Matar khalees 30
by @nusybee143
*****MATAR KHALEES*****
✍️Nusy bee
Page 30
Cikin in Ina tace"eh.....um....uh ......wawwallhi.....da...da... qawa ta nake waya"duk ta firgice
Kwata-kwata bai yarda ba,amma da yake ba ta wannan yake ba ya kalle ta fuskar shi babu rahama yace
"Ina kuka kai Deeja ke da ƙawar ki?
Me kukayi mata?
Me yasa kuka raba ta da mijin ta?"
Miƙewa tsaye tayi,tana so tayi tsiwa amma babu fuska ba,a tsorace tace"ni ban san inda take ba,ni ban ma san auren ta ya mutu ba"
Imran yayi ƴar dariyar takaici yace "Are You for real?
Baki San auren ta ya mutu ba,ashe ban san wacece ke ba!"
Kuka ta fara tace"Ni wallahi ban san me yake faruwa ba,kawai dai......."
"Hold it please!"ya daka mata tsawa"wallahi sai na wulaƙanta ki if I find out da sa hannun ki a ɓatan Deeja, wallahi sai kinyi nadamar sani na"
Ranta ya fara ɓaci,a zafafe ta fara magana tana kuka"shikenan babu dama tayi tafiyar ta wani wajen sai a zarge ni?ita ƙaramar yarinya ce da......."bata ƙarasa ba taji shuuuuu a kunnen ta,sai daga baya ta fahimci marin ta Imran yayi,irin marin da rabon da ayi mata irin shi ta manta lokacin,zuruu tayi tana kallon shi kukan ma ya ɗauke batare da ta sani ba
"Don't let me repeat my self,ki nemo Deeja,ko zama na dake ya ƙare"yana kai wa nan ya juya ya fice daga ɗakin
Zamewa Umaima tayi ta zauna akan tiles tana jan numfashi,tashin hankali ba'a saka maka rana!take kanta ya fara juyawa saboda shiga tashin hankali,a wannan yanayin ta ɗauki mayafi da key ɗin motar ta tayiwa gidan Nadiya tsinke
Nadiya tana zaune a parlour tana cin cup cake tana danna waya umaima ta faɗo kamar daga sama
A firgice Nadiya ta kalle ta tace "lafiyar ki kuwa?"
Umaima ta zama yaraf akan kujera tana faɗin"ba lafiya ba Umaima, Umaima ina cikin wani hali,a kowanne lokaci aure na zai iya mutuwa,kinga kunci na Nadiya"ta juya mata side ɗin da Imran ya mare ta tace"Dr ne ya mare ni kinga"
"To fa!me kika masa haka?"Nadiya ta faɗa tana gutsirar cake ɗin hannun ta
Umaima ta share hawayen ta tana faɗin"wai cewa yayi in nemo Deeja?yanzu ina zan fara neman Deeja fisabilillahi?"
"Deeja kuma?wacece haka?"a cewar Nadiya tana kwanciya a kan three sitter da take zaune
Umaima ta kalle ta da mamaki tace"Deejan ce baki sani ba?matar mijin ki fa da suka rabu"
Nadiya ta yamutse fuska tana taɓe baki tace"ɓata tayi ashe?shine ake tuhumar ki?lallai ma an gaishe su"
Umaima ta marairaice tace"don Allah ki taimaka min mu nemo ta kar aure na ya mutu Please"
"Toooo!Ni kuma da nemo Deeja?au Allah?gaskiya ya kamata a daƙile siyar da wiwi a ƙasar nan"duk wadannan maganganun da takeyi ko kallon banza umaiman bata ishe ta ba
Umaima da ta fuskanci raina mata hankali Nadiya takeyi sai ta fusata tace"Nadiya naga kamar maganar nan ma Baki ɗauke ta a matsala ba ko?"
"Matsala? Allah ya kaɗa ta can ya bar ku da kayar ku hajiya"
Hawaye ya zubowa Umaima tace "kenan baki ɗauki matsala ta a taki ba?"
"Me ya shafe Ni da matsalar ki har da zan cusa kaina a cikin ta?"
Umaima ta miƙe a fusace tace"eh zaki faɗa hakan bayan nayi miki komai,to wallahi ko ki fito da Deeja ko na tona miki asiri idan yaso aurenki ya mutu kafin nawa,don nasan halin ki nasan abinda zaki aikatawa"
Wata dariyar rainin hankali Nadiya tayi sannan ta gintse kamar ba ita ba tace"yaro yaro ne!kar nake kallon ki Umaima,wai ma kin manta ni malamar ki ce kuma uwar ki a makirci da tuggu?to kar ki fara abinda bazaki iya ba,kar ma ki jefa kanki a uku"
Zama dirshan Umaima tayi ta fashe da kuka cikin karayar zuciya tace"don Allah Nadiya Kar kiyi min haka,ya zanyi,kin juya min baya,yaya Najeeb ya juya min baya,ga Dr ma,ku kaɗai ne hope ɗina,ya kuke so nayi ne?"
"Kije ki tambayi ragowar biyun don wataƙila su suna da Lokacin ki,amma ni kam bani da lokacin sauraren haukan ki"tana kai aya ta nufi uwar ɗakin ta,har ta kai ƙofa ta juyo tana kallon umaima da har yanzu take kukan tashin hankali tace "idan kin fita ki ja ƙofar parlourn"ta sa kai ta shige ɗakin ta
Cikin tashin hankali Umaima ta miƙe ta fice daga gidan,kai tsaye gidan fauwaz ta nufa, Afra na zaune tana yanke wa haneef farce sai ganin Umaima tayi a kanta,a ɗan tsorace tace"Malama Lafiya?"daga yanayin fuskar ta za'a iya gane haushin da taji na abinda umaiman tayi mata
Amma da yake umaima tana cikin tashin hankali bata kula ba,ta zauna gefen Afra tana faɗin"ina fa lafiya Afra, Imran zei iya rabuwa dani,ina cikin tashin hankali"
Afra ta ɗan buɗa ido da mamaki tace"ikon Allah!to me kikayi masa?"
Umaima ta warware mata labarin kaf tun daga lokacin da nadiya taga Khalees har auren su da sakin Deeja da abinda ya faru yau bata ɓoye mata komai ba
Shiru Afra tayi cike da ɗimbin mamaki,zuwa can tace"ya kuke da wannan nadiyar ne?"
"Nima ban sani ba,amma yaya na Najeeb yace cousin ɗin mu ce"wani kallo Afra tayiwa Umaima tace"shine dalilin da yasa kikayi mata hanyar da ta auri engineer ko dai da wata a ƙasa?"Umaima ta sunkuyar da kai ta kasa bata amsa
Afra tayi murmushin takaici tace"uhm!umaima kenan!Ni kishin miji na nakeyi da Deeja, saboda ina da yaƙinin babu wani mai hankalin da zai samu Deeja a matsayin mata yayi wasa da damar shi,tunda na samu labarin auren ta da mijin da yafi nawa komai na zubar da makaman yaƙi na,lubaisa ma haka,amma ke saboda ƙiyayya da hassada ce a ranki sai da kika shigar da wata ƙawar ki kika tarwatsa mata farin ciki da ta ɗauki lokaci mai tsawo tana nema
Mu kanmu son zuciya ne ya rufe mana idanu saboda Imran ɗin nan a wulaƙance ta samo shi ta mayar dashi mutum,amma yau an wayi gari akan wata can da bai san asalin ta ba yayi mata cin mutunci,to Ni dai babu abinda zan iya,kuma wannan haliman da kike magana duk wani rashin mutunci da wata fitsara da kike taƙama da ita ta zarce ki,don haka Ni kar kija min magana,miji na yana nan,tun wuri ki koma gidan ki,nima kar kija yaji aure na ya fara rawa"
"Allah sarki Deeja baiwar Allah!"Muryar fauwaz sukaji,a firgice suka waiga suka kalle shi,yana sanye da jallabiya milk colour yana tsaye fuskar nan babu Rahama
Sai da hantar cikin su ta kaɗa,afra ta firgita don tasan itama nata auren zai iya fara rawa
A nutse ya ƙaraso ya samu waje ya zauna sannan ya dube su yace"kun bani mamaki,wannan abu yayi min ciwo sosai, Afra,wallahi ba don kinyi nadamar abinda kukayi ba da yau babu abinda zai hana Ni sakin ki
Ku in banda rashin iymani bakwa ganin cewa Deeja marainiya ce?kuma ita mutum ce da ko magana bata dame ta ba ballantana shiga shirgin wani?to don Allah meyasa zaku matsawa rayuwar ta?
Shi kanshi Dr auren ki da yayi shine sakayyar abinda yayi wa Deeja,don ke dai wallahi ba matar zama bace
Duk halin da kuke ciki da najeeb ina sane"
A tsananin kiɗime umaima ta ɗago ta kalle shi idanun ta a waje, fauwaz yayi murmushi yace"well!you think kuna yin dabara kuna ɓatar da hankalin mutane ke da Najeeb babu wanda ya sani ko?to tun barowar ki garin ku taura,da Abinda yayi silar zuwan ki garin nan na sani,kuma saura ƙiris mijin ki ya sani"
Faɗuwa tayi a gaban shi tana faɗin"don girman Allah ka taimake ni ka rufa min asiri,na roƙe ka"
"Zan rufa miki asiri but in one condition"gyaɗa Kai takeyi tun ma kafin taji sharaɗin,bai damu ba ya cigaba"sai kin datse kowacce alaƙa dashi wanda ya mayar da rayuwar ku kamar waina a tanda daga ke har Imran,idan nace alaƙa ina nufin kowace iriyar alaƙa"da sauri tana share hawayen ta tace"Ni dama don babu yadda zanyi ne,amma na kai watanni biyar ma yanzu ko haɗawa bamuyi ba,nima dama bana son alaƙar"
"Wannan ya rage naki kuma,na biyu kuma wanda shine ma yafi Zama wajibi,ki nemo min ƴar'uwa ta"
Umaima kukan ta ya ƙaru,tashin hankali ya mamaye ta,ita ina zata ga Deeja? meyasa ake ɗora mata alhakin ɓatan ta,ko kallon ta fauwaz bai sakeyi ba ya kalli Afra yace
"Ke kuma,duk abinda kikeyi kinayi ne don kinga alamun ina son Deeja ko?to Kar kiji da wai,ina son ta fiye da yadda kike tunani ina son ki,kuma duk ranar da na ganta ki shirya zama daita a matsayin kishiya ko ki bar mata gidan"
"Wallahi abban haneef na amince,na yarda zan zauna daita a matsayin kishiya nayi alƙawari"Afra ta amsa har yanzu zuciyar ta bata daina bugawa ba
Ɗaga kafaɗa yayi gami da taɓe baki alamar bai damu ba,ya fice daga parlourn
Umaima babu shiri ta koma gida,zama tayi tana tunanin mafita,zuwa yanzu kukan ma ya ɗauke mata,sai kanta da yake sarawa, abubuwa sun taru sun cunkushe mata
Wayar ta ce ta ɗauki ruri,a ɗan firgice ta kalli wayar,ta janyo tana duba mai kiran
Ganin Najeeb sai da gaban ta ya faɗi,ta daure ta ɗaga ta kai kunne,kafin tace komai taji yana faɗin
"Malama kina raina min hankali!na buƙaci kuɗi daga gare ki naji shiru,na buƙace ki kina ta min yawo da hankali,to na baki nan da awa uku,ina son ganin ki"
Cikin kuka tace"haba yaya Najeeb!wai me yake damun ka ne?na gaya maka ina cikin damuwa amma maimakon ka tausaya min sai ƙara min wata damuwar kakeyi,ya kake so nayi ne wai?"ta ƙarashe cikin ɗaga murya
"Ke ballagaza!kama kanki!!kar ki sake ɗaga min murya,or else na ɗauki mummunan mataki akanki,ina ruwa na da wata damuwar ki ta banza? Abinda nace idan bazakiyi ba ki gaya min!"
Cikin kuka tace "bazan yi ba wallahi,na gaji da halin ka,haba!"
Wata dariyar rainin hankali yayi yace"I see,to ko me kika gani kar ki zarge ni,ki zargi kanki"yana kai wa nan ya kashe wayar shi
Takurewa tayi tana zubar da hawaye, rayuwar ta ce ta baya take rotating akan ta,wani irin kuka mai ciwo ya ƙwace mata,amma duk da haka gwara waccan rayuwar akan ƙazamar rayuwar da Najeeb ya jefa ta, mahaifin ta ya faɗo mata a rai, ta sake fashewa da kuka mai ciwo,zuwa yanzu kaso saba'in da biyar cikin ɗari na hope da take dashi a komai ya tafi
To pa 🥺 umaima ya dai??
#Nusy_bee