Matar khalees 19
by @nusybee143
*****MATAR KHALEES*****
✍️Nusy bee
Page 19
A hankali ta girgiza masa kai,yace"amma kuma jikin ki da zazzaɓi"ita dai shiru tayi bata ce komai ba
Gefe ya ja ta ya zaunar da ita,sannan ya kalli uban tulin kayan wankin,ya maida kallon shi kanta gami da tambaya
"Waye ya baki wannan wankin?"
Cikin yanayi na ciwo ta amsa"gwaggo ce"
"Ita ta baki wannan uban wankin?"ya tambaya a fusace
A hankali ta ɗaga kai
Ya girgiza kai zuciyar shi cike da damuwa, lokaci guda kuma ya miƙe gami da kama hannun ta,suka shiga cikin gidan,ko ta kan kayan da ya shigo dasu bai bi ba
Kai tsaye ɗakin ta ya nufa daita ya kwantar da ita,yana fitowa suka yi kiciɓus da luba,ta firgita ƙwarai da gaske,don tasan waye Isma'il musamman akan ƴar gudaliyar nan zainaba,amma sai ta basar,cike da yaƙe da inda-inda take faɗin
"Ah!mutanen Amurika ne yau a gidan namu?Barka da sauka"
A daƙile batare da ya kalle ta ba yace"Barka"
Bai fi mintuna goma ba suka suka shigo da likita,ya dudduba zainab ya rubuta mata magunguna sannan yace a tabbatar taci abinci kafin ta sha,bayan likitan ya fita Isma'il ya tambaye ta ko ta ci abinci,ya sha mamakin jin cewa bata ci ba,cikin ɓacin rai ya fice daga gidan
Abinci ya samo mata mei rai da lafiya da kanshi ya bata sannan ya bata magani,da yaga ta ɗan dawo hayyacinta sai ya miƙe ya ɗebo kayan da ya shigo da su,ya juye mata tsarabar da yayi mata a gaban ta
Kayan sawa ne,sai takalma da kayan ciye-ciye iri-iri, sai ta hau murna da tsalle-tsalle,ta manta da ciwon da ke jikin ta,shima Isma'il sai ya damu kanshi da farin ciki,ya tattare mata kayan sannan ya fita zuwa ɗakin luba
Da sallama ya shiga ta amsa da rawar jiki,ya gaishe ta fuska babu yabo babu fallasa,ta amsa tana ta faman wage baki haɗe da faɗin"Masha Allah ismaila!Yaya karatun?"
"Karatu mun gama alhamdulillahi"
"To Masha Allah!yanzu sai aiki ko?"
Ya ɗan kalle ta a kaikaice ya ƙara ɗauke kanshi yana faɗin"shima an samu"
"To lamari yayi kyau,sai aure ko?"
Kamar yace shima an samu sai yaga kamar tambayoyin nata da rainin wayo a ciki,don haka sai yace"gwaggo bari na leƙa cikin gari"bai jira cewar ta ba ya fice daga ɗakin
Yana fita Luba ta leƙo ɗakin zainaba,a lokacin zainaban ɗin bacci takeyi,a fili ta furta"eh lallai,wato an samu sake har da bacci!to dole ki tashi ki ƙarasa aikin nan,ke zainaba! zainaba!!"ta shiga ƙwalla mata kira
A firgice zainab ta farka, Luba ta tsaya a kanta tana yi mata kallon banza,gaban ta ya faɗi,ta miƙe zaune tana kallon luban,cikin gadara Luba tace"wato don isa da ƙwarewa har da bacci don kinga wancan saƙagon ya dawo ko?to maza ki tashi ki ƙarasa yi min wanki na"
Shiru zainab tayi gami da zuba mata idanu, Luba ta daka mata tsawa har sai da ta firgita,ta miƙe jiki na rawa ta nufi tsakar gidan domin ƙarasa wankin
Tana cikin yin wankin malam Ishaq ya dawo tayi masa sannu da zuwa ya amsa cikin kulawa, cikin farin ciki take shaida masa dawowar Isma'il
Shima ya cika da farin ciki,ya tambaye ta
"Yana ciki?"ta bashi amsa
"A'a ya fita,amma inaga ya kusa dawowa,ka zauna ka jira shi"babu musu malam Ishaq ya shige cikin gidan,ita kuma ta cigaba da aikin ta
Tana cikin yin wankin Isma'il ya dawo,da sallama ya shigo,ta amsa cikin farin ciki,ganin ta tana wankin ya sanya ranshi yayi mummunan ɓaci,cikin fushi yace
"Zainab ba na hana ki wannan wankin ba?"
Tsoro ya kama zainab,ganin shi cikin fushi tace"gwaggo ce tace nayi wallahi"
"To ajiye,wuce mu je"babu musu ta ajiye ya kama hannun ta suka wuce cikin gidan
Jin Muryar malam Ishaq ya wuce ɗakin mahaifinsa,da sallama ya shiga,malam Ishaq na zaune yana cin abinci,yayi matuƙar farin cikin dawowar ɗan nashi,suka zauna suka kama hira,basu ɗau lokaci ba ya sako masa batun zainab
Cikin rashin walwala yace"gaskiya baba ya kamata a tausayawa zainab,don a ƙananun shekarun ta bai kamata ace ana bata ayyuka fiye da ƙima ba,gashi bata da lafiya"
Malam Ishaq ya numfasa yace"wallahi Ni kaina abin yana damu na Isma'il,don dai bani da yadda zanyi ne,amma na bar komai a hannun ka,ka ɗauki matakin da ya dace"
Isma'il ya gyara zama yace"na gode baba,yauwa,dama ina so na shaida maka wani Company ya bani ya bani aiki a can san Fransisco ɗin,kuma nan da next month zanje na fara yi musu aiki"
"Masha Allah alhamdulillahi! gaskiya nayi farin ciki, Allah ya taimaka"
"Ameen baba, godiya nake"
"To batun aure kuma fa?"ismaila?"a cewar malam Ishaq
Ismail ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin jin nauyi yayiwa malam Ishaq bayanin faɗima balarabiyar ƙasar Yemen
Har malam Ishaq ya fara murna sai ya ɗan yi shiru kafin yace"anya ismaila?baka ɗauko fin ƙarfin ka ba kuwa?"
Ɗan murmushi Isma'il yayi sannan yace"ai tuntuni mun fahimci juna har iyayen ta sun sanni,kuma sunyi na'am da ni"
Murmushin malam Ishaq ya faɗaɗa yace"to Allah ya sanya albarka, Allah ya kaɗe fitina". Isma'il ya amsa da"ameen baba"
Cikin sati biyu zainab tayi kyau ta murje ta maida jikin ta,bata kowane aiki sai wanda baza'a rasa ba,sai wanda Isma'il ya bar ta tayi,abin yana damun Luba sai dai babu yadda zatayi
Ana isaura kwana Shida ya koma san Fransisco ya shawarci malam Ishaq akan cewa yana so ya mayar da zainab gidan sakina,malam Ishaq ya nuna musu babu damuwa,don haka ya sanar da zainab cewa ta shirya kayan ta
Ba ƙaramin murna tayi ba, washegari ya ɗauke ta zuwa azare,sakina tayi matuƙar murnar ganin ƴar'uwar ta, Isma'il ya damƙa ta a hannun sakina tare da yi masa fatan alkhairi
Watannin shi uku da fara aiki a ƙasar America akayi auren shi da faɗima,bayan auren ne ya ɗauki zainab ya tafi da ita,a lokacin ma sakina tana laulayi,yayi matuƙar taya ta murnar samun ƙaruwa,domin zuwa yanzu babu wulaƙanci da gore-goren da bata sha daga wajen dangin miji duk sai akan haihuwa,to yanzu dai ta samu ciki bayan shekaru goma sha biyu da tayi da yin aure
Rayuwar zainab ta chanja a ƙasar US,yanda faɗima take son ta da nuna mata kulawa yana faranta mata,haka shima Isma'il,kuma ya sanya ta a makaranta mai matuƙar tsada, cikin lokaci ƙanƙani ta sauya baki ɗaya
Isma'il bai manta da mahaifin shi da kuma ƴar'uwar shi ba,don haka yana kula dasu sosai,da sakina ta haihu faɗima da zainab sun zo suna,sun taho mata da kaya tuli guda, yarinyar ta ci sunan surukar ta hajiya Fatima amma suke kiran yarinyar BINTU
Yau dai na karya record nayi post biyu a rana ɗaya 🤣🙃😅
#Nusy_bee