BA NI DA IKO...

BABI NA SHIDA

by @fareedaabdallah

6)

Kwanaki bakwai da dawowar Ramatu cikin gidan, sannu a hankali al'amura suka fara canjawa. Komai ya fara tafiya yadda Ramatu take so, muƙaminta na Uwargida mai ƙarfin ikon faɗa aji ko da rai ba ya so da ta rasa a baya, sannu a hankali a yanzu take samunshi.

Mal Balarabe ya fara zama mata Raƙumi da Akala, duk abinda ta ce mishi ko da a zuciyarsa ba ya so haka yake aikatawa. A hakanma wai don tana tsoron Hajiya, wacce ta ƙara kawo idanu sosai ta zuba ma al'amarin zamantakewar tasu. Abinda da sam ba ta da shi.

Shi yasa Ramatu take bin komai cikin siyasa da iya zaman duniya. A ɓangaren Binta kuwa ido ta kawo ta zuba ma al'amarin, a zuciyarta take mamakin yadda komai na al'amarin Malam ya tasamma sauyawa lokaci ɗaya.

Idan ba gizo idanunta ke mata ba ma sai take ganin kamar Malam yana jin tsoron Ramatu ne, abinda yasa ta ce tsoron Ramatu yake ji shi ne, bayan ta gama kwanaki biyun girkinta cikin rashin daɗin rai saboda abinda ya faru waccan ranar. Ko da girkin Ramatu ya shiga, ta shirya zuwa gaishe da Malam a turakarsa kamar yadda ya kafa musu dokar duk wacce ba ita ke da girki ba idan gari ya waye za ta same shi a turaka su gaisa, idan tana da wata buƙata ma duk a wannan lokacin za ta isar mishi.

Shi kuma daman ba ya shiga ɗakunansu ya duba lafiyarsu sai idan ya shirya zai fita Gona ko kasuwa. Tana isa ƙofar turakar Malam tun daga kicin Ramatu ta daka mata wata gigitacciyar tsawar da yasa ta dakata babu shiri.

Tinƙis-tinƙis ta tako daga kicin tana aika mata wani mugun kallo kamar za ta rufe ta da duka. Tana isa kusa da ita bata yi wata-wata ba ta finciki hijabinta da ƙarfi ta ja ta baya, tayi taga-taga kamar za ta faɗi, daƙyar ta iya tsayawa kan ƙafafunta tana mayar da numfashi cikin firgici.

"Tooo rasa kunya ɓeran tanka... Ina kike ƙoƙarin zuwa? Ai daman jiranki nake yi."

Ta tofar da miyau a gefen ƙafafun Binta ta cigaba da cewa!

"Au! Ashe fa baki da labari duk waɗannan dokokin na zalunci da aka kafa su saboda ke na rushe su ko?"

Tayi wata dariya ta rainin hankali da cin galaba, sannan ta leƙa cikin turakar ta ce da Malam

"Ai sai ka fito ka faɗa mata wannan gaisuwar na safe daga yau ka soke shi. Sannan kuma in dai ba ranar girkinta ba baza ka je ɗakinta wani duba lafiyarta ba, bazan ƙara yarda a fake da guzuma a dinga harbin karsana ba. Sannan abinci da take aje maka a ɗakinta in dai ranar girkinta ne shi ma wannan dole ta daina shi a gidannan. Ah to! A bi doka a zauna lafiya, maza fito ka tisa mata maganganun da na faɗa, don naga kamar bata yarda ba."

Abin mamakin da yasa Binta ta kusa kifewa shi ne yadda Malam ya fito daga turakar tasa, sannan kuma ya sake maimaita mata maganganun Ramatu. Kanshi a ƙasa, ya kasa haɗa ido da ita sam!

"Yauwa! Kin dai ji daga bakin wanda ya ajiye ki. Don haka idan kunne ya ji jiki ya tsira. Malama sai a ja tsinin ciki a bar nan ko?"

Daƙyar Binta ta iya kai kanta ɗaki saboda mamaki da tashin hankali. A wannan ranar, haka ta yini cikin fargaba da damuwa, zuciyarta cike da fargaba da tsoron kar su cigaba da tafiya a irin wannan baƙon yanayi da ya fuskanto su, ta san in dai aka ce a haka za a cigaba da tafiya lallai akwai matsala.

Daga ƙarshe da taga tunani na neman yi mata illah a matsayinta na mai juna biyu sai kawai ta tattara tunanin komai ta aje a gefe ɗaya. Ta mayar da rayuwarta kaso sittin cikin ɗari zuwa sasan Hajiya. In dai ba ranar girkimta ba ba ta zama balle takaici ya dame ta.

*******

Larabar ƙarshen watan Safar na ko wace shekarar musulunci. Ita ce ranar da Bahaushe ke kira da Larabgana. A cewar wasu a wannan ranar ne Allah SWT yake saukar da duk wani bala'i da zai faru a wannan shekarar. Amma fa a zahirin gaskiya wannan magana bata inganta ba, wasu malamai sun ce molonka ce kawai ta Malam Bahaushe.

Shi yasa a al'adar bahaushe yake kiyaye wannan rana sosai. A shekarun baya, duk wasu muhimman al'amura ko sha'ani basa aikata shi a wannan ranar. Saboda sun camfa ta a matsayin rana ce ta bala'i da masifu.

A maimakon aikata wasu shagulgula ma sai ko wani magidanci ya killace iyalansa. Bayan rufe duk wani abu da yake a buɗe saboda tsoron kar guguwar bala'i ta zo ta afka musu. A gidajen masu ilimi suna yin alwala ne su da iyalansu suyi sallolin nafila, su ɗauki lokaci mai tsawo suna addu'o'i. Wasu gidajen kuma a zamanin can baya har gishiri suke jiƙawa su sha suyi wanka da iyalansu. A cewarsu wannan kariya ce daga masifa da bala'i.

A daren talata, wayewar garin Larabgana. A wannan dare ne naƙuda ya tasar ma Binta gadan-gadan. Sai kuma aka yi sa'a a wannan ranar girkinta ne. Da tashin hankali sosai a fuskar Malam ya je ya sanar ma da Hajiya halin da ake ciki.

Har zai wuce ɗakin Ramatu, sai kuma yayi tunanin ya kamata ya faɗa mata. Ya daɗe yana buga ƙofar kafin ta amsa, cikin bambamin masifa ta fara tambayar wanene ke buga mata ƙofa a wannan dare?

"Ni ne. Kiyi haƙuri, Daman zan faɗa miki ne Binta kamar naƙuda take yi. Yanzu zan je can gidan Alh Inusa ne in roƙe shi alfarmar ya taimaka ya ɗauko motarsa mu kaita asibitin gwamnati..."

"Asibiti kuma? Wani irin asibiti ana zaune ƙalau?"

Buff! Sai ga ta ta buɗe ƙofa ta fito waje, daga ita sai ɗaurin ƙirji.

Cikin masifa ta ce

"Kai Malam kalleni nan, sa idonka a cikin nawa."

A ɗan tsorace ya ɗaga idanu yana kallonta kamar yadda tayi masa umarni.

Ƙanƙance idanuwanta tayi tana ƙara tsuke fuskarta ta cigaba da magana.

"Ni da nake uwar gidanka haihuwa nawa nayi tare da kai?"

"Shida"

Ya amsa cikin sanyin murya.

"Duk haife-haifen da nayi maka akwai wacce na taɓa yi a asibiti?"

"A'a!"

Ya sake amsawa a hankali, zuciyarsa cike da fargaba.

Ɗaurin zaninta ta kwance ta banƙaro mishi cikakkun mamunanta amma sun kwanta har ciki, tayi mishi far da idanunta sannan ta gyara ɗaurin zanen ta cigaba da magana

"Yauwa! to tunda ban taɓa haihuwa a asibiti ba babu matar da za ka auro don za ta haihu a ce sai an kaita asibiti. Kana ji na!?"

Tayi masa tambayar da tsawa-tsawa.

"Eh! Eh! Na ji."

Ya amsa da rawa-rawar baki.

"Yauwa Balarabena..."

Ta ɗan bubbuga kafaɗunsa tana dariya.

"Yanzu dai je ka da sauri, duk yadda Hajiya za ta matsa maka akan ku je asibiti kar ka yarda. Ta haihu a gida, kamar yadda nake haihuwa. Kuma tana haihuwa ka zo ka sanar min da abinda ta haifa."

"Toh!"

Ya amsa. Sannan ya wuce zungwui-zungwui zuwa turakarsa, inda ya bar Hajiya da Binta tana gurmususu.

Yana isa bakin ƙofa ya tarar da Hajiya ta tallabo Binta suna fitowa daga ɗakin.

"Hajiya lafiya? Ina za ku je?"

Ya tambayeta da sauri, idanunsa cikin na Binta, da tausayi yake kallon yadda ta haɗa zufa tayi kashirɓin. Sai cije laɓɓan bakinta take yi da ƙarfi tana sakin nishin wahala.

"Zan shirya ta ne mu tafi asibiti. Ka samo motar?"

Hajiya tayi maganar tana yi mishi wani kallo, kamar bata ji wani ɓangare na maganganun da Ramatu tayi mishi ba.

Yayi shiru cikin tunanin umarnin da Ramatu tayi mishi, kuma ko kaɗan ba ya son saɓa mata. Ba ma shi da ƙwarin gwuiwar da har za tayi mishi umarni ya saɓa. Da sanyin murya ya ce

"Ai Hajiya motar nan bai samu ba. Haƙuri kawai za muyi... Allah ya sauke ta lafiya... Ta haihu a gida... Ai kinga ma ko Ramatu duk haihuwarta a gida take yi..."

Kukan azaba da Binta ta fashe da shi, sannan ta tafi gaba ɗaya za ta duƙe a ƙasa yasa shi da Hajiya suka yi saurin tallafota suka miƙar da ita tsaye suna jera mata sannu.

"Yi sauri Balarabe kama min ita muje can ɗakinta. Ina ga haihuwar ta taho gadan-gadan. Muje can ɗin na gama haɗa duk abinda za ta buƙata."

"To Hajiya. Allah ya raba lafiya.

Sannu a hankali ya kamata suna tafe tana hutawa idan naƙudar ya murɗa mata har suka isa ɗakinta. Can gefe guda a uwar ɗakin Hajiya ta shimfiɗa babban ledar da ta ɗauko a ɗakinta. Tun zamanin haife-haifen Ramatu ta tanade ta.

A yadda Hajiya tayi tunani da farko, ganin yadda naƙudar ke tashi babu wani lafawa tunda suka isa ɗakin ta zaci cikin ƙaƙanin lokaci Binta za ta haihu. Sai dai kuma wankin hula yana nema ya kaisu dare, haihuwa kama-kama sai kuma aji ɗif!

Suna cikin wannan halin har sanyin asubah ya fara kawo jiki. Gaba ɗaya Binta ta galabaita. Sau huɗu Malam yana yi mata tofi a ruwa tana shanyewa amma babu labari. An jiƙa mata hannu ya fi sau biyar, shi ma dai ba labari.

Cikin damuwa da tashin hankali Hajiya ta fita falo gurin Mal Balarabe, ta ce

"Balarabe, gaskiya ina ga tunda dai haihuwar nan ta yi jinkiri da yawa ko za ka je ka kira mana Anty Jimmalo? Ka ga yanzu zamanin ya canja, haihuwar ma a zamanance ake yi. Gaskiya ba fata nake yi ba amma ina jin tsoron afkuwar matsala akan haihuwar nan, tunda ka ga yarinyar nan ta galabaita. Wata kila Jimmalo baza ta rasa taimakon da za ta bata nasu na Likitoci ba."

"To shi kenan Hajiya. Dama acan asibiti ita Jimmalon ce take yi mata awo. Bari a kira ta."

Da saurin gaske ya fice daga ɗakin.

Duk da nisan da ke tsakanin gidansu da na Aunty Jimmalo nan da nan ya isa gidan. Yana ƙwanƙwasa ƙofar gidan a zuciyarsa yake tunanin yadda a baya suka ƙyamaci karatun Nurse da Jimmalon ta jajurce sai ta yi, musamman da ya kasance bata fara karatun ba sai da tayi aure. Da yake mijinta Alhaji Mamuda wayayyan mutum ne, haka ya bata goyon baya da ƙarfin jikinsa da na aljihu, da aurensa a kanta haka take tafiya can cikin birni karatu, ba ta komawa garin sai ƙarshen mako. Duk zagin da ake yi mata suka sa auduga suka toshe kunnuwansu, sai ga shi cikin hukuncin Allah bayan ta gama karatun na tsawon shekaru al'ummar ƙauyen ba ƙaramin moruwa suke yi da iliminta ba.

Mace ce mai kirki da sanin ya kamata, ko mutum bai da ko sisi haka za ta duba shi ko iyalinsa ta basu magani da allurai. Kuma duk tsawon dare idan aka kira ta karɓan haihuwa haka take tafiya ta bar yara da mai gidanta. Har zuwa sadda Allah yayi ma mijinta Alhaji Mamuda rasuwa, bawan Allah mutumin kirki, mai taimako da son al'umma, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa...

A daidai lokacin aka tambayi wanene daga can cikin zauren gidan, kuma cikin sa'a ita da kanta Jimmalon ne take tambayar.

"Hajiya ni ne... Sarkin noma, Malam Balarabe. Don girman Allah ki taimaka min yadda kika saba, Wallahi Binta ce tun farkon dare take naƙuda, amma har yanzu Allah bai kawo iyaka ba..."

"Subhanallahi! Jira ni, Ina zuwa."

Ta faɗa da sauri. Ko minti biyar ba'a yi ba ya ji ana buɗe ƙofar gidan.

"Mu je."

Suka kama hanya da saurin gaske.

Sun isa gidan daidai lokacin da Ladanin unguwar ya kwaɗa kiran sallar farko. Kamar shigar Aunty Jimmalo cikin ɗakin ake jira, wani ƙwayar magani guda ɗaya ta ɓallo ta saka mata a baki, naƙudar ta sake tasowa gadan-gadan babu lafawa.

Mintuna goma tsakani cikin hukuncin Allah haihuwar ta taho gaba ɗaya, wani ƙaƙƙarfan nishi da tayi abinda ke cikinta ya taho da mahaifa gaba ɗaya.

Ƙaƙƙarfan ƙaran kukan jariran da ya karaɗe ɗakunan gaba ɗaya shi ya isar ma da Hajiya da Malam da ke falo Binta ta haihu. A tare duk su biyun suka haɗa baki gurin cewa

"Alhamdulillahi."

Suka miƙe tsaye, jikkunansu babu inda ba ya rawa saboda farin ciki. Sai kuma Malam ya tafi ƙasa gaba ɗaya yayi sujadar godiya ga Allah.

Ita kuwa Hajiya cikin ɗakin ta shige, idanunta cike da ƙwallar farin ciki. Har lokacin bakinta bai daina hamdala da furta kyawawan kalaman yabo ga rabbil izzati da ya gajarta musu wahala ba. Abinda aka haifa yana hannun Aunty Jimmalo ta yanke masa cibiya.

"Sannu da ƙoƙari Jimmalo. Sannu sannu. Allah yayi miki albarka."

"Amin Hajiya."

Anty Jimmalo ta amsa da murmushi a fuskarta, lokaci ɗaya kuma ta fara goge ma jaririn jiki da Man Zaitun.

"Ma sha Allah! Tubarakallah! Da alamun wannan Sarkin noman da ƙarfinsa ya iso duniya."

Hajiya ta faɗa tana kallon ƙaton fari kar ɗin jaririn da ake goge ma jiki. Duk a tsammaninta namiji aka haifa.

Ɗan jimmm tayi cikin ɗaukewar numfashi na wasu ƴan sakanni bayan ta ji abinda Anty Jimmalo ta ce

"Hajiya wannan ba Sarkin noma bane, kishiya kika samu. Sarkin noman dai yana tafe in sha Allahu a haihuwa ta gaba."

A zabure, kuma cikin tashin hankali Binta da ta samu kanta da ƙyar ta yunƙuro daga kwance, idanunta a warwaje ta ce

"Anty da gaske mace na haifa ba namiji ba? Idan wasa kike min don Allah ki daina..."

"Wallahi da gaske mace kika haifa Binta. Ga ta nan ƙatuwa da ita Tubarakallah."

Anty Jimmalo ta faɗa ba tare da gane inda maganganun Binta suka dosa ba, domin ta share mata tantama ma sai ta ɗaga jaririyar da har lokacin take canyara kuka ta nuna mata matantakarta.

"Kin gani? Mace ce. Sai ki ƙara gode ma Allah da ya saukeki lafiya ba tare da wata babbar matsala ta faru ba. Ki saka mata albarka, da ɗa namiji da ƴa mace duka kyaututtuka ne daga Rabbil Izzati, kuma ko wane jinsi Allah ya baki fata da addu'ar da za kiyi shi ne Allah yasa mata albarka yasa mai jin ƙan iyaye ce."

"Hakane Jimmalo. Amin ya Allah."

Hajiya ta amsa cikin sanyin jiki. Sai kuma ta ƙarasa gurin Binta ta damƙo hannayenta tana kallon yadda idanunta suka cicciko da hawaye.

Murmushin ƙwarara gwuiwa tayi mata, sai kuma ta ce

"Ki ce Alhamdulillahi."

"Alhamdulillahi"

Binta ta maimaita, da saukar wasu zafafan hawaye a idanunta. Zuciyarta cike da wani irin ƙunci da fargaba.

Domin Allah ya sani ba mace ta tsammaci za ta haifa ba, duk da ta sani Likitoci basu san gaibu ba, amma bata taɓa tsammanin za a samu akasi a hoton da aka yi mata a can Kaduna ba.

Ko da wani ido Malam zai kalle ta da abinda ta haifa tunda ta kasa samar masa da cikar burinsa?

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi ala ni'imatihi tatimmus salihat"

Kalaman da ta samu bakinta da maimaitawa kenan, har zuwa lokacin da ta ji ƙuncin zuciyarta ya fara sassautawa bata daina maimaita su ba.

*****

Daƙyar, da jan ƙafafu Malam ya isa ɗakin Ramatu, bayan kunnuwansa sun jiyo masa munanan maganganun da bai tsammaci jin su ba dangane da abinda aka haifa ba.

A bakin ƙofarta ya tarar da ita. Fuskarnan a ɗaure katamau, tunda ta jiyo kukan Jariri har cikin ɗakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye. Hankalinta a tashe, take ta zurga-zurga tsakanin cikin ɗaki da ƙofar ɗaki, a fili take addu'ar Allah yasa ba namiji Binta ta haifa ba, idan kuma namiji ne Allah ya ɗauki rayuwar jaririn da ta uwarsa da gaggawa.

"Me ta haifa?"

Ta tambayi Malam da fargaba mai tsanani.

"Mmmmma ce."

Ya amsa mata daƙyar, kuma a rarrabe. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajur.

Nannauyar ƙatuwar ajiyar zuciyar da Ramatu ta sauke yasa shi ɗaga idanu yana kallonta.

"Taɓɗijan! Lallai Malam ka ga ta kanka. Inna lillahi..."

Tayi maganar tana kama haɓa, da kakabi cikin yanayin mamaki da tashin hankali.

Shi dai Malam har lokacin kallonta yake yi, yana jin duk maganganunta tamkar an buɗe zuciyarsa an zaunar da su daram!

"To bari ka ji... Ba baki nake maka ba, amma ina tabbatar maka da an haifa maka bala'i da masifa a cikin gidanka. Yau ranar Larabgana... Sannan namijin da aka gama maka ƙarya da cika bakin za a haifa ba'a haifa ba, aka haifo mace, macen ma a rasa ranar da za'a haifeta sai ranar da Allah yake saukar da duk bala'in da za su faru a wannan shekarar. Lallai kayi ta kanka Malam, domin ga taka bala'in nan ta fara sauka."

Tana gama jero mishi munanan maganganun, masu kama da saukar ruwan dalma a zuciyarsa ta shige ɗakinta da sauri ta rufo ƙofa, ba tare da tunanin mummunan halin da zai iya shiga ba.