KUSKURE

004

by @takwalam

KUSKURE

004

✍️ Ayshakwalam

INAAYA

Tun daga wannan ranar ya zama na idan na dawo daga makaranta Safar zata dauka littafi na a boye tayi min dukkan assignment din da aka bani, sannan zata shigo kitchen ta taya ni aiki ko da zan koreta to ba zata tafi ba,  ranar wata Monday da wurwuri na tashi nayi wanka sannan na taho kitchen na fara hada kayan wanke wanke, Basu da yawa sosae saboda na rage su sosae da daddare kafin na kwanta, ina cikin wanke wanken naji takun tafiya a tsakiyar parlon, a hankali na taka zuwa parlon Dan naga wanene, idanuna ya sauka akan idanun Abba da yake sanye da jallabiya fara tas hade da hular da bahaushe yake cewa tashi ka fiya naci, ya kalle ni nima na kalle shi se nace

"Ina kwana?"

Ya kalle ni ya Kara kallo na, Amma Allah ne masani, ban sani ba ya amsa ni Bai amsa ni ba ban sani ba, nasan dai yayi tafiyar shi daga parlon, na koma ciki na shimfida sallaya nayi raka'a biyu ta asuba se Kuma na daura abinci, zaku ce to bana damuwa? Ina damuwa da yadda baya kula ni, ba sosae ma yake amsa gaisuwa ta ba, Kuma ance min wai shi mahaifi na ne, eh ance ne Dan da sunan shi nake bearing , ance wai da aka haife ni bayan shekara Daya se mahaifiya ta se ta rasu, bayan ta rasu shi Kuma Abba Bai bada ni wajen dangin ta ba, se ya barwa Maman Safar a hannun ta, Maman Safar ta hada ni da Safar da sauran siblings din mu take rukon mu, a zama na da ita bazan iya cewa ga rana daya da Maman Safar ta saka hannun ta ta dake ni ba, amma Wani lokacin ina Jin gwara ace Maman Safar duka na take akan abin da take yimin ...

"Yaya Inaaya, tunanin me kike? Dankalin zai Kone"

Naji muryar Safar a kusa dani, da sauri na dago na kalle ta, har ta saka uniform a jikin ta, na kalla frying pan din da Irish din ke ciki sun fara zama brown, da sauri na tsame ba tare da na kalle ta ba nace nagode, se Kuma na Dan ja baya saboda man yayi zafi kafin na zuba wani, ta kalle ni tace

"Yaya Inaaya, kije ki shirya bara na taya ki"

Na kalle ta ina son nace mata a'a se tayi saurin fadin

"Kije lokaci Yana tafiya, Dan Allah ki bari zan karasa Miki"

Haka na tafi da sauri nayi wanka sannan na shirya na dawo kitchen din har ta gama tana kokarin soya kwai, na karba nace ta deba musu suci nasu kada su makara, ta deba sannan ta zuba min tace

"Kici kema kinji?"

Na danyi murmushi a Raina ina ayyana cewar blood is always thicker than water. Se da na gama komai da komai har na kammalla saka uniform kafin naji Maman su Safar tana kwala min kira, na aje socks din hannu na na fito na tsugunna na gaishe ta kafin na jira naji complain din da zatayi.

"Ni nace ki dinga tashi tun hudu kina yin aiki?"

Na kalle ta she's looking damn serious, tana nuna kanta da yatsan hannun ta, nace

"A'a Amma cewa kikai se na gama komai kafin na tafi makaranta"

"A yaushe na fada? A gaban wa na fada? Yaushe nace se kin gama aikin ki ki tafi makaranta. Kede Inaaya munafuka ce, kede bakya son zaman lafiya, burin ki kawai kiga ban zauna lafiya ba, to ki cigaba zanyi Miki dukan da zaki kasa tashi idan kika sake min irin haka"

Na gyada mata Kai na kawai, Amma bance komai ba saboda bansan me zance din ba, na mike ganin ta kama staircase ta koma sama zuwa dakin ta,  na shiga na saba school bag dita na nufi waje dan tafiya, ina tafiya a hankali saboda nasan akwai sauran lokaci, na kusa karasawa school se naga motar Abban su Safar ta wuce ni, se Kuma ta dawo baya a hankali, ya tsaya gefe na yace

"Waye yace ki taho da kafar ki?"

Na juya na kalle shi, se Kuma nayi shiru bance komai ba, to me zance? Se nace shi yace? Bayan da kunne na naji Yana fadawa su Safar kada su sake ya ganni a motar su, ya kara tamke fuskar shi yace

"Ko ba magana nake Miki ba? Bude ki shigo kina bata mana lokaci"

Na girgiza kai nace

"A'a Abba zan tafi da kada ta"

Wani kallo yayi min, irin are you sane? Tace

"Ni kike yiwa musu?"

Haka na bude gefen seat na shiga, yaja motar shi ya cigaba da tafiya, har da cemin na saka a unguwa ana zagin shi a unguwa, a makaranta an fada masa cewar bana note, bana assignment Dan haka idan nasan cewar ba zan yi karatu ba to na fada masa ya cire ni yayi min aure,

"...ba damuwa ta bane ba dan nayi Miki aure, da ki saka a dinga zagi na gwara nayi auren ki tun da shi kika zaba, ke ba good grades ba , ke ba komai ba..."

Yana fada ni Kuma ina kuka, to me zanyi idan ba kuka ba? Bani da Wani Abu da zanyi tun da dai bansan ma ni menene matsayi na cikin gidan ba, Safar dake kusa dani ta rike hannuna tana fada min a hankali

"Kiyi hakuri Yaya, komai zai wuce watarana"

Na kalle ta, Safar! Safar!! Bazan taba mantawa da ita ba. Se da ya sauke mu cikin makaranta sannan yace na bishi muje wajen principal, haka na bishi ina kuka sosae Wanda shi ma se da ya dago yace

"Ba zaki rufe min Baki ba? Wani abun nayi Miki? Ko dukan ki nayi?"

Da sauri na girgiza kai Amma na kasa Daina kuka, I was feeling very hopeless and worthless a wannan lokacin, ji nake kamar na shake kaina na mutu Amma ya zan kashe Kai na ba yadda zanyi, haka na cigaba da bin shi har office din principal, tana ganin shi ta mike tana murmushi tare da bamu izinin shiga, hannun ta ta masa stretching, shima yayi stretching nasa sukai handshake kafin tace ya zauna, ni ma tace na zauna, se ta fara gaya masa halin da nake ciki a school karshe haka aka tattaro duka Malaman da suke daukar subject din da nake offering, duka suka zo Amma magana Daya ce I'm not paying attention a aji, bacci nake, bana note, bana assignment I'm stupid and worthless duka suka haka ce, bulalar dake aje gaban principal Abba ya dauka ya dinga duka na da ita, se da Sir Halilu ya karbe ni sannan principal tace wannan term din shi ne  grace din da zasu bani, idan banyi making exams dina ba to kora ta zasuyi, haka na mike bayan sun sallame ni na tafi class ina Jin Wani irin radadi cikin jikina Amma ciwon da zuciya ta take yi yafi na jiki na.

Bayan kowa ya tafi Madam Nanah, food and nutrition teacher din mu ta samu principal bayan kowa ya tafi tace mata

"Ma, kina ganin wannan yarinyar lafiyar ta kalau?"

Principal tace

"Kamar me fa?"

Madam Nanah tace

"Is like akwai Wani Abu daga gida, Ma yarinyar Nan da kafa take zuwa, da kafa take komawa gida, Kuma abun mamakin tana da siblings su Kuma Baban ke kawo su, do you think it's normal? Ya kamata mu duba yarinyar Nan muga abin da yake faruwa"

Principal tace to amma Babu abin da tayi, se Madam Nanah ce kullum ke kula dani, kullum da safe se tazo class dinmu ta ganni ta Kuma tambaye ni ko ina da matsala se de na girgiza mata Kai kawai.

A fateful Wednesday, na dawo daga islamiyya, ina tafiya a hankali saboda na dan samu saukin aiki a wajen Maman su Safar. Nasan yawancin masu fita jogging, ko walk ko stroll suna fita ne da sassafe Amma wannan da nake gani kullum idan na dawo daga islamiyya mamaki yake bani, Yana sanye red da farin jersey, wandon da Bai Kai knee length din shi ba shima fari ne da ja se canvy din shi fari tas Yana jogging towards me, na cigaba da tafiya a hankali har muka zo dab da juna, se ya tsaya tare da bude jarkar hannun shi ya fara Shan ruwa, anan ne na karaso inda yake se naga ya sakar min murmushi, na dauke Kai na, na cigaba da tafiya, ya sake biyo ni tare da fadin

"Ko baki jin Hausa ne? I said hi"

Na Kara kallon shi he's fair ma'ana Yana da haske, Yana da dogon hanci as if biro aka bashi akace ya zama yadda yake son hancin shi ya kasance, sede idanun shi akasin nawa da suke dara dara na shi kananun ne, you can mistaken him for irin Koreans dinnan tunda idanun su yafi na Chinese da Japanese girma, fuskar shi akwai side burns da suka saka fuskar ta zama bushy but wallahi I like it, ganin yadda yake Wani kashe mun idanun shi da Wani smirk da yasa naji butterflies a ciki na, yasa da sauri naja kafafuna, na cigaba da tafiya ta slowly ko nace lazily ya cigaba da biyo ni Yana fada min

"Kinsan na Dade ina ganin ki ko? Bari na tuna lokacin da na fara ganin ki"

Se yayi shiru Yana lissafin da yatsun hannun shi, Amma Kuma Bai Daina Bina ba, yace

"Yawwa sati bakwai kenan! I remembered ranar ba islamiyya kika je ba, kinje sayo ko bread ne?"

Ya fada Yana daga kansa sama sounding very desperate to recall, ni Kuma se kallon shi nake, Dan tuni mun tsaya

"Na ganki kina ta sauri zaki koma gida, tun ranar nake binki, sunan ki Inaaya Abdullahi Atawami ko? Kina makarantar Success academy a SS2, islamiyar ki Khalid Ibn Walid? Aji shida ko? Mahaifiyar ki ta rasu ko? Kannen ki Safar, Al_amin, Fahad da..."

Da sauri nace

"Heeee! Ya akai kasan komai nawa? Kai waye?"

Da sauri yace Yana daga hannu in surrender

"Saboda ina son ki, saboda haka yasa nayi digging deep akan ki"

Se kawai na wuce ina ta sauri a tunani zai iya sace ni tun da ya Riga da yasan komai nawa, ina shiga nayi kicibis da Nu'uman da yake kokarin fitowa, Yana gani na yace

"Yaya Inaaya, Hajiyan Atawami tazo"

Na danyi faint smile saboda har lokacin gaba na faduwa yake nace

"Yaushe? Tana ina?"

Yace

"Tana parlor, kiyi sauri ta kawo nono da fura da dabino"

Nayi murmushi na shige ba tare da na waiwaya ba balle naga mutumin dake tsaye Yana kallon mu da idanun shi da bansan me suke min cikin zuciya ta ba!

KUSKURE ba kyauta bane ba, ma'ana is not free.

Pay N1k to

3091721807

First Bank

Aisha kwalam Hassan

Send evidence of payment to

***

And get access to our telegram group or you can access it on Arewa books.

©Oum A'eesh