RASHIN SANI

PAGE 07

by @sumy6163

馃挮馃挮RASHIN SANI 馃挮馃挮

STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.

Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.

PAGE 07

Yau kusan kwana uku kenan babu mai amsa gaisuwar Aimana a gidan, hatta kuwa Dada ta dauke mata wuta, daga gaisuwa shikenan, duk wani hira da zolaya da Dada ke mata ta daina.

Ita kuwa Dada ta daukewa Aimana wuta ne sabida tana jin tsoron kar ya kasance yawan goya mata baya da kin yadda da ainbinta da take yawan yi shiyasa Aimana zama haka, don ko yanzu ma bata tsira ba,mutane na fadin kakarta ce ta daure mata kugu shiyasa take duk abinda taga dama.

Abun duniya ya taru yayiwa Aimana yawa, wannan shariya da ake mata shi yafi komai daga mata hankali.

"Ta samu su Baba ta tambaye su ko wani abun tayi, sukace ba komai, kuma ta basu hakuri amma har yanzu ba abinda ya canza.

Karamar magana ta zama babba, yau sati biyu kenan ba mai kula Aimana a gidansu,tun tana tsammanin abun na wasa ne, sai taga ba haka bane, kaf gidan Abdul ne kawai me kulata, Shi yake rarrashinta yana kwantar mata da hankali, damuwar ta ma bata san me tayi ba, bata san meke faruwa ba, gashi Dada ma taki gaya mata komai.

A bangaren Daddy kuwa yana can yana ta processing yanda Aimana zata samu admission, dayake mid term ne, yanzu,sun rufe daukan dalibai.

Duk wannan wainar da ake toyawa Aimana bata da labarin, tunda yanzu mutanen gidan ba kula ta sukeyi ba, kuma Abdul ma bai sani ba bare ya labarta Mata.

Yanzu haka Aimana sun tafi jss 2, a yayinda Abdul an zama senior.

Dakyar da sudin goshi Daddy ya samowa Aimana admission, dayake yana da kafa sosai a ministry of education, shiyasa abun yazo masa da dan sauki.

A cikin sati uku ya kammala mata komai, saura tafiya kawai.

Saidai hajiyar fa har yau bata san meke tafiya ba, ga tunani da kewan Kamal da ya addabe ta fiye da ko yaushe, Allah Allah take sati hudu ya cika ko zata ganshi.

Wani lokacin daki take shiga tayi ta kuka, ya Kamal yaki zuwa, gashi kowa ya juya mata baya, har Dada da take tsammanin duk wuya duk rintsi tana tare da ita.

Wata safiya tana kwance a dakinta ita kadai tana tunani, don yanzu ta daina zaman tsakar gidan, taga an turo kofar dakin ana kokarin shigowa, duk a tsammanin ta Abdul, tana shirin masa tsiwar shigo mata daki da yayi ba sallama, sai taga ashe Mama ce, sadda kanta tayi tana tunanin yau kuma me tayi Mama ta biyo ta har daki, a ranta tace "Allah kasa Mama ba duka na zatayi ba".

Cikin mamaki ta dago kanta ta dubi Mama da ta zauna a gefenta a kan katifa, sai taga fiskar ta a dan sake ba kamar kullum ba.

In... Inn...Inna kwana Mama, ta gaisheta cike da zullumin yau dinma ko zata masa.

Ga mamakinta sai taji Mama tace, "lafiya Aimana" wani farinciki ne ya lullubeta, bata san sanda ta fada jikin Mama ta saki wani kuka mai cin rai ba.

Yaushe rabon da Mama ta kalleta, bare ta amsa mata gaisuwar ta, kuma harda kiran sunanta.

"Ya isa haka kukan mana Aimana" ko in tashi in tafiyata, tunda kuka zaki tasa ni a gaba kiyita yi".

Da sauri ta girgiza kanta tana share hawayenta, "kar ki tafi Mama na daina kukan, don Allah Mama kiyi hakuri, Allah ba da gangan na buge ki har wayanki ya fashe ba ranan, bazan sake ba Mama ki daina fushi dani.

Tsakanin uwa da 蓷a sai Allah, tausayin diyarta ce ta kamata, har taji itama idonta na kokarin tara ruwa, dama duk kwanakinnan daurewa kawai takeyi don ta ladaftar da ita.

"Kinga yi shiru, share hawayen naki tukun sai muyi magana"

Da hanzari kuwa ta hau goge fuskanta, saidai tana sharewa wani na kara fitowa, dakyar ta tsayar da kukan.

Mama ta dubeta tace "fasa min waya da kikayi ba shine laifinki ba Aimana, ai ba yau kika fara fasa min wayaba, laifinki daban ne, kinsan me kikayi?"

Girgiza kai yayi.

Mama tace"bude baki zakiyi kimin magana".

"To Mama, kiyi hakuri, bansan me nayi ba"

Nan Mama ta bata labarin abunda ya faru da yarinyar da ta daka, har kiranda mai unguwa yayi wa Baba.

"Aimana wannan shine dalilin fushin mu dake, meyasa kika zabi ki rika jawa iyayenki magana, kina tozarta tarbiyyar da muke baki,meyasa Aimana, bamu isa dake bane, ko kuma ke dince baki ga zaki iya mana biyayya ba".

A'a wallahi Mama, kun isa har kun wuce ma, wace ni Mama da bazan muku biyayya ba, don Allah kiyi hakuri, na miki alkawari daga yanzu bazan sake ba.

"Sau nawa Aimana, sau nawa kina min irin wannan alkawarin, kuma ki dawo ki karya shi".

"insha'Allah Mama wannan karon bazan karya ba".

"To Allah yasa, don Allah Aimana ki kasance ya ta gari wacce iyayenta zasuyi alfahari da ita, ki rika hakuri Aimana, lallai shi hakuri sakamakonsa mai girma ne, ayoyi da hadisai da yawa sunyi magana akan hakuri, kuma nasan an muku a islamiya, saidai kuma in aikine bakiyi dashi, ko ba'a muku ba?"

"Anyi mana Mama"

"Au to kinsani Kenan kike takewa"

"insha'Allah Mama daga yau zan rika kokarin kwatantawa".

" Au to kwatantawa ma zakiyi kenan, to Allah yasa, Allah kuma ya shiryamin ke Aimana.

"Ameen Mama"

"Kullum ina gaya miki Aimana kuma bazan gaji ba,yauma zan kuma"...

"Ke macece ce, ita mace da kamewa aka santa, ta haka ne zata sayawa kanta mutunci da daraja a wurin al'umma, fada ba naki bane, kina mace mai zai kaiki fada a titi,kina zubarwa kanki mutunci, fada a titi ai sai ballagazar mace wacce bata san darajar kanta ba"

Nasiha sosai Mama ta Mata cikin nitsuwa, sai fatan Allah yasa zatayi anfani dashi.

Aimana tace,"nagode Mama, ke din uwa ta gari ce, Allah ya barmin ke, kiyita min addu'a Mama, Allah ya shiga al'amura na".

"insha'Allah Aimana, kullum kuna cikin addu'ar mu, duk iyaye na gari basu manta 'ya'yansu a cikin addu'arsu, yanxu ki tashi ki wanke fuskanki kije Babanku yana son ganinki".

"To Mama bara naje"

"Yi maza, Allah ya miki albarka"

Ta tashi tashiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta nufi wurin Baba a falo.

Tana zuwa ta zauna a kasa kusa da kafarshi tace...

"Baba ina kwana, an tashi lafiya"

"Lafiya qalau", Baba ya amsa mata fuska ba yabo ba fallasa.

Jin shiru ba magana yasa Aimana ta dago da kanta, ganin yanayin fuskan Baba sai yasa jikinta yin sanyi, a ranta tace"Baba har yanzu bai huce ba kenan".

Sadda kanta tayi tace,"don Allah Babana kayi hakuri ka yafe min, na tuba Baba, bazan sake ba".

Baba ya gyara zama ya fiskance ta soaai kafin yace "Aimana"

"Na'am Baba"

"Aimana, 'ya'ya nagari sune masu sanya iyayesu farinciki, masu gudun bacin ransu,masu biyayya a garesu, masu bin umarninsu koda baiyi daidai da nasu ra'ayin ba, amma ke gabadaya kinyi hannun riga da wadannan halayya, shin ke a wani sashe kike son ajiye kanki Aimana?"

Cikin sheshshekar kuka tace"kayi hakuri Baba"

"Kinfi kowa iya bada hakuri, amma ke meyasa wannan hakurin bakya iya yinshi?, yana daga cikin dabi'un na muminai da mutanen kwarai, hakuri da yafiya, tabbas wadannan abu guda biyun suna da wahalar yi, amma idan ka daure zuciyar ka ba komai bane".

Numfashi yaja ya dubeta tana ta faman sheka kuka, yasan hukuncin da suka mata ya tabata sosai, duba da har wani rama tayi a cikin sati uku kacal.

Ya nisa yace "Aimana ki gaya min mai yasa baki jin maganar da muke miki, shin kin raina mune ko kuma don kina ganin ke kadai Allah ya ban shiyasa kike abinda kika ga dama, kina ganin kamar bazan iya yanke tsatsauran hukunci a kanki bane? to kinyi kuskure".

"Kayi hakuri Baba, in Allah ya yarda bazan kara bata maka rai ba"

"To Allah yasa, a wannan Karon kin min abunda raina yayi matukar baci,fiye da yanda kike tunani, kuma a dalilin haka na zartar da wani hukunci a kanki".

Kirjin Aimana ya buga da karfi, to wani hukunci ne Baba ya yanke a kanta, ba irin tunanin da baizo zuciyarta ba.

Baba yaci gaba da cewa," yau wace rana muke?"

"Yau Asabar Baba" cewar Aimana.

"To daga yau ki fara lissafi, wani sati in Allah ya kaimu ranar lahadi, Yaya zaizo ya dauke ki....

Da sauri ta katse Shi da cewar "ina Daddy zai kaini kuma Baba, don Allah kar kace in bar gidannan, kayi hakuri Baba wallahi bazan sake bata maka rai ba".

"Ba gidan zaki bari ba Aimana, makaranta na canza miki, zaizo ne ya daukeki ya kaiki makarantar".

Hankalinta yadan kwanta jin cewar Baba ba korinta zaiyi a gidan ba, to amma meyasa Baba ya canza mata makaranta, kuma wani makaranta ne ma.

"To Baba, wani makaranta ka canza min, yana da nisa ne, ko a unguwar su daddy yake, amma dai zan rika zuwa in dawo ko Baba, kar kace in zauna a gidan Daddy gabadaya.

Wani tausayinta yaji, yasan Aimana bata son matsawa ko nan da can, itadai ta zaga ta dawo ta samesu a gida shikenan, ko gidan Daddy da take son zuwa, bata iya musu ko kwana biyu ne.

Girgiza kai yayi yace," ko daya Aimana, makarantan kwana na mai dake, wato nan FGGC Gusau".

"Innalillahi wa inna ilahi raji'uun, Baba Kamin rai kar ka kaini makarantan kwana, ai na ce maka na daina rashin ji, Baba duka sukeyi, ga senior sai suyi ta cin zali, na tuba Baba don Allah ka barni inci gaba da zuwa makaranta na a nan, na maka alkawarin bazan kuma rashin ji ba".

"Saidai kiyi hakuri Aimana, amma na riga na yanke wannan hukunci, zanga ko kin dauki nasihata, zanga ko ke din ya ta gari ce".

Baba ya fadi haka ne don yasan in ba hakan yai ba maganar bazata kare yanxu, zatayi ta mishi magiya me da roko.

"Shikenan Baba insha'Allah zan maka biyayya, bazan sake kin jin maganar ka ba".

"Yawwa Aimana haka nake son ji, Allah miki albarka".

"Ameen Baba"

Daga nan nasiha ya mata sosai kafin yace ta je.

Koda Aimana ta koma dakinta, fadawa tayi a kan katifarta,ta sanya wani kuka mai taba zuciya.

Tunani take ta yaya zata rayu a inda babu su Baba, ba Dadanta, ba ya Abdul dinta, ba ya Kamal.

A take ta tuna Baba yace ran lahadi zata tafi, a ranta take fadin "what if ya Kamal baizoba har lokacin, shikenan zan tafi ban ganshi ba, bamuyi sallama ba, ni ya zanyi da raina ne, yanzu haka zan tafi sai nayi wata kusan uku banga ya Kamal ba, anya zan iya kuwa".

Haka tasha kukanta ta koshi ba wanda ya sani, tana nan kwance har bacci ya dauketa, ba ita ta farka ba sai azahar, ko fitan Baba ma bata sani ba.

Tashi tayi ta dauro alwala ta gabatar da sallan azahar, addu'a tayi sosai akan Allah yasa Kamal yazo kafin ta tafi.

Haka rayuwa taci gaba da gudana, Aimana ta zama wata iri, sukuku da ita,ko abincin kirki bata ci, ta sawa ranta tunanin yanda zata rabu da iyayenta da yan'uwanta taje inda ba wanda tasani.

A gefe guda kuma tunanin Kamal ne ya addabi zuciyarta, kullum tana saka tsammanin ganinsa amma haka rana zai fito har ya fadi ba labarinsa.

A haka satin ya kare, yau ya kama Asabar, wanda gobe kuma da sassafe Daddy zaizo su wuce, gashi har yau ba labarin Kamal, zuwa yanzu Aimana ta cire tsammanin zaizo, watakila babu rabon zasuyi sallama.

Mama nata shirya mata kayan tafiya, bama wasu masu yawa bane, ga provision nata a gefe, Baba yayi kokari sosai, duk da Daddy yace shi zaiyi komai amma Baba ma saida yayi nashi.

Jiki a mace ta dubi Mama tace, "Mama don Allah bari naje nawa su Hamida sallama, tunda kinga gobe da wuri zamu tafi, watakila bazamu hadu ba".

"To jeki mana Aimana, ki gaida min umman tasu"

"To Mama zataji"

Ta fito sanye da hijabinta ruwan hanta, ya kuwa haska ta sosai tayi kyau, saidai raman da tayi.

Sallama tayi a kofar gidan su Hamida.

Daga ciki ummah ta amsa mata.

Shigowa tayi, ba kowa a tsakar gidan, sai ta nufi falo, da sallama ta shiga ta samu Ummah a dan kishingide tana hutawa.

Sunkuyawa tayi har kasa tace " ina kwana Ummah".

"Lafiya qalau Aimana, ya kike, ya Maman taki?"

"Lafiya qalau Ummah, tace ma na gaisheki"

"Ah to Masha Allah, ina amsawa".

Tambayar Mama tayi ko su Hamida na nan don taji gidan shiru.

"Suna nan Aimana, na aike su nan baya ne yanzu zakiga sun dawo"

Zama tayi suna dan taba hira da Mama kafin su dawo.

Ba jimawa kuwa suka dawo, ganin Aimana suka shiga murna, janta sukayi suka wuce dakinsu.

Humaida ce tace, "dazu kuwa mukace Mama zamu shiga dubaki don jiya bakije makaranta ba kuma bakije islamiya ba".

"Ai ku baku da kirki, tun jiyan me ya hanaku zuwa dubani, Saida kuka ga nazo zakuyi wani borin kunya, nasan da ya Kamal na nan da ya dubo ni tun jiya".

Ba haka bane, kinsan muna dawowa muka wuce islamiya, koda muka dawo kuma Ummah ta samu aiki, shiyasa.

"To ai shikenan", daga nan suka shiga wani hiran daban, anan take gaya musu maganar tafyarta makaranta gobe"

Da fari basu yarda ba saida ta ranste musu ta tabbatar musu gobe zata tafi kafin suka yarda.

Sunyi jimamin rabuwa da kawartasu harda kukansu, kafin sukaje suka gaya wa Ummah, addu'a sosai ta mata da fatan alkhairi Hadi da nasiha irin na manya.

Aimana ta mata godiya sannan ta tafi.

Su Hamida suka rakata, Saida suka je waje ta kama hannunsu tace...

"Don Allah in ya Kamal ya dawo ku gaya mishi ina gaishesa kuma zanyi kewansa, kuce masa nayi ta jiran shi bai dawo ba, ina masa fatan alkhairi".

Idanunsu cike da hawaye sukace mata zasu gaya mishi sakonta, daga haka sukayi sallama ta wuce gida.

Washe gari kuwa karfe bakwai Daddy ya iso, ko kafin bakwai da rabi sun gama komai sai tafiya.

Haka suka rabu, ko Mama ma saida tayi kuka a boye, Dada kam ma kin fitowa tayi a dakin a cewarta bazata iya ganin tafiyar Aimana ba.

Abdul kam ai ba'a magana, kankame juna sukayi da Aimana suna kuka dakyar aka rabasu, da har Baba yace aje dashi yayi mata rakiya, amma Daddy yace bazai iya rarrashi biyu ba, sudai gama a nan.

Suka shiga mota suka dau hanya.

To Aimana fatan alkhairi.

Motarsu na karya kwanan fita unguwarsu, adaidaitan da Kamal yake ciki itama ta shigo.

Caraf kuwa Aimana ta hangoshi, saidai lokaci ya kure, "ya Kamal meyasa baka zo tun lokacinda nake bukatar kazo ba sai yanzu, saidai duk da haka naji dadin ganinka kafin na tafi, Allah ya sada mu da alkhairi.......