin ki,kin ga sai kiyi abin da kika ga dama ko?"
"Kuma nima akwai wani hatsabibin boka da na samo,ya bani siddabaru yace na binne a maƙabarta,hakan zai sanya ya tsane ta har yaji baya ƙaunar ko ganin ta a kusa dashi,kinga dole ta bar gidan ko na uban ta ne"
Nadiya ta amsa"good job! Allah ya bar mu tare,da alama kuna damuwa da al'amura na,idan na gama da ita sai na koma kan waɗannan matsiyatan ƴan uwan nashi,nan gaba ko kallon shi zasu yi sai dai daga nesa
Umaima ta buɗe baki da niyyar yin magana Deeja ta faɗa falon fuskar ta babu alamun damuwa,duk da cewar ta tsorata da lamarin su,ganin ta sai suka sha jinin jikin su,ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya a raine,sannan ta ɗauke kanta ta shige ɗakin ta
Sun firgita sosai,don sun ga alamun hirar su,don haka suka chanja hira
Tun daga lokacin ta sake zage dantse ga kulawa da take bawa kanta da yaron ta,a haka har tsawon sati guda
A lokacin ne Khalees ya dawo,a lokacin Deeja bata nan tana wurin aiki,don haka Nadiya ta samu cikakkiyar damar ƙulle ƙullen ta na kissa da kisisina da sharri,shi kuwa Khalees ya bi ya haye kai
Da ta dawo tun a parking space taga motar shi,hakan ya tabbatar mata da dawowar shi,hakan bai dame ta ba,kanta tsaye ta shigo cikin gidan
Bata same su a parlour ba,hakan bai dame ta ba ta shige ɗakin ta
Bayan Isha'i tana jin su a parlour suna ta shewar su,ta so ta fito amma sai ta tuna da cewa zai iya yi mata wulaƙanci a gaban Nadiya,don haka tayi zaman ta a cikin ɗakin ta
Washegari sun haɗu dasu a kitchen,batare da damuwa ba ta gaishe su,amma ko kallon banza bata samu ba,bata damu ba ta cigaba da harkar gaban ta, Nadiya sai kwarkwasa da kisisina takeyi masa,shi kuwa sai faman tarairayar ta yakeyi,ko kallon su Deeja bata sake yi ba,tayi aikace-aikacen ta ta kammala ta fice daga kitchen ɗin
Tsawon kwanaki uku kenan,da dawowar Khalees,amma ko sannu bata haɗa su da Khalees ba,idan tayi masa magana ma baya amsawa, don haka ta haƙura da yi masa magana
Dawowar ta kenan daga Wajen aiki,tana shigowa parlourn taji an bangaje ta,da sauri ta ɗago don ganin waye, Nadiya ce
Ganin Nadiya ce ta san magana take nema,don haka ta mayar da kallon ta kan fuskar wayar ta
Dawowa tayi da baya ta kalli Deejan a ƙasƙance tana faɗin"oh sorry fa!na ɗauka akuya na bangaje shiyasa kika ga ban damu ba"
Wani banzan kallo Deeja ta watsa mata sannan tace"kar ki damu,nima dama sai naji kamar bangazar batayi min kama da da ta mutum ba,nayi tsammanin tinkiya ce ta bangaje ni shiyasa ban kula ba"
A zafafe Nadiya tazo wajen tana yi mata kallon wulaƙanci tace"ke!ki shiga taitayin ki ko kuma jikin ki yayi tsami"
Wani watsatstsen kallo Deeja ta watsa mata na sama da ƙasa sannan tayi wani murmushin rainin hankali tace"haba yarinya!ko wanda ya dire ki bai isa ba ballantana ke!!"
Cikin ɗaga murya ta shiga faɗin"wanda ya kawo ni fa kika ce, luvly kana jin abinda kike cewa"
Faɗar hakan ya tabbatar wa Deeja cewa Khalees ne ya shigo parlourn,sai ji tayi yace
"Ai tuntuni dama ta nuna tafi ƙarfi na,don haka dole ta bar min gida na"ya ƙaraso inda Deeja take ya zaro takarda a envelope ya miƙa mata yana duban ta a wulaƙance yace"kije na sake ki saki ɗaya,ki tattara ki bar min gida,dama ban ɗora miki idda ba"
Gaban ta ne yayi mummunan faɗuwa a ranta ta furta"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"tare da amsar takardar,bata kuma magana ba ta wuce ɗaki
Tana jiyo shewa da habaice-habaicen nadiya,tayi mata banza,ta kwashi abubuwan ta masu muhimmanci ta zuba su a mota ta fice daga gidan
Sai da tayi ƴar doguwar tafiya sannan tayi parking tana nazarin wajen zuwa,daga bisani ta yanke shawarar wucewa gidan ta da ta gina, saboda dama tuni ta zuba komai
Ƙerarren gida ne dake unguwar Na'ibawa,duk da ƙarami ne amma ya tsaru sosai,ta shigo da motar ta ta rufe gidan ta shiga ciki
Kwanan ta biyu babu wanda ta sanarwa mutuwar auren ta,sai dai akwai abinda ta shirya,don a ganin ta lokaci yayi da ya kamata ta samu farin cikin da ta rasa shekaru masu yawa,don haka ta ɗauki hutu a wajen aikin ta,ta soma shirye shiryen barin garin
Satin ta biyu ta gama shirya komai,motar haya ta hau airport,daga nan ta haye jirgin su zuwa in da take fata...
Ayi min afuwa Please
#Nusy_bee