PAGE 10
by @sumy6163
💫💫RASHIN SANI 💫💫
STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).
Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.
Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.
PAGE 10
Aimana tana fita ta hango Mrs Rafi'at, ta karasa wurinta, sai taga ta miko mata kulan abinci mai kyau dashi, karba tayi ta mata godiya, anan take gaya mata gobe za'a kawo mata kayan abincin, sai ta rika dafawa itama, da to ta amsa mata ta shige.
Koda ta koma dakinsu ta samu su Hafsa suna jiranta tazo suci abinci, zama tayi sukaci tare, Hafsa ce tace "Kinga Aimana mu tare muke abincinmu muci tare, don mu biyu ne a dakinnnan ko last term ma, sai yanzu da muka zama uku da kika zo"
"Aimana tace, nima sai mu hada mu rikayi tare, tunda mun zama uku, sai daya tayi breakfast,daya tayi lunch, daya kuma tayi dinner,ya kukace?"
"Eh hakan ma yayi" cewar Hafsa.
Daga nan suka cigaba da hiransu tunda yau ba abun yi.
Washegari asabar suka shirya karfe tara, suka tafi ajin hadda, bayan an mata tadribi, sannan aka bata class dinda ya dace da ita, duk da dai ba karatunsu daya ba, kowa da suranda take.
Zuwa can aka turo kiranta, ta dauka Mrs Rafi'at ne, don ita ta kawo mata breakfast ma da safe.
Saidai me tana zuwa ta hango motan Daddy, duk da tana fushi dashi hakan bai hanata kara saurin tafiyarta ba don ta cimmasa da wuri, gani take kamar idan batayi sauri ba zai koma.
Baya cikin motar lokacin da ta isa wurin, kuma office na principal a kulle, kawai ta juya ta nufi office na Mrs Rafi'at.
Sallama tayi aka amsa tare da mata izinin shiga, tana shiga kuwa ta hango Daddy a zaune, da gudu taje ta fada a kansa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.
Daddy ya shiga rarrashinta,yana dan bubbuga bayanta alamun tayi shiru, dakyar ta tsagaita da kukan, sannan ta dago ta dubi Daddy tace...
"Daddy me yasa kuka barni a makaranta, me yasa bazan koma gida naga su Mama ba, Allah Daddy na bar rashinji, duk abunda aka hanani bazan sake yi ba, Daddy zan rika jin maganar Ku, don Allah Daddy ka tafi dani, kar ka barni anan.
Jikin Daddy yayi sanyi sosai amma haka ya daure yace "Aimana kiyi hakuri kinji diyata, ai kamar gobe ne zakiga kin koma gida, nidai abu daya nakeso dake, ki dage ki bawa mara da kunya, inason ne duk randa kikaje gida kowa yasha mamakin ki, so ki dage sosai kuma ki kwantar da hankalinki,kiyi karatu, and insha'Allah zan rika zuwa miki every month".
Haka Daddy yayi ta rarrashinta har dai daga baya ya shawo kanta, har ma ta mishi alkawarin zata dage tayi karatu, kodan tasa iyayenta alfahari da ita.
Daddy yaji dadi matuka ganin ta hakura ta kwantar da hankalinta, yace tazo suje mota yazo mata da suprise, ta kuwa bishi cike da zumudin son ganin wani suprise ne haka Daddy ya kawo Mata.
Suna zuwa kuwa Daddy ya bude back seat, me zata gani, Abdul ne a ciki yana hakimce yana game da wayar Daddy.
Ai yana ganinta da hanzari ya fito, suka rungume juna cike da farincikin ganin junansu, kafin daga baya Aimana ta janye,tace..
"Ya Abdul Kaine, Allah sarki dan'uwa rabin jiki, ina su Mama da Dada,meyasa kai kadai kazo?.
"Kai Aimana, surutu kam na nan har yanzu, to wanne zan fara amsawa".
"Duka", ta bashi amsa.
"Okay, na daya dai nine ba wani ba, na biyu kuma su Mama suna lafiya harma sunce in gaisheki, sannan in gaya miki sunyi kewarki, na uku kuma bansani ba, shikenan".
"Allah sarki, Mamana, nasan sai tafi kowa yin kewata, nima ina kewarsu, ina ya Kamal kuwa, meyasa baizo ba!"
"Ai kinsan Kamal yana makaranta, amma shima yace a gaisheki sosai, har tsaraba ya bayar in kawo miki".
"Dagaske kake, ya Kamal ya baka abu ka kawo min, don Allah nuna min, ka bani in gani, meyene ya baka ka kawo min" ta fadi cikin zumudin son ganin abinda Yayan nata ya bayar a kawo Mata.
"Relax mana yi a hankali, ai zan baki ne tunda na riga nazo dashi, bazan koma dashi ba".
Ya bude boot, ya shiga fito mata da tarkacenda suka zo mata dashi, kwalin indomie, sai couscous da macaroni da spaghetti duka kwali daya aka hada su, sai soyayyar mai da manja, ga kayan tea, harda karamin flask, da sauran tarkace, farinciki ya kama Aimana,duka wannan nata ne, ai ko wata biyu zatayi ba lallai ne ta iya cinyesu ba.
"Ya Abdul kana da jan rai, ina sakon ya Kamal din?"
"Au duk wannan basu burgeki ba kenan kike nufi?"
"Sun burge ni mana, na matsu dai naga sakon my sweet bro ne"
"Ai shikenan", ya fito da fanta ya bata yace gashi nan.
Cikin farinciki ta karba, tace "Ayya ya Kamal wato favourite na ya sayo min, ina missing dinka Yayana, and nagode.
Daga nan kuma ya fito da na Dada,da nasu Hamida ya bata, ya bata na mama, soyayyar miya ne da dan yawan, ga danbun mama, ga kuma soyayyar kifi mai dan yawan shima, sosai taji dadi, anan suka wuni da Abdul, ya dauko karamin kafet a motan Daddy ya shimfida musu, Daddy kuma ya basu wuri su sake abinsu, ya wuce wurin principal nasu wanda ya dawo ba jimawa.
Sosai Daddy yake mamakin yanda suke son junansu,ko wadanda suka fito ciki daya iyaka, abin ba karamin burgeshi yakeyi ba, ko dayake sufa har yanzu basu san cewa ba ciki daya suka fito ba, duk tsawon shekarunnan ba wanda ya taba fada musu.
Har la'asar kafin Daddy yace da Abdul su wuce, dakyar suka rabu da Aimana, kamar kar su tafi haka takeji.
Haka ta tattara ta koma dakinsu, don dai yaukam tayi missing class, saidai kuma gobe in da rai.
Ta sanya wa kanta kwarin gwiwa, ta kuma kidiri niyar yin karatu tukuru, sai ta bawa mara da kunya kamar yadda Daddy yake so, bazata taba kunyatashi ba, insha'Allah sai anyi alfahari da ita.
~~~~~~
Daddy sun isa gida lafiya, suka tarar da Dada nata faman sababi, sai Daddy ya zo ya dauko mata Aimana, ai ba haka sukayi dashi ba, cewa yayi zai kaita yau taga Aimana, shine zai kama yayi tafiyrsa ya barta.
Dama Daddy ya shiryawa hakan, don yasan dama sai anyi, shi kuma yaki tafiya da ita ne gudun kar taje ta tada masa balli, Mama kuwa da kanta tace bazata ba, don tasan bazasu kwashe da dadi da Aimana ba idan ta ganta.
Daddy kam yasha bala'in Dada kuma tace ba abuda zai gaya mata kodai ya kaita taga Aimana,ko kuma yaje ya dauko mata jika.
Dakyar da sudin goshi Dada ta hakura, shima saida Daddy ya tabbatar mata idan aiki ya ragu masa zaizo ya kaita, kafin ta saduda, amma sunsha sababi Kam, tace duk basu da imani basu da tausayi, musamman ma Mama kamar ba ita ta haifi yarinya ba, tana gani a dauketa a kaita uwa duniya amma ta kasa magana, sudai ba baka sai kunne.
~~~~~~~
A bangaren Aimana kuwa ta kwantar da hankalinta, karatunta kawai tasa a gaba, dama gata da kokari sai kuma Allah ya dafa mata, nan da nan har tayi nisa sosai a karatunta, don tayiwa kanta alkawarin hada alqur'ani kafin ta kammala secondary school nata, to kuma dama tana da haddan ta daidai gwargwado tun kafin tazo.
Cikin ikon Allah hutu ya kare, zuwa lokacin kuwa Aimana ta hada izifi mai yawa, kuma taji dadin karatun.
Saura kwana biyu a dawo aka rufe hadda, ran Asabar, kowa ya tattara kayanshi ya mayar asalin dakinsu, Aimana ma ta maida nata, a ranan sukayi duk wani shirinsu na komawa makaranta kamar su wanki da guga da dai sauransu.
Ran Sunday kuwa dalibai suka fara dawowa, kwatsam sai ga Daddy yazo, sosai Aimana tayi farinciki da ganinsa, ya kuwa taho mata da provision nata komai da komai, hatta maggi da dakakken yaji mai dadi, kamar wata macece tayi shopping din.
Yake baki tayi tana kallon tarkacen tana jin dadi, can kuma tace, "Daddy bakazo da Abdul ba, su Mama kam yaushe zasu zone, kodai basu son ganina ne?"
"Suna so Mama Aimana, basu sanma zanzo ba, shiyasa Abdul ma bai biyo ni ba, don ce musu nayi zan tura kudi a saya miki provision"
"To Daddy meyasa baka fada musu ba?"
"Hmm, Aimana ai rigiman Dada nake gudu, don cewa zatayi sai tazo, kuma kinga jikin girma, tafiyan da dan yawa zai bata wahala".
"Hakane Daddy, amma da watakila Mama zatazo"
Ai na fada miki Aimana, bana son su ganki yanzu, nafison lokacin da zasu ganki sai sunsha mamaki, kedai keep trying your best, malamin haddanku ya yaba sosai da kokarinki, so Keep it up".
"Shikenan Daddy insha'Allah, yanzu in ka tafi sai yaushe?"
"Next month insha'Allah zanzo kinji, Allah miki albarka"
"Ameen Daddy"
Daga haka sukayi sallama, tace ya gaishe mata dasu Dada in ya koma, tana son tambayan kamal amma sai ta kasa, batasan me yasa ba, sai taji nauyin tambayar Daddy,haka har ya tafi.
Ta tattara tarkacenta ta kai daki, su Asma'u ma sun dawo, suka hadu suka gyara dakin fes dashi,daga nan aka dora daga inda aka tsaya.
Ganin kokarin Aimana yasa principal nasu ya bawa Daddy shawara akan tayi JSSCE dinta kawai ta wuce SS 1, don ya tabbatar zata iya.
Daddy yayi na'am da shawarar principal din kuwa, ba tare da ya shawarci kowa ba ya biya mata kudin jarabawa.
Lokacinda ta samu labari ba karamin farin ciki tayi ba, har sallar dare tayi tana rokawa Daddy alkhairin duniya da lahira, haka yan dakinsu suka tayata murna, kawarta Hajara tace...
"Oh su Aimana, yanzu fa ana dawowa hutu, shikenan kin zama senior mu, na tayaki murna, Allah ya bada sa'ar jarabawa".
"Ameen kawata, nagode" daga haka suka cigaba da wani hiran daban.
Koda lokaci yayi Aimana ta rubuta exam nata na gama karamar sakandare, sai kuma jiran sakamako, lokacin kuma aka musu hutun makaranta, kasancewa third term ne, babu hadda, sabida haka Aimana cikin kwarin gwiwa da zumudi ta hada kayanta, yau zata koma gida, taga Mama da Dada,da Babanta da ya Abdul nata, sannan tana ta zumudin ganin sweet brother ta Kamal.
Da wuri Daddy yazo ya dauketa suka wuce, wajajen karfe goma suka isa, ai ko gama parking mai kyau Daddy baiyi ba Aimana ta balle marfin motar tayi cikin gida a guje, ko sallama bata tsaya yi ba, tana hango Mama tsaye a tsakar gida ta nufeta da sassarfa kamar zata kife don sauri.
Mama ji kawai tayi an fado jikinta an mata wata irin runguma tare da fashewa da kuka, saura kadan su zube.
Tana dagowa tayi arba da tilon diyarta, ai bata san sanda ta kara rungumota sosai ba, ba karya tayi missing nata dayawa, kusan wata bakwai ake nema batare da ta sanyata a ido ba, basu taba rabuwa na sati bama bare wata.
Dagota tayi da kyau ta kare mata kallo sannan tace..
"Kece Aimana, sai yaushe zaki san kin girma ne eye,to kukan kuma fa, uhmm"
Kara karfin kuakanta Aimana tayi.
Mama tace "to ya isa haka mu shiga ciki".
Dakin Dada Mama ta kaita, ai Dada nayin arba da Aimana ta mike ta kamota hade da rungumeta, sannan ta sake dago ta ta kalle ta, sai murmushin farin ciki takeyi, tama kasa magana.
Suka samu wuri suka zauna, suna zama kuwa sai ga sallaman Daddy da Baba sun shigo tare,dama bai fita ba yana jiran yaga isowarsu tukun, suma dakin Dada sukayi anan akayi gaishe gaishe, Mama ta kawo musu kayan kari a nan, don tasan Daddy bai karya ba, bare kuma Aimana da take dokin zuwa gida, bayan sun karya Daddy ya wuce gidansa.
Nan kuwa aka bude sabon babin farinciki da hira, Dada kam ta kasa barin Aimana matsawa ko nan da can, Aimana taga gata iya gata, abubuwan ci har ta rasa wanne zataci, Hamida ma sun shigo, suka kawo mata wainar fulawa mai dadin gaske, basu suka bar dakin Dada ba saida aka kira azahar, kowa ya nufi yin sallah.
Aimana na shiga dakinta tayi tsalle ta fada kan lallausan katifarta da tayi missing,tace, "Home, sweet home", ga dakin a gyare fes ko ina na daukan ido,tasan wannan aikin Mama ne, ga wani kamshi na musamman na tashi.
Saida ta gama juyinta a katifarta kafin ta tashi ta shiga bayangida, wanka ta fara yi, irin wanda ta dade batayi ba, ga ruwa isashshe tayi yanda ranta yakeso, kafin ta dauro alwala ta fito ta tada sallah, bayan ta idar tayi addu'a kafin ta nade abin sallan ta ajiye a gefe, ta haye katifarta da niyar bacci.
Koda ta rufe ido don tayi bacci, sai kawai tunanin Kamal ya fado mata, baya nanne, taso tambayar Hamida dazu, sai kuma ta tsinci kanta da jin kunyar tambayarsu a idon Mama, sai kuma tashiga tunanin to meyasa take jin kunyar hakan yanzu, bayan ada ko gaban wa zatayi maganar Kamal baya damunta.
Haka dai tayi ta juyi tare da tunanin Kamal, karshe dai baccin da batayi ba kenan har aka kira la'asar, ta tashi ta dauro wani alwala ta tada sallah.
Tana cikin sallar Mama ta leko don ta tasheta,sai ta samu tana ma sallah, sai kawai ta juya.
Tun karfe biyu Abdul ya dawo, amma ba wanda ya fada masa Aimana ta dawo,a nufinsu wai a barta ta huta, don indai ya sani to kuwa sai ya tasota,basu san itakam ma tana can tana faman tunanin masoyinta ba.
Sai bayan ta idar ta sake wanka,ta feshe jikinta da turaren, kafin ta fito tana ta baza kamshin.
Wuri ta samu kusa da Mama ta zauna, tana mata hiran makaranta, sai ga sallaman Abdul, aka amsa masa, yana shigowa ya hango Aimana zaune kusa da Mama, sai ganin abun yayi kamar gizo, kulle idonsa yayi ya sake budawa, still dai Aimana yake gani, ai da hanzari ya isa inda suke zaune da Mama, ya zauna shima a gefen Aimana tare da riko hannuta, yana so ya kara tabbatar da itace, tace..
"sis kece, ko gizo kike min?"
"Nidin ce dai bawani gizo"
Farinciki fal ranshi yau gashi ga tilon kanwarsa, hira sukasha a wurin tare da Mama har magariba, koda yayi korafin ba'a fada masa yau zata dawo ba Mama tace tana sane tayi ai da ta fada masa bazaije islamiya ba, cewa yayi..
"Kamar kuwa kin sani Mama, ai da dani za'aje dauko ta, amma ba damuwa next time bazanyi missing ba insha'Allah".
Suna cikin hira suka ji sallamar.......