002
by @takwalam
*KUSKURE*
✍️ Ayshakwalam
002
*INAAYA*
Early 2000s
Kowanne dalibi cikin ajin sauri yake ya fita saboda ya tafi gida, Amma ni naji anyi ringing bell har sau uku Wanda yake tabbatar da school is over, it's time to go home Amma ni ina zaune akan seat dina ban tashi ba, se da kowa a Ajin ya kammalla hade kayan shi a bag kafin Kuma ya rage ni daya kowa ya fita, kafin sluggishly na fara tattara kaya na ina zubawa cikin backpack dita, Wanda shi ma se da ya dauke ni kusan mintina goma sannan na goya jakar tawa na fito daga Ajin, hatta compound din makarantar student kadan suka rage, ina zuwa kofar makaranta na kalla ko ina wai ko da zanga driver din gidan su Safar, Amma ko kyallin su ban gani ba, haka cikin nutsuwa nayi ta tafiya da tarin tunani cunkushe cikin Kai na, Babu abin da nake Banda tunanin idan naje gida irin tarin aikin da yake zaune prettily Yana Jira na, nasan Maman su Safar ba tayi girki ba, kilan wanke wanke ma na safe baa bawa iya tayi ba, ni ake Jira na dawo nayi, na saki ajiyar zuciya lokacin da nayi saurin matsawa gefe saboda bike da ya kusa bigeni, dukda bai buge ni ba se da ya juyo yace
"Uwar ki! Ke mahaukaciya..."
Sauran maganar tashi ban ji ba saboda ya wuce tabi iska, na saki ajiyar zuciya na cigaba da tafiya na wajen awa Daya kafin a gajiye na karasa gida, ina shiga su Safar na kokarin shiga mota saboda islamiyya, tana gani na ta fasa shiga motar ta taho tare da fadin
"Inaaya, se yanzun kika karaso? Sannu. I looked for you ban ganki ba shiyasa muka taho"
"Liar!!!"
Na fada a zuciya ta, hannun ta da ta rike nawa na kwace a hankali ba tare da na furta komai ba na wuce cikin gidan na su, da safe fa naji Baban Safar na fada ma Maman Safar kada ko da wasa ya Kara ganin sun dakko ni a mota, yace musamman ita Safar din, Kuma jiya da daddare I clearly heard Maman Safar na fadawa Safar duk ranar da ta sake bari na shiga motar su se tayi mata duka, but Safar been Safar shiyasa take nuna min ai ta neme ni Bata same ni ba. Ina shiga na tarar da Maman Safar tana tsaye ita da bakuwa, da sauri na karasa na gaishe su, tace
"Ina kika tsaya?"
Nayi shiru saboda me zance mata? Ta daka min tsawa tace
"Ko ba Inaaya nake yiwa magana ba?"
Na kalle ta idanuna sun fara kawo ruwa nace
"Kiyi hakuri!"
Tayi tsaki sannan nayi saurin mikewa zuwa dakin da nake, da sauri na cire kayan jiki na na shiga bandaki na watsa ruwa sannan na fito na saka wata Riga marar nauyi na fito zuwa kitchen, na Dan tsaya ina kallon pile of wanken wanken dake cikin sink, na fara dauka a hankali ina Kai su waje har na gama sannan na gyara kitchen din nazo na fara wanke wanke, ina tsaka da wannan wanke wanken se gata ta shigo
"Ya Baki daura abinci ba? Me zan bawa bakuwa ta?"
Nayi saurin mikewa tare da dauraye hannu na na karasa gaban gas din na daura tukunya, se da na zuba ruwa kafin ta fita bayan tayi min kashedi me kaushi. Bani na gama komai ba se dab da maghrib, na wuce daki ina Jin yadda duk jiki na ke ciwo, wanka na sake yi sannan nayi sallah kafin na fito Dan sake yin wanke wanke, anan muka hadu da Baban Safar, na gaishe shi sannan na wuce kitchen, na samu kowa yaci abinci, nayi wanke wanke sannan na zuba abinci naci kadan naji ciki na ya cushe, anan zaunen bacci ya fara dauka ta, se kawai na sulale a wajen na fara bacci, bansan har baccin da nayi ba se naji a hankali ana tashi na, cikin sauri na mike na dubi iya tace
"Inaaya, Maza tashi ki tafi daki kiyi bacci"
Nayi mata godiya tare da wucewa daki ina hada hanya, se asuba da na tashi kafin na tuna ai jiya banyi sallar isha ba, nayi sannan nayi asuba na fito na hada abincin safe na koma na shirya, karfe bakwai har na bar gidan, ina ta tafiya har su Safar suka zo suka wuce ni a cikin motar Baban su. Lokacin da na karasa makaranta takwas da minti takwas nasan na makara haka aka saka ni wankin toilet nayi missing first two periods kafin break, ina zuwa class na tarar Mrs Martha ta shiga Kuma banyi English assignment din da ta bamu ba, tana cewa ayi submitting na fara tunanin yadda zanyi, na dauka littafin na tsaya a tsaye, confused saboda bansan me zanyi ba, a'a zuwa zanyi nace mata ba ni da lafiya ne ko zance mata na manta littafin, ina tsaye har turn dina yazo, ina zuwa tace nayi ko banyi ba? Nace mata banyi ba, tace to na fita, na fita nayi kneel down se da period din yayi over kafin tace na biyo ta, Muna zuwa ta kaini office din student affairs tace gani Nan ta kawo ni saboda ta gaji da halayen na, test dina zero, bana assignment, a class daga bacci se tunani, ita ta gaji, kafin ta gama rant din ta se ga malamar biology da na physics sunzo wucewa a'a ai suma se suka ce dama yanzun zasu je office din VP academic su fada masa halayen na, a karshe aka saka sergeant ya zane ni ya fasa min jiki sannan na koma class, tun da na shiga class din na koma can karshen class na zauna, na dinga kuka, kuka fa ba kadan ba, irin kuka mai ihun nan, saboda ji nake kamar zuciya ta zata fito, kamar wannan kukan shi ne zai saka naji dadi na Kuma ji sanyi. Few class mate dina da suke cikin ajin suka zo waje na suna lallashi na, Amma I was too tired, too exhausted! Wannan wacce irin rayuwa ce, Babu dadi Babu Kuma afuwa a cikin ta?
Ina zaune se ga Safar ta shigo kusan a guje ta shigo, tana zuwa ta fado Kai na tare da rungume ni a jikin ta, tana fadin
"Me ya faru? Me kika yi aka dake ki?"
Ban kula ta ba, kamar yadda ban daina kukan ba, jiki na duk radadi yake yimin saboda sergeant dinnan ba shi da imani ko kadan, kamar yana cikin talauci ne se a bashi mutum ace ya daka,to se naga tamkar Yana huce haushin talaucin da yake ji akan wannan mutumin.
Zuwa karshen school jiki na yayi tsami, har Wani dan zazzabi nake ji Yana son rufe ni, na dai mike a hankali na fita daga makarantar, lokacin daidaiku suka fara tafiya, ina ta tafiya na ma yi nisa mukai clashing da driver din gidan su Safar zai je dakko su, nayi kamar ban gan shi ba na wuce na cigaba da tafiya ta abuna, ina shiga gidan suna shigowa suma, na nufi sama dakin Maman su Safar na gaishe ta, ta kalle ni da kyau kafin tace
"Ba ki da lafiya ne?"
Tsoro nake nace bani da lafiyar ma, se na girgiza kai na alamar a'a lafiya ta kalau, tace
"Daga makaranta an Aiko ba Kya zuwa islamiyya, haka kika zaba rayuwa ko Inaaya? Haka kike so ko? Ke baki Maida hankali ana boko ba ke baki Maida hankali a islamiyya ba? Kinfi son ki zauna dakikiya jahila ko?"
Na daiyi shiru ina sunkuyar da Kai na, hawaye suna min tsere a fuskata, yanzun fisabillilahi laifi na ne rashin zuwa islamiyya ko nata? Kuna kallon tarun aikin da nake yi cikin gidannan, ina na samu damar zuwa naje makaranta ko nayi karatu, na share hawayen na dago a hankali nace
"Kiyi hakuri...'
"Ai kullum maganar kenan, yi hakuri, Dan Allah ba zan Kara ba. Je ki kanki kika yiwa ba rayuwar ki bace ba. Ni dai Allah ai ya gani, na saka ki a makaranta"
Na fito daga dakin na nufi kasa inda nake zama, ina shiga na cire kaya na, farar long sleeve din duk ta baci da abun bulala, na danyi sniffing kadan kafin na cire skirt din na shiga wanka na fito, Iya na gani zaune Saman katifa tace
"Inaaya, kin dawo ashe?"
Na danyi faint smile nace
"Eh na dawo Iya, yanzun zan zo kitchen din"
Se ta girgiza kai tace
"Yau na yi Miki komai, maza kici abinci ki saka uniform ki tafi islamiyya"
Wani sanyi naji cikin zuciya ta at least yau bazan kwasa uban aikin nan ba, nayi mata godiya sannan na saka uniform na biyo bayan ta, su Safar na zaune suna yin lunch na kalle su suna suka kalle ni na dauke Kai na karasa zuwa kitchen, ina saka kafa ta naga Maman Safar tana tsaye gaban gas tana zuba abinci cikin disposable plate, da sauri na juya dan tafiya ta kwala min kira, jiki a sanyaye na dawo, ko kafin ma nayi magana ta fara fadin
"Ina zaki je da kika fita? Salon ata zagi na bana Baki abinci ko?"
Ni dai nayi shiru ta Miko min transparent disposable plate din da ta gama zuba abincin a ciki tace
"Ki wuce ki tafi kada ki makara"
Na karba nayi godiya sannan na tafi, ina tafiya a nutse kamar yadda na saba, har power bike din nan dake wucewa yazo ya wuce, se nace nayi kusan shekara ina ganin bike dinnan Amma ban taba ganin fuskar me bike din ba, kasancewar Yana rufe fuskar shi da hular kwano, na karasa makarantar da babu dalibai sosae kasancewar lokaci Bai karasa ba, haka na zauna a gurin zamana naci abinci kafin Kuma na dakko qurani ina tilawar inda na yi missing, Allah ma yasa inada pen Qur'an dinnan wanda Ramo ta kawo min da taje umrar cikin azumi.
Ina ta zaune Yan class na shigowa daya daya, suna min sannu da jiki ashe Safar tace musu bani da lafiya. Can se naji ana kwala min kira, na rufe quranin na juya ina kallon kofar, Ramo ta shigo tare da rungume ni tace
"Inaaya sannu, yau nake cewa Hajiya zan zo na duba ki idan an tashi"
Nayi murmushi nace
"Ba komai, ya kwana biu?"
Muka gaisa ta tambaye ni jiki na and stuffs kafin muka fara karatu. Ramo dai sunan ta Rahma Aminu, duk yadda nake dari dari da mutane Rahma still tana kula ni, bata damuwa da rashin sakin jiki na Hakan yasa nima na saki jiki na da ita, amma dukkan mu bamu san gidajen juna ba, haduwar makaranta rabuwar bakin gate inji mu da fadi. From looks din Ramo yar masu kudi ce so komai nata zaka gan shi unique and expensive shiyasa ma bana sakin jiki da ita sosae saboda kada ace ai na nace mata saboda kudin su, ita kuwa ina ruwan ta haka take kula ni babu abin da ya dame ta.
KUSKURE ba kyauta bane ba, ma'ana is not free.
Pay N1k to
3091721807
First Bank
Aisha kwalam Hassan
Send evidence of payment to
***
And get access to our telegram group or you can access it on Arewa books.
©Oum A'eesh