001
by @takwalam
*KUSKURE*
Ayshakwalam
001
*ZUNNURA*
Mama dake tsaye a kaina tun lokacin da Suhail ya shigo yace mata Aliyu na Jira na, shiyasa ta biyo ni daki Dan taga yadda zan shirya, na aje rigar hannuna nace,
"Mama ki tafi mana, zan shirya fa"
Na fada ina narairaice fuska, ta kalle ni kamar me fadin ke din? Ke din da na sani ce zaki shirya a dadin Rai, tace
"Babu inda zanje, ki hanzarta ki fita Yana jiran ki"
Ikon Allah shi nake gani a gurinnan, shi kenan saboda nayi shekara talatin da uku banyi aure ba se ya zama kamar irin na shekara dari dinnan, bana manta ranar da na cewa Mama na yarda zan aura Aliyu, Mama sujaddar godiya se da ta kusa mintina talatin a duke tana godewa Allah akan karkato da hankali na da yayi, su fa kannen Mama sunce wai Amarya ce tayi min asiri shiyasa banyi aure ba, ni dai nace da Mama kar ta biye musu babu Wani asiri da akai min, lokaci ne baiyi ba Amma yanzun kam tunda yayi ai magana ta kare gashi nan har ana Shirin yin aure. Na zura rigar sannan na gyara zaman hular Kai na ina Jin Biebie dake can karshen gado tana fadin
"Yaya Zuzu da dai kin cire hular nan kin saka wata, gaba Daya color din Bai tafi da outfit din ki ba"
Kafin na Bata amsa, Mama tayi caraf tace
"Maza Biebie taso ki zaba mata wata"
Na sake Baki kuwa ina kallon bayin Allah Nan, karshe dai haka ina tsaye Biebie tazo ta shirya ni sannan tace min I'm good to go, waya ta na dauka na fita zuwa parlon su Ahmad inda yake zaune Yana danna wayar shi, na shiga da sallama a Baki na, a take ya dago ya zube idanun shi cikin idanuna, kwarjinin shi, haibar shi, kimar shi da darajar shi, shi ne abin da kullum yake Kara saka ni cikin son shi, ina kaunar shi, kaunar da bansan zaka iya yiwa mutum ba, ya kalle ni se ya sake min murmushi me kwantar da zuciya yace
"Gimbiya ta!"
Na karasa a hankali kamar me irga takun da nake na zauna kujerar dake facing din shi nace
"Naam! Na barka kana ta Jira ko?"
Yayi murmushi yace
"Girman ki ne ai, how are you?"
Na amsa da alhamdulillah sannan muka dan fara Hira cikin nutsuwa da shaukin bege. Aliyu dai ba sa'ana bane ba, ya girme ni Dan a kalla zai bani shekara goma ko fiye da Hakan, mun hadu da shi a sallar idi, na dawo daga sallar idi suma sun dawo, ance wai ba'a zaben matar aure a ranar sallah, Amma Aliyu ya zabe ni a ranar sallah.
"Sweetie har yanzun dai bawan Allah yana Jira kice a saka Rana"
Na danyi murmushi nace
"Ni Kuma? Ni ai na gama nawa"
Yana murmushi yace
"A'a ke kika ce fa na dakata se kin gama background check din ki, ashe kin gama bansani ba"
Ya fada fuskarshi na fitar da Wani irin annuri madaukaki, na nuna Kai na da yatsan hannuna nace
"Ni Kuma? Ni nace ka tsaya? Ni ban fada ba. Wanne background check Kuma? Bayan ka Riga da ka gudu da zuciya ta tuntuni"
Wannan karon ba murmushi yayi ba, dariya yayi, irin dariyar Nan da zaka San mutum a nutse yake, zuciyar shi is at ease irin ta yayi, nima se nayi murmushin saboda da gaske ina son shi ina Kuma kaunar shi, ai da ya dago daga dariyar se ya fara making plans na auren mu da yake son ya kasance in the shortest time possible. Bayan munyi sallama ya tafi nima na dawo cikin gida.
ALIYU
Tukin ma da yake cike da nishadi yake yin shi, saboda zuciyar shi na cikin sukuni da farin ciki, Bai karasa gida ba se da ya tsaya ya saya bread sannan ya Kara musu da yoghurt hade da sayan tsire ya nufi gidan. Yana shiga da kan shi ya bude gate ya shigar da motar shi sannan ya Maida gate ya kulle ya nufi cikin gidan, Abdallah ya fara gani shi da Anisa suna karasa assignment din su, suna Jin sallamar shi suka aje books din su tare da nufo shi yi masa oyoyo, shima ya aje kayan hannun shi ya rungume su Yana tambayar su makaranta, a haka kafin su sake shi Madam ni gidan ta fito kamar daga kitchen, doguwa ce baka Bata da kiba Amma fa kyakyawa ce ta gaske, ta fito fuskar ta dauke da murmushi tace
"Sannu da dawowa"
Ya saki yaran tare da Maida dukkan hankalin shi kanta yace
"Yawwa! Ya kika baro su"
Ta karaso tare d daukar ledar bread din da ya aje tace
"Suna gaishe ka"
Ya gyada Kai sannan ya nufi daki, se ta Dan kalle shi cikin zolaya tace
"Wannan wanka haka ai se nace zance kaje"
Wata irin muguwar faduwar gaba ta ziyarce shi lokaci Daya, da sauri ya juyo Amma ita har ta shiga kitchen ma, se ya saki ajiyar zuciya ya wuce daki tare da rage kayan jikin shi ya zauna Saman gado yayi shiru, he's contemplating, Kai ba haka bane ba Kai ba contemplating yake ba, he's confused, he's scared ya zai fuskanci Habiba yace mata zai Kara aure? Ta yaya zai fara fada mata aure yake nema? Ta ina zai kalla idanun ta yace mata...
Tunanin shi ya katse Jin turo kofar da akai, ya dago ya kalle ta se lokacin ya lura da kayan da yake jikin ta, wata blue din adire ce a jikin ta, dinkin da akai beading da wasu kananun beads da hasken bulbs dinnan ya haska, se dinkin ya haska ta, ta karaso ciki tare da fadin
"Ya kazo Nan ka zauna, Muna jiran ka muci abinci"
Ya mike da sauri hade da ruko ta yace
"I'm missing you"
Tayi murmushi tace
"Wanne irin missing gani a kusa da kai"
Yace
"Duk da haka, ina Jin kamar kinyi nesa Dani"
Ta janye jikin ta daga warm embrace din shi tace
"Come on muje muci abinci, after all yau Daren ai naka ne"
Yayi murmushi ya bi bayan ta zuwa inda yaran su ke zaune har sun fara ma cin abincin na su, yaran hudu ne, Sadiq shi ne babba Wanda Yana karamar secondary, se Nurain Wanda shima a secondary yake, se Anisa ita Kuma tana primary da kanin ta Abdallah da ke shi ne karami Kuma Habiba Bata Kara haihuwa ba tun daga kan shi. Cikin utmost silence suka ci abincin, wannan tarbiyar Habiba ce no phones, no noise a dining dole aci abinci cikin nutsuwa. Bayan sun gama suka danyi Hira kafin zuwa karfe Tara kowa yaje ya kwanta anan ne fa Habiba ta nuna ma Aliyu tarin Yara ba shine tsufa ba, a'a ta nuna masa she's still wannan Habibar tashi da yake so.
"Yaya Zuzu mama tana Kiran ki a parlon Baba"
Biebie ce ta shigo ta fada min sakon Mama, cikin sauri na tashi saboda ina son Mama bana hada sonta da na kowa a cikin zuciya ta, flower hannu na na aje na fito bayan na gyara zaman karamin veil din Dana yafa Saman boubou jiki na, ina sakkowa naga Amarya tana ta shige da fice daga kitchen zuwa parlon ta, nayi kamar ban ganta ba na wuce se naji tace
"ZUNNURA!"
Na tsaya ba tare da na juyo ba, ta zo gabana fuskar ta da murmushi tace
"Naji abun alheri, Allah ya Sanya alkhairi. Ashe lokaci yayi Kuma, dama haka aure yake shi ai loka.."
"Nagode"
Na Bata amsa na wuce parlon Baba, Yana zaune Saman kujerar, itama Mama tana zaune Saman kujerar da alama Hira suke , shigowa ta yasa duka suka Maida hankalin su Kai na, Mama na kalla se kyafta min idanu take, nayi kamar ban gane me take nufi ba, na zauna ba tare da na kalle shi ba nace
"Sannu da hutawa!"
Yace
"Yawwa ZUNNURA, na kira naji ya kukai da Aliyu?"
Nace
"Mun daidaita zan aure shi"
Se naga yayi murmushi yace
"To ma shaaa Allah, Allah ya Sanya alkhairi. Amma se kin rage wannan muguwar zuciyar taki, se kinyi hakuri Saboda Kinga matar shi da shi zaman lafiya suke kada ki je kiyi destabilizing masa gidan shi"
Na kalle shi kamar zanyi magana se Kuma naji muryar mama na fadin
"Zuzu kije, ki Jira ni dakina'
Na gyada Kai na fita daga dakin, wato shi Baba har Yana da bakin da zaice min wai kar na destabilizing gidan wasu, mu Kuma gidan mu da akai destabilizing fa? Amarya da ya biyewa ta lalata mana komai a gidan mu da? Idanuna suka ciko da kwalla har yau bazan taba manta cin mutuncin da amarya tayi mana a gidannan ba, har shima Baban bazan iya mantawa ba balle na yafe musu.
"Kinga abin da nake fada miki ko? Nace Miki Zunnura Bata gaishe ni"
Mama tayi murmushi tace
"A'a haba dai! Ya zaka ce Bata gaishe ka?"
Yayi murmushi irin nasu na manya Bai Kara cewar komai ba se zancen Shirin biki, ni kuwa sama na koma tare da dakko dukkan abin da nake bukata saboda akwai advert da nake yiwa brand din royco. Kitchen dina na wuce Wanda aka ware min anan nake creating content dina, se da na gama rubuta komai da zanyi sannan na kira Hafsa ta hayo tayi min setting light da camera da komai kafin Kuma na fara content din.
Duk yadda Aliyu yayi kokarin sanar da Habiba maganar auren shi da Zunnura ya kasa, ya kasa ya Kuma rasa wannan kwarin gwiwar da zai tunkare ta da maganar, so bayan an tsayar da ranar biki yaje ya samu mahaifiyar shi, bayan sun gaisa cike da girmama juna yace
"Hajiya ban fadawa Maman Sadiq zanyi aure ba fa"
Hajiya dake tauna goro tace
"Eh Hakan yafi ai"
Ya Dan kalle ta yace
"Yafi Hakan?"
Ya tambaya still guilt na cin shi, saboda ko jiya da daddare se da tace masa
"Yallabai ni na kasa gane kanka kwana biyu, baka dawowa da wuri, ko aiki ne ya matsa maka?"
Nan ma Kai ya sosa yace
"Kamar kin sani fa, Wani target aka bamu muyi achieving Amma soon komai zai zo karshe "
Tayi murmushi tace
"Ayya Allah ya bada sa'a nasan ka gaji ka kwanta"
Ya kalle ta a lokacin kaso mafi yawa na zuciyar shi na fada masa ya fada mata, wannan shi ne best moment Amma ya kasa, ya kasa tattaro courage din da zai fada mata a karshe haka ya kwanta zuciyar shi Babu dadi. Ita Kuma Habiba ko da wasa Bata taba tunanin Hakan ba saboda Aliyu ya iya takun shi. Itama Kuma Zuzu tayi kokarin ganin Bata shiga harkar gidan shi ba.
"Eh yafi hakan yafi, yafi sauki sede kawai ta ganta, Kuma kasan abinnda baka San da shi ba , ba zaka iya lalatawa ba!"
KUSKURE ba kyauta bane ba, ma'ana is not free.
Pay N1k to
3091721807
First Bank
Aisha kwalam Hassan
Send evidence of payment to
***
And get access to our telegram group or you can access it on Arewa books.
©Oum A'eesh