RUFAFFEN DUMA

54

by @khairatup01

RD
54

A cikin mota kuwa hannayenta biyu ya kama yace "Are you okey?" Ta gyaɗa masa kai amma ta tsorata da wanann mutumin da ace ya kama wuyan ta fa? Murɗe mata wuyan zai yi ko kuma kawai shaƙa zai kai mata? Tuno irin izayar ma da zata sha kawai ya saka ta kulle ido ta cukuikuye rigar Muhammad da ke kwance take a kan ƙirjin sa. 

Hannunsa ya saka yan shafa bayanta a hankali yana lallaɓa ta tayi shiru ba abinda zai faru an kama shi ai kuma yana tare da ita ba zai bari a yi mata komai ba. Suna isa gida da kan sa ya haɗa mata tea da biscuits ya bata ta ci, sai da ya tabbatar da ta cinye tas ta shanye tea ɗin gabaɗaya sannan ya bar ta. Maganin bacci ya ɓallo a wayence ya bata ta sha a matsayin maganin ciwon kai. Tana sha ko kwakwarar mintuna goma ba ayi ba bacci ya kwashe ta, ya zamar da ita ta kwanta ya kashe fitila ya bar mata ɗakin. 

Zaman da yayi tunanin yadda zai sa ido a kan masana fasahar nan ne, saboda yana ji a jikinsa za a iya Canjawa a ɓatar da gaskiya hakan ya saka dole ya soma tunanin wata mafitar bayan wannan can ya tuno da mafitar ɗaya ce Abdallah. Shi ne babban shaida na gani da ido a laifukan su na baya. Ya saka Abdurrahman ya tabbatar da ya ba wa expert ɗin nan manyan kuɗaɗe ta yadda ko da wasu daga cikin yaran su Waziri da ba a sani ba za su kai mai cin hanci ya ƙi yin na su aikin amma ya karɓi kuɗin su ta yadda zasu gamsu da zai yi na su aikin. Ya gaya masa da ya fito da shedar da Shehnaz tayi rikoding da kuma ita kan ta a kai ta kotu a zama na biyu. 

Wayarsa ce tayi ƙara ya duba sai ya ga maigadi ne ya kira shi. Yana ɗagawa yace "Ya akai yi?"

"Akwai baƙi Yallaɓai sun ce wai su yan'uwan Hajiya ne." 

Ya ɗan yi jim sai ya kunna tab ɗin gefensa wajen Camera ya duba sai ya ga Mama ce da Zubaida sai Yusuf. Ya maida wayar kan kunnen sa yace "Su shigo. Ka gayawa Isa ya shigo da su nan main palour."

"An gama Yallaɓai."

Ba a wani ɗauki dogon lokaci ba sai ga su sun shigo da sallama. Tashi yayi tsaye ya taro su. 

"Sannu da zuwa Mama."

"Sannun mu Muhammad."

Ya nuna musu wurin zama. Bakinsa ya kasa rufuwa da kansa ya tashi ya shiga kitchen ya kawo musu kayan kwalam ya ajiye. Mama tana murmushi ta tambaye shi ya gida ya kuma fama da jama'a. Yace komai lafiya lau.

Zubaida ce tayi ƙarfin halin tambayar Maryam. Yace "Wallahi bacci take yi. Tunda ta dawo bata yi wani baccin kirki ba muka tafi Abuja. Yau kuma aka soma sauraron ƙarar ga ciwuka a jikinta shi ya sa na bata maganin bacci ko ta huta na san ta da taurin kai ko da na dage ta kwanta ba zata kwanta ɗin ba."

Mama tace "Aiko ka kyauta kam don na san halin ta da kafiya ,da ba mamaki fa tana nan tana wani aikin yanzu bata son hutawa. Ban san lokacin da Maryam tayi baccin kirki ba ina ga in tana bacci ma tunani take akan wani aikin." aka sa dariya. 

"Mama ku ci wani abu mana."

Mama tace "A'a ba abinda zan ci Muhammad sai dai ko su." Ta faɗa tana kallonsu Yusuf.

Yusuf ma yace "Alhamdu lillahi a kashe nake kam."

"Mama saboda ni ba dan ki ba ne?" Hakan da ta ji ya faɗa ya sa ta ɗauki nama guda ta sa a baki ta tauna tace "Shi kenan?"

Yayi murmushi yace "kin fita Mama ko ba soso da sabulu."

Tayi murmushi kawai. Can kuma tace "Ba ma yi ta zama ba ko. Ku tashi mu tafi."

Muhammad yace "Haba dai tafiya Mama tun yanzu? Don Allah ki bari sai dare sai na maida ku da kaina ma. Ita ma na san zata so ta gan ku."

Mama fa tace ai bata san zancen ba sai sun tafi ba zasu zauna ba. 

Da ƙyar Muhammad ya lallaɓa su suka yarda suka koma suka zauna. Barin masu aikinsa ya tafi yace ayi girki akwai baƙi a gidan.

*

Wai Waziri hadda ni Barau zaka ɓoye wa ɗaya fuskar ka? Ni za ka ƙo gayawa cewa kai ne Boss? Gaskiya ba zan yafe maka ba Wallahi!" Barau ya faɗa cike da fushi yana nuna Waziri.

Waziri kuwa ko a jikinsa wai don duniya ta shaida shi ne Boss kuma mallakin kungiyar su. Taɓe bakin sa ma yayi yace "Barau kai ne ka jawo mana wannan masifar har sirrin mu ya fallasu ya tonu a idon duniya, kai ne nan ka tuna mana asiri."

Barau ya daki kafaɗar Waziri yace "Ni kuma? Ni za ka ɗora wa laifi? Waye ma ya koya min duk wani iskanci da cin amanar ne? Ina zaman zamana a ƙauye ina noma ka jawo ni cikin wannan cakwakiyar kuma ka kulle ni ka ƙi gaya min waye wanda muke jin maganarsa kamar yadda muke son numfashin mu ashe kai ne. Tir da kai Waziri. Kana kallo na ga samu na ga rashi. Na samu kujerar Gwamna amma an tsige ni wai ni kuwa waye ya kai ni asara ne a duniyar nan? Na zama asarare ,bankadadde. Na kashe 'yata saboda kar na rasa kujerar nan ashe a banza wai kai Waziri a ciki ma kai wa ya san ka ne? Don mugunta komai da suna na da sa hannuna ake yi , kowanne asusun da suna na aka buɗe. Ni sai yanzu ma ƙwaƙwalwarta ta hasko min abinda kake nufi wato in mutu ni kadai ku kuma ku tsira ko? To Wallahi sai dai mu nutse dukanin mu in har zan nutse to tabbas dukan mu sai dai mu nutse tare can ƙasan ruwa. Ba zan tafi ni kaɗai ba. Komai ma ni nayi asarar sa ai."

Waziri ya tashi tsaye shi ma a fusace yace "Kai Barau ya ishe ka haka, nace ya ishe ka haka. An gaya maka ni ban yi asarar ba? Ba ka ganin Nimra an tsare ta ita ma ? Ba ka ganin Zuwaira zan bari ita kaɗai a duniyar nan ba. Na sani sai na yi gidan Yari amma ba tare da 'yata ba."

"Oh! Ni ne wawa da ɗora ni a kan keken ɓera ko? Ka koya min cewa kuɗi su ne kawai gaskiya duk wasu dangi ɗa ,mata iyaye duk bayansu ne kuɗi da mulki su ne kan gaba. Amma kai kana kukan an kama maka 'ya ni da ka zuga ni na kashe ta fa? Ni da ka saka na bawa nas allura ta kashe min Ayra fa? Ni hotiho ko?"

"Barau ba kai kaɗai ba ne a cikin wannan abin ba , muna da yawa me yasa su basa kuka sai kai? Ka ƙyale mu mana mu ji da ɗaya wato ɓacin sunan da muka samu. Mun bar wa iyalan mu abin kunyar da ba zai kankaru daga jikinmu ba."

Barau ya koma da gefe ya zauna a kan wani katako da aka yi kamar gado yana bin mutanen ɗakin da kallo ɗayan bayan ɗaya. Wasu kuma suna wani ɗakin saboda suna da yawa aƙalla yan kungiyar sun kai su hamsin kashi-kashi kowa da manufarsa, maza da mata. 

"Yanzu shi kenan suna, arziƙi, mutane ,mutuncin da muka ɗauki shekaru muna ginawa ya tashi a banza kenan? Kamar ƙiftawar ido ya zube kenan? Kenan mutane yanzu suna da lasisin da zasu iya ci mana mutunci ko? Sai a samu wani ma ya zage mu ido cikin ido ko?" Wani Aminu ya faɗa ɗan kasuwa ne.

"Shi kenan dogon buri ya kai mu ya baro mu ga shi kuma koma zero daga lamba ta ɗaya." Baita ya faɗa.

Wata da ake kira Christian tace "Boss! Shi kenan ba zaka iya yin komai ba? Shi kenan kana kallo za a tarwatsa mana rayuwar mu?"

Waziri ya kalle su yace "A magana ta gaskiya kowa ya yi ta kan sa kawai shi ne abinda zan iya faɗa. In ma da akwai wanda yake ganin zan iya yin wata dabarar to ya gane cewa ni nan na zama ban san komai ba, dukanin wasu dabara sun ƙare min ,sun kwance min. Da ina da wata dabarar da tuni ba a zo nan ba. Sannan da na fitar da Nimra. Hannun da yake kan mu kuma na ƙasar ƙetare ba zasu iya yi mana komai na taimako ba su dama policy din su kenan in an kama ka kayi ta kan ka su fa da zarar ka daina musu amfani su ma zasu watsar da kai. Kawai dai ku sani wannan tafiyar ta mu ce ta zo ƙarshe amma ba zai zama an daina aikata shi a duniya ba sai dai a sauya taku da kuma yan wasa ku ɗauka iya ka ƙarfin wasan namu kenan."

"Duk laifin ka ne Barau da ka ke cewa ana ajiye takardu saboda records ga shi nan records ɗin mu sun kai mu sun baro mu. Da ace ƙonawa muke yi da lafiya lau yanzu muna da hanyar ƙwatar kan mu amma yanzu ina ba zai yiwu ba. Tun farko babbar kuskuren ku da baku kashe su Paul ba kuka ajiye su gashi yanzu sun zame mana mashi a cikin idanuwan mu. Maryam kuwa ta zame mana barkono." Sule Imam ya faɗa yana jin haushin Barau.

Barau ya san gaskiya aka faɗa ga shi yanzu sun faɗa cikin tarko. Tuni ɗakin ya yi tsit kowa ya kame bakin sa. Yau wai su ne a cikin wannan ƙaramin ɗakin, ba ac ba fanka ba gado ba karida ba kujera ba, ba,ba ,ba ,ba ɗin ma tayi yawa.

*
Isha!

Yana shiga cikin ɗakin tana tashi. Zaunawa tayi tana miƙa idanuwanta a kulle. Kafin ta ɗire hannunta ya sure ta sama yana juyi da ita.

Kanta ta kama da ya yi mata nauyi tace "Wayyo Allah! Kai na zai faɗo Sadauki daina yi mini hajijiya don Allah Wayyo Allah!."

A hankali ya zamo da ita ya zaunar da ita kan sofa ɗin da ke kan gadon yana dariya. "Afuwa masoyiya. Kin tashi lafiya?"

Ta gyaɗa masa kai. Ya sa ƙaramin bakinsa ya kai mata sumba a kan goshi ,ya gangaro kan hancinta sai ya koma kan kumatun ta. Ita dai bata ce mai komai ba sai da ya yi nasarar sumbatar bakinta sannan ya sake ta. Tana dariya tace "Yau soyayya ake ji Mr?"

Kansa ya ɗora akan kafaɗar ta yace "Uhm!" 

Murmushi tayi ta ture kan sa ya ko danna mata maintsini a hannu ta ce "Wash, ka kashe ni Sadauki ka ɗago mini fata." Da sauri ya buɗe idanuwansa ya kamo hannun ya gani. Ya dungure mata kai yace "Lair" 

"Allah akwai zafi."
Ya sumbaci gun yace "Zai dai ai na love ne. Tashi kiyi wanka ki sauko palour ga su Mama fa tun yamma suke gidan nan kina bacci. Inyee sarauniyar Muhammadu Sageer."

Ta ware idanuwnta waje tace "Amma shi ne baka gaya min ba ka tsaya neman magana?"

"Yanzu na gaya miki." Ture kansa tayi daga kan cinyarsa ta . Tashi tayi da sauri ya shige banɗaki. Ya kwanta a tsakiyar gadon ya rungume filo yana murmushi.

A gurguje ta fito ta shirya. Sai da tayi sallah tukunna sannan ta sauka ƙasa. Tun daga benen farko ta hangi Mama a zaune kan one seater da Yaya Yusuf.

Da gudu ta sauka daga kan benen tace "Oyoyo Mama Oyoyo."

Mama tana dariya ta tashi tsaye ta rungume Maryam tace "Auta an manta da Mama."

"A'a Wallahi. Mama ba laifina ba ne." Suka zauna suka ci gaba da hira. Bakinta ya ƙi rufuwa. Sai suka koma hira a tsakanin su su uku Zubaida dai na kallonsu. Ita yanzu bata iya sakewa sosai saboda ta lura fa ta kamu da soyayyar Yusuf kunyar sa take ji duk da ta so ta gane kamar shi ma yana son ta don sai yayi ta kallonta in ta kama shi ya waske. Ta lura yana da tsananin jin kunya kuma ba mai son magana ba ne ba har gara ma in yana tare da Mama yana dadewa yana hira a falon shi ma sama-sama. Ita dai ta rasa yadda zata yi da wannan son da ya kamata.

Sun jima suna hira kafin suka ga dare ya soma sosai.. Nan Mama fa ta dage sai sun tafi dare yayi. Haka ba yadda ta iya ta hau sama ta gaya masa Mama zasu tafi. Ya saka yallabiya baƙa ya sauko ƙasa. Hannunsa dauke da wata ƙaramar leda fara da layi-layin baƙi a jiki. 

"Mama wai tafiya ba za ku kwana ba ko?"

Mama ta harare shi tace "In kwana a ina?"

"Mama a gidan Auta mana."

"Allah Ya kiyaye Muhammad. Mu dai mun yi nan."

"Ku tsaya mu sauke ku." Ya faɗa yana kallon Maryam yace "Ɗauko mayafi."
Da gudu ya haura sama ta zaro wani mayafi suka tafi kai su gida. A baya matan suka zauna shi kuma Yusuf a gaba suna ta hira har ya sauke su a gida. Daga can wani wuri ya kai ta suka sha ice cream ya sai mata shawarma suka koma gida a gajiye.