Matar khalees 31
by @nusybee143
*****MATAR KHALEES*****
✍️Nusy bee
Page 31
Zama tayi dirshan a ƙasa tana tunanin mafita,ji takeyi dama tun farko mutuwa,amma tabbas tayi wauta,tayi tsalle ɗaya mai jefa mutum rijiya yayi dubu bai fito ba,duniya ta ruɗe ta da yawa,ta sake fashewa da kuka tana faɗin
"Ni umaima na cuci kaina,naga ta kaina,nasan abinda nayi ne yake bibiya ta,kaicon rayuwa ta!"
"Ai baki fara kaico ba umaima!munafuka,matsiyaciya, tsinanniya,amma dai bakin uwa ne a kanki ko?dama ke mutuniyar banza ce? dama ke ɗin karuwar Najeeb ce?na godewa Allah da bai bani haihuwa da ke ba annamimiya!"Imran ne mai faɗar wadannan maganganu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, fuskar shi a matuƙar ɗaure da ɓacin rai da tashin hankali
Wayar shi ya jefa mata a fusace yana faɗin"Umaima!a yau na fahimci kuskure na na auren ki,nayi nadama mara amfani ta auren ki,ashe ragowar wani ƙato ce ko ma nace ƙatti?kuma da auren ki kike fornication?the worst part ma da aboki na?wato da ke dashi dukkan ku mutanen banza ne,Ni zaku cuta Ku ci amana,shine kuka shiga tsakani na da khadija ya cuso ki don ku cuce ni"yayi murmushi mai ciwo yana kallon umaima da ke daskare tana kallon wayar shi da hotunan ta da najeeb suna sheƙe ayar su yake,ya cigaba da cewa
"Nayi miki alƙawarin sai na ganar da ke kuskuren ki daga ke har babban matsiyacin,sannan magana ta ƙarshe,ki nemo min ƴar uwa ta,idan ba haka nima na ɓatar dake"yana kaiwa nan ya ɗauki wayar shi ya take ta ya fice daga ɗakin
Sai a yanzu ta ji wani kukan ya kubce mata,nadama mara amfani ta cika zuciyar ta,a fili ta furta "ya Allah ka taimake ni,Deeja ina kika shiga ne? Allah ka bayyana ta"
*** *** ***
Ita kuwa Nadiya ta kunna ta ƙure volume tana bin waƙar tana rausaya, Khalees ne ya shigo ɗakin kamar an jefo shi,a raine ta kalle shi tace
"Tun ɗazu ka fice,ina kaje?"
Wani watsatstsen kallo ya bi ta dashi,sai da taji hantar cikin ta ya kaɗa,bai ce mata uffan ba ya wuce closet ɗin shi ya fara loda kaya a cikin trolley,yana gamawa ya janyo ya fito,da mamaki ta dube shi tace"ina zaka?"
"Kar ki kuskura ki biyo NI,zakiyi danasani"abinda yace mata kenan ya fice
Mamaki ne ya ƙamar daita,lallai ba shakka aikin ta yayi sanyi,don ita dai a iya sanin ta ko kara ta ajiye Khalees baya iya tsallakewa ballantana har ta kai su ga haka,da sauri ta ɗauki figigin mayafi ta ɗora akan English wears ɗin ta tayi waje,tun kafin ta baro parking lot take zuba mahaukacin horn,bawan Allah jiki na rawa ya buɗe,kafin ta fita sai da ta tsaya ta auna masa zagi da cin mutumci sannan ta fice,tana fita yace"da izinin Ubangijn ka'aba yadda asalin matar gidan nan mutuniyar kirki ta bar gidan nan kema sai kin barshi ita ta dawo,ai Allah nace"ya koma kan benchin shi yana tuna nagarta da halin ƙwarai irin na Deeja
Ita kuwa Nadiya Kai tsaye gidan bokan ta ta nufa,bayan ya gama ƴan dube-duben shi ya kalle ta rai a ɓace yace"kinyi sake mahaifiyar shi ta ɓata mana aiki,yanzu ko da wasa bata sakewa da addu'a,har ƙannen shi ta shi ya sanya sunayi,sannan bata tsaya anan ba,akwai wani abokin aikin shi mijin naki, mahaifiyar shi ta haɗa kai da wannan mutumi tana bashi ruwan addu'a yana bawa mijin ki,aikin mu ya lalace sosai"
"Na shiga uku!"ta faɗi cikin ƙaraji tana dafe kai,"yanzu ya zanyi?"
"Mafita ɗaya ce,ga wannan maganin"ya miƙa mata wani ƙulli yace"ki zuba masa a abinci,ki tabbatar yaci,yana ci shikenan zaki samu kanshi kamar baya ko ma fiye,amma idan bai ci ba za'a iya samun matsala"da rawar jiki ta amshi maganin tana faɗin"zai ci ma,zan tabbatar da yaci"ta ajiye masa kuɗin shi ta fice daga ɗakin nashi
Tana komawa gida babu ɓata lokaci ta ɗora girki,white rice ta dafa da miya taji kifi,ta san shine favourite ɗin Khalees,ta tsala wanka ta sanya sexy English wears ta zubo da kitson attachment da tayi bayan ta,tayi wa fuskar ta light make up ta zauna tana danna waya tana taunar chewing gum,a lokacin ana ta sallar Isha'i amma ba ta ita take ba
Tun lokacin take jiran dawowar shi shiru,har tara shiru,goma shiru,sai hankalin ta ya fara tashi,ta ɗauki waya ta fara kiran shi,amma switch off,hankalin ta ya fara tashi,don sai lokacin ta tuna cewa ya ɗauki jakar kaya,ai bata san lokacin da ta ɗora hannu aka ba ta kama gunjin kuka,faɗi take "na shiga uku na lalace,asiri na ya tonu"
Kafin washegari da safe wasu ƙuraje masu ruwa da mugun wari suka feso mata a dukkan ilahirin jikin ta,ga ƙaiƙayi da raɗaɗi da suke mata,da ta kalli kanta a madubi ita kanta sai da taji ƙyanƙyami, bata taɓa shiga matsanancin tashin hankali da masifa irin wannan ba,ta koma bata da aiki sai kuka da tunanin mafita
***** ***** *****
Ta nutsu sosai a gidan Auntyn ta Nusaiba tana jin daɗin rayuwar ta,yau kwanan ta shida kenan a US, Rayuwar su sukeyi ciki ita da Aunty nusaiba da yaran ta Amra da Ajmal,sai auta Adnan,gaba ɗaya ta manta da wani abu wai shi ɓacin rai ko damuwa
Affan kuwa koyaushe yana hannun ƙanin mijin ta Safwan da Allah ya ɗora masa ƙaunar yaron,shi kanshi Affan yanayin san Francisco ya karɓe shi yayi fresh abin shi
Suna zaune a parlour suna kallon wani American film,yaran duk basa nan sun tafi makaranta,hatta Safwan ya fita aiki, Deeja ta ɗago ga kalli auntyn tata tace cikin shagwaɓa"Aunty"
Cikin kulawa Aunty nusaiba tace"ya dai auta?"
Deeja ta zauna daga kishingiɗar da tayi tana kallon ta tace"Aunty na ganki Amma banga Yaya Yusuf ba"
Murmushi aunty Nusaiba tayi tace"inna bata gaya miki baya US ba?"
"Ta gaya min,amma kuma ai bazaki rasa sanin inda yake ba ko?"
"Eh!yana tokyo,a can yayi karatu kuma ya fara aiki,yau kwanan mu sha shida da dawowa matar shi ta haihu,yaushe kike zuwa?"
Da mugun zumuɗi Deeja tace"ko yau a shirye nake wallahi"
"Lallai kam,to be ready next week in Sha Allah zamu tafi,amma muna dawowa zan nema miki admission ki yi masters ɗin ki idan kin yarda"
"Yeah Aunty!na yarda, wallahi dama na so ɗorawa kawai ban samu dama bane"
"Okay,in Sha Allah idan muka dawo sai ki ɗora karatun"
Murna Deeja ta rinƙa yi har da tsalle,Aunty nusaiba sai kallon ta takeyi tana murmushi
Satin ta biyu a ƙasar suka cale zuwa ƙasar Japan,tun a airport taga yayanta Yusuf,sai da gaban ta ya faɗi da ta ganshi,don babu in da ya baro mahaifin su sai hasken fata,da gudu taje ta rungume shi tana hawaye,ya rungume ta yana shafa kanta,kafin ya ɗago ta yana kallon ta da murmushi,yace"Are little sister?
Kin girma fa! lokacin da muka bar ki You was just a little girl"
Murmushi Deeja tayi tana nuna masa Affan da ke hannun Aunty nusaiba tace"yanzu nima gashi na dire little baby"dariya sukayi daga shi har matar shi hanan da ke rungume da ƴar babyn su safna
Farin ciki iya farin ciki kam Deeja ta shige shi,taga soyayya ta ga kulawa daga kowanne angle, Yusuf ma daina fita aiki yayi,kullum yana tare da ƴan uwan nashi ana ta shan raha da hira,ga matar shi mai kirki da barkwanci
Satin su ɗaya a Japan suka tattara suka koma US,Deeja taji tamkar su kar su rabu,amma hakan bai hana ta farin ciki ba
Satin su uku da komawa Deeja ta fara ɗaukar lecture a Cambridge University cikin farin ciki da nasara,karatun nata yana gara mata yadda take so,don taji sauƙi ma Aunty nusaiba ta samar mata Nanny da zata rinƙa kular mata da Affan,ƴar ƙasar Uganda, dattijuwa mai tsafta
***** ***** *****
Babu irin cigiya da neman da Khalees da Imran basu yiwa Deeja ba,gidajen rediyo da na tv babu in da basu kai cigiya ba, Khalees har wani ɗan ƙaramin hauka yayi,ya zabge ya rame ya fita hayyacin shi,ko abinci baya iya ci sai Imran ya lallaɓa shi yake shan yoghurt ko tea,yanzu haka ma ya janye shi zuwa Lagos don abin nashi ya fara yawa
Suna zaune a ɗakin hotel ɗin da suka sauka,waya ce a hannun Khalees ɗin ya ƙurawa hoton su shi da Deeja idanu,sunyi kyau a hoton dukkan su sunyi murmushi,sunyi hoton ne a wani lokaci da suka shirya zasu je gaida Hajiya yace mata"ƴan matan Abdul kinyi kyau fa"
Tayi murmushi tana masa hararar wasa tace"don kar nace ka chanja kar ƴan mata suyi min shigar sauri shine kayi riga malam masallaci?ko baka san ka fi Ni kyau ba?"shine yayi dariya ya janyo ta yayi musu hoton suna dariya,suka hau musu akan wanda yafi kyau,ƙarshe sai da suka ɓata lokaci suka fita, dukkan hotunan Deeja da ke wayar Nadiya ta goge su,wannan ne kaɗai saboda son hoton da yakeyi ya ɓoye shi Nadiya bata ganshi ba
Imran da ya shigo yanzu ya tsaya yana kallon yadda hawaye ke zubo masa yana kallon wayar shi,yasan abinda yake kallo don wannan hoton shine abokin hirar shi,abincin shi, walwalar da duk wani farin cikin da ya rage masa, tabbas ya jinjina irin son da Khalees yakeyiwa Deeja,ya ƙarasa inda yake yayi tapping kafaɗar shi,ya ɗago a sanyaye yana kallon shi,ya samu waje a gefen shi ya zauna
Cikin kwantar da murya yace"Ni kam Khalees why not mu koma gida mu tuhumi matan mu kan batun Deeja,nasan Umaima bazata iya ɓatar da Deeja ba,amma nasan idan Nadiya ta aikata wata ɓarnar musamman wadda ta shafi umaiman zata gaya mata,so definitely indai sune suka ɓatar da ita idan muka tuhume su zamu samu hint"
"Kana ganin hakan mafita ce?"a cewar Khalees yana kallon shi
"In Sha Allah,mu jarraba hakan"
#Nusy_bee