PAGE 06.
by @sumy6163
⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡
_*(pages of my destiny)*_
STORY AND WRITTEN BY:
Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Page 06.
Kiyi haƙuri Aishatu, ni Hassan mijinki na amince zan zauna da ke ko da na wani irin hali, ko da ke mayyar ce da gaske bare kuma na san ba haka ba ne, kai wallahi ko da kuwa aljana ce ke zan zauna da ke, ba zan taɓa iya sakinki ba.
Salati su Gambo da ke tsaye a wurin suka sanya, Huse ta ce, "Wai ka san me ka ce kuwa Hassan, ka na cikin hayyacinka kuwa, ka san abin da ka ke fada, ko dai ta yi maka wani siddabarun ne irin na su na mayu, tab! Dankari."
Gambo ta amshe da faɗin, "Au, to ke dama kin tsanman zata bar shi haka ne, sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ya kafe kai da fata sai da aka yi wannan ƙaddararren auren."
Ɗago rinannun idanunsa ya yi ya dubi Gambo kafin ya daka mata wata tsawar da ta razana mazauna wurin, "Ke Gambo!! Akwai sa'anki ne a nan, kar in ƙara jin bakinki munafuka, tashi ma ki bamu wuri."
Sum sum ta miƙe ta fita, don ba ƙarya ta firgita da yanayinsa. Ƙwafa Huse ta yi ta bi bayanta tana yaɗa habaici da zagi. Yaya Salisu ne kaɗai ya rage. Bayan ya bi kannen nasa da kallo ya mai da dubansa garemu. Faɗa ya shiga yi mana da nasiha kafin daga ƙarshe ya dubi Hassan ya ƙira sunansa. Bayan Hassan ɗin ya amsa Yaya Salisu yaɗaura da faɗin, "Ka daure zuciyarka ka yi abin da Inna ta ce, bin umarnin iyaye wajibi ne, kar ka bari ta yi fushi da kai, saboda fushin iyaye yana tare da fushin Ubangiji, ka yi mata saki irin wanda zaku dawo da zamanku idan komai ya lafa."
Tuni gudun hawayena suka ƙaru bayan jin maganar da ta fito daga bakin Yaya Salisu. Dubansa Hassan ya yi da wani irin yanayi da na kasa fassarawa ya ce.
"Hakan ya na nufin ke nan Yaya kai ma ka yarda da abin da suke faɗi a kan Shatu?, kuma ka bada goyon baya wurin sakinta?" Girgiza kansa ya ke kafin ya ce, " Bazan iya ba, wallahi bazan taɓa iyawa ba, har abada ni Hassan bazan taɓa iya furtawa ko rubutawa Shatu takardar saki ba, ai ko Ubangiji ya ce kar a yi wa wani biyayya wurin saɓa masa, sakin Shatu zunubi ne, bata da haƙƙin kowa, bazan saki matata ba."
"To ya ka ke son muyi Hassan, ka san dai halin Inna, tun da ta faɗa sai an yi. "
"Taimako ɗaya za ka min Yaya, kawai ka ce wa Inna anyi sakin, ni kuma zan maida Shatu gidansu ta yi jinya, zuwa lokacin da zata ji sauƙi, komai ya lafa sai ta dawo, ka yi min wannan alfarmar don Allah Yaya." Ya haɗe hannunsa alamun roƙo.
Ɗan jimm Yaya Salisu ya yi kafin daga bisani ya ce, "Shi kenan Hassan, zan maka wannan afarma, Allah ya sa hakan shi ya fi alheri." Yana gama magana ya tashi ya fice shi ma aka bar mu mu biyu.
Matsowa Hassan ya yi kusa da ni, ya yi ta rarrashi na sai da ya ga na rage damuwa kafin ya shiga ya haɗo min kayan sawata, abun hawa ya je ya samo, shi kaɗai ya tallafe ni ya kai ni har cikin motar, ya dawo ya ɗauki kayan da ya haɗa min. Ina jin yanda su Huse suke ta shewa suna faɗin Allah ya raka taki gona, a je can a cinye iya da Baba, wataƙila suma suna taɓawa.
Wani malolon baƙinciki ne ya ke ziyartata duk lokacin da aka aibanta iyayena. Bayan Hassan ya dawo da jakan kayana muka ɗauki hanyar gidanmu. Godiya kawai na ke wa Allah da tasbihi a raina, yau kuma irin shafin da littafin ƙaddararta ta buɗo min ke nan. Aure wata ɗaya na koma gidanmu. Alhamdulillahi.
A cikin motar haƙuri Hassan ya ke ta faman bani, yana rarrashi na haɗi da kalaman kwantar da hankali. Jin sa kawai nake yi, don na tabbatar a yanzu ban ga abin da zai kwantar mini da hankali ba. Na yi nadama, nayi danasanin zuwa wannan suna, sai dai abu idan aka ce ƙaddara, to ba yanda ka iya, baka isa ka tsallake ta ba.
Ko da muka iso gidanmu, Hassan ya cicciɓo ni a hankali, duk da ina jin yanda ƙafar tawa ke raɗaɗi, amma haka na daure ban nuna masa ba. Ya yi sallama kafin ya shiga da ni.
Hajjo ta na kwance tsakar gida tana shan hantsi, kawai sai gani tayi ya shigo da ni a tallafe kamar jaririya, salati ta sanya ta na tambayar abin da ya same ni bayan ta shimfiɗa tabarma ya ajiye ni a kai. Bai amsa ta ba sai ma fita da ya yi ya shigo da jakan kayana.
Dafe kirji na ga Hajjo ta yi tana faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihi taji'uun, me zan ga ni yau ni Mariya, me yake faruwa ne wai?" Ta kalli wannan ta kalli wancan, dukanmu kowa ya kasa magana, tambayar duniyan nan ta mana ba wanda ya tanka mata. Ni dai ina zaune sai ido, don zuwa yanzu kukan ma na daina sai zuciyata kawai da nake jin tana zafi. Shi kuwa Hassan hawaye kawai ya ke yi ya kasa furta komai.
Hajjo shiru ta yi ta na kallonmu, kafin ta jawo lulluɓi ta yafa, ta shuri takalmanta ta yi waje, ashe yaro ta je nemowa ya ƙira mata Baffajo. Ba jimawa kuwa ya iso gidan. Tambayar abin da ya faru shima ya yi, ba wanda ya tanka, sai da ya birkice, ganin ransa ya ɓaci ya sa da ƙyar na buɗe baki da muryata da bai fita sosai na ce masa, "Ba komai fa Baffajo, kawai dai ƙafata ce ta ji ciwo, shi ne ya dawo da ni gida, don can ɗin ba kula sosai zan samu ba, shi yasa ya dawo da ni gida.
Baffajo ya dubi Hassan yanda yake ta sharɓan kuka ya kaɗa kai ya ce, "To yanzu kai Hassan matar taka ta ji ciwo shi ne kake ta faman wannan kukan kamar wani abu ne ya faru?, to Allah ya kyauta." Cewar Baffajo.
Hajjo kam ji na kawai ta yi ba wai don ta yarda ba, sai dai ganin kamar ba mu cikin natsuwa ya sa ta fadin, "To ai shikenan, Allah ya sauwaƙe."
Sai Baffajo ne ya samu zarafin tambayar garin yaya hakan ta faru. Na ce, "Tsautsayi Baffa"
Shi ma ɗin Allah ya kyauta kawai ya ce, ya shige turakarsa. Hassan ma sallama ya min ya tafi da alƙwarin zai dawo anjima ya duba ni.
GIDAN INNA.
Al'ummar gidan Inna kuwa yau kamar sallah don farinciki. Tun bayan da Yaya Salisu ya sanar da su Hassan ya saki Shatu saki ɗaya. Dama ya tarar Inna tana ta masifa dole ne sai Hassan ya saki Shatun, don Huse tas suka faɗa mata abin da Hassan ɗin ya ce, har da ƙarin gishiri.
Huse bata koma gidanta ba sai bayan azahar, bayan sun gama bidirinsu, da aibanta Shatu da iyayenta, Gambo kuwa sai goshin magariba ta tafi. Kowaccensu cike da farinciki sun raba mata da dakin mjinta, su kuma suka koma nasu.
(Wato duniya ta lalace, a rayuwar da muke yi yanzu kowa kansa ya sani, ba wanda ya damu da me dan'uwansa ke so, idan mutum ya samu kowa ma ya rasa ba damuwarsa bane, an manta da hadisin da annabi yake faɗin "imanin ɗayanku baya cika, har sai ya so wa ɗan'uwansa abin da yake so wa kansa".
Kowa aibinsa yake ɓoyewa ya ke hango na wani, kowa take lafinsa ya ke ya hango na wani. Wallahi da a ce kowa zai dinga duba kurakuransa yana gyarawa, bazai ga na wani ba, don da ya gyara wannan zai hango wani, kun ga kenan bai gama da nashi ba ma, bare ya samu lokacin hango na wani. Allah ya sa mu dace, ya kuma bamu ikon gyarawa).
SHATU.
Zamana da Hajjota sai na fara samun natsuwa da kwanciyar hankali, tana kula da ni sosai, kuma ƙafar ma tana sauƙi, sai dai har yanzu ba na takawa. Kullum Hassan sai ya zo sau biyu ko uku, kuma ko wani zuwa da zaiyi sai ya taho min da abu, kaji kuwa tsallaken kwana ɗaya kawai yake yi. Yaya Salisu ma bayan kwana biyu yake zuwa ya duba gyaran da ya yiwa ƙafar.
Yau kwanaki na goma a gida, kuma a yau ne Yaya Salisu ya warware gyaran da ya wa kafar tawa, ta yi kyau kuwa, sai kumburin da bai gama saɓewa ba har yanzu. Sanda ya bani ya ce in dinga dogarawa da shi ina tafiya.
Bayan tafiyarsa ne Hajjo take tambayata wai me ya sa ba wanda ya zo duba ni a yan'uwan Hassan sai Yaya Salisu kaɗai? Na dube ta na ce.
"Hajjo ai kin san ba wani shiri sosai muke yi da su ba. Huse kan ma jego take, Adda Habiba kuwa wataƙila bata ji ba tunda ta yi nisa."
Hajjo ta ce, "Amma dai ai ciwo ya shafe komai, duk wannan ba uzuri ba ne, ita kanta Innar taku bata zo ba, bata kuma turo ba."
A nan kam bani da amsa sai shiru, ƙare mini kallo Hajjo ta yi ta ce, "Tun dawowarki na fahimci akwai abin da ke faruwa, na sha kamaki kina zaune kina tunani, wai me ya ke faruwa ne, zamanku da Hassan ɗin ne akwai matsala?"
Na girgiza kai na kafin na ce "Ba matsala tsakanina da shi, matsalar dai da 'yan'uwansa ne." Nan na kwashe komai na faɗa mata ina hawaye.
Abin da ban taba jin Hajjo ya yi ba yau shi tayi. Wata ƙatuwar ashar ta lailayo ta ce, "Kan bala'i, wallahi idan an isa shegiya nake, 'yar tawa za a laƙaba wa maita, dama abin da ya faru kenan ki ka ja bakinki ki kayi shiru? lallai kuwa Zainaba ta tsokalo tsuliyan dodo, ashe har ta mance wace ce ni, tabbas ta manta baya, idan banda ma Baffajo da ya tsaya tsayin daka a kai na, ai da duk ƙauyen nan ba wanda ya isa ya ɗaga min yatsa ya sauƙe ban karya ba. Zainaba da zuri'arta sun tafka babban kuskure wallahi."
Tana gama magana ta zari mayafi ta yafa, ta shuri takalmanta ta yi waje, duk ƙiran da nake mata bata ko juyo ba bare ta ji me nake faɗa. Sandata na dogara na yi hanyar waje ina ƙwalawa Hajjo ƙira, sai dai da fitana ko ƙuranta ban gani ba, wani yaro na ƙira na ce masa ya duba min Baffa a makaranta. Ciki na dawo na zauna jugum ina mai danasanin sanar da Hajjo wannan labari, da a ce na san abin da zai biyo baya kenan da na ci gaba da ajiye shi a raina.
Ina nan zaune Baffajo ya shigo, tambayata ya yi abin da ke faruwa, nan na sanar da shi komai da kuma yanda Hajjo ta harzuƙa ta fita.
Dafe kansa na ga ya yi kafin ya ce, "Kassh! Ai fa al'amari ya riga ya lalace, tun da kika ga Hajjo ta fita haka to sai abin da Allah ya yi, bari na yi maza na bi bayanta." Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa.
Shiru na yi ina addu'ar Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi.
HAJJO.
Hajjo tana fita hanyar ta ɗaya ta nufi gidan Inna, ko sallama bata yi ba ta afka, nan ta tarar da ita kishingiɗe bisa tabarma tana shan fura.
Inna ta dago ta ce, "A'a, lafiya kuwa Mariya, kya shigowa mutane gida ba ko sallama, sai ka ce gidan kafurai?"
Hajjo ta dubeta da kyau kafin ta ce, "Zainaba kenan, ai a inda akwai aminci ake nemowa mazauna wurin aminci, ba zuwa nayi don in nema miki aminci ba, zuwa nayi inji ba'asin abin da kuka yiwa ɗiyata."
Inna tasowa tayi daga wurin da take ta zo har gaban Hajjo ta nuna mata yatsa ta ce, "Hmmm, ɗiyarki? ɗiyarki fa kika ce, idan kin manta ne sai na tuna miki."
Kar ki faɗa min maganar banza Zainaba, ina son ki bani gamsasshiyar hujjar da ya sanya ki laƙabawa ƴata maita, idan kuma ba........"
"Idan kuma me? Na ce idan kuma me ye? An ce mata mayyar kiyi abin da zakiyi Mariya, ba mayyar ba ce, ganin idona ta tsallake yarinya ta farfaɗo, wani hujja ki ke nema da ya fi wannan?"
Wani dariya Hajjo ta yi kafin ta ce, "iya wannan ne hujjar ta ki, to wallahi tun wuri ki maza ki janye wannan ƙage da kike mata, idan ba haka ba kuma kinsan mai zai biyo baya, ke kinsan wace ce Hajjo, kin sanni farin, kin san me zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba, wallahi tun wuri ki fita a gonata. Kuma ki faɗawa ɗanki ya maza ya kawo min takardar sakin Shatu don ta gama zama da dangin marasa mutunci."
." Hmmm, saki kuma?, Yo ai sai dai idan cikashe mata sauran biyun zaiyi, kuma ki zuba ido ki gani, idan dai ni na haifi Hassan a cikina, yau zai aikowa mayyar ƴarki sauran cikon sakinta. "
Ina nan ina jiransa, idan kuma bai sakar mini 'ya ba to tabbas shi ba d'an sunnah ba ne.....✍️✍️