BABI NA BIYU
BA NI DA IKO...
©Fareeda Abdallah
Bismillahir rahmanirraheem
In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.
Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages daga page 1 zuwa 10 in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a nan Whatsapp da Arewa books.
Ƙungiyar masu karatun Bati ku zo mu saka labule😍 Duk da dai na sani ƙaunar rubutunmu shi ke sa idan kun ga an fitar da shi ku karanta ko da baku siya ba, me zai hana ku ji tausayin wahalar typing ɗin da muke yini yi ku zo da ɗaiɗaya ko a ƙungiyance muyi muku sauƙin farashi don ku samu damar karanta littafin a paid group ba tare da fargabar Allah ya isar mu za ta bi ku ko baza ta bi ku ba? Idan kun shirya bin wannan tsarin da na zo da shi ku tuntuɓe ni ta wannan lambar ***.
2)
Ɗaya daga cikin halaye masu burgewa tattare da Malam Balarabe shi ne, yana da faɗa idan an taɓo shi, amma sam ba shi da riƙo, yanzunnan zai fututtuke yai ta zuba bala'i kamar bai san daga inda mutum ya fito ba, amma in sha Allahu a bashi mintuna goma ƙwarara, tsaf zai manta wani saɓani ya shiga tsakaninku.
Mafiyawancin lokuta ma shi da kanshi zai fara jan mutum da wasa da dariya, har ya haɗa da yima mutum tsokana idan ya ga abokin faɗan nasa na ɗaure fuska. Irin haka ne yanzu ya faru, yana fitowa daga wanka ya ga Ramatu zaune a ƙasa cikin turakarsa ta zuba tagumi da hannu bibiyu, idanunta sun ƙara kaɗawa sun yi ja sosai, kamar bai san ɓacin ran me take yi ba sai ya fara jan ta da tsokana.
"Ummm na ce ba Ramatu, wai ni kam yau sarautar uwargidan ce ta motsa kika murɗa kambu kika dama koko ba tare da kin soya mana ƙosai ba?"
Fuskarsa cike da fara'a yake maganar.
A hankali ta ɗago idanunta ta zuba cikin nasa, ko da taga irin fara'ar da ke fuskarsa sam zuciyarta bai sauka ba. A madadin ma ta ji dama-dama sai wani ƙarin ɓacin ran ne ya turnuƙeta, a zuciyarta take sake girmama rainin wayau irinna Malam. Ji dai cin mutuncin da yayi mata yanzunnan, ba kuma akan kowa ba sai akan Binta, Bintan da jiya - jiya ta shigo cikin gidannan, amma saboda tsabar zalunci da son zuciya irinna Malam a fakaice sai ya dinga ci mata mutunci akan abinda bai taka kara ya karya ba, don kawai ya nuna mata yanzu fa ludayin Binta ne ke kan dawo a zuciyarsa.
Kuma saboda ya raina mata wayau sai bayan ya gama wulaƙanta ta sannan zai zo yana mata dariya. Saboda ya maida ita jaka wacce bata san ciwon kanta ba. Duk yadda taso sakin fuskarta kasawa tayi, maganganun da ya faɗa mata sai maimaituwa suke a kunnuwanta kamar yanzu ne ya gama faɗa mata su.
Tayi ƙwafa a zuciya, a fili kuma sai taso tayi dariyar yaƙe, dariyar da a maimakon ya fito sai ya saka fuskarta ya wani yanƙwane kamar za ta saka kuka.
Sai da ta haɗiyi wani miyau mai kauri da ɗaci, sannan ta buɗe baki daƙyar ta ce
"Yau injin Tsahare ne yake ba ta matsala. Tun sassafe Zakiyya da Hasiya suka kai niƙan ƙosan har yanzu basu dawo ba, ko da na aika Ruƙayya akan cewa idan babu niƙan su ɗauka su kai wani gidan sai Tsaharen ta ce ayi haƙuri, ta bada uzurin gyaran injin take yi yanzu za ta gama. Na ji ka ce sammakon zuwa gona za kayi shi yasa na kawo maka Kokon ka fara sha, ga ɗumame can na ɗora a wuta..."
"Babu damuwa, Kokon ma ya isa. Idan na fita zan tsaya gidan Kuluwa in ci waina kafin in wuce gona."
"Uhmmm!"
Ramatu ta amsa a taƙaice. Ganin ya juya baya yana ciro kayan da zai saka a cikin akwatinsa na ƙarfe yasa ta galla ma bayansa harara. Tana ganin zai juyo tayi gaggawar daidaita yanayin fuskarta.
Shirinsa ya cigaba da yi hankali kwance. Sai da ya gama tsaf, ya naɗa farin rawaninsa da ya ɗan fara shan jiki a matsayinsa na Sarkin Noma, sannan ya zauna a kan kujera ya buɗe kwanon Kokon. Yadda ta ciko kwanon da koko cike taf har baki yasa shi kallonta baki buɗe, kamar zaiyi magana, sai kuma yayi shiru.
Da taka-tsantsan ya ɗaga kwanon Kokon ya kai bakinsa ya kurɓa, da ƙyar ya haɗiye saboda yadda kokon yayi tsami sosai, ya sake kurɓa a karo na biyu, nan ma ya haɗiye da ƙyar. Kamar zai cigaba da shan kokon sai kuma ya ajiye a ɗan fusace, har sai da kwanon yayi tangal-tangal kamar zai zube sai kuma bai zube ba.
Fuskarsa babu walwala ko kaɗan ya ce
"Amma saboda Allah Ramatu sau nawa ina miki magana akan wannan tsamiyar da kike cikawa a cikin koko? Wai ma na zaci shi koko idan za a dama ba ya buƙatar tsamiya? Ko ba haka ba ma tun kwanakin baya na faɗa miki Binta ba ta son tsamin nan, ƙwarnafi yake saka ta saboda cikin da yake jikinta. Saboda Allah ko da ma ya zama dole sai kin saka tsamiyar me yasa baza ki zuba kaɗan ba?"
"Yanzu shi kenan Malam ni komai nayi ban iya ba indai akan Binta da cikin jikinta ne?"
Ramatu tayi maganar muryarta na rawa, bayan ta yi iya ƙoƙarinta ta kasa danne zuciyarta tayi masa shiru kamar yadda ta saba. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, cikin ƙanƙanin lokaci hawaye suka fara tseren sauka daga idanunta. Bakinta na rawa ta cigaba da magana da sakin maganganun da suka daɗe suna nuƙurƙusarta a zuciya.
"Shi kenan? Don kawai tana da ciki? Sai kace a kanta aka fara yi maka haihuwa a gidannan? Kafin ita ni yara nawa na haifa maka? Ko kuwa don ni Allah bai bani haihuwar ɗa namiji ba sai in zama bolar zuba shara a gurinku? To kar ka manta Malam, haihuwar ɗa namiji ba ni ce zan iya ba kaina ba. Da ina da ikon ba kaina na rantse da Allah bazan taɓa haifar ƴa mace ba..."
Shurar takalmansa yayi ya saka, tana cikin sakin baƙaƙen maganganun da suka sa ransa yayi mummunan ɓaci ya fice daga ɗakin, ba tare da ya biye mata ba. Duk da dai da farko Kamar zai biye mata suyi babu daɗi, amma da ya tuna kusan kullum irin nasihar da Hajiya take yawan yi masa akan ya dinga ƙoƙarin dannar zuciyarsa kar yayi magana idan yana cikin maɗaukakin ɓacin rai, sai kawai ya ga fita daga ɗakin shi ne mafi alkhairi. Don Wallahi a yadda ransa yake ɓacennan zai iya rufe Ramatu da duka, mummunar ɗabi'ar da duk tsawon shekaru goma sha uku da yayi tare da ita bai taɓa yi ba.
Ko bayan fitarsa bata daina sakin maganganu ba, sai da ta gama zazzage cikinta tas sannan ta ƙara fashewa da ƙaƙƙarfan kuka, kamar wata ƙaramar yarinya. Sa'arta ɗaya ɗakunansu na nesa kaɗan da turakar Malam, amma tabbas da sai yara da Binta sun jiyo kukanta.
Tsaf ta share hawayenta, ta miƙe ta fice daga ɗakin ba tare da ta bi ta kan kwanon Kokon da Malam ya ƙi sha ba.
"Innanmu ga niƙan, ta ce wai kiyi haƙuri Injin ne..."
"Je ki ajiye min a madafa, ina zuwa."
Ta katse Zakiyya a fusace, kai tsaye ta nufi ɗakin Binta, zuciyarta na wani irin tafarfasa kamar za ta kama da wuta.
Saboda tsananin ɓacin rai ko sallama bata samu sararin yi ba, yaye labulen tayi a fusace ta shiga cikin ɗakin, karaf idanunta ya faɗa cikin na Binta, tana zaune a tsakar ɗaki da kofin shayi a gabanta tana sha, ga wani ƙaton biredi ajiye a gefe ɗaya. Ga kuma babban gwangwanin madarar gari da robar Bonvita ajiye a gefe ɗaya.
Abinda ya ƙara ninka ɓacin ranta kenan, wato su saboda rainin wayau da zalunci sai Malam ya tasa su gaba da dauron koko da waken ƙosai, ita kuma Matar so ƴar Gwal ya siya mata kayan shayi tana sha duk sadda take so. Ah lallai, ba damuwa.
Tayi ƙwafa mai ƙarfi. Ta balla ma Binta harara da jajayen idanunta kamar za su faɗo ƙasa. Da murya mai ƙaraji ta ce
"Ke Binta?"
"Na'am! Yaya."
Ta amsa da sanyin murya. Jikinta a ɗarare, don Allah ya sani tana tsoron Allah tana tsoron masifar Ramatu.
"Gani na zo ki faɗa min abinda kike nufi da ni a gidannan. Ca nake tun satin da ya wuce na gindaya miki dokar zuwa gaishe da Malam ki nemi guri ki zauna kamar ranar girkinki?"
"Eh! Kin hana ni."
Ta sake amsawa da sanyin murya. A zuciyarta tana jin babu daɗi na yadda kusan ko wane lokaci ita ke fara janyo abinda zai kawo cece kuce tsakaninta da Yaya Ramatu. To amma ita ma ya zata yi? Duk yadda take so ta kiyaye Malam ba ya bata damar hakan, shi da kanshi yake hana ta tafiya, ita kuma baza ta iya saɓa ma umarninshi don kawai ta faranta ran Ramatu ba.
"To faɗa min. Raini ne da wulaƙanci ke sa idan kika je mishi barka da asubah ranar girki na kike daɗewa? Ko kuwa iskanci ne da son ki gwada min ke ƴar bariki..."
Hankalin Binta a tashe ta katse Ramatu ta fara magana cikin rawar murya.
"Kiyi haƙuri Yaya Ramatu. Wallahi duk abin bai kai nan ba. Allah ya sani ba na aikata wani abu komai ƙanƙantarsa a gidannan don in cusguna miki. Kiyi haƙuri don Allah..."
"Na ƙi inyi haƙurin, da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bayar? Munafuka annamimiya da an fara magana sai ki dinga wani sussunnar da kai kina magana sanyi-sanyi ke ga ki ta Allah. To bari ki ji in faɗa miki, ba dai wannan cikin da kike ƙaryar za ki haifi ɗa namiji ke sa kina zuba min iko da mulkin mallakar da kika ga dama ba? Mu zuba ni da ke, za ki gani. Shege ka fasa, ɗan halak sai yanka."
A karo na biyu ta sake jan wani ƙaƙƙarfan ƙwafa, ta kaɗa kai ta fice daga cikin ɗakin.
Saboda haushi da baƙin ciki ƙosan da bata tsaya soyawa ba kenan. Daman rana ta fara yi, haka ta rarraba ma yara koko, ta zuba a kofin silba ko rufewa bata yi ba ta aika ma da Hajiya sasanta. Ƙullun ƙosan kuwa ta tsula mishi ruwa, ta zuba maggi da mai ta juya ta zuzzuba a gwangwanin alale ta ɗora akan wuta.
Bata jira ya nuna ba ta bar ma babbar ƴarta Zainab mai kimanin shekaru goma sha biyu ta fice zuwa gidan mahaifinta Malam Musa.
******
"Ramatu tun ɗazu kin tasa ni gaba kina ta kuka, idan baza kiyi magana ba don Allah ki fita ki bani guri. Kinga yanzu ƙarfe goma da rabi, ɗalibai sun gama dawowa daga bara za mu fara karatu..."
Cikin kuka, ta fara kora ma mahaifinta bayanin duk abinda ke faruwa a gidan aurenta, tun daga sadda Malam Balarabe ya auro Binta, da irin romon wulaƙancin da take sharɓa kamar ba auren soyayya suka yi da Malam ɗin ba.
"Ni babban damuwata Baba haihuwar Ɗa Namiji da aka tabbatar za tayi. Da farko ko da ta samu ciki ban wani ɗaɗara kaina da ƙasa ba, saboda na san ita ma za ta iya haifar ƴa mace, kuma watakila haihuwar ƴaƴa matan a gurin Malam yake, don haka na kawo idanu na zuba ma rawar ƙafar da Malam yake yi, a gefe guda ina ta addu'a ina haɗawa da sadaka Allah yasa ta haifi ƴa mace in ga yadda Malam zaiyi. Amma kuma wannan tunanin nawa ya kau ne bayan ta je babban asibiti a cikin binni an ɗauki hoton cikinta sati biyu da suka wuce. Likita ya tabbatar mata da Ɗa namiji za ta haifa Baba..."
Tana zuwa nan a maganarta ta ƙara fashewa da kuka, cikin kukan, ta cigaba da magana tana share majina da gefen hijabinta.
"Tun da ta dawo da takardar bayanin likita, Mu'azu ɗan gidan Malam Iliya ya karanta ma Malam cewa an tabbatar namiji ne a cikin Binta, Malam ya ƙarasa juya min baya gaba ɗaya. A fili yake min gori kan ƴaƴa mata da na haifa na cika mishi gida da su kamar ni na ba kaina haihuwarsu"
Ta kai ƙarshen maganganunta da labarin duk irin baƙaƙen maganganun da Malam ya caccaɓa mata a yau.
"Subhanallahi! Yanzu shi Malam Balarabe da iliminsa yake miki gori akan haihuwar ƴaƴa mata? Kuma in ba jahilci ba ta ina Likita zai tabbatar da abinda Allah ya ɓoye? Su likitocin da suka ɗauki hoton cikin suna da ilimin gaibu kenan da za su ce ɗa namiji za ta haifa?"
Malam Musa yayi maganganun da ɓacin rai a fuskarsa.
"Baba ka san ita Binta aurenta na farko a birni tayi, kuma ta haifi yara uku duk maza kafin auren ya mutu. To shi ne ta ce ma Malam akwai wani babban asibiti a birni da take zuwa awo, suna da wani inji da suke ɗaukar hoton ciki da mahaifar mace, duk abinda yake ciki mace ko namiji za su gani su faɗa, har ranar da za ta haihu ma suna faɗe, kuma bata taɓa tsallake ranar ba. Shi ne jikinsa na rawa ya bata kuɗaɗe masu yawa ta je asibitin aka ɗauki hoton, sun ma faɗa mata haihuwarta saura kwanaki goma sha tara."
Shiru Malam Musa yayi yana jujjuya maganganun da Ramatu ta faɗa mishi a zuciyarsa. Ransa ya ɓaci sosai da abinda ta faɗa mishi Malam Balarabe Sarkin noma yana yi mata, musamman gori akan ƴaƴa mata wanda ba laifinta bane. Can kuma sai ya ce
"Babu komai. Ki koma gida, ki kwantar da hankalinki. Da yaddar Allah ƴaƴa matan da yake gudu su ne za su zamo mishi ababen alfahari. Na san duk wannan abin yana yi ne don zai samu magaji, dama kwanakin baya can Bashari yazo yana bani labarin irin sa'insar da ya gudana tsakanin Malam Haruna da shi Balarabe, kin san tunda aka naɗa Balarabe a matsayin Sarkin Noman garinnan suka daina shan inuwa ɗaya da juna. Malam Haruna yana ganin shi yafi cancanta da muƙamin, tunda a shekarun baya can duk garinnan babu wanda yake noma buhunan hatsin da yake nomawa, duka-duka shekaru uku ne da Balarabe ya zarce shi a yawan buhunan hatsi, sai kuma aka yi sa'a a lokacin Mai gari zai naɗa muƙamin Sarkin Noma sai kawai ya ba Balarabe tunda Amininsa ne.
A yadda Bashari ya faɗa min, a wannan ranar da suka yi sa'insa a maganganun da Malam Haruna ya goranta ma Balarabe har da gorin ko ya faɗi ya mutu bashi da magaji. Ƴaƴansa duk mata ne, yana mutuwa labarin nomansa da muƙaminsa na Sarkin noma zai zo ƙarshe. Don haka dole ki ga Balarabe yana rawar jiki akan ɗa namijin da za a haifa mishi, amma kuma wannan bai zama hujja da zai wulaƙanta ki da ƴaƴanki ba."
Ya sake yin shiru a karo na biyu. Can sai kuma ya ce
"Idan ya san wata ai bai san wata ba. Ki je gida kawai, zan yi ma tufkar hanci."
"Amma Baba..."
"Haba Ramatu. Daɗina da ke gajan haƙuri, ba ni na ce ki je gida ba?"
Ta gyaɗa mishi kai.
"To ki je kawai. Na san matakin da zan ɗauka. Ki kwantar da hankalinki kawai ki zuba idanu ki sha kallo."
"To shi kenan Baba. Na gode."
Tayi maganar da ɗan murmushi a fuskarta.
Har ta miƙe za ta tafi ta isa gurin bakin ƙofa ya kira sunanta.
"Ramatu?"
"Na'am Baba."
Ta amsa haɗe da waigowa tana kallonsa.
"Nan da kwanaki uku zan aiko Haladu ya kawo miki saƙo. Ki kwance a leda ki jefa shi a Salgan gidanku. Ina fatan kowa na cikin gidanku anan yake bahaya?"
"Eh Baba."
"Madallah. Ki jefa kawai a cikin salgan ki je ki cigaba da harkokinki."
"To Baba. Allah ya ƙara girma."
Tayi masa addu'ar da farin ciki sosai a fuskarta.
"Amin ya Allah."
Yana kallonta da sakakkiyar fuska har ta fice daga ɗakin.
Daga nan shagon waje na mahaifinta inda yake ganawa da baƙi kuma yana ba manyan gardawansa karatu ko cikin gidansu bata shiga ba ta kama hanyar gida. Tana tafe tana tunanin irin matakin da Babanta zai ɗauka akan lamarin, duk da dai bai faɗa mata ga abinda zai yi ba, ta sani ko ma menene abu ne da zai ɗaga darajarta da ta ƴaƴanta a gidan Malam Balarabe.