1&2
MANARAH
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
DEDICATED TO
ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai maki a duk inda ki ke. 🫶🥰
PG 1&2
Ihu da kururuwar neman agaji da ake ne suka fito da duk jama'ar da ke cikin gidan. mutuwar tsaye kowa ya yi cike da tashin hankalin abin da na mujiyarsu suka hasko masu.
Umma da ke tsaye lokaci ɗaya ta ji kafafuwanta na neman kasa daukarta, ji da ganinta tsayawa suka yi na wucin gadi.
Ba shiri ta yi zaman 'yan bori tare da saka hannuwanta biyu ta dafe kanta da ke barazanar tarwatsewa.
Alhaji da ke tsaye bai san sa'in da wayar hannunsa ta faɗi ba. Hajiya ce ta fara salati da sallallami
"Kai Hisham! Yanzu duk faɗan da ake maka baka ji ba. Faɗa da karuwa a cikin gidan Mahaifinka"
Ta ƙarasa Maganar ta na ƙoƙarin fizge figaggiyar yarinyar da ya ke jibga tamkar Allah ya aikosa.
Ganin ba shi da niyyar saurarenta tsakiya ta shiga tare da riƙe belt ɗin.
A matukar fusace ya ɗago kansa idanunsa sunyi jajur, jijiyoyin kan shi sun tashi.
"Ki fita a tsakani kafin in bi ta kanki. In ban kawo mace a gidan mahaifina ba a gidan uban wa kuke so in kaita? Har kin manta ke ce kika kulla makircin da Alhaji ya ce in ya kara gani na da mace a Hotel ko wani wuri bani ba shi. Na dawo kawo mata a gidan nan shi ne za ki zo kina mini katsagal, ko ki kauce ki bani wuri ko in haɗa dake. Shi gurbin ido ai ba ido bane"
Ya karasa Maganar a fusace.
"Ki matsa ki ba mu wuri. Cin mutumcin juna ai ba baƙon abu ba ne a wurinmu. Wallahi sai ka san wa ka daka"
Budurwar da ke bayanta ta fada.
"Bakin ki bai mutu ba kenan"
Ya karkashe maganar tare da zabga nata belt. Hajiya da ke a tsaki ihu ta daka lokacin da belt ɗin ya sauka a gadon bayanta, ba shiri ta ba su wuri suka ci gaba da dambatuwa.
Umma da ke yashe a ƙasa baƙin cike ya kawota wuya ba ta san sa'in da ta miƙe ba.
Zafafan marukan data ɗauke Hisham da su ne suka saka shi sakin belt ɗin ya dafe kumatunsa.
"Hisham! Hisham!! Ya Allah ka dauki rayuwa in huta da wannan bakin ciki"
Kukan da ya ji karfinta ne ya tilasta mata datse maganar.
"A huce Umma. Ban cika son in GA kina Kuka ba kinsan kaf gidan nan ke ce me kaunata. Na san sauran duk munafukai ne biyayya da bin umurninki ya saka na daina kai mata gidana ko Hotel. Yanzu duk shiryuwar da na yi na koma kawo Bebs ɗina gidan nan Umma bai yi miki ba?"
Tsawar da mahaifinsa ya daka masa ce ta saka shi yin shuru, amma babu alamar tsoro ko ɗar a tattare da shi.
"Kana zubar min da mutumci a cikin gidana na sunnah ka kawo karuwa Hisham? Anya akwai ƙwaƙwalwa a cikin kan ka kuwa. Ko da ya ke lokaci na ɗibar maka sai na saka kayi nadamar da baka taba yinta ba. Jikina ya jima ya na bani anya kai jinina ne kuwa?"
Tamkar harbin bindiga haka Umma ta ji maganar mijin nata ta daki zuciyarta.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Alhaji anya ka san abinda kake fada kuwa? Kada ɓacin rai ya sa ka furta abinda ba shi ba ne. Kar ka sheganta ɗan ka tare da lalata aurenmu na har abada"
"Aa fa Safiya! Ki barsa ya faɗin abinda ke ransa. Ni kaina na sha tambayar kai na anya ba kwashe-kwashe kika yi aka haifa wannan fitinannen yaron ba"
Rufe bakinta ya yi daidai da shaƙar wuyanta da Hisham ya yi.
"Karya ne! Ki sheganta ni kinfi kowa sanin wace ce tsaye a gabanki. Ban hada Mahaifiyata da kowa ba a kanta sai a mutu har liman a cikin gidan nan"
'ya'yan Hajiya da ke tsaye a gefe ganin abinda ya yi ma mahaifiyarsu a fusace suka yi kansa da duka. Sai dai ko gezau! Ya ki sakar mata wuya.
Ganin gida ya rikice ya saka Deena sulakewa BA tare da kowa ya sani ba.
Alhaji da ke tsaye ya na kallon abin kamar a fim. Gidansa ne ya koma haka? Hisham ɗin da ya haifa ne ke riƙe da wuyan Matarsa wadda matsayin uwa take a wurinsa.
Duƙawa ya yi ya ɗauki wayarsa tare da karata a kunne.
Da kyar da jiɓin goshi Umma ta yi nasarar ɓanɓare Hisham. Ba a ɗauki dogon lokaci ba suka ji sautin motar 'yan sanda.
Shigowarsu cikin gidan ta saka Umma jin gabanta ya yanke ya daɗi.
"Ga shi can. Ku kama shi ku kulle har sai na bukace shi"
Alhaji ya karasa maganar tare da nuna masu inda Hisham ya ke.
"Ka saurareni don girman Allah! Duk lalacewar naka naka ne. Hannunka ba zai taɓa lalacewa ba ka yanke ka yar"
"Kiyi min shuru! Sai dai in bai isheni da ciwon ba ne tuni na yanke ɗan banza na yar. Ina ki ka ƙara furta ko da kalma ɗaya ce a tare zan saka a haɗa muni ku a kulle"
Mutuwar tsaye Umma ta yi, hawayen da ke fuskarta cak suka tsaya. Hausawa suka ce ko mutuwa ta na tsoron idon mahaifi amma a gaban idanunta jami'an tsaro suka tasa ƙeyarsa suka fice. Ta kasa kwakkwaran motsi sai da kaf mutanen da ke wurin kowa ya watse ya rage daga ita sai Hajiya da ke dafe da wuyanta.
Jajen idanunta ta kafeta da su.
Murmusawa Hajiyar tayi tare da dafa kafaɗar Umma.
"Safiyyatu kenan! Ko ba komai a yanzu na san kin fahimci ruwa ba sa'an Kwando ba ne. Sannan kin gane haihuwar namiji bata ƙareki da komai ba fa ce masifa da tashin hankali. Shekara goma na kwashe a cikin gidan nan kafin in Samu haihuwa, kwatsam na haifi mace. A haka na yi ta tara 'ya'ya mata, Mijinmu ya auroki ne domin ki haifa masa Magaji sai ga shi wata goma kin aje masa ɗa namiji. Amma tambayar da nake so in yi miki ita ce ɗa namijin ke da shi ya zame maku kwanciyar hankali ne? In dai ina numfashi ko zanyi yawo tsirara Magaji sai ya zame maku makashi"
Ta na kaiwa nan ta rabata ta wuce.
Duk da ba yau ce rana ta farko data faɗa mata irin waɗannan maganganun ba. Tabbas na yau sun kara sakata cikin firgici da tashin hankali.
Da kyar ta karasa ɗakinta tare da zubewa saman gado. Bedside ta bude, hoton Hisham ta fiddo.
Kafe shi da ido ta yi ta na kukan zuci.
"Tarbiyya, ilimi, addini. Da su muka rene ka, lokaci ɗaya ka canza daga Hisham me addini da tsoron Allah ka koma Hisham wanda baya jin kunya bare tsoron fushin mahaifinsa. Kuruciya ta banyi abubuwan da kake yi ba bare in ce ni ka gada haka shi ma Mahaifinka"
Kukan da ta samu ya zo mata ne ya saka ta rage raɗaɗin da take ji.
Hisham kuwa duk da ya na can amma zuciyarsa na wurin Umma. A cell aka watsa shi. Mutum biyu da ya iske da sauri suka miƙe tare da furta Me gida.
Da mamaki ya ke kallonsu domin yau ce rana ta farko da ya fara ganinsu.
"Me gida kamar baka gane ni ba ko. Ni ne fa wanda ka taba yi ma nasihar in bar yin sata in kama sana'a ka manta har jari ka bani?"
Dariya Hisha yayi domin shi da ya ke ɗan iskan kansa, ta ya zai yi ma wani nasiha ya daina iskanci.
"Ba ni bane kalleni da kyau dai malam"
Hisham ya fada ya na kokarin zama.
Dayan ne ya karbe zancen
"Wallahi me gida kai ne. Ka manta a can garin da muka fara zama kai ne shugaban babban masallacin garin. Wallahi kai ne ga shi nan har gemon na gane. Ka manta kai ne ka ce mu bi Allah mu daina abubuwan da muke. Me gida don Allah ka daina nuna kamar baka gane mu ba, ni abinda nake tambaya Me ya kawo ka cell?"
A karo na farko da ya ji faɗuwar gaba ta ziyarce Hisham. Da gaske suke yi domin a fuskarsu babu alamun wasa. To in haka ne wa suka gani kenan?...
Meenat A 'Yandoma
***
MASU BUKATAR LITTAI SU SHIGA NAN CIKI👇👇👇