Cahapter 5
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*****
BOOK 1
PAGE 5️⃣
*ZALIKA*
Zaune suke a ƙaton falon da ya gaji da haɗuwa, hira suke sama-sama kowanne yana danna wayarsa. Mubin ne ya jingina da jikin kujera yana ajiye wayarsa a kusa da shi ya kalli Zalika ya ce
"Ina son magana da Baffa amma wallahi tsoro nake" Baki Zalika ta taɓe da kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce
"Maganar mai? Kaima da ka shafawa kanka lpia da wannan tunanin ka san dai ko ma wace magana ce Baffa ba saurarenka zai yi ba gwara ma ka faɗawa Mamy, don ni yanzu na cire faɗawa Baffa abu ma saboda ba saurarena zai yi ba" Ta faɗa tana maida hankalin ta kan waya.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce
"Ni ba wata magana nake so mu yi ba kawai dai ina so mu zauna mu tattauna, ina nufin mu yi hira irin na ɗa da uba" Ya faɗa idanunsa suna yin jawur tamkar zai yi kuka hatta a muryarsa raunin hakan ya bayyana.
Zalika ta ce
"Uhum in ji mai ciwon haƙori, ni wallahi har mantawa ma nake da Baffa idan magana ko damuwa ta same ni, kuma ko da na ji shauƙin son magana da shi a matsayinsa na mahaifina ina kawar da hakan domin na san abu ne mai wahala, shi ya nuna ba ya buƙata to mu ma mai zai hana mu danne zuciyarmu?" Iska Mubin ya fesar haɗe da sakin ajiyar zuciya ya ce
"Ni wallahi ina kasa jurewa wani lokacin, abin yana birgeni kuma yana bani sha'awa idan na je gidan abokaina na gansu suna hira ana raha da mahaifinsu amma mu mun mallaki komai na rayuwa amma mahaifinsu bashi da lokacinmu, sannan ba wai ayyukan ne suka masa yawan da ba zai sauraremu ba, shi fa tun asali ma haka yake babu ruwansa da lamarin ƴaƴansa, sai dai Mamy ta maye mana gurbin mahaifi da mahaifiya" Mubin ya faɗa cike da damuwa.
Mamy da take laɓe tana jin su duk sai jikinta ya yi sanyi, tabbas ta san kowane ɗa yana da burin mahaifinsa ya tattuna da shi ya ji damuwoyinsa, amma su basu san daɗin mahaifinsu ba gashi dai yana raye amma sun zama marayu ta ɓangarensa, ita kanta ba ya zama da ita, ƴaƴansu sai ita za ta kula da su, kama daga tarbiyarsu da zama da su ta ji abin da yake damunsu ko shawara fa sauransu.
Shi abin da ya ɗauka guda ɗaya shi ne idan ya ajiye kayan abinci da kuɗi to ya gam da fannin iyali, ya ɗaura ragamar tarbiya da komai a wuyan mahaifiyarsu a cewarsa shi uba ɗaukan nauyin gidan ne kawai ya rataya a wuyansa, ita kuma uwa ita ce za ta basu tarbiya, bai san cewa tarbiya ba ta mutum ɗaya ba ce, tarbiya ta uwa da uba ce duka, ba zai yiwu a ce uwa kaɗai ta ɗauki wannan ragamar ba, don tarbiya ta kowa ce.
A hankali ta fara takowa daga inda take dama a ɗan koridon bedroom ɗinta na ƙasa ta tsaya take jin hirarsu da take dakar mata zuciya. Tana tahowa tana ƙarewa falon kallo yadda aka kashe dukiya a gidan amma kuma an samu naƙasu a wajen gudanar da zaman gidan, ta rasa mijin ta wane irin mutum ne shi kaifi ɗaya da ba ya sauyawa daga kan aƙidarsa.
Tana zuwa cikin falon ta buɗe baki cike da kulawa, fuskarta washe kamar gonar auduga ta yi sallama cike da kulawa da nuna soyayya da ƙauna ga yaran nata, Zalika ce ta amsa ita ma tana murmushi saɓanin Mubin da ya sadda kai bai amsa sallamar ba kuma bai kalli Mamy ba. Duk da Mamy ta ji babu daɗi a ranta na ganin yanayinsa kuma ta san damuwarsa domin ta ji abin da suke tattaunawa, ko da a ce bata ji ba to dama ta san damuwar ƴaƴan nata tun da basu da wata matsala a rayuwa sai ta mahaifinsu, matsala ce wacce tun asali aka tashi da ita kuma ta yi ƙoƙarin kawo gyara da maslaha amma abin ya ci tura!.
Idanunta ne suka nemi fitar da ruwa, amma ganin Zalika ta mayar da hankalinta kwacakom kanta sai ta yi ƙoƙarin dannewa, faɗaɗa fara,arta ta yi ta ƙaraso falon ta zauna tana mai cewa
"To ko dai falon iya ƴan uwa ake buƙata a ciki ni na zo na kawo kaina" Ta faɗa cike da wasa rana son kawar da damuwar da ta gani shimfiɗe a fuskar Mubin, amma har lokacin bai ɗago ba kuma bai yi magana ba. Zalika ce ta ce
"Kai Mamy har ma da wani hirar ƴan uwa da za a ce uwa ba za ta zo ta ji ba, bayan ke kaɗai ce ginshinƙin mu ke kike kulamu ke kike ɗauke duk wani nauyin da zukatanmu suka yi" Ta faɗa tana kallon fuskar mahaifiyar tata.
Mamy ta gane mai qannan kalaman na Zalika suke nufi amma kuma bata son ta ɗora ƴaƴanta a ragamar da za su cigaba da ganin laifin mahaifinsu duk da ta san yanzu sun yi wayo sun fahimci komai game da halayyar mahaifinsu, duk da a baya ma tun suna yara suna iya ganewa domin suna tamabayarta bare kuma yanzu da suka mallaki hankalin kansu.
Cikin zolaya ta sake cewa
"To ai na ga ɗan uwanki ko ɗaguwa bai yi ya kalleni ba, ba dole na ce ko zancen da ya shafi ƴan uwa kuke yi ba" Ta ce tana kallon Mubin.
Mubin wanda rauninsa ne yake son bayyana kamar ba namiji ba abin da ya sa ya ƙu ɗago fuskarsa ba ya so Mamy ta ga yana cikin damuwa kuma ya san damuwarsu damuwarta ce ko kaɗan bata sukuni a duk lokacin da ɗayansu ba ya cikin walawal, sannan abu ɗaya ne ya hana shi yin magana shi ne va ya son muryarsa ta fallasa abin da yake cikin zuciyarsa.
Mamy da take kallonsa cikin sanyin murya ta ce
"Mubin ɗina" Zuciyarsa ce ya ji ta ƙara karaya ya fara tunanin cewa wannan kalmar tana faranta masa rai fite da tunanin mai tunani, sai dai tabbas daga ɓangare ɗaya yake jinta wato ɓangaren mahaifiyarsa, zai so a ce ya ji daga mahaifinsa ma amma ina tun da yake bai taɓa ganin wani sassauci ko kulawa da soyayya daga mahaifi ba. Idan ya ga abokansa suna yabon mahaifinsu a status ko dun ɗora hoton mahaisin suna my hero, farin cikinmu Allah ja da kwana mahaifinmu, wasu suke faɗin mahaifina abokina, wata ta ɗora bani da aboki ko abokin shawara sai mahaifina. Waɗannan kalaman suna sosa masa zuciya abu ne da bai samu ba abu ne da yake ganin mahaifinsa ya tauye musu jin daɗi da kulawa.
Mamy a karo na biyu ta ce
"Mubina ɗina taurarona" Bai san lokacin da ya ɗago kansa ba ya zubawa mahaifiyarsa jajayen idanunsa tamkar ranar ya fara arba da fuskarta, kallonsa suke daga ita har Zalika, idanunsa jajawur fuskarsa cike da damuwa ƙarara, a gefe ɗaya idanunsa suna kwararar da wasu hawaye. Yana ɗagowa sai ya buɗe bakinsa dakyar ya haɗa laɓɓansa ya ce
"Mai ya sa sai mu? Mai ya sa daga ni sai ƙanwata ne muka rasa wannan damar Mamy? Mai ya sa mahaifinmu babu ruwansa da bamu kulawa Mamy, kullum fuskarsa a ɗaure, bama ganin dariyarsa tamkar ba a taɓa halitta tausayinmu a zuciyarsa ba" Zalika ita ma da Mubin ya sosa zuciyarta domin ita ma ƙarfin hali kawai take yi, kalamansa sun tada mata mikin da ke cikin zuciyarta a take nata idanun suka shiga tara ƙwalla, domin ta san a rayuwa babu mai gane damuwarka sai wanda yake cikin irin halin da kake ciki, ma'ana yanzu da take jin kalaman Yayanta da kuma ganin ruwan hawayensa suna kwaranya sai ta ji duk duniya babu wanda zai fahimci damuwarsa sama da ita domin ita ma tana damuwa makamanciyar tasa.
Mamy kuma idanunta ta ɗauke daga kallon Mubin ba tate da ta furta ko uffan ba, ba tare da ta bashi amsa ko da ɗaya ba ce daga cikintambayoyin da ya jero mata ba, amma har ga Allah ji take tamkar ta rushe da kuka ko ta samu sauƙi da salama a zuciyarta a kan halin da take ganin ƴaƴanta a ciki, saboda ta san ita kaɗai ba za ta basu kulawar ɓangare biyu ba ko da ta yi ƙoƙarin hakan su dole zuciyarsu za take wasi-wasi a kan lamuran cikin gidan nasu wanda mahaifin nasu ne sila.
Danna zuciyarta ta yi domin a matsayinta na mahaifiya a gare su babu buƙatar ta nuna rauninta a wannan waje domin damuwar za ta musu illa, hakan ya sa ta ɗago ta yi murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ta ce
"Kowane ɗan adam yana da jarawarsa a rayuwa, sai dai idan ya jure watarana komai zai zama labari, komai zai zama tarihi tamkar ba a taɓa yi ba" Ta faɗa yana ruƙo hannun Mubin ta dawo da shi kusa da ita ya zamana suna zaune a tare Mamy a tsakiya su kuma kowa yana gefenta hannuwanta ta sanya ta dafo kafaɗunsu ta ce
"Ku zama masu jajircewa, ku zama masu riƙe ibada tare da jajircewa a dukkan lamuran rayuwarku, kar ku bari wani abu yale rage muku jin daɗin rayuwa, duk wanda ya riƙe Allah to tabbas ba zai yi nadama ko da na sani ba" Ta faɗa tana juyawa ɓangare Zalika ta kalle ta, ta sake juyawa ɓangare Mubin ta kalle shi, su duka har lokacin da ruwan hawaye a saman fuskar kowa.
Zalika ce ta ce
"Mamy wallahi wani lokacin sai inmke ganin kamar ba Baffa ba ne ya haife mu, to ko yana da wata matar a wani waje da wasu ƴaƴan shi ya sa su yake musu walwala mu yake ƙume mana fuska?"
Kafin Mamy ta yi magana Mubin ya yi karaf ya ce
"Ko dariya ba ya yi, sai fushi da hantararmu kamar dai ba ya son mu, ai na san idan mu kaɗai ne ƴaƴan nasa to zai so shi ma yake zaunawa da mu ko ya bamu kulawa"
Mamy ta ce
"Sau nawa zan faɗa muku ku yi haƙuri ne wai? Na ce muku akwai lokaci yana tafe wataranan mahaifinku zai zama kamar kowane mahaifi"
Zalika ta ce
"Allah ya sa amma dai ina ga sai bayan mun bar wannan duniyar don Baffa ba na jin akwai ranar da zai sauya, ko ya canja ra'ayi.
Mamy ce cike da harzuƙa ta ce
"Wai ya kuke so in yi ne?"
Mubin ya ce
" Mamy mun san kin yi ƙoƙari kuma kina kan yi amma dai ni na san tarbiyya ba ta uwa kaɗai ba ce. Uba yana da rawar gani mai girma a kan iyalansa idan ya nuna ƙauna da kulawa, ya saurari yaransa, zai fi sa su girma da kwanciyar hankali da ƙima, dan aka bar uwa ita kaɗai, yara za su rasa ginshikin ɓangaren uba amma ki yi haƙuri" Mubin ya faɗa yana saka hannu ya ɗauke hannun Mamy daga kafaɗarsa ya miƙewa ba tare da ya ce uffan ba ya bar falon.
*JIDDA*
Gabaɗaya jikinta karkarwa ya fara ganin Umma ta ɗaga hannu za ta sharara mata mari, saboda ta san zafin hannun Umma idan har ta mare ka sai ka gwammace kiɗa da karatu. Domin tana da zafin hannu don hannun ta tamkar hannun wani namiji babu laushi ko kaɗan . Karkarwar da jikinta ya fara kwandon yana neman suɓucewa, Umma wacce sai da hannunta ya kusa isa fuskar Jidda sannan ta hangi Abba ya taho daga hanyar ƙofar gida don alamar farin yadin jikinshi ta hango, sosai faɗuwar gaba ta ziyarce ta amma saboda kissa da kisisina da iya bariki irin na Umma a take ta shiga kokawa da ƙwaƙwalwarta, don ganin ta ƙirƙiri abin da zai gusar da wannan mugun ganin da Abban ya kusa yi.
Cike da tsantsar baki ta saki wata ƴar bazawarar dariya, hannun nan da ta yi niyyar marin Jidda da shi sai ta ƙarasa gefen fuskar Jiddar a hankali ta shafi kuncin Jidda ɗata hannun kuma sai ta riƙe haɓar Jiddar tana cewa
"Allah ya miki albarka Jidda ya baki miji na gari inda za ki huta, ubangiji ya baki ƴaƴa masu miki ɗawainiya kamar yadda kike mini, Allah jiƙan itayenki da rahma" Wannan kalaman na Umma ne ya sa Jidda wacce ta rikice take jiran saukar zazzafan marin na Umma da sauri ta buɗe idanunta tun daga lokacin da ta ji Umma ta shafa fuskarta haɗe da haɓarta amma jin kalaman na Ummar ya ankarar da ita akwai abin da yake faruwa.
Wani yawu Jidda ta haɗiye muƙut, ganin fuskarta ta tsira daga mari, Abba kuwa wanda ya yi mutuwar tsaye da ganin ɗaga hannun Umma mamaki da al'ajabi suka saukar masa ya fara tunanin mene ne halan yake shirin faruwa, sai dai lokacin guda Umma ta sauya masa akalar tunaninsa daga mummunan zaton da ya fara mata zuwa kyakkyawan zato da yake mata a kullum domin kyawawan halayenta da take nunawa a gabansa da kuma rashin nuna bambanci tsakanin Jidda yarinyar da yake riƙo da kuma ƴarta ta cikin ta wato Aliya.
Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauka tare da fata ɗaga sagaggun ƙafafunsa don tun lokacin, da ya ga Umma ta ɗaga hannu ta nufi fuskar Jidda ya ji komai ya tsaya masa cak!.
Baki ya buɗe cike da raha ya yi sallama, a lokacin Umma ta riƙe da gefen kaɗar Jidda, Jidda kuwa sai a lokacin ta gane dalilin da ya sa Umma ta fada aiwatar da ƙudurinta a kanta, yanzu ta fahimci ashe zuwan Abba ne ya dakar da Ummar daga marinta.
Umma kuma cike da nuna bata san da zaman Mai gidan nata a inda yake ba, ta juya da sauri tana ƙara faɗaɗa fara'arta ta shiga amsa masa sallama, tare da ɗauke hannu daga saman kafaɗar Jidda da ta riƙe tana mai cewa
"Maza an Jiddona a je a kai kanukan kicin" Cike da ƙarfin hali Jidda ta amsa mata da faɗin
"To" Tana nufar kicin don har lokacin bata dawo daga duniyar tsoro da fargabar marin da Umma ta yi niyyar mata ba. Umma tana sakin Jiddar ta juya da fara'arta ta irin mutanen kirki masu dattako ta nufi Abba tana ta karɓi ledojin hannunsa tana faɗin
"Sannu da zuwa sannu da zuwa, sannu da zuwa jan gwarzo, uba na gari ga ƴaƴansa miji na gari ga matarsa, Allah bada tsawon rai da kwana mai amfani, an dawo daga hidima da ƙoƙarin nemawa iyali abinci da za su ci, Allah yi jagora ya sauƙaƙa maka hanyar nema" Ta ringa jero addu'ar tana gaba yana biye da ita yana ta amsawa da
"Amin ya rabbil alamin" Ɗakinsa ya shiga, sai da ya zauna a bakin gado ta ƙara masa sannu da zuwa sannan ta fito da ledojin ta damƙawa Jidda a kan cewa komai a ajiye shi a mazauninsa, fruit ɗin kuma ta yanka. Ruwa ta kaiwa Abba banɗakinsa na ɗaki sai da ya shiga wankan ta fito, suna haɗa ido da jidda wacce take zaune da kayan fruit a gaba tana saka su a wata roba mai ruwa tana wankewa, wata gagarumar harara ta jefawa Jidda kamar idanunta za su faɗo, da sauri Jidda ta kawar da idanunta ta maida hankali ga abin da take yi. Umma wani tsaki ta doka har guda biyu tare da juyawa ta shiga kicin ɗin kayan abincin Abba ta ɗakko ta ajiye a waje guda.
Abba sai da ya yi alwala ya fito daga banɗakin jallabiya ya saka ya fesa turare ya ɗakko carbinsa ya fito, lokacin ana ta kira magriba, Jidda lokacin ta gama zubawa Abba kayan fruit ɗinsa a plate ta rufe ta ajiye a kusa da abincinsa da Umma ta ajiye, sai kuma na Ummar a wani plate ɗin sai nasu ita da Aliya a plate ɗaya, ta san wannan ƙa'ida ce in dai Abba yana nan tare suke cin abu.
Umma da ta gama alwala ta buɗe baki ta ce
"Jidda maza ki ajiye wannan kayan ki yi alwala ki yi salla, ƴar uwat taki ma ki musu magana su fito an kira sallah" Da to ta amsa ta shiga ɗaki za ta ɗakko abin sallah.
Abba ya ce
"Jidda sarkin aiki" Ya faɗa cike da kulawa yana ƴar dariya. Murmushi ta yi ta ce
"Ina jin daɗin in ga ina aiki" Murmushi ya yi ya ce
"To ai sai a je a gaishe da ubangiji kin dai ji abin da Ummarku ta ce" Da to ta amsa masa tana jin wani farin ciki don Abba shi kaɗai ne mai ƙaunarta tana jin daɗin yadda yake ƙaunarta. Yana fita sai ga Aliya da Amatullahi sun fito kallo ɗaya suka yi wa Jidda da take shimfiɗa tabarmi a tsakar gidan, tun da ita tana fashin sallah, waje suka fita Aliya za ta takawa Amatullahi, a ƙofar gidan suka yj sallama don ta san Abba ya dawo dama magana ce a kan saurayin da ta gani kyakkyawa tana cewa burinta ya zo gare ta ya bayyana kalmar so a gare ta ita kuwa dole ta yi watsi da Kasim saurayinta da yake mata wahala duk da bashi da wani ƙarfi sai don ƙaunar da yake mata kuma yana son ya faranta mata ganin tana son a bata.
Aliya sallah ta yi haka ma Umma suka zauna, Jidda tana ɗaki gudun kar a mata wani abun. Abba sai da aka yi sallar isha'i ya shigo gidan, yana shigowa da sallama vayan an amsa ya nufi tabarmarsa ya zauna, Aliya ta masa sannu da zuwa Umma ta shiga ƙwalawa Jidda kira tana faɗin mai take a ɗakin. Jidda tana fitowa ta je ta durƙusa ta gaishe da Abba tare da masa sannu da dawowa. Ya amsa cikin fara'a yana musu addu'a
Abincin da Aliya ta zubo musu a plate ɗaya suka shiga ci, Aliya tana wani jan Jidda da hirar tana ta ƴar dariya, haka ma Jiddar ta ɗan saki jiki duk da ta san kawai na ganin Abba ne. Sai da suka gama suka shiga shan fruit ɗin. Bayan kowa ya gama aka shiga hira tamkar dai babu ƴar tsama tsakanin Jidda da Umma da Aliya. Abba yana ta musu murnar kammala jarabawa da gama makarantar buɗar bakin Umma sai ta ce
"An kammala karatu kam sai shafa lalle" Ta faɗa tana ƴar dariya tare da fakar idanun Abba ta yi wa Jidda wani kallo irin na za mu ga da wanda za a ɗaura miki aure.
Abba gyaran murya ya yi ya ce
"Tabbas dama wannan ne burina duk wacce take son ɗora karatu sai dai ta ɗora a ɗakin mijin ta" Jidda gabaɗaya ta ji hankalin ta ya tashi saboda ta san Abba bashi da burin da ya wuce ya aurar da su rana ɗaya da ita da Aliya, gashi ita ko tsayayyan saurayi bata da shi bare kuma a yi zancen aure.
Aliya ma duk da haɗuwarta da Ibrahim yau hakan ya sauya mata tunani daga auren Kasim amma dai ta san ita ko da a ce mai za a yi ba za ya kasa samun miji na kerewa sa'a ba ko da a ce ana gobe ɗaurin aure ne ta tabbata ba za ta yi kwantai ba.
Haka dai aka tattauna kafin daga bisani kowa ya je ya kwanta.
Bayan kwana biyu.
Misalin ƙarfe biyu da minti ashirin na dare ne, alarm ɗin da Jidda ta saita a wayarta ya shiga ruri, cikin bacci ta ji ƙaran da sauri ta tashi ta danne wajen sifikar wayar da ƙarfi kafin ta saka hannu da dakatar da alarm ɗin. Duk da wannan namijin ƙoƙarin da ta yi amma hakan bai hana Aliya tashi daga bacci ba cike da ɓacin rai ta buɗe idanu lokacin har Jiddar ta kunna fitilar wayarta.
Zaune ta tashi tana mutsirtsika idanu, gaban Jidda ne ya faɗi amma bata ce komai ba, wata doguwar hamma Aliya ta saki ko bakin ta bata rufe ba, bata taoron shaiɗanu su shige bakin su samarwa kansu mazauni a bakinta. Cike da bala'i murya ƙasa-ƙasa gudun kar iska ta kai maganar ɗakin Abba, don ta san Abba kamar mai kunenn miciji haka yake wajen jin magana, bare shi ma da ba wani baccin dare ba yake don ta tabbatar yanzu da za a je ɗakinsa ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara a kan sallaya za a same shi ko dai yana sallah ko kuma yana karatun qur'ani.
Tana mata wani kallo ta ce
"Jidda wai mene ne hakan? Sau nawa zan ce miki ki dajna saka wannan ƙaran alarm ɗin yana katse mini bacci da mafarkai masu daɗi, ni wallahi ban taɓa jin wannan al'amari ba a zo gidan mutane a hana su sakat da sakewa ake damunsu da shiga haƙƙinsu" Ta faɗa cike da wulaƙanci tana wani kauda kai gefe, ruwa ne ya taru a kwarmin idanun Jidda ta tsaya tana ƙarewa ƙeyar Aloya kallo da yake ta juyar da kai gefe irin na wukaƙanci. Murya a dishashe ta shiga faɗin.
"Aliya ni kike yi wa gorin gida?" Kamar an wanda Aliyar take jiran tambayar ta ce
"To in fitsari banza ne kaza ma ta yi mana" Furta furucin wannan ya yi daidai da gangarowa maƙalallun hawayen da suke cikin idanun Jidda, cike da jin babu daɗi a ranta ta ce
"Aliya wai kam ko kin manta Jiddanki? Ni ce fa Jidda wannan ƙawar taki tun ta yarinta, ni ce fa wacce kike so da tsananin ƙauna, ni ce wacce muke wasa bacci kawai yake rabamu, ni ce fa za mu wuni tare amma idan za mu rabu da kuka ake rabamu saboda shaƙuwa da ƙauna. Amma Aliya yanzu saboda iyayensa sun kwanta dama ƙasa ta rufe idanunsu shi ne kike min wasu abubuwa wanda ban taɓa zato da tunanina ba, shin ko kin daina so na ne? Muna rayuwa tamkar ƴan biyu babu mai shiga tsakaninmu muna son junanmu amma lamuran duk sun taɓarɓare sun jagule shin ina matsalar take?"
Duk wannan jawabi da kalami da Jidda ta yi ta vayan kunnen Aliya ya wuce don ko gizau bata yi ba, bare Jidda ta saka ran cewa kalamanta za su yi tasiri a zuciyar Aliya, don ta lura Aliya ta sauya gabaɗaya, zuciyarta ma tamkar wanda ta ƙeƙashe daga tausayi da jin ƙai!.
Yatsina fuska ta yi ta ce
"Yankan uwa ai ya ishi ɗan tayi ishara, ke yanzu kina zaman jiran sai na furta miki kowace kalma da bakina, hankali da tunaninki basu isa su baki amssoshin tambayarki ba?"
Hawayen idanunta sun fara gudu tamkar an kunna famfo, tana jin yadda ruwan hawaye yake gangatowa har ta saman hancin ta, a gefw ɗaya yana gangara har wuyanta.
Cike da alhini da damuwa haɗe da sanyin murya ta ce
" Au haka ne?"
Aliya ta ce
"Tabbas ya kamata ki fahimci RUWA CIKIN COKALI ya ishi mai hankali wanka" Tana faɗar hakan ta juya baya ta kwanta abin ta.
Jikin Jidda sanyi ƙlaw ta juya za ta fita dama alwala za ta yi domin gabatar da sallar nafila, har ta je bakin ƙofar za ta fita ta tsinkayi muryar Aliya tana faɗin.
"Ba za ki gane ba Jidda tabbas babu ƙarya na ƙauna ce ki kuma tamkar ƴar uwa na ɗauke ki, sai dai ba zan ɓoye miki tun daga lokacin da muke zuwa makaranta tare sai kowa yake son ki ni ko oho, idan kika yi fashin rashin zuwa makaranta ko na kwana ɗaya baki da lafiya daga malamai har ɗalibai tambayar ki suke, idan na yi fashi ko shekara zan yi babu mai nemana daga islamiya har boko. Tsananin ƙoƙarin ki da farin jini ya sa Abba ma kika ciri tuta a wajensa, tun daga wannan lokacin matsayin ki a zuciyata ya ragu sannan uwa uba da muka isa munzalin ƴanmatacin samari suka miki caaa duk da kyau da diri da nake da shi na tsarin halittar ƴa mace wacce za ta ja hankalin duk wani cikakken namiji mai lafiya a jika amma sai ya zamana kowa ke yake kallo, duk inda muka taka sai dai samari su biyo mu gida idan kuwa suka zo kowa ya aiko yaro sai dai a ce ana yi wa Jidda magana!Tun daga wannan lokacin na fara kallon kyauna a matsayin muni tun da ga shi dai ana faɗin farar mace alkyabba ta mata amma ni nawa fari da kyan ya zama tamkat shuɗaɗaɗn lokacin"
Tun da ta fara magana bakin Jidda yake a buɗe ta rasa abin da za ta ce kanta gabaɗaya ya kulle tana tunanin shin dama wannn ne ummul aba,isin rabuwar kawunansu da Aliya, to ita ta ce samarin su zo nemanta ita da vata ma kula su hatta maganar malamai da ɗalibai ba ni na ce so ƙaunace ni ba ashe shi ya sa ko da muka fara karatun N.C E bata son kowa ya raɓe ni kenan hassada Aliya take min? Ta shiga jerawa kanta tambaya w zuciyarta, bata da amsar da Aliya domin tana ma tunanin lokacin sallar ta yana wucewa a banza ita kuma a rayuwa tana son ribatar lokacin ta kafin mutuwarta ta riske ta.
Ko da ta fita ta yi alwala ta dawo Aliya ta juya tana bacci bata sake cewa komai ba, sallah ta yi raka ',a huɗu ta zauna ta ringa jerowa iyayen ta addu'a domin ta san tsakanin ɗa da iyayen da suka riga gidan gaskiya babu abin da suke buƙata sai addu'a. Bayan ta gama musu ta yi wa kanta da Abba, ta yi wa Umma da Aliya tare da yi wa dukkan sauran musulmi.
Sai da ta yi sallar asuba ta yi karatun qur'ani sannan da gari ya yi haske ta koma ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita.
Bayan faruwar haka da kwana biyu, Aliya ta shiga wasi-wasi a kan tunanin Ibrahim da yake yawan addabar zuciyarta, sai dai ta yi sawun zuwan kamfanin da ta ga sun je an buɗe sun shige da motarsu amma ko barin ta ta shiga mai gadin ba ya yi, sai dai ta saka a ranta idan kere yana yawo zabo yana yawo watarana za a haɗu.
Ta ci gaba da riƙe Kasim ɗinta tana lallaɓawa tare da jiran gawon shanu na zuwan Ibrahim domin idan ta samu Ibrahim dole Kasim ya kama gabansa a cewar ta, shi kuma Kasim saboda ƙaunar da yake mata koyaushe sai hidima da kashe mata ɗan kuɗin da yake samu yake.
Rayuwa tana ta tafiya, yau fari gobe baƙi dama haka rayuwa take a wajen kowa ta kowane ɓangare, bijirowa da fitar da abokin rayuwa da Abba ya yi wa Aliya da Jidda shi ne abin da ya saka Jidda a wani hali, domin ta san bata da kowa, ita yanzu ko wuni za ta yi tana yawo ta dawo gida babu mai tsayar da ita bare a biyo ta gida, gashi dai ta san Abba bai san cewa bata da manemi ba, tun da shi yana wuni a kasuwa sannan ya san dai da Jidda akwai manema bai san cewa yanzu kiɗa da rawa sun sauya gabaɗaya ba. Ta shiga damuwa musamman yanzu da Umma ta sako ta a gaba da rashin manemi kuma mashini tana faɗa mata cewa sai dai a bada ita sadaka tun da baƙin jinin ta ya saka bata da manemi, duk da ita Jidda ta san Allah ne yake bayarwa kuma aure lokaci ne kamar haɓo yake idan ya zo sai an yi. Gorance gorancen da Umma take mata ya sa ko zaman gidan fita yake a ranta bare yanzu da sun kammala karatu sai islamiya Jiddan take zuwa Aliya dama ta yi bankwana da zuwa islamiya saboda ta ga Abba ba zaman gida yake ba ita kuma Umma bata takura msta wai ai ta iya karatun sallah, bata san cewa uwa ita ce makarantar farko ta ɗanta ba, ilimi ya zama dole ga kowa kuma wajibi ga mace domin ita ce makarantar farko ta ƴaƴanta da ma al'umma baki ɗaya.
Kamar kullum yau ma sa da ta gama aikin gidan tsaf ta yi wanka ta saka kaya tare da ɗora hijabin makarantar ta, fitowa ta yi tana riƙe da jakar islamiya, Umma da Aliya suna zaune suna tattunawa, sallama ta musu babu wanda ya kula ta, juyawa ta yi ta fita daga gidan, a zuciyarta tana tuno lokacin tata mahaifiyar tana raye yadda take ta mata addu'a da fatan alkairi idan za ta tafi makaranta amma yanzu saboda bata raye in har ba Abba ba ne to babu wani mahluƙi da yake mata addu'a ita damuwarta ma guda ɗaya ce da aba a san inda wani daga cikin danginta yake ba, tun daga kan dangin uwa kama zuwa dangin uba.
Tana ta zancen zuci ta nufi makarantar ta shiga aji lokacin har an fara ɗorin karatun hadisi, kusa da aawarta Salama ta zauna ta fito da nata littafin suka ci gaba da sauraron malam.
A can gida kuwa Jidda tana fita Umma ta taɓe baki ta ce
"Wahalalliya ce wannan yarinyar in banda rashin aikin yi islamiya dai tun ana yara ake abu ɗaya, yanzu an zama ƴanmata har ana shirin shiga ɗakin miji amma ba za a haƙura ba" Aliya ta yi wata dariyar rainin wayo ta ce
"Umma sai faɗi kike wai za a shiga ɗakin miji to in dai ba ita kaɗai za a saka a ɗakin ba waye zai kashi wanann?"
Umma ta ce
"Kuma fa haka ne, ai wallahi malamin nan da ya yi wa yarinyar nan maganin baƙin jini, samari suka daina wannan rawar ƙafar zuwa ƙofar gidan nan ai dole in koma in masa kyauta, yanzu shiru kike ji in ta fita ko kare ba ya biyo ta"
Aliya ta ce
"Wallahi kuwa Umma ai kin yi farar dabarw, da yanzu ni za ta tashi ta bari a gidan ake cewa ƴarki ta yi kwanta"
Umma ta ce
"Ai sai dai in bana raye, amma matuƙar ina numfashi Aliya Jidda bata isa ta tafi ɗakin miji ta barki a gida ba" Sosai suke ta hira abin su.
Ibrahim tun daga ranar da ya yi tozali da Jidda bai samu sukuni ba, sosai sonta yake azalzalar zuciyarsa, kuma ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen zuwa ƙofar gidansu har sau biyu amma bai ga wulginta ba, shi kuma yana jin nauyin ya aika kiranta, kuma ma idan zai aika wa zai ce? Shi bai san sunanta ba. Daga Daddy har Mummy babu wanda ya san wainar da yake toyawa sai dai sun ɗan fara lura da yanayinsa don ya sauya, sai dai da suka tambaye shi dalili amsa ɗaya ce ita ce kawai ba ya jin daɗin jikin sa gar doctor su na gida Abba ya kira a kan ya duba lafiyarsa amma babu abij da yakr damun lafiyarsa.
Kamar kullum yau ma yana zaune a tangameman falonsa da yake part ɗinsa, zaune yake a kan kujera, sai karamin tebur a gabansa, laptop ɗinsa ce da ƙaramin kofi mai ɗauke da coffee. Aiki yake a laptop ɗin amma hankalinsa yana ga tunanin Jidda, ɗan matsar da laptop ɗin gefe ya yi ya ɗauki coffee ɗin ya sha kaɗan ya mayar da kofin kan ƙaramin kofin glass ɗin ya ajiye, ganin ya rasa sukuni ya rufe laptop ɗin ya kashe fitilun duka na falon ya nufi bedroom, toilet ya shiga ya yi alwala ya fito ya hau gadonsa wanda ya sha shimfiɗar lallausan zanin gadon MAMAN AFRAH mai kyau gashi da ƙwari sannan zanin gadon mai ɗauke da bargo ne wanda aka shimfiɗa ɗin ma mai faiba a ciki ne ya yi matuƙar kyau ɗinkin. Hawa ya yi ya kwanta yana ɗakko wayarsa da take ajiye daga gefen gadon ya danna ya duba time, ajiyewa ya yi tare da yin addu,a ya shafe jikinsa tare da lumshe kyawawan idanunsa, cike da tunaninta nannauyan bacci ya ɗauke shi.
Washe gari ko da ya tashi da tunanin ta ya tashi, sai ya ɗaukawa kansa alƙwarin duk inda take in har tana garin Kano sai ya nemo ta ya ba idanunsa abinci ko zai samu salama a zucuya da ruhinsa. Da yamma ya shiga ya yi wanka ya fito ya shirya cikin tsaddaden yadin kufta wanda aka yi wa adon zare na ɗinkin hannu, saƙar ɗinkin ya yj matuƙar amsar ash colour yadin. Bayan ya kamala shiryawa ya ɗakko hula mai ash mai ɗauki da ratsin fari da ɗan blue wanda bai ciza ba da aka ɗan yi wani layi-layi da shi a jikin hular, kallonsa yake a madubi yana yabawa kansa kyau ɗin da ya yi, turarukansa da suka gaji da haɗuwa ya feshe jikinsa da su a take ɗakin ya gauraye da daddaɗan sansanyan ƙamshi mai ratsa zuciya!.
Mummy ya sanar cewa zai je wajen abokinsa Abeed, yana fitowa ya ɗauki wata sabuwar ash ɗin mota ya shiga sai sheƙi take sai dai glass ɗin kotar baƙi ne ba a ganin wanda yake ciki, mai gadi ya buɗe masa ƙofa yana ɗaga masa hannu da masa fatan alkairi, don da gani an ga tafiya ta musamman saboda ko direba bai bi ta kansa ba, horn kawai ya yi wa mai gadin shi ne amsar maganar da yake masa a zuciyarsa kuma yana amsa addu'ar da mai gadin ya masa.
Kan titi ya nausa motar yana tafiya a hankali karatun qur'ani yana tashi a motar, tun da ya zo inda zai gangara gidan da yakr tsammanin gidan su Jiddan ne, inda ya hanga ta shiga ranar nan, gabansa yake tsanani da mummunar faɗuwa bai san dalili ba amma ya alaƙanta hakan da SO.
Misalin ƙarfe biyar ya zo wajen amma kuma har biyar da rabi babu wanda ya fito ko ya shiga gidan da yake tsammanin ganin Jiddan. Dama ba a ƙofar gidan ya yi parking ba daga can gefe ne, har biyar da arba'in babu kowa sai mutane da suke ta hada -hada da kuma yara suna ficewa sai dai shi bai san ya zai yi ya ce a mata magana ba. Yana nan sai ya hangi wata budurwa ta taho rana zuwa ta nufi gidan, zuciyarsa tana raya masa ya fita ya tambaye ta amma kuma shi ko kaɗan ma yarinyar bata masa ba yanayin shigarta da ma tafiyar da take, hakan ya sa ya koma ya jingina, don hatta karatun ya kashe kawai zaman jiran tsammani yake. Bayan ta shiga gidan jim kaɗan sai gasu sun fito su biyu ransa ne ya ɓaci a lokacin da ya ga Aliya wacce suka fito da Amatullahi wacce ta shiga gidan yanzu. Ko kaɗan ba ya son ma'amalar Aliya da Jidda don a ganinsa basu dace da yin ƙawance ba ji ya yi kamar ta fito ya ce daga yau kar su ƙara zuwa gidan su Jiddan.
Har suka ɓacewa ganinsa ransa a ɓace, daga can ya hango wasu ƴanɓata guda biyu sanye da dogayen hijabi, suna tahowa, idanunsa ƙurrr a kan Jidda don tun daga ganin da ya mata na farko bai taɓa manta kamaninta da kuma yanayin tafiyarta mai nutsuwa ba, ko ƙiftawa ba ya yi gani yake idan ya ƙifta zai rasa ganinta har abada. Zuciyarsa tana masa zillo so yake ya yi amfani da wannan damar ya fito daga motar ya tunkare ta ya faɗa mata sirrin zuciyarsa amma faɗuwar da gabansa yake ba ya ji ma idan ya fito bakinsa zai bashi haɗin kai na gabatar mata da kansa. Jidda wacce suke tafiya da Salama ƙawarta haka suka taho har suka zo daidai motar da Ibrahim yake ciki, dama hira suke abinsu amma maganar da suke basu gama ba kuma za su rabu domin gida Salamar ma za ta wuce.
Ganin motar da take gefe a ajiye kasancewar gilashin baƙi ne basa ganin wanda yake ciki, ƙarasawa suka yi suka jingina da motar, Ibrahim da yake ciki gabaɗaya an dagula masa lissafi da farko ma da ya ga sun nufo motar ga ɗauka suna ganinsa domin ya manta cewa gilashin na waje ba ya ganin wanda yake cikin motar. Kamar ya fito ya gudu haka ya ji sai da ya ga sun tsaya a jikin motar hankalinsa ya kwanta, ya rasa dalili amma dai yana tunanin saboda bai taɓa tunkarar wata ƴa mace da sunan so ba ne. Kasancewar Jidda ba baya ta juyawa motar ba gefen kafaɗarta ne ta jingina ita kuma ƙawar ta juya baya, yanayin tsayuwar da Jidda ta yi ya ba Ibrahim damar kallonta sosai.
Salama ce ta ce
"Ke ma Jidda na faɗa miki ki daina damuwa kike addu'a kawai Allah zai baki mafita...
'Jidda?" Ibrahim ya furta a zuciyarsa
'Dama sunanta Jidda,.kenan Hauwa'u ce?' Ya tambayi zuciyarsa.
Yana ƙara jefawa zuciyarsa tambayar
'To mai yake damunta ake bata haƙuri?' Ya jefawa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa. Hannu ya kai jikin gilas ɗin saitin inda take tsaye ya dafa wajen.
Jidda idanunta cike da ƙwalla ta buɗe baki ta ce....
Furucin da Jiddar ta yi suka daki kunnuwan Ibrahim lokaci guda ya ga duhu ya maye hasken da yake gani, gabansa yana faɗuwa jin tashin hankalin da ya kai masa ziyara lokaci guda, da sauri ya koma ya zauna jingine da kujerar saɓanin da da ya ɗan taso yana taɓa jikin gilashin. Kansa ne ya sara da mugun ƙarfi yana jin ba zai jure wannan furucin na Jidda ba...
MAMAN AFRAH
***