PAGE 6
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 6
Tamkar wadda wani mummunan abu ke farautar ranta, haka ta dinga falfala gudu ina ta faman bin ta. Duk inda ta jefa ƙafarta nan ni ma nake jefa ta wa. Ga unguwar tamu tsit! ba mutane tamkar an yi ruwa an ɗauke, wanda tun azal haka ta gada.
Kuka nake ina kiran sunanta da kuma neman agajin mutane duk da cewa ban ga ko tsun-tsu ya wulga ba.
Daman daga ka fito titin gidanmu ka nauso kaɗan za ka tarar da corner mai shimfiɗe da wata kwaltar wacce ta miƙe ta ɗauki hanyar babban titi baki ɗaya.
Ina karyo kan corner É—in, caraf! Idona ya sauka akan Ammie wacce wata mota ta kaÉ—e ta fit É—aya ta yi ta mulmula akan titin sanadiyyar buguwar da ta yi.
Kan ta na yi ina mai sake kwaɗa ihun da duk wani mahaluƙin da ya ji ni sai ya tausaya mini, lokaci guda muka isa gareta ni da wani mai Keke-napep tare da Mata guda ukun da ya ɗauko a cikin Napep ɗin ta sa.
A gigice na rungumota jikina ina wani irin gurnanin Kuka na tashin hankali da ruÉ—ewa.
"Ammie... Ammie..! Ammie dan Allah ki tashi.... Ammie please don't do this to me, Wallahi idan kika yi haka baki yi mana adalci ba... Ammie.."
Cike da tausayi mai Napep É—in ya ce.
"Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki akwai sauran numfashi a tare da ita, gashi.. Duba ki gani..."
Cikin gigita na É—ago na kalle shi tare da Matan da ke tare dashi na ce.
"Kalli Jini yanda yake fitowa ta hanci da bakinta bawan Allah.. Daman ga shi ba ta da lafiya, wallahi ba ta da lafiya...."
"Allah sarki! Ki yi haƙuri in sha Allah za ta tashi..."
Kallon gefen da Matan ke tsaye ya yi yana mai saka hannayensa ƙarƙashin ƙeyar kanta ya ce.
"Malamai dan Allah ku taimaka mu saka ta a napep ɗinnan mu kai ta asibiti ka da mu tsaya ɓata lokaci."
A tare mukayi nasarar sanyata wanda nice na fara shiga sannan aka shigo da ita na rungumeta zuwa jikina.
"Kunga yan da Allah ya yi ikon sa ko? Dan Allah ku yi haƙuri, ku je ku samu wani ya ƙarasa da ku inda za ku tafin."
"Ba komai, Allah ya bata lafiya."
Matan su ka amsa lokaci É—aya suna ma su juyawa su ka wuce.
Mutumin da ya kaÉ—e Ammiena duk budurin da muke yana zaune a motarsa wanda nasan yana ciki hankalinsa kwance yana kallon mu, sai dai mu ba ma iya ganin sa kasancewar motar tasa duk tinted ce, gaba É—aya ba ka iya hango komai sai tsananin duhu sai dai shi dake ciki yake iya hango na waje.
Sosai na ƙurawa motar ido ina kallonta da mamakin da ya kusan sumar dani. Bayan ya ga mai Napep ɗin ya tayar ya hau hanya shima sai a sannan na hangosa a dai-dai lokacin ya tayar da motar ya wuce abin sa.
"Baiwar Allah wace asibiti zan kai ku?"
Wannan tambayar ita ce ta sanyani dawowa daga duniyar tunanin da na abka inda zuciyata ta dugunzuma zuwa ga motar da ta kaɗe mini Ammie na har ta ɓacewa ganina....
"Baiwar Allah na ce wace Asibitin zan kai ku?"
" Daman a Sokoto muke ganin likita duk farkon wata domin tana da matsalar ƙwaƙwalwa..."
"To ai yanzu kinga halin da take ciki dole tana da buƙatar agajin gaggawa, idan ki ka ce za ki nufi Sokoto da ita a yanzu koda a motar gida kuke ai akwai hatsari da kuma barazana ga lafiyarta, kingadai yan da ta ke ta faman zubda Jini."
Cike da gamsuwa da bayaninsa na jinjina kaina na ce.
" To ka kaimu Jan-bulo. Daman can ne farkon inda muka fara jinyarta a lokacin baya wanda daga nanne aka yi referring É—inmu zuwa Sokoto."
***
Federal Medical Centre,
Gusau, Zamfara state,
Nigeria.
Har muka isa asibitin hawayena ba su daina tarara ba, ina yi ina hango makomarmu ni da Bahrain idan yau Ammie ita ma ta faɗi ta mutu. Muna zuwa ba ɓata lokaci muka shige Accident and Emergency unit da ita. Bayan sun gama ɗaukar dukkan bayananmu nan take su ka shiga ba ta taimakon gaggawa. Bayan kusan hour biyu sun shuɗe sai ga wani likitan ya fito ya miƙo mana takarda ya ce muje mu biya sannan kuma naje na ɗauko katinta wanda na ce mun taɓa jinya nan a baya.
Cikin nuna damuwa mai napep ya ce.
"Likita da fatan tana lafiya."
Jinjina kai likitan ya yi da murmushi a fuskar sa ya ce.
"Da sauƙi In sha Allah."
Kallon sa ya mayar gare ni ya ce.
"Alhamdulillah! Daman ɗa zu, ina ƙoƙarin karya corner ne sai kawai ta fito ta gabana ni kuma cikin sauri na yi ƙoƙarin na kauce mata, sai wancan mutumin shima ya karya kan motar sa ba shiri, maimakon ta tsaya a inda take sai ta sake komawa hannun sa shi kuma yana ta ƙoƙari amma bai yi nasarar kauce mata ba, domin a tsiyace yake da mugun gudun da ba zai iya tsayawa a lokaci ɗaya ba. To kin san halin mutane a yau, musamman masu kuɗin nan, abu kaɗan suke jira, tun da naga bai fito ba na fahimci cewa sam bashi da niyyar ya taimaka shiyasa ban ma nufesa ba. Yanzu ga wannan... "
Ya ƙarashe maganar yana mai sanya hannu a cikin aljihun wandonsa ya ciro kuɗi ya ƙirga sannan ya miƙo mini yana faɗin.
" Ki yi haƙuri dubu biyar ce ba yawa, wallahi cinikin kenan da na yi. Amma ki ɗauko wayarki ki kira babanki ko kuma mu tafi na kai ki gida ki taho da wani, kada na barki a nan ke kaɗai."
Girgiza kaina na yi ina ta faman share hawayena na ce.
"Ka barshi kawai ai ba laifinka ba ne, ko a hakan ma mun gode sosai Allah ya biya. Ko ba ka bamu komai ba ka fiye mini wanda ya kaÉ—e ta ya tsaya yana jiran mutuwarta, da wannan taimakon har abada ba zan manta da kai ba. Ina da waya amma ba layi a ciki, sannan kuma a yanzu gaskiya ni ce kaÉ—ai zan iya zaunawa da ita kafin na samu kiran en uwanmu su zo."
"Allah sarki! To muje na kai ki gidan ki É—auko abin da za ki É—auko sai na dawo dake."
Sosai na lumshe idanuna a cikin Napep É—in ina ta lissafin rayuwa har muka iso dai-dai inda aka kaÉ—e Ammie, daga nan ya tambayeni cewa ina ne gidanmu, sai na nuna masa.
Ina shiga na tarar da Bahrain zaune ya haɗe kai da gwiwa yanata faman kuka. Yana ganina ya taho da gudu ya ƙanƙameni sosai yana faɗin.
"Aunty Beena na ji tsoro sosai, na dawo ke da Ammie ba kwa nan, gidan su Humaida ma ba kowa, mai gadi ma baya nan..."
Ni ma É—in rungume sa na yi, cikin rarrashi na ce.
"Ka yi haƙuri Bahrain...Ka yi haƙuri. Muna asibiti Ammie ba lafiya, ka dai san yanayin jikinta ba sai na faɗa maka ba. Abin da nake so da kai a koda yaushe ka zama jarumi sannan ka ƙwarara kan ka domin mu samu ciwon Ammie ya warke baki ɗaya.....Mu je na ɗauko katinta da ATM card sai mu tafi asibiti."
" To Aunty Beenafah, ina mata addu'a Allah ubangiji ya bata lafiya. Ai ko a Islamiyya kullum sai na cewa Ra'is ya sanya mahaifiyata a addu'a ba tada lafiya."
"Yauwa yaron kir ki. Zo... Zo mu tafi ana jiranmu a waje."
Ciki na shiga na ɗauko mana duk wani abin da nasan za mu buƙata domin in dai zaman asibiti ne na riga da na saba a yanzu. Wuri na ɗauko na kwashe tuwon sannan na juye miya daban na mayar da komai ciki sannan na janyo ƙofa domin dai ba mu taɓa rufe gidan ba tunda muke. Ko gate ɗin ma haka muka barshi bayan na sakaya muka shiga napep ɗin muka koma asibiti.
Muna shiga aka sake bamu wata takarda again gashi ko ta farkon da akace muje mu biya bamu biya ba.
Wurin biyan kuɗin mukaje wanda nan take aka caji kuɗi kusan dubu ashirin da takwas da ɗari bakwai, ƙuri! mai Napep ɗin ya yi yana kallona domin da alama ya razana.
"Karka damu akwai kuÉ—i a tare dani zan biya, ko tsaya mana da ka yi kawai na gode sosai."
Bayan mun biya mukaje muka karɓi magani muka koma still tana ciki ba'a fito da ita ba. Muna nan aka shige da case folder ɗinta, sai a sannan na ce mai napep ya aramin wayarsa na kira likitanta. Ina kiran sa yana jin ni ce ya kashe ya kira ni back.
Bayan mun gaisa na shaida masa halin da muke ciki da kuma cewa da suka yi na kawo mu su card É—inta.
Umarni ya ba ni da cewa na je na kai musu waya ya yi musu magana ko kuma na ba su numbernsa su kira sa.
Ba ɓata lokaci na yi duk abin da ya ce wanda su da kan su suka karɓi numbern ta shi su ka kirasa.
Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare aka fito da ita zuwa Psychiatric Unit da ke cikin asibitin. Gida aka sake turani na ɗauko magungunanta na dawo. Sai a wannan lokacin Ashiru mai Napep ya yi mini sallama ya tafi gida.
Still a daren ranar nan sai da aka sake bani takarda na je na biya kuɗin wani maganin kusan dubu talatin, na karɓo a pharmacy na kawo musu.
Sai da muka kwana huɗu a asibitin sannan Ammie ta farka,sai dai kuma, farkawa marar daɗi cikin mummunan yanayi wanda ya sakani kuka, kuka fiye da wanda nayi a baya. Domin sabbatu ta shiga yi ba sama da ƙasa, ta ƙarfin tsiya ta shiga neman cisge aikin da akayi mata a hannun damanta sanadiyyar karaya da ta samu. Cikin tsananin ɗaga murya da ƙaraji na shiga ihun kiran likita domin ba zan iya ɗagawa na barta ba.
Halin da Ammie ta shiga a wannan lokacin haƙiƙa ya sakamu cikin tashin hankali da gigita. Hali ne wanda ko maƙiyanta ya kalle ta sai ya tausaya mata.
Nan take likitoci suka shigo suka rufu akanta, bayan sun gama dubata ba jimawa bacci ya É—auke ta da alama allurar bacci suka yi mata.
Mun share kusan sati Ammie tana cikin wannan halin wanda har ta kai ta kawo ma bana son ta farka gudun kada ta tashi ta nemi fama ciwon ta.
Ga damuwar Bahrain ta wani fannin tana matuƙar sosa mini zuciya, bana son ganin sa cikin halin da yake.
Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. A hankali a kwana a tashi muka shiga cikin sati na biyu wanda Alhamdulillah! Jikinta ya fara sauƙi ciwon ta shima da sauƙi sosai domin a yanzu ta daina farkawa cikin firgici da tsoro ko kuma sabbatu. Sai dai idan ta farka tayi shiru bata cewa komai ba.
Yau ma koda ta farka, a lokacin ina zaune gefenta na ƙura mata ido kawai ina kallonta yayin da Bahrain ke can waje akan tabarma da waya a hannunsa yana sauraren karatu.
"Allah sarki Ammiena! kin farka?"
Na furta mata hakan ganin yanda ta ƙureni da kallo. Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana kallona kamar yanda ta saba sannan daga ƙarshe ta gyaɗa kanta a hankali ta mayarda idanunta ta rufe sai hawaye. Cikin sauti marar tashi ta ce.
" Bani ruwa Beenafah.."
Da sauri na buÉ—e locker na É—auko ruwan gora na bata tasha a hankali na mayar a locker sannan na kalle ta cike da wani sabon tausayin ta na ce.
"Sannu Ammie, Allah ya baki lafiya, Allah yasa wannan ciwon ya zamto kaffara. Kada ki zafafa tunani kin ji Ammie,Bari na kira likita."
Ina fitowa na kalli Bahrain na ce.
"Bahrain ka je Ammie ta farka, zan je na kira likita yanzu."
***
Sati Uku mukayi a asibitin, wanda mun kashe kuɗi sun kai dubu ɗari huɗu da wani abu. sai sayen magani muke, yau wannan gobe wannan. Amma Alhamdulillah! Abu mafi muhimmanci shine, ta samu sauƙi sosai wanda wannan shi ne babban burinmu.
Yaya Ashiru, wanda ya zamto Yayana a yanzu domin ya tsaya mana a lokacin da ban yi tsammani ba. Da shi muke duk wannan zirga-zirgar, ko sau ɗaya bai taɓa nuna mana ya gaji ba, kuma duk wani abin da ya kamata ace naje nayi shi yake tsayawa tsayin daka ya yi mana shi, hakan yasa na ji sa wani mutum na daban a cikin duniyata.
***
Ranar Monday da safe likita ya kirani office É—insa ya bani takardar sallama tare da takardar refferal zuwa asibitin Sokoto inda muka saba jinya.
Amma ya ce zamu iya zuwa gida mu shirya zuwa kwana biyu sai mu tafi, domin condition ɗinta ya yi sauƙi sosai In Sha Allahu babu wata damuwa. Yaya Ashiru shine wanda ya zo ya kaimu gida da kansa.
A daren da muka koma gida ne naje shagon Baba mai shago na bashi katin Daddy na ce ya É—auki numbern wayarsa ya kira shi ya ce mi shi Beenafah ce.
Na fi minti talatin a tsaye bai kira ba, daga ƙarshe na ba shi ɗari biyu na ce ya saka kati ya kira mini shi.
Sake kiransa ya yi ya miƙomin wayar na kara a kunnena, ƙirjina na dukan uku-uku na yi masa sallama.
✍️ OUM-AMEER ✍️