KUSKURE

003

by @takwalam

*KUSKURE*

✍️ Ayshakwalam

003

_"Jama'ar Allah jama'ar Zuzu! Ya kuka kasance? Ya kuka tashi?"_

Wannan shi ne ya kasance line din da nake yi duk lokacin da zanyi voice over akan videos dina, na kasance mutum ce sananniya wadda ta shahara a fagen girki a social media, tun ina yi babu Wanda yasan da zama na har na fara samun views din mutane, a hankali a hankali da consistency da addua da komai se gashi kusan kowanne FYP se kaga content dina.

Na kammalla girka tuwon shinkafa da zaayi pairing da miyar danyar kubewa, wadda na saka mata royco cubes a ciki, Kuma tayi not just advert da gaske it was a Banga, ina gamawa na gyara gurin sannan nayi packaging kadan daga ciki na kira me delivery dina nace yaje ya Kai ma Aliyu, Hafsa dake nannade komai da mukai aiki da su tace

"Yaya Zuzu, Yaya Aliyu fa kika ce? Idan Yana gida fa?"

Nayi murmushi nace

"Se yasan yadda zaiyi kawai"

Tayi dariya nima nayi dariya abuna muka fito zuwa dakin Mama, ta dawo daga dakin Baba ina zama ta fara min fadan rashin gaishe da baba da nake

"Ba Kya kyautawa Zunnura, kome yayi ai mahaifin ki ne, ke yanzun idan kika haihu kiga Dan ki Yana treating din ki haka me zaki ji?"

Na kalle ta, ganin ranta ya baci se nayi murmushi nace

"Mama kiyi hakuri, ni fa ina gaishe shi, shi ne fa baya gani, beside duk lokacin da zamu hadu to kuwa ba muhallin gaisuwa bane ba"

Ta gyada Kai kawai ba tace komai ba Kuma, ni na tafi daki na shiga capcut Dan editing videos din da mukai. Ba tare da na kira shi nace masa na bada Sako a kawo masa ba, na bar shi a matsayin surprise!

*ALIYU*

"Hajiya kamar dai oda taji wannan maganar zai mata ciwo shiyasa na kasa fada mata, ko na turo ta ki fada mata da kanki?"

"A'a! Ka barta idan akai auren se kafada mata ai duk haukar da zatayi ba zaiyi tasiri ba tunda amarya ta sauka a gidan ta"

Ya saki ajiyar zuciya ya ayyana Anya kuwa daidai ne, Anya ya kamata yayiwa zuciyar da take son shi haka? To Amma ya zaiyi? To Amma wannan shi ne kadai solution din, ba zai iya ganin Habiba in pains ba, ba zai iya cigaba da hada idanu da ita a lokacin da tasan neman aure yake ba, sede idan ya Riga da ya kawo matar wannan it's ok. Yana Nan zaune Imam kanin shi ya shigo, suka gaisa tare da yi masa Allah ya Sanya alkhairi, yace

"Anty Habiba fa? Amma dai ka gaya mata ko?"

Ya girgiza kai Yana kallon Hajiya dake kallon Imam din, yace

"What? Baka fada mata ba? Hajiya kinji Bai fadawa Maman Anisa ba"

Yaya tace

"Ni nace, Kuma nace kada ya fada mata, Kuma Kuma na hane ku da fada mata"

Se Imam yayi shiru Bai Kara cewar komai ba, anan ne fa me delivery ya kira shi akan zai kawo masa Sako, ba tare da ya tambaya sakon meye ba ko daga wajen waye ba, kawai ya turawa me delivery number Habiba akai sakon wajen ta.

Lokacin da me delivery ya Kai sakon, dawowar ta kenan daga asibiti, ta karba katon basket din me hade da malmalar tuwo uku, Miya daban, se grilled chicken part guda biyar, lemon kwalba na champagne da fruit box, tayi ta kallon box din da aka manna sticker a jiki da _Heavenly taste by Zuzu_ , se da ta tamabaye shi waye yace a kawo, se shi ya Bata number Aliyu Hakan yasa ta karba ta shiga da shi kitchen ta aje sede jikin ta Bai kawo komai ba, Amma dai mamakin ganin abinci take, ta gyara gidan tas ta daura abinci sannan kan ta gama tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin embroidery material da yayi mata Kyau na asali. Se maghrib bayan ya gama waya Dani kafin ya nufi gida, nayi hakuri sosae da ban tambaye shi ko yaga Sako na ba, mun dai danyi lovey dovey talks din mu kafin ya wuce gida bayan yayi sallar isha. Yana shigowa ya samu yaran har sunci abinci suna Shirin bacci, suka gaishe shi sannan suka tafi makwamcin su, daki ya nufa inda ya same ta tana waya da colleague din ta d take night duty, ta kira ta fada mata an samu me ciki wata takwas Kuma hoto ya nuna yaron ba shi da Rai, Amma mijin ta yaki ya yadda ayi inducing din ta, Habiba ta dafe Kai cikin kosawa tace

"Ki kira Wanda yake call ki fada masa, idan yaso se aga idan zaa iya amfani da consent din ta. Calm shift kinji? Yallabi ya dawo let me attend to him"

Duka sukai dariya kafin ta sauke wayar daga kunnen ta tace

"Sannu da zuwa yallabai! Ya aiki ? Ya Hajiya? Sannu"

Ya Dan rungume ta yace

"Sannu ya naki aikin? Though naji yanzun ma baza su barki ki huta ba"

Tayi murmushi tace

"Wallahi fa, na kagu suyi appointing sabuwar matron nayi stepping daga wannan acting din"

Yace

"A'a na fiso ki cigaba, it really suit you"

Tayi murmushi kafin ta tamabaye shi ina zasu ci abinci, yace suje parlor, tare suka tafi Yana ta zolayar ta tana ramawa, se da ta shiga kitchen dakko tray din da ta shirya abinci kafin idanun ta suka sauka akan wannan basket da akai delivering dazun, bayan ta kawo tray din se ta koma ta dakko basket din ta aje masa, ya kalla sannan ya kalle ta saboda yadda ta tsare shi da wannan idanun nata, se lokacin ya tuna ashe fa yasa an kawo Sako gida, Bai San sakon menene ba, Bai masan wanda ya Aiko da sakon ba se yanzun da yaga basket a gaban shi ganin sticker heavenly taste by Zuzu, yasan wannan aiken daga wajen baduwar shi ne, yayi saurin masking yanayin shi yace

"Oh wai Baki ci ba? ke nayiwa order fa"

A hankali Habiba ta yaye transparent ledar da aka rufe basket din da shi, a zuciyar ta Kuma karo na farko taji anya yallabai da gaske yake, ganin abincin da ke ciki tace

"Wannan ba nawa bane ba, ka manta bana Shan kubewa?"

Yayi saurin fadin

"Ikon Allah, swallow da egusi nace, kilan an samu mistake ne"

Ta tura basket din gefe tace

"Muci abinci"

Aliyu Yana kallo haka baici abincin wajen Zuzu ba, hasalima ko naman Bata saka musu ba ta cigaba da cin abincin ta hankali kwance, se da suka gama yace

"To mu Sha fruit din ko?"

Ta kalla basket din kamar zatace Wani Abu se Kuma ta fasa, instead ta dauka ta sake wanko su ta yanka ta kawo masa, yayi yayi ta Sha tace a'a ta koshi.

Washegari da safe Habiba na tashi, ta tattara abincin har naman da ke ciki tace maza Sadiq ya fita ya bawa almajiri a waje, ya nufi wajen zai Kai se ga Aliyu Yana shigowa ya dawo daga morning jogs din shi, ya kalla Sadiq ya kalla abincin hannun shi, se yace

"Ina zaka Kai abincin?"

Yace

"Amma ce tace a kaiwa almajiri"

Se ya saka hannun shi ya amsa ya dawo ciki ya same ta a kitchen tana hada sandwich, ya aje kwanukan yace

"Haba darling, idan ba zaki ci ba mu ba se ki mana dumame muci ba, Amma almajirai fa"

"Budurwar ka ce ta aiko maka?"

Ta fada tana aje wukar hannun ta Saman chopping board din, da sauri ya girgiza kai saboda se da yaji kamar she's seeing through him, yace

"A'a aaaa! Kamar Yaya?"

Ya tambaya zuciyar shi kamar zata fito saboda tsoro da ya shige shi, tayi murmushi tace

"Kaje ka shirya ka dawo na zuba maka tuwon"

Ya sake ajiyar zuciya ya juya zai fita se ya dawo

"Amma dai kin yadda cewar ba budurwar gare ni ba ko?"

Tayi murmushi tace

"Haba dai, wasa nake ai kace ba zaka taba kula wata ba, ka tuna kace idan dai kayi zancen aure to na tabbatar aljanu ne akan ka?"

Fuskar shi tayi Wani haske saboda firgici, he remembered vividly lokacin da yake gaya mata, saboda idan zai tuna lokacin tana amarya ne, tace masa tana da kishi, tace masa Bata son kishiyar, Dan Allah ya zauna da ita ita kadai, kada yaso wata ita Kuma tayi masa alkawarin zame masa komai a duniyar Nan, shi Kuma se yace mata ba zai taba mata kishiya ba, ba zai taba kallon wata yace Yana so ba, Kai duk ranar da taga yayi aure to ta sani aljanu suka shafe shi, Kai har ce mata yayi idan taji yayi budurwa ta Kai shi ayi masa rukiya! Se gashi Kuma Allah yayi ikon sa bayan shekara sha biyar idanun shi sun gano masa wadda ta gigita shi, ta tafi da dukkan wata nutsuwa ta shi.

Wattanni uku ne kawai da suka gabata akai sallah karama, a wannan ranar na gama duk abin da zanyi da wuri na shirya cikin Applique lace dina da akai masa dinkin gown, na saka hijab da yayi kyau da lace din na dauka praying mat dita ni da Biebie muka tafi masallaci, bayan mun idar da sallah muka nufi inda na aje mota ta, ina kokarin shiga waya ta dake hannu na ta subuce ta fadi, shi Kuma a lokacin Ya Sako kafar shi kenan se kuwa ya taka ta, that's how ni Zunnura na hadu da Aliyu, daga wannan lokacin Muna hada idanu chemistry ya fara faruwa , that's the beginning of our love story. Aliyu ya kasance irin mazan da nake so, mazan da suke yayan mutunci suka San mutunci, a wattannin da mukai tare ko sau daya bai taba aibata matar shi ba, Kai baya ma maganar su, tun bayan da yace min he got family Bai sake zancen su ba, haka nima ban sake bi ta kansu ba, a gani na bani da Wani hadi da su yanzun idan ba na shiga daga ciki ba.

KUSKURE ba kyauta bane ba, ma'ana is not free.

Pay N1k to

3091721807

First Bank

Aisha kwalam Hassan

Send evidence of payment to

***

And get access to our telegram group or you can access it on Arewa books.

©Oum A'eesh