RASHIN SANI

PAGE 13

by @sumy6163

💫💫RASHIN SANI 💫💫

STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).

Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.

Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.

PAGE 13

Biki ya kankama gadan gadan, su Aimana kirjin biki, sai shiga take tana fita kamar wata uwar mata, wai ita ana bikin favourite sis, tare sukaje rabon kati, ita take raka ta duk inda zataje, koda mai gyaran jiki tazo, Aimana tace ita ma sai an mata, tare ake musu, saidai ba iri daya ba, ita na daidai ita ake mata.

Koda aka shiga satin biki, sai sungulla ya karu, hakan sai yasa Aimana takan wuni ma ba tare da ta kira Abdul ba, a cewarta zai fada mata idan Kamal yazo, tunda tace ya tabbata ya fada mata.

Ranan laraba sukayi bridal shower, Aimana ba kadan ba tayi kyau musamman kuma dayake an mata gyaran jiki kuma ya karbeta sosai, tasha kunshi hannu da kafa, kasancewarta fara sai ya fito yayi das a kan fatarta, su Aimana an gyagije kamar ba diyar mallam Tahir ba.

Karfe shida suka dawo gida, sallah kawai sukayi ko takan abinci basu bi ba, daga nan suka shiga wani hudima daban.

Washegari sukayi walima, an gayyato manyan malamai, suka baje wa jama'a ilimin, anyi nasiha mai ratsa jiki, musamman akan zaman aure da kuma biyayyar miji, an kuma tabo fannin iyaye da kuma tarbiyyar 'ya'ya anci ansha an raba gift, ga souvenirs mai dauke da hoton amarya, komai Masha Allah.

Ranan juma'a, dubban mutane suka shaida daurin auren Nana Fatima Abubakar da angonta, Sadiq Maitama.

Aimana fa ba zama itace nan itace can, duk abunda amarya take bukata Aimana ce zatayi ko ta kawo Mata, gabadaya ta sa ran watakila Kamal zaizo daurin auren, don Humaida ma sunzo duk event dinda akayi, kuma Ummah ma tazo walima kuma yauma tazo.

angwaye sun shigo sun kwashi gaisuwa, anyi hotuna, sannan suka koma masukinsu, don gobe tare zasu wuce da amarya.

Aimana ba ita ta samu kanta ba sai can yamma, taje ta karbo wayar Adda Nana ta dannawa Abdul Kira, yana dagawa ko sallama batayi ba ta shiga tambayar sa ko Kamal yazo.

Wallahi ko Aimana, kinada matsala, wai nikam uwar me ma Kamal din zai baki ne, da kika damu kina son yazo, to baizoba.

Cikin sanyin jikitace, "Kayi hakuri ya Abdul, bansan na dameka ba"

Tana fadin haka ta kashe wayar, kawai sai ta kifu a wurin ta shiga kuka, wanda ita kanta bata san na menene ba.

Mama da ta shigo dakin tun dazu, ganin yanda Aimana ta wuce da sauri, don ita ta dauka wani abune ya faru, taji duk abunda sukace, dayake wayar a speaker take.

Wani matsanacin tausayin Aimana ya kamata, tabbas Aimana tana son Kamal, "Ya Allah idan akwai alkhairi a wannan al'amarin ka tabbatar dashi, idan kuma babu, ya Allah ka musanya musu Shi da mafi alkhairi, ya Allah ka kawo wa zuciyar wannan baiwar taka dauki".

Juyawa tayi ta fita, Aimana bata san ma Mama ta shigo har ta fita ba.

Abdul ko jin yadda Aimana tayi magana cike da karaya da sanyi, sai yaji kamar bai kyauta mata ba,a take yabi Kiran, Saidai Aimana tana gani,bata dauka ba, bata son yaji tana kuka, tasan zai shiga damuwa, shiyasa taki dagawa.

Hankalinsa ya tashi matuka, idan akwai abunda yake kiyayewa bayan fushin iyayensa to fushin Aimana ne, baya son ko yaya ne ya ganta cikin damuwa.

Kokarin kara kira yaci gaba dayi, amma saida ya kusan 14 miss call ba amsa, cikin gidan ya nufa, yana zuwa ya wuce sashin da yasan amarya na ciki, don ya tabbatar ana zai samu Aimana.

Koda ya tambayi ina take Nana tace bata sani ba,ta dai karbi wayanta ta fita, fita yayi ya nufi main parlour, ya tambayi Aimana bata nan, ba inda bai nemeta ba, Mama tana kallonsa yanda ya rikice, har tayi kamar zata fada masa, sai kuma ta fasa, gara a barta tayi kukan ko zafinda take ji a ranta zai ragu, kuma tasan ganin Aimana haka shima sai ya shiga damuwa.

Haka ya karaci bulayin nemanta bai ganta ba ya hakura.

Aimana kuwa tana can taci kuka har ta gaji, bacci ne ya dauke ta a wurin ba tare da tasani ba, Mama da ta shiga taga tana bacci, sai ta tofeta da addu'o'i ta fita ta barta, ba ita ta farka ba sai kusan magariba, shima karar waya ne ya tada ta.

Tashi tayi ta shiga toilet ta wanko fuskanta, sannan ta fito taje kaiwa Nana wayarta.

Mama tana nan a wurin bata tashi ba saida taga fitowar Aimana tukun, Allah sarki uwa Kenan, duk yawan mutanen gidan ba wanda ya kula da halinda Aimana take ciki, amma dayake Mama uwace, duk inda take idonta na kan yaranta.

Haka aka karashe wannan yini, washegari kuwa aka tashi da shirin kai amarya gidanta, mutum goma ne zasu bi jirgi, ciki harda amarya, yayinda sauran zasubi mota, don haka su da wuri suka wuce.

Aimana tana cikin masu tafiya a jirgi, sai rawan kai take, uwa angon kare, ta manta da abunda ya faru jiya tuntuni.

Abdul ne ya shigo da safe bayan 'yan tafiya sun tafi, gidan ya rage,daga su Mama masu tafiya da amarya sai 'yan tsirarin mutane da suka rage, Dada Petel ma tazo, da yaranta duka guda biyar, ya durkusa ya gaida iyayen nasa, kafin ya shiga tambayan Aimana.

Ummie ce tace masa tana can tare da amarya

Mikewa yayi ya shiga wurinsu, ganin Aimana yayi sai rawan kai take wai ita zata shiga jirgi, gabadaya ta manta abunda akayi jiya, ta inda Aimana ke burgesa Kenan, bata riko, amma fa Aimanar yanzu ba ta da ba.

Ganin haka shima sai ya waske, ya gaida Adda Nana, Aimana kuwa ta gaida shi, Adda Nana tace, "Oh su Aimana anyi hankali harda gaida Abdul".

"Ba dolen mutum ba, ko yasha suburbuda, ai nake fada miki Adda Nana, makarantan nan ba karamin gyara Aima yayi ba".

Dariya suka yi gaba daya, Aimana tace "sai kayi kuma, kaga ni yau banda lokacin kulaka, anjima kadan muna bisa hazo".

"Wai Adda Nana wannan yarinyan zakusa a jirgi, tabdi lallai akwai kwaba, kar dai aje ta kunyataku a gaban mijinki, a gane bata taba shiga jirgi ba, kodayake, wannan ko a motar ma bata taba doguwar tafiya ba". Cewar Abdul

Aimana kuwa gyara zaman ta tayi tace, ai sai kayi tayi, nidai na fada maka yau banda lokacin Ka, bazan kulaka ba ma bare mu rabu muna fada, kaga idan na tafi akace na mutu, shikenan zaka rika tunani da fadan karshe da mukayi".

A take fara'ar fuskansa ta Ragu,yace, "banason maganar mutuwa yanzu Aima, insha'Allah sai kin girma kinyi aure kin haifa mini yara kyawawan, da kaina zan kaiki har dakinki".

Wani murmushi Aimana ta saki, a take ta fara hasaso gashi an daura aurenta da Kamal, an kaita gidansa, suna rayuwa cikin jin dadi, harda yara.

Firgit ta dawo daga tunanin da ta tafi, jin Kamal ya girgizata, ta kallesu gabadaya sun zuba mata ido.

"Meya faru", ta samu kanta da tambaya cike da haushi, don Abdul ya katse mata tunanin ta mai dadi.

Abdul yace, "ba dole ki tambayi mai ya faru ba kin zauna kina ta murmushi ke kadai kamar wadda akawa albishir na kujeran Makkah".

Sai kuma ta sake sakin wani murmushin,yace "ikon Allah"

Adda Nana da take lura da ita tunda akayi maganar aure take ta murmushi, itama murmushin tayi kafin tace...

"My Aima wa aka samo mana ne, don dai wannan murmushin kam da biyu".

Zaro ido tayi tace, "Adda Nana, wani irin wa aka samo kuma, kawai dai wani abu nake tunawa".

"Kodai wani mutum kike tunawa ba" Abdul ya fada yana dariya.

"To inma wani mutum dinne sai yaya, kaga ya Abdul banson fada dakai, amma sai kaja munyi ko, tam"

"Yi hakuri my sisto, rabu dashi, anjima ma ina zai ganki"

"Kuma haka nefa"

Haka suka cigaba da hiransu cike da raha da jin dadi, har aka zo aka kira Nana don ta shirya sannan tayi sallama da iyayenta, kafin suka watse.

Misalin karfe biyu jirginsu ya daga, sun isa lafiya, an Kai amarya gidan iyayen miji, kuma an tarbe su cikin mutunci da gimamawa, da dare akayi dinner kuma ya kayatar, daga nan kuma aka wuce da amarya gidanta, washegari kuma yan biki zasu juya.

Da safe misalin karfe goma suka dunguma sukaje suka ga gidan amarya, Masha Allah, Daddy ya zuba mata dukiya, gida yayi kyau, daga nan suka mata sallama suka tafi.

Sunsha kukan rabuwa, kafin su watse, aka barta a gidan mijinta da halinta,a ranar kuma suka juyo, sun isa lafiya kowa tayi hanyar gidanta, biki kuma ya kare.

Aimana duk ciwo take ji a gabbanta, lokacin bikin bataji wannan gajiyar ba sai yanzu, ashe haka bikin yake, gashi ta cinye sati biyu a hutun ta duk akan bikin nan, saura mata sati biyu, acikin sati biyun kuma ta kashe sati tana huta gajiya, yanzu haka saura sati ta koma, still ba Kamal, ta kuma kudiri aniyar duk wuya duk rintsi sai ta ganshi.

Yau ta kama saura kwana uku ta koma, amma Kamal bai zoba, bayan ta gama abunda zatayi tace wa Mama,zata wurin su Afrah, Mama tace to ta gaida Ummie idan take.

Tana fita ta tare dan sahu tace FUGUS zai kaita, da yake akwai dan kudi a hannunta, hankalinta kwance aka fara tafiya, bata tuna komai, ita kawai burinta ganin Kamal.

Suna isa ta sauka ta biyashi kudinsa, ta doshi gate din makaranta gabanta sai faduwa yakeyi, haka dai ta daure ta shiga, tayi tafiya mai nisa sosai kafin taje inda dalibai suke.

Wasu yanmata ta gani, ta musu sallama, sannan ta tambayesu, department na medicine, suka mata kwatance.

Tayi ta bin kwatancen har ta iso, nan kuma ta fara tunanin ta ina zata fara nemansa, haka dai ta sa kai ta shiga, wata ta tambaya ko tasan Kamal Muhammad, tace mata bata sanshi ba, haka ta tambayi mutum yakai hudu, kafin wani ya fada mata inda zata sameshi.

Ta doshi wurin gabanta na faduwa sosai, cak kuma ta tsaya, idan taje, tace masa me, ta kasa jure rashinsa, ko kuma me, tana mace ta biyo shi, ai ta zubda ajinta, shi dayake namiji bai biyo ta ba itace zata biyo shi, ta shiga girgiza kanta tana fadin no, a take ta fara tuna maganar da Asma'u ta fada mata kafin su dawo hutu...

"Aimana zan fada miki wani abu, tunda kinga ba sake dawowa zanyi ba, nasan kina son Kamal, amma kar ki yadda ki zubar da kimarki ta ya mace a gabanshi, kasaitacciyar mace itace wacce ta iya kame kanta, ta iya ajinta, kuma itace wacce bata taba barin wani kofarda wani namijin zai kawo mata wargi, ki kula sosai Aimana, kada ki bada kofa komin kankantarta wanda zaisa Kamal ya fahimci kina sonsa, ki barshi yazo ya nemi soyayyar ki da kansa, kuma karkiyi saurin sallmawa, sabida zai gane dama jira kikeyi, sai yafi ganin kimarki da darajarki, idan ya sha wahala kafin ya samu soyayyar ki, kada ki yarda kuma ki bashi a bagas, kuma karki sakar masa zuciyarki har sai kin fahimci iya zurfin soyayyar ki a zuciyarsa, amma fa sai kin jure, duk wuya duk rintsi kada ki bari sonsa yayi galaba a kanki, ina miki fatan alkhairi, Allah ya nuna mini bikin Aimana da Kamal".

Wani ta kurawa ido yana zaune ya bata baya a lokacinda take wannan tunanin, tana gama tunanin kuwa ta juya ta fara tafiya.

Juyowa yayi sabida yanda yaji gabansa nata faduwa, gabadaya ya kasa sukuni, aikuwa ya hango Aimana tana tafiya, bayanta kawai yake hangowa, zuciyarsa taki nitsuwa, kawai sai ya tashi ya fara binta yana son ganin wacece.

Sauri sauri,gudu gudu yake tafiya don yana son ya cimmata, baifi saura taku uku ya isa gareta ba wani ya kwala masa Kira, fasa karasawa yayi ya juya ya koma.

Cak Aimana ta tsaya jin an anbaci sunan kamal, juyawa takeson yi taga da gaske Kamal nata ne,ko kuwa wani Kamal dinne daban, duk iya kokarinta kar ta juyo ya faskara, zuciyarta ta rinjayeta a wannan Karon saida ta juya, amma bataga kowa ba sai wasu yanmata daga gefe suna zaune, "To kodai kunne nane yaji kamar an kira Kamal, kai a'a tabbas Kamal yana kusa dani, inajin haka a jikina, but where".

Juyawa kawai tayi ta fita daga department din ta kama hanyar gate, tana zuwa ta tari adaidaita ta wuce gidan Abba.

Koda ta isa ta samu Ummie tana waya, tana shiga kuwa taji tace gata nan ma ta iso, ita shaf, ta manta da idanta fita sai Mama ta Kira ta tabbatar ta isa inda tace zata.

Ummie tana gama wayar ta juyo tana tambayar ta ina ta tsaya tun dazu, kusan awa Mama take waya tana tambaya ko ta iso, saidai ganin yanayin Aimana ya tsorata ta, ta kamo hannunta ta zaunar da ita, itama ta zauna a kusa da ita, ta shiga tambayar ta meya faru,meya sameta.

Kwanciya kawai tayi a kafar Ummie, ta saki wani irin kuka mai tada hankali.

Hankalin Ummien kuwa ya tashi ba kadan ba, ita duk tunaninta wani abune ya sameta ko a hanyar zuwa.

Cike da tashin hankali take dada tambayar ta, "Wai Aimana menene, meya faru, ki min magana", ganin dai da gaske ba maganar zatayi ba yasa Ummie daukar waya ta dannawa Mama Kira, har ya kusa shiga kuma ta kashe, don tasan yanzu idan ta fada mata halinda Aimana take ciki, sai tafi kowa shiga tashin hankali.

Ajiye wayar kawai tayi a gefe, ta shiga rarrashin Aimana tana bubbuga bayanta, zuwa can kukan ya dan tsaya, ta kwala kiran Ruma, tana zuwa ko har zata fara tsallen ganin Aimana sai ta lura da halinda take.

"Ki kawo min ruwan sanyi", Ummie ta umarceta,

Juyawa tayi ta je ta dauko ruwa mai sanyi sosai ta kawo, Ummie ta karba ta bawa Aimana tasha, kafin ta sake kwanciya lip a jikin Ummie, da haka har bacci ya dauketa, Ummie ta gyara mata kwanciya, cike da tunanin me ya sameta, bata taba ganin Aimana cikin wannan yanayin ba, Allah dai yasa lafiya.

Sosai tayi bacci kafin ta farka, rass abunta ta tashi, kamar ba itace take ta rusa kuka ba dazun, koda Ummie ta tambaye ta sai cewa tayi wani abun tausayi ta gani a hanya, bata kai yamma ba ta koma gida.

Tana komawa kuwa Mama ta hau tuhumarta a ina ta tsaya, bata isa gidan ba har sai kusan bayan awanta daya da fita, rasa abun fada tayi, can dai tace taje gidansu Hamida kafin ta wuce.

Da zuciya daya Mama ta yarda, don iya saninta da Aimana bata mata karya.

Aimana kuwa tana can tana tajin haushin karyarda tayi wa Mama, abunda bata taba ba amma yau tayi akan Kamal.

Haka ta kare hutunta ba tare da ta sanya Kamal a idonta ba, ta tattara ta koma makaranta, sai kuma bayan wata goma shadaya zata waiwayi gida........