Matar Khalees

Matar khalees 38

by @nusybee143

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Post 38

Deeja tayi murmushi tace"zanyi maka ƙoƙari in Sha Allah,duk da stubbornness ɗin ta tana jin magana ta, a matsayi na na babbar yaya

Wani kallo sukayi mata duka su biyun, sannan suka fashe da dariya a tare,buɗa ido tayi sosai tana musu kallon ƙarin bayani, Khalees yana dariya yace"karo na farko a tsawon rayuwa ta da naga babbar yaya da auta sun haɗu waje ɗaya"kawar da kai tayi tana ɗan murmushi,ita fa a tsawon rayuwar ta dama ba wai tana ƙaunar sunan bane,amma bata taɓa jin sunan ya yarfa ta irin yau ba,amma saboda ƙi faɗi sai ta kalli Khalees tace"ai suna ne kawai,a family Mutum nawa na girma?ko baku san ina da ƙani ya rasu ba?idan Dr baka sani ba ai shi abban Affan ya sani"Khalees yana dariya yace"anyi haka,kin girmi mutane na manta,kamar yasmin,kin girmi fadila,kin girmi Mima,kin girmi Mubarak,kin......"

"Aa Ni fa ban ce na girme su ba,kunga a bar maganar kawai"ta faɗa tana shan mur

Imran yace"Hajiya Deeja kenan,ko bayan shekaru ɗari kaga mutum ka tambaye shi komai amma banda halin shi,ke kam Allah yayi miki arzikin son girma sai gashi kin zo a kalen hanji"

"Naji nace a bar maganar"ta faɗa tana zaro idanu"zanyi magana da umaima,zata dawo in Sha Allah"

"Kiyi mata barazanar yace idan bata amince ba zai amshi ƴar shi"a cewar Khalees yana murmushi,

Deeja tace"wa?umaiman?ita da tace na ɗauki yarinyar ta bar mini?amma idan baban ta yana so sai na bashi,tun ma lokacin ko zama batayi,"Imran yayi dariya yace"shiririta!baka san Umaima bane idan ta kafe akan abu,nayi mamakin yadda ta yarda ta biyo Deeja, gaskiya kinyi Sa'a,ko kuma yet she is feeling guilty na abubuwan da tayi miki ne"Deeja tace"whatever,sannan akwai abu ɗaya da nake roƙon ka Please"

Yace"ina jin ki"Deeja tace"ka koma Bauchi ka daidaita da mahaifin ka, it's already time,ko ba komai ka san abinda ya faru ba laifin shi bane,no matter what bazai taɓa juya maka baya ba,kuma for now ka bashi enough space, kusan six years,why not baza kayi letting komai ya wuce ba? I know yadda bai san Aunty Ramlah ba dole zaiyi kewar ka as the only son da ya mallaka"ta ƙarashe tana tsare shi da idanu

Da Imran da Khalees duk kallon ta sukeyi har ta ƙarasa bayani,a hankali Khalees ya mayar da kallon shi ga Imran da ya sunkuyar da kanshi yana tuna baya, Khalees ya dafa kafadar shi yace"all is well friend, Deeja tana da gaskiya, ba'a fushi da iyaye no matter what happen,I know you well friend,nasan ba fushi kayi ba but it's already time ka nemi sasanci da dady,You will never regret it in Sha Allah"Imran ya jinjina kanshi,a sanyaye yayiwa Deeja godiya sosai,yayi mata sallama suka fice shi da Khalees,ya ɗauki Affan da yake ta ƴan wasannin shi suka fita tare

Sati biyu tsakani Deeja, Afra,lubaisa da zakiyya suka ziyarci Umaima a motar Deeja,tana parlour ta goya little Deeja da ke jin rigima sai zaga parlourn takeyi,ta kunna suratul Nur a waya sai bi takeyi,ita kuma mama lami tana kitchen tana dafa musu abincin dare,sai jin sallamar su tayi

Da sauri ta leƙo,tana ganin Deeja ta tafi da gudu ta rungume ta tana dariya,duk da cewa kiyya ta san labarin komai amma tayi mamakin chanjin da ta gani a wajen umaiman,gashi yanzu asalin farin ta ya dawo,tayi fes da ita, dama umaima akwai gayu da iya kwalliya, yanzun ma tana sanye da English wears riga da wando pink colour,ta ɗauke gashin ta da baƙin ribbom. Afra tana kallon ta tace"lallai umaima!wato mu duk baki ganmu ba ko?"da sauri ta saki Deeja ta rungume su ɗaya bayan ɗaya tana murmushi,ta ja su suka shiga parlourn, kiyya ta amshi little Deeja tana kallon ta

Nan da nan ta kawo musu drinks da snacks tana faɗin"yau anyi surprising ɗina"lubaisa tace"sistern ki ce ta tattago mu"Umaima tayi murmushi ta kalli Deeja da take danna waya tana murmushi itama, kiyya tace"Ni kam ban ma san sanda aka tambayi abban su ba,sai ce min yayi wai khadija tace zamu fita"Afra tana dariya tace"ballantana kuma abban haneef,jira yakeyi auta tace ayi yace an gama"da tsokana ta faɗa tasan Deeja bata ƙaunar,ai kuwa ta ɗago ta zabga mata harara,duk suka kama dariya

Sun ɗan taɓa hira da raha, Deeja ta tambaye ta game da karatu,cikin zumuɗi take sanar mata da cigaban da ta samu,yanzu haka tayi wajen izu ashirin da biyar,ga litattafai na addini,game da institution kuwata fara lecture a MAAUN in da take karantar business administration,su kansu su Afra ba ƙaramin burge su Deeja tayi ba,a hankali Deeja ta shigo da maganar Imran

Ɗif umaima tayi bata sake magana ba,suka haɗu suna ta roƙon ta ta koma, Afra tana murmushi tace"nayi missing ɗinki sosai sister,gidanmu ma yayi missing ɗinki,kuma Dr ma yayi missing ɗinki sosai"Deeja tace"kuma ko ba don shi ba ki taimaka ki koma don takwara ta,she will be very happy ace ta tashi gaban iyayen ta duka biyun,sai ta fi jin dadin tarairayar da zaku mata"kiyya tace"seriously Umaima ko da nasan da Bama shiri ranar da Imran ya sake ki da abban su Aisar ya sanar min komai game da ke banyi bacci ba,I wish kin koma ɗakin ki,mu haɗa kanmu gaba ɗaya"ta ƙarashe tana murmushi, lubaisa ma tace"indai kika ƙi komawa Dr Imran to daga yau na daina yarda da love,indai naku ya mutu to I'm very sure namu Ni da ya abdallah yana mutuary"sukayi ƴar dariya,cikin sanyin murya Umaima tace"zan koma,ko don yarinya ta,i still remember Imran yayi min komai"shewa suka saka dukan su kamar ƙananan yara suna tafi

Baayi cikakken wata guda ba aka mayar da auren Umaima da Imran,har taura Imran yaje ya nemi auren ta,bayan sati uku kuma ya mayar da ita can ya sasanta tsakanin ta dasu,daga can suka wuce Bauchi

A Bauchi ya gamu da abin mamaki,don mahaifin shi kuka ya rinƙa yi yana neman yafiyar shi da mahaifiyar shi,ya sanar masa Zulfa'u ta haukace tun sanda aka samu ƙaramar ƴar ta da salma da ciki,ita kuma Ameera da cutar AIDS,shi kuma ya tattara yaran ya mayar da su wajen mahaifinsu ita kuma ya sake ta

Imran ya sha mamaki sosai,ya jinjina ikon Allah,ya gabatar da Umaima a matsayin ta na matar shi, Alhaji alƙasim ya sa musu albarka sosai 

Imran ya bawa mahaifin shi labarin ƙanwar shi Ramla da mahaifiyar shi ta haifa,tayi aure itama a Abuja,har da yaran ta uku,dady yace"Allah sarki Aysha,don Allah ka nemar min yafiyar ta"

Kwanan su shida a Bauchi yau,sosai Umaima take girmama dady, kullum cikin yi masa hidima take,don sai taga kamar nata mahaifin

Deeja ce ta kira ta tace ta tambayi Imran zata je bikin ƙanwar Mima idan ya amince su tafi tare,tunda Deeja ta ambaci Mima gaban ta ya faɗi,don Allah shaida tana mugun tsoron Mima,gashi yanzu zata je gidan su,kuma bazata iya yiwa Deeja musu ba

Wajen ƙarfe biyar suka sauka gidan su Mima a azare,Mima bata wulaƙanta umaima ba,amma ko kaɗan bata sake mata ba,suna zaune a ɗakin miman suna hira, Mima na bawa Deeja labarin zuwan inna haleema takwarar ta gobe, wadda ta kasance ƙanwar mahaifin su ce

Mima tace"Allah ya kaimu goben,kice gobe da shafta,mama bilki fa?"

"Mama bilki maybe itama tazo goben, maybe kuma sai jibi"

"Allah ya kaimu"a cewar Deeja,suka cigaba da hirar su

Ita dai Umaima tana takure a gefen gado tana kallon yadda suke yin hira,sai su koma musu,sai su fara zagin juna sai su cigaba da shewa,a hankali ta goge hawayen ta tana jin kewar ƴan uwa,don ba wai sun saba da dangin ta bane har yanzu

Gashi tsoron maman su Mima ya kama ta ganin irin kallon da take bin ta dashi, shiyasa ma tunda ta rakuɓe a ɗaki bata fita ko'ina ba

Mima ta shiga ɗakin mahaifiyar su da sallama,mama sakina ta amsa, Mima ta samu waje ta zauna tace"gani mama"

Mama sakina tace"Mima wacece wannan wadda Deeja tazo tare da ita"

Mima ta taɓe baki tace"oho,kwashe kwashen auta ne,amma wai naji ance surukar ƙanwar Mamie babba ce"

"A ina take?"a cewar mama tana kallon ta

"Nace miki ban sani ba fa,ki tambayi Deeja"mama bata sake magana ba, Mima ta fice ya koma ɗakin ta

Bata samu Deeja a ɗakin ba sai Umaima da babyn ta take ta kuka,dama bata saka ran samun Deejan ba saboda zataje gidan Aunty Aziza,wadda itace immidiates ɗin Aunty Bintu,ko kallon Umaima da ke fama da little Deeja batayi ba,ta faɗa toilet don yin wanka

Umaima ta san matsalar little Deeja,bata bacci sai anyi mata wanka,gashi ita dai bazata iya tambayar ruwan wanka ba,dama dai Deeja tana nan ne,kuma mugun tsoron Mima takeji,haka ta miƙe tana ta jijjiga little Deeja da take sake mimmiƙewa tana tsala ihu

Sai da Mima ta gama shirya wa,ganin abin na little ba na ƙare bane ta kalli Umaima fuska babu yabo babu fallasa tace"ko bata da lafiya ne?"umaima ta girgiza kai,Mima tace"to lafiya take irin wannan kukan?"

"Ina ga ko wanka take buƙata"Umaima ta bata amsa

"Ko an saba mata wankan kafin tayi bacci?"Umaima ta gyaɗa kai

"Ikon Allah!shine bazakice a baki ruwa kiyi mata wanka ba?"bata jira cewar umaima ba ta fice daga ɗakin,bayan ƴan mintuna da dawo da baho da ruwan zafi,da kanta ta daidaita ruwan ,ta amshi little tayi mata wanka ta shirya ta,tun kafin ta gama little tayi bacci,ta kwantar da ita a hankali,tayi mata addu'a ta tofa mata,batare da ta kalli Umaima ba ta fice daga ɗakin, umaima sai bin ta takeyi da kallo,tana fita tayi murmushi ta koma kusa da ƴar ta ta kwanta itama

Sai wajen ƙarfe tara Deeja ta dawo,a parlour ta samu Mima tana yiwa Mee'ad kitso, ta sauke Affan da yake bacci ta kwantar da shi a kan kujera tana faɗin"wash Allah na"

"Gantali daɗi,sai yanzu?"a cewar Mima, Deeja ta harare ta tace "sai dai uwar gantali daɗi"Mima tace"seriously Baki da kirki Deejo,kin bar matar mutane kin tsallake kinyi tafiyar ki"

"Ayya!wallahi nayi mata tayin zuwa, tace a'a naje na dawo"Mima ta taɓe baki tace"ƴar ta sai kuka takeyi,wai ashe wanka take buƙata,tsabar sokwanci ta kasa tambayar ruwan wanka"Deeja ta kwashe da dariya tace"tsoron ki take ji ne, kullum kina haɗe mata rai kina mata tsawa,gashi don wulaƙanci kika je har gidan mijin ta a gaban mijin ta kika faffalla mata mari, leemo Allah ya shirya min ke"Mima tayi ɗan murmushi tana taɓe baki tace"ai kuwa ta haɗu da wahala"Deeja tayi dariya ta miƙe ta shige ɗakin da Umaima take

Washe gari ƴan biki suka fara halarta, kasancewar yau za'ayi event na Farko, Umaima dai ba don Deeja ba da tuni ta koma gida saboda har yanzu tana da tsoron shiga mutane,tana lafe a ɗakin Mima,daga ita sai wayar ta,don little ma Deeja ta amshe ta suna tsakar gida ana raha,bayan la'asar inna haleema da mama bilki suka iso kusan a tare,Mima sai raha da wasa da dariya sukeyi,bayan sun gaisa da mama sakina suka wuce ɗakin Mima inda Umaima ke zaune tana chatting da mijin ta

Sai da suka zauna sannan umaima ta gaishe su cikin girmamawa,bin ta sukayi da kallo suna amsawa,ɗauke kanta tayi ya cigaba da danna wayar ta,mama bilki ta kalli Mima tace"Mima ina kuka samo ƴar INNALE?"

Mima ta ɗago kanta cikin mamaki tace"wacce innale kike magana akai mama?kuma wacece ƴar tata?"daidai nan Deeja ta shigo da sallama

Inna halima tace"nima Ina ganin ta innale kawai na gani a tare da ita"

Mima ta kalli Umaima da tun ambaton innale na farko ɗago kanta a firgice tana kallon su inna haleema,mama bilki ta ciro wayar ta ta fito da hoton innale, wadda asalin sunan ta maimunatu ta miƙawa Mima

To pa 🥺me yake shirin faruwa ne?

#Nusy_bee