PAGE 4
GANIN IDO 🥀🥀
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 4
Yau tun da muka wayi gari na ɗauko wanki ina yi bayan Bahrain ya tafi islamiyya kasancewar yau Asabar ce. Ina cikin yi Ammie ta fito ta zauna tana tayani har kusan ƙarfe sha biyu saura na rana, bayan mun kambala na zuba mata ruwan wanka sannan na gyara wuta na sake ɗora ruwan zafi a tukunya daga nan na zari hijabina sai wurin Baba mai Shago.
Bayan na gaishe da shi ya amsa na ciro takardar da ke É—auke da lambar wayar Dr. Basheer na bashi na ce dan Allah ya kirasa ya ce masa Beenafah ce É—iyar Patient É—insa Mulaifa Zayd Hudaif.
Yana gama faɗa masa haka ya yanke wayar ko minti ɗaya ba'a ƙara cikakke ba sai gashi ya kira.
Cike da ladabi na gaishe da shi sannan na ce.
"Daman naga mun shigo Sati uku cikin na huÉ—u, shine na ce bari na tuna maka kada kuma a zo a samu matsala."
Daga can ɓangaren ya ce.
"Haka ne gaskiya, to amma ai date ɗinda za ku dawo yana nan rubuce a jikin takardar da na baki kamar yanda a ka saba. Na san tabbas satin da zamu shiga ne amma ban riƙe date ɗin ba, sai ki duba ki gani."
GyaÉ—a kaina na yi na ce.
"OK to, In Sha Allah!"
"Sannan magana ta gaba kuma a ina ne za'a tura muku da kuÉ—in?"
"Ina ga ka manta ne Likita, amma Numbern Account ɗin tana nan jikin form ɗinda aka bamu muka cike domin sharaɗinma shine, dole account ɗin sai yana da alaƙa da Ammie to kuma na ta ɗinne wanda Daddy ya buɗe mata na saka."
"Ok to. In Sha Allah, zan sanar da su cewa lokaci ya yi, zuwa gobe ko jibi za'a tura da su."
ĆŠan rusunawa na yi kaÉ—an tamkar ina a gabansa na ce.
"Mun gode sosai Likita, Allah ya saka maka da mafificin alheri ya biya maka dukkan buƙatunka."
Ina gama wayar na miƙawa Baba mai Shago na ce.
"Na gode sosai Allah ya saka da alheri Baba. Don Allah kada ka gaji dani, ga ATM card ɗinmu ka riƙe ta a wajenka, ina so ka taimaka ka bamu Shinkafa da Wake da Mai da Magi, wallahi yau kwana na biyu kenan bamu ɗora tukunyar abinci ba, dan Allah ka taimaka mana."
"Kayan kamar na nawa za'a bayar?"
Ɗan Jim! Na yi ina nazari sannan daga ƙarshe na ce.
"Ka kashe mana dubu biyar har da gawayi ma."
"To É—an jirani yanzu ina zuwa."
Ina nan a tsaye ya auna komai ya bani daga nan na yi masa godiya sosai na koma gida.
Ina zuwa na É—ibi Waken na gyara na zuba a tukunyar da na É—ora kafin na fita, daga nan na je na yi sallar Zuhr sannan na dawo na ci gaba da gyara shinkafa ina faÉ—awa Ammie yanda mukayi da Dr. Basheer.
****
Wasa-wasa tun kafin lokacin tafiyarmu ya cika nake zuwa neman Daddy bana samun sa wanda da alama ya yi tafiya ne. Har lokacin kuma ya cika muka shirye muka je Sokoto muka yi kwana É—aya muka dawo still bai dawo ba. Munyi kwana É—aya ne kacal kasancewar gwaje-gwajen da duk aka yi wa Ammie sun nuna komai lafiya, babu wata matsala mai yawa a wannan karon.
Dubu ɗari da hamsin ne kuɗin tallafin da zamu riƙa samu duk wata idan lokacin zuwanmu asibiti ya yi, hakan yasa koda muka dawo iyaka dubu sha biyu ne suka rage a hannuna domin tun kafin ma mu tafi na riga na karɓi kayan Baba mai shago sun kai na dubu takwas.
Addu'a sosai na shiga yi ina fata da saka ran duk inda Daddy yake Allah yasa ya dawo nan kusa.
Sai da muka cika sati ɗaya da dawowa cif, a daren ranar misalin ƙarfe biyu da rabi na dare bayan na raka Ammie banɗaki mun dawo, kamar an ce na leƙa window kwatsam sai ga motar Daddy na hango an yi parking dai-dai inda yake ajiye ta idan ya dawo da dare.
Cikin wani irin farin ciki na kalli Ammie dake ƙoƙarin tayar da Salla na ce.
"Ammie Daddy ya dawo! Wallahi Daddy ya dawo. Zo.....Zo ma ki hango motar sa da idonki ki gani."
Na ƙarashe maganar tare da janyo hannunta kamar wata zararra ina nuna mata.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana mai bi na da kallo ta ce.
"Allah maji roƙon bayinsa Beenafah. Ni ina ganin kada ma ki yi masa zancen kowane kuɗi kawai ki yi masa zancen abinci, ina ga hakan kawai ya wadatar. Wallahi Ba na jin daɗin yanda mafi yawan lokuta Bahrain yake zuwa makaranta batare da ya sanya komai a cikin sa ba... "
Hannayenta na kama guda biyu ina mai ƙara kwantar da murya, na ce.
" Ba Bahrain kaɗai ba Ammie, har ke kina da buƙatar wadataccen abin Ci da Sha domin ƙwaƙwalwarki ta ƙara samun nutsuwa da aiki yanda ya kamata..."
Cikin kalamai ma su nuna zallar karaya ta ce.
" Ina ma ace Abbie shima yana nan tare damu. Da yanzu komai na nan yanda yake, da yanzu Sajjad É—ina shima yana raye! Da...."
Hannuna na sanya da sauri na toshe mata baki tare da girgiza kaina ina mai fashewa da wani irin kuka, na ce.
"Kash Ammie! Ashe ba kullum ana miki nuni akan yarda da ƙaddara ba? Har abada babu danasani a cikin hukuncin Allah Ammie, Babu fa wanda yake da ikon rubutawa kansa ƙaddara fa ce abinda Allah ya nufesa da shi. Abbie addu'armu yake buƙata akoda yaushe. Sannan a kullum ina so ki ci gaba da sakawa a ranki cewa babu wani laifi da kika aikata, ba ki aikata komai ba. Ki yi haƙuri Ammie na! Ki ƙara haƙuri, Allah yana tare da masu haƙuri."
Ina gama faɗar haka na rungumeta sosai ina mai ƙara lafewa a jikinta yayinda zuciyata ta sake jin wani sabon tausayinta na daɗa huda sassa da ɓargon jikina.
Cikin tausasa kalamai masu ƙwarara gwiwa na yi nasarar sanyata komawa bacci domin bana so abun ya ƙara ta'azzara kada kuma a samu wata sabuwar ɓarakarda ban san ranar fita ba.
Sai dai kuma ni tun wannan farkawar da na yi, ban sake runtsawa ba har gari ya waye wanda ƙarfe bakwai na safe ma a ƙofar Mummy Zaliha ta yi mini.
Ina nan shanye a wurin tamkar wata garar kunya har misalin ƙarfe takwas da rabi sannan sai ga Daddy ya fara fitowa. Idonsa na sauka a kaina ya ce.
"A'a! Beenafah. Ke ce? Yanzu daman nake zancen aje a kira mini ke, kun ji ni shiru kwana biyu ba na nan tafiya na yi."
Wani irin sanyin rahama ne na ji ya ratsa zuciyata wanda har ban san lokacinda na lumshe idanuwana ba tare da cewa Alhamdulillah!.
Mummy Zaliha ce ta fito tare da Humaida da kuma twins É—inta wato Aunty Hassana da Hussaina. Dukkan su cikin shirin fita unguwa suke da alama ma ba garin za su tsaya ba ganin yanda drivern su da kuma Biba ke ta famar fito musu da jakunkunansu.
Ina ganin ta fito na shiga gaisheta har su Aunty Hassana wanda a daƙile suka amsa min gaisuwar ta wa ba tare da ma sun ko kalli inda shirgina yake ba musamman Mummy har suka shige mota gaba ɗayansu suka wuce suka barni daga ni sai Daddy sai kuma Biba da ta juya ta koma ciki.
"Ki na jina Beenafah? Daman due ta wasu 'ƴan abubuwanda suka ta so, kamar transfer da na samu daga wurin aikina da kuma dalilin makarantarsu Husaina. Haƙiƙa suna shan wahala idan buƙatar zuwa gida ta kamasu saboda nisanda ke akwai daga Abuja zuwa nan Zamfara. Kin ga sai sun hawo jirgi daga can zuwa Sokoto, sannan daga can Sokoto su ƙara hawo Mota zuwa nan kinga akwai wahala. To shi ne muka yanke shawara ni da Hajiya Zaliha cewa yakamata mu koma can domin ni in samu sauƙi su ma kuma su Husainar su samu sauƙi. A taiƙace dai zamu koma Abuja da zama.... "
Zuciyata ce ta buga da ƙarfi har ban san lokacin da na miƙe tsaye ba haɓa na rawa na ce.
"Abuja Daddy! To ni da Ammie da Bahrain fa?"
"Eh daman ku ai za ku ci gaba da zamanku a nan ne...."
Tamkar gilashin da aka rotsawa dutse haka na ji zuciyata ta tarwatse lokaci ɗaya jin cewa wai mu a nan za mu zauna. Cikin matsanancin firgici na faɗa kan ƙafafunshi tamkar wata zararra ina mai fashewa da kuka na ce.
" Dan Allah Daddy ka rufa mana asiri kada ka bar mu a nan na roƙeka. Daddy wa muke da shi da har za ka barmu a nan? Don Allah kar ka yi haka..."
"To cewa na yi ba zan cigaba da É—aukar nauyinku ba ne da har ki ke wannan kukan?"
"Ba zancen É—aukar nauyinmu ba Daddy. A duk faÉ—in Gusau kai ne kaÉ—ai muka sani, ta dalilin ka muke zaune a nan..."
"Ki bari in mutu tukun Beenafah kafin ki yi ƙoƙarin binneni. Ni kin ji na ce miki kuna da wani bayan ni ne? Daman ina nufin ku zauna a nan kafin na tafi can na yi settling, daga baya idan komai ya daidaitar mini sai in aiko a tafi daku. Tsawon shekara huɗu cikin ta biyar nake ɗauke da nauyinku a kaina; Ciyarwa, shayarwa, sutura, magani, hatta makaranta da na kashe kuɗina na saka ki ƙarshe asara nayi saboda daina zuwa da kikayi, na ɗauki nauyin ciwon mahaifiyarki. Duk da haka ban gaji ba sai da na kwashi maƙudan kuɗi na bayar wurin yi wa jaririn da yake cikin zanin goyo aiki wanda sai bayan na gama wahala ya mutu. To yanzu dan Allah Beenafah duk irin wannan wahalar da na yi daku tsawon lokaci mi zai sa na kasa ci gaba da kulawa da ku? Kar fa ki manta har account na buɗe muku ina tura muku kuɗi a ciki. To ko yanzu ba kasawa na yi ba, kuma ba zan fasa yi muku duk wani taimakon da na saba yi muku ba ko don kasancewarku jinin ɗan uwana. Kawai dai idan na koma can tare da ku a yanzu, wahala ƙara maye mini za ta yi domin rayuwar Abuja ta banbanta da ta Gusau, saboda haka ku yi zamanku a nan, ga gida nan babu mai tashin ku a ciki. Daga baya sai in aiko a tafi daku idan na shirya, kuma In Sha Allah zan ci gaba da tura muku kuɗi kamar yanda na saba..."
Tamkar an jefo Ammie daga sama, haka na ganta kwatsam gaban Daddy tana yi mai wani kallon mamaki da al'ajabi na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta fashe da kuka a hankali kuma ta koma dariya. Tayi kuka tayi dariya lokaci ɗaya tare da nuna shi da yatsa tana faɗin.
"Dr. Bello Wazeer! Alhaji Mudassir Wazeer... Dr. Bello Wazeer... Alhaji Mudassir Wazeer... Bello.. Bello.. Dr.. Bello.."
Girgiza kansa yayi yana mai mayarda kallon sa gareni ya ce.
"Beenafah ki kamata ki mayar da ita ciki please. Sai kun ji Saƙo in sha Allahu zuwa wata ɗaya."
Sake matsawa na yi gaban sa bayan na rirriƙe Ammie cike da magiya ina wani irin kuka mai cike da ƙunci na ce.
"Daddy dan Allah dan darajar Allah karka yi mana haka. Daddy ko yanzu da kake tare damu ya muka ƙare ballantana ace ka yi mana nisa? Daddy Bahrain... Bah...."
✍️ OUM-AMEER ✍️