RASHIN SANI

PAGE 08.

by @sumy6163

💫💫RASHIN SANI 💫💫

STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.

Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.

PAGE 08.

Aimana bata daina kallon adaidaitan ba har saida ya bace mata, kafin ta juya ta daidaita zamanta cike da kuncin zuciya.

Kamal ko mai adaidaitan na sauke shi ya kalli su Hamida, sunyi cirko cirko a kofar gida, kuma da alamun sunci kuka har sun gaji.

Zuciyar shi yaji ta tsinke gabanshi ya fadi, mai yake faruwa ne, tin jiya yake fama da faduwar gaba, gabadaya ya kasa sukuni, shiyasa ma yayi sammakon zuwa yaudin, Allah yasa dai lafiya.

Cikin sarewa da mutuwar jiki ya karasa kusa dasu, Abdul ya kalla da alamu sun nuna yaci kuka sosai, ya matso kusa dashi yace...

"Me yake faruwa ne Abdul, ya na ganku a tsaye haka a waje?"

Abdul ya kara fashewa da sabon kuka ya fada a jikinsa yace..

"Ya Kamal Aimana ce"

Da karfi kirjinsa ya buga, da hanzari yana rawar baki yace, "me ya faru da Aima, wani abu ya sameta ne?, gaya min don Allah".

"Ya Kamal Aima ta tafi makarantan kwana, yanzunnan Daddy suka wuce, watakila ma kaga motarsu a hanya".

Wani gwauron numfashi ya sauke tare da sauke ajiyar zuciya, ya dan samu relief jin cewa ba wani abu bane ya samu Aimana, tunda tana cikin koshin lafiya, Alhamdulillahi.

Kamo Abdul yayi ya hau rarrashinsa da bashi baki, ya nuna mishi yayi hakuri Aimana ba mutuwa tayi ba, kuma ba ta tafi Kenan har abada ba, nan da yan kwanaki zaiga har term ya kare tazo, addu'a kawai zaiyi ta mata, Allah ya bata sa'ar abunda taje nema.

Da haka ya lallaba shi ya koma cikin gida, duk da shima daurewa kawai yakeyi, da yasan Aimana zata tafi yau, da yayi kokari ya zo tun jiya,ko tun Friday,yanda zasuyi sallama sosai.

Wani iri yakeji a ranshi kamar bazai kara ganinta ba, tin jiya yaso zuwa amma sai wani abu ya tsaidashi.

Ya juya ya kama hannun kannensa suka shiga gida.

Ummah ya hango a tsakar gidan tana yan aikace aikacenta, tunda ta lura yau masu mata aikin basa cikin walwala, sai ta dauke musu aikin take kayanta.

"Ah ah, kaga mutanen jami'a yanzu kake tafe, lale maraba, irin wannan dako sammakon haka, ko dai kewar mune ya maka yawa".

Yake kawai Kamal yayi, ya sunkuya ya gaisheta, ta amsa masa cike da farincikin ganinsa.

Nisawa yayi yace, "Mama dama Aimana zata tafi makaranta shine ko a waya ba wanda ya gaya min?"

"Kayi hakuri Kamal, muma sai jiya ne ta shigo ta gaya mana, kuma ba wanda yayi tunanin gaya mana".

"Shikenan Ummah, Allah ya bada sa'ar

karatu"

"Ameen kamalu"

"Koda Hamida ta isar masa da sakon Aimana, sai yaji ba dadi, RASHIN SANIN tafiyarta ne ya hanashi zuwa, da ya sani da ya bar komai yazo, haka Allah yaso.

~~~~~~~~

Aimana sun isa makaranta lfy, direct Daddy ya kaita wurin principal din makarantan mai suna mu'azu Bappa, aka gama duk abinda ya rage.

Aikawa yayi aka kira masa senior mistress nasu,ya hada ta da Aimana yace taje ta kaita hostel a Sama mata daki, sannan a bata uniform da duk wasu abubuwan da ya kamata ta mallaka, gobe Monday zata fara attending class.

"A kula da ita soaai Mrs Rafi'at, don wannan din 'ya taceh".

"Kar ka samu damuwa sir, za'a Kula da ita yanda ya kamata"

Ta kama hannun Aimana suka wuce, office nata suka fara zuwa, tace ta zauna, ta Kira mai alhakin bada uniform ya kawo Mata.

Suna zaune kuwa sai gashi ya kawo mata su, uniform ne guda biyu, sai sports wear,shima guda biyu, sai kuma na islmiyar su, shima guda biyu.

Senior mistress dinne ta karba, Mrs Rafi'at , kamar yadda Aimana taji principal ya kirata daxu a office nashi.

Ta bude ta duba taga zasu mata kafin ta mika mata, tare da cewa "muje in nuna miki hostel naku".

Tashi kawai Aimana tayi ta bita, don bata jin zata iya magana a yanzu, Daddy ma fushi take dashi, shiyasa ko sallama bata masa ba ta wuce abinta.

Mrs Rafi'at da kanta ta kai Aimana har hostel nasu,mai kyau dashi, ta zaba mata daki, sannan ta saka wasu suka taya Aimana shigar da kayanta wanda wani security ya kawo mata har kofan dakin, don ita a office na principal ta Bari, tama mance tazo da wasu kayan.

Ko wani daki mutum hudu ne, hakama dakin su Aimana, saidai da alama wadanda suke dakin sun girmeta, sai daya da zasuyi sa'an juna.

Mrs Rafi'at ta dubi daya daga cikin yan dakin tace tazo.

Tana zuwa ta rusuna tace "gani Ma"

Yawwa Asma'u, ga 'kanwa nan na kawo miki, pls you should be her guide, duk abinda ya kamata ki nuna mata, wannan din da kike gani, she's like a daughter to your principal, please Asma'u take good care of her.

"insha'Allah Ma, i will try my best".

Ta kamo hannun Aimana suka wuce ciki, kallonta tayi tace, "so cute, Masha Allah, ya sunanki?"

Aimana da take jin wani iri, sabida tsintar kanta da tayi a inda bata taba tsammani ba, a kuma cikin mutanen da bata sansu ba, ta dubi wacce aka kira da Asma'u tace..

"Aimana Tahir Balarabe"

"Uhmm what a sweet name, I'm Asma'u Bashir, sannan ta mika mata hannun,nice meeting you".

Hannu kawai Aimana ta iya mika mata tare da girgiza kai tana murmushi, ko ba komai tana ga wannan kamar zatayi kirki.

Sauran yan dakin ne suka matso suma suka mika mata hannu, dayar tace"I'm Hajara isma'il". dayar kuma tace, " Fatima Kabir Usman.

Amsa musu tayi cikin dan murmushi, ta mika musu hannu itama tare da fadin "nice meeting you"

Suka hada baki wurin fadin "nice meeting you too".

Taimaka mata sukayi tayi arranging kayanta a wardrobe na dakin wanda ya kasance kashi hudu ne, kowa da nasa, sannan suka damka mata makullinta don ta adana, saboda kowa rufe nasa yakeyi.

Ta karba tare da musu godiya.

Hajara ne tace mata "wani class kike?.

"Jss 2", ta amsa mata.

"La ashe class namu daya", sai kuma ta tsagaita da dariyan tace, kodayake bansan wanne za a kaiki ba, nidai B class nake.

Asma'u ne tace "to tunda baki tambaya ba bari na gaya miki, ni dai SS 2 nake, Fatima kuma SS 1, sai ku kuma yan jss.

Murmushi tayi tace"to Allah ya zaunar damu lafiya, ya kade fitina a tsakanin mu".

Ameen duk suka amsa, shiru Aimana tayi sabida rashin sabo, Fatima da hajara kuwa sun fice sun tafi laundry, daga ita sai Asma'u, ita kuma tana rubutu, da alama assignment ne takeyi.

Washegari Monday,tun asuba suka tashi, taga kowa ta sabi bucket,tana ta tunanin mai zasuyi.

Asma'u ganinta a zaune yasa ta tuna ashe fa bata san kan komai ba tukun, tace..

"Aimana tashi ki dauko bucket muje mu samo ruwan wanka, yi maza kar mu makara".

Ta duba agogon dakinsu karfe hudu da yan minuna, mamaki ya kamata, ko sallar asuba basuyi ba zasuje samo ruwan wanka, to kodai su anan basa salla ne?"

"Yi maza mana Aimana,kar mu makara"

Muryar Asma'u ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, dauko bokitin ta tayi, sabo fil dashi ta bi Asma'u suka fita.

Mamaki ne ya kama Aimana, gani tayi ana bin wani dogon layi kowa da bokitin shi a hannu, wasu har fada sukeyi.

Duban Asma'u tayi tace, "aunty Asma, muma yanzu wannan layin zamubi?"

Shi zamubi Aimana,ai shiyasa nake ta cewa kiyi sauri, in kika kai anjima kadan saidai ki tafi class ba wanka", kalli can kiga, ta nuna mata Hajara dake gaba tace "kinga Hajara da ta fito da wuri tana can gaba, shiyasa nake ta ce miki muyi sauri"

"Ikon Allah", Aimana ta samu kanta da fada.

Suna nan suna bin layi,har akazo kansu, suka diba, suka wuce.

tana ganin wasu sai sun sha wahala sunbi layi sun debo sai seniors su juye,sai sun koma sun sake bin layi kuma kafin su diba, ko kuma in sunzo wurin basa bin layi suke diba su tafi, kuma ba wanda ya isa ya tanka, wai su senior.

Jinjina Kai Aimana tayi tace "wata rayuwa".

A haka suka wuce toilet, nan taga abunda ya shallake tunaninta, don shiga kawai akeyi ba'a jiran sai wani ya fito, don in kince zaki Jira, to kuwa bazakiyi wankan ba, haka Asma'u taja hannuta suka shige wani bayi, yan mata uku ne a ciki.

Tana gani Asma'u ta shiga tube Kaya, amma sai ta bar wani vest dan dogo a jikinta mai laushi ta fara wankan ta.

Tana nan tsaye taga wata ma ta shigo ta fara wankanta, ita kanma pant kawai ta bari kuma ko a jikinta taci gaba da wankan.

Can Asma'u ta juya taga Aimana na tsaye bata da niyar wankan, yafito ta tayi tace "kiyi wankan ki, nan ba ruwan wani da wani, in kuma kinki saidai ki fito mu tafi ki fasa wankan".

Ganin bata da wani mafita yasa ta tube tabar hijabin jikinta tayi wankan dashi, tana gamawa ta mai da kayanta da jikakken hijabin suka koma dakinsu, a nan suka samu su Hajara har sunyi sallah, suna shiryawa.

Suma sallan sukayi sannan suka shirya cikin uniform nasu, karfe shida suka fita, kowa yaje dinning don karban breakfast .

Shayi ne da bread, yawanci Mondays shine breakfast nasu, saidai shayin ba rahama, gashinan dai kamar fitsari, alamun bai samu wadataccen ganyen shayi ba, kuma baiji sugar ba.

Tana gani wasu student din suna fitarda sugar suna karawa, wasu harda madara,wasu ko harda Milo, sai ta tuna da nata a daki, ai da tasan haka akeyi data dibo.

Dakyar ta samu ta tura bread din kadan, shayin kam bata iya sha ba haka ta barshi.

Daga nan assembly suka wuce, sai ta rasa layin wani class zata bi, kawai sai tabi Hajara.

Bayan gama assembly, Asma'u ta raka ta wurin Mrs Rafi'at, bata nan tace ta jira ta yanzu zata dawo ita zata wuce class kar tayi late.

Da to Aimana ta amsa mata kafin ta tafi ta barta a nan.

Ba jimawa kuwa sai ga Mrs Rafi'at ta dawo.

Aimana ta gaishe ta, cikin sakin fiska ta amsata, sannan ta mike tace muje in nuna miki class naki.

Mikewa Aimana tayi tabi bayanta har suka iso bangaren da classes suke, a nan ta kaita jss 2B, hakan kuwa ya mata dadi, yanzu ajinsu daya da Hajara Kenan, Mrs Rafi'at ta gabatar da ita a matsayin sabon student nasu.

Seat aka bata daga can tsakiya, gashi Aimana akwai son zama a front seat , Saidai ba yanda ta iya haka ta hakura ta zauna, already akwai teacher a class din sai kawai aka cigaba da darasi.

Subject uku sukayi kafin suka fita break, nan ma karba sukaje sukayi, bayan sun gama suka koma class.

Karfe daya aka tashe su, kowa ya nufi dinning ya karba abinci sukaci kafin su koma dakinsu.

Bayan la'asar kuma, karfe hudu suka tafi islamiya, wadanda ba musulmai ba kuma suka tafi evening service, da dare kuma akwai tutorial.

Gabadaya Aimana ta gaji, ace mutum ya tashi tun karfe hudu,yana sungulla daga wannan sai wannan, yini guda ba hutu, sai karfe tara zasu dawo dakinsu, shima in kana da assignment a lokacin ne zakayi.

"Wash Allah na, wallahi na gaji, kuma yanzu haka mutun zai rika yi kullum?"

Asma'u tace "haka zakiyi kullum, weekend ne kawai muke dan hutawa, shima kuma lokacin ne zakiyi wankin kayanki,kiyi kitso da duk wani abunda zakiyi".

"Tabb lallai kam, akwai aiki, yanzu haka kullum mutum zaiyi ta gajiya, jin jikina nake kamar ba nawa ba, duk ciwo yakeyi"

"Don dai baki saba bane, da kin kwana biyu shikenan zaki saba", cewar Hajara.

Fatima tace " nifa farkon zuwana har ciwo nayi saboda stress, amma ba gashi yanzu na saba ba, in kinji ana daily routine to shine wannan" ta karashe da dariya.

Tabdi, to Allah ya kyauta.

Har ta kade katifa zata kwanta, ta ji Hajara na fadin "note din fa Aimana, ko baza kiyi ba yau".

Ji tayi kamar ta sa ihu, ashe wai tana da note, gashi dayawa, don sunyi nisa sosai, next week ma zasu fara second CA.

Juyawa tayi ta kalli Hajara tace, "yaukam bazan iya ba saidai gobe".

"Da dai kin daure kinyi ko kadanne, kinsan fa note din dayawa, kowani subject kuma sai kin kofe".

"To Hajara ki tayani don Allah".

"Ai bame yiwa wani note, don in aka ga rubutun wani wani a takaddanki dake dashi kun shiga uku".

"Innalillahi wa inna ilahi raji'uun, ina cikin jalala".

"Yanzu da surutun da mukeyin nan da kinyi ko page daya ne".

Haka ta karbi note din ta fara yi, ba ita ta kwanta ba sai shadaya, kuma gashi dole karfe hudu zata tashi.

Haka Aimana take rayuwa a makaranta, a hankali take sabawa da rayuwar makarantan.

Sannu a hankali Aimana ta fara zama popular, saboda Aimana dai hali bai canza ba, bata daukan raini, kuma kana tabata zata rama, don bata barin sai ta kwana, musamman data samu goyon bayan wata senior, sister Blessing.

Haka kawai jinsu ya hadu, sai take ce mata daughter, ita kuma Aimana take kiranta da Momy, ta daure mata kugu a makarantan, ba mai tabata ko sata aiki kamar yadda akewa sauran junior din, kana mata abu kuwa zata kaika wurin Blessing taci kaniyarka.

Saidai fa duk tsiyan Aimana akwai kokari, don irinsu ne ake kira gifted, kana zuba mata tana diba, ita da tazo daga baya har tafi wasu dayawa kokari.

Saidai duk tsawon wannan lokacin Kamal na nan makale a ranta, 'yan dakinsu ba wanda baisan labarin Kamal ba, su duk sun dauka yayanta ne uwa daya Uba daya, basu san abun ba haka bane.

Abun mamaki da sukayi exam sai ga Aimana tayi na biyu, murna a wurinta kamar me.

An samu hutu, dalibai kowa nata murnar komawa gida ciki kuwa harda Aimana, don ba karya tayi kewan gida, kuma tayi kewan Kamal ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida.

Saidai wani tashin hankali ta shiga jin labarinda Mrs Rafi'at take sanar da ita......