Chapter 5
A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa ya zube su cikin nata. Ƙirjinsa ne ya fara bugawa ganin Kiyyan a gabansa. Tana nan a yarda take kyakykyawar gaske sai ma wani kyau da ta ƙara musamman yanzu da ta zama budurwa sosai… Idanunta ta juya sosai kafin ta juya a fusace ta bar inda yake wani irin zafi da huci take ji a zuciyarta… “KI….YYA..” ya daure ya haɗa furucin sai dai ko kallonsa bata yi ba. Ta cigaba da tafiya tana ƙarewa yanayin ginin gidan kallo. Yana nan a sanin da ta yi masa sai dai an yi renovating ɗinsa. Babban gida mai part shidda manya manyan gaske kamar irin gidajen India. Jadda ce ta kama hannunta don bata son a lokacin kowa ya san da zuwanta. Sai da ta damƙi hannun nata sannan ta kalli Zayyad da Abba Mahmud ya yi saurin jan hannunsa yana furta Zayyad yaushe ka zo ne?” Da ƙyar Zayyad ya haɗiye wani abu da ya ji ya tsaya masa a maƙoshi ya lumshe idonsa murya a can ciki ya ce “Just now…” Ya bi bayan Zakiyya da kallo da take sanye da wasu Riga da wando ta kawo Hoody ta ɗora a kansu sai hula a kanta kayan sun mata kyau sosai. Ya dinga jin zuciyarsa na wani irin bugu.
Har sun yi gaba Jadda ta juyo tana kallonsu “Ban ce ku sanar da kowa zuwanta ba.” Abba Mahmud ne kawai ya ɗaga kai banda Zayyad da yake jin wata irin faɗuwar gaba ga wata kunyar Abban nasa da yasa ya ji ya kasa sakewa, duk abubuwan da suka faru suna sake dawo masa daki daki a kwanyarsa. Abba Mahmoud ya ɗan damƙi hannunsa alamar kulawa yana murmushi ya furta “Kana mamaki ko? Zayyad ashe Kiyya na raye tsawon wannan lokacin familyn Mamanta suka ɓoye mana” Zayyad ji ya yi hannunsa har rawa yake cikin na Abban ya rasa mai zai ce masa. Abban ya ɗan bi shi da kallo kafin ya furta “Ka shiga ciki, ka yi wanka ka huta don na san a gajiye ka ke, amma kuma ai ba wanda ya san da zuwanka, definitely na san part ɗinka ba a share yake ba, ka shiga wajen Jadda kafin a gyara.” Ya ɗan sosa kai yana sunkuyar da kansa a hankali ya furta “Am sorry once again Abba” “Shsssh! Zayyad let bygones be bygones pls. Abinda ya shige ai ya Riga ya shige and I know komai ma ya faru ne saboda yarinta yanzu na san da kuɗi aka ce ka yi ba zaka aikata ba” Zayyad ya haɗiye wani kakkauran yawu yana ji kamar Abban ya ɗau wani dutse ya ɗora masa ne. Haka suka jera da shi har parlorn Jadda. Inda suke zaune da Kiyya ga abinci da abin sha duk masu aiki sun dire mata. Sai dai bata ci komai ba asali ma wanka take son yi kawai sai kuma son ganin ƴan uwanta, ga ganin Zayyad da ta yi ya taso mata da wani miki a ƙasan zuciyarta. Don haka a zaman da ta yi ma, zaka gano yanayin damuwa a tattare da ita, hanayenta a tallafe da ƙuncinta ta kuma zubawa Family picturensu ido. Wani irin hoto ne mai girman gaske da ya mamaye bango guda a parlorn Jadda, duka ahalin ZAWIYYA ne a ciki a haka take bin su da kallo tana kallon fuskokin jama’ar da ba zata taɓa mancewa da su ba. Idonta ya tsaya a kan hoton Mahaifiyar Zayyad ta wani irin sakin huci a hankali ta lumshe idonta.
Sallamarsu Abba ce tasa ta dawowa cikin hayyacinta, sai dai ganinsa tare da Zayyad yasa ta amsa murya a ƙasa kafin ta miƙe ta yi cikin bedroom ɗin Jadda. Jadda ta furta “Maza ki yi wanka sai a sanar da jama’ar gidan zuwanki.” Ta ɗaga kai kawai tana jin wani irin weakness a tare da ita.
Sai a sannan Jadda ta kalli Zayyad tana amsa gaisuwarsa ta furta “Kai kuma Zuwan bazata haka? Abinda baka saba yi ba.” Ya ɗaga kansa Abba Mahmud ma ya ce "nima yanzu tuhumar da nake masa kenan Jadda, me ya faru Zayyad ka yi zuwan bazata haka?” Ya lumshe idonsa kafin ya fara basu labarin dalilin zuwan nasa. Jadda ta kawo ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Tabbas Kiyya na da rai Zayyad, kai ma idonka ya gane maka haka, ba wanda ya san da hakan sai mahaifiyarta da danginta, koma me suka aikata ba kowa ya jawo ba sai kai da uwarka, duk da abinda ya Riga ya wuce ya wuce, ba zan dawo da hannun agogo baya ba, ban ga kuma laifin uwar Zakiyya da danginta ba sun cancanci su yi hakan" Zayyad dai kansa a ƙasa ya kasa koda kwakwkwaran motsi, shi kaɗai ya san yanayin da yake ji tattare da shi a zuciyarsa da gangar jikinsa gaba ɗaya, wani irin huci yake ji yana fitowa haɗe da nimfashinsa, nadama mai girman gaske yake ji a ransa, fiye da lokutan baya, bai san dalili ba ko don yanzu yaga Kiyya a gabansa ne, bai san da wani ido zai kalleta ba…
Wankan ta yi ta fito daga toilet ɗin Jadda tana tsane kanta, idonta cikin babban hotonta da yake ɗakin Jaddan. Bata manta sanda aka ɗauke shi ba. Ta ƙarasa wajen ta tsaya cak tana nazarin hoton kamar yau aka ɗaukeshi ranar sunan Zuhair da Zuhaira ne. Ta lumshe ido tana sake tuno sanda aka yi Hoton bayan Zayyad ya gama sakata kuka akan bata kai masa ruwan da ya aikata daƙƙowa ba da wuri, ya mata wani irin naushi da sai da yasa ta zube a ƙasa kukan da ta sha ya bayyana a idonta don ga idon ya kumbura kaɗan. Kiyya ta lumshe ido tana datse leɓenta tana sake jin wani irin zafin tsanarsa a ranta. “Yi maza ki shirya, sai ki ci abinci ko?” Ta juyo muryar Jadda a kusa da ita. Da sauri ta janye jikinta daga kusa da hoton, ta ɗan sakarwa Jadda murmushi tana ɗaga kanta. Jadda ta juya ta fita tana jin wani irin yanayi a tare da ita. Gaba ɗaya gani take Zakiyyan ta canja mata, kamar ba Kiyya mai kazar-kazar raha da barkwanci ba. Bayan fitar Jadda kayanta ta buɗe ta ciro wasu Riga da wando ta saka. Sun matseta sosai kamar yarda ta saba da su, bata iya saka wasu kayan ba wanda suka wuce English wears ba. Ta matse kanta da hair band. Ta fita parlorn tana zabga wani irin zazzafan ƙamshin turare. Da sauri Zayyad ya janye idonsa daga kanta. Bata zauna a wajen ba kanta tsaye ta nufi ƙofar da zata fitar da ita harabar gidan. Ba ma ta ji kiran ba.
Duka yaran gidan suna harabar suna wasa. Da ido ta dinga bin su kamar yarda su ma suka dinga binta da idanun. Wasu a cikinsu sun santa, wasu kuwa ko haifarsu ba’a yi ba sanda ta bar gidan. Murmushi ta dinga sakar musu ɗaya bayan ɗaya tana jan hannunsu ga mamakinsu kuma duk ta san sunansu, ba kowa ke gaya mata ba sai Abbunta da kullum idan ya je sai ya nuna mata hotunansu ya kuma bata labarinsu. Farin ciki take ji mara misaltuwa, farin cikin kasantuwar ta a cikin zuri’arta. Ta ware ido tana kallon yaran da suka dare da gudu bayan ta ce musu
“My name is Zakiyya Zawiyya…..”
wasu ƙiris ne basu faɗi ba, har hakan ya bata dariya don da alama sun tsorata ne da jin sunan, sun san ta mutu din ana yawan basu labarinta, me yasa yanzu za’a ce tana da rai?
Da wani irin gudu suka shiga sashen Baba Babba, don iyayensu majority suna can wajen suna hira idan ka ɗauke Mammy da Ammy…
Da sauri su Umma suka ɗago suna kallonsu kafin su haɗa baki wajen furta
“Lafiyarku kuwa?”
Zahir ya girgiza kai yana furta “Zakiyya is back Umma, ga Zakiyya can bata mutu ba ta dawo yanzu muka ganta.”
Wata irin hajijiya ta ji tana son kada ita, ba ita ba hatta muƙarrabanta da suke zaune sai da gabansu ya faɗi kusan a tare suka ce
“Wace Zakiyyan ka ke faɗa?”
“Zakiyya Zawiyya…..!”
Kiyya da take shigowa ta furta tana bin su da kallo fuskarta fal murmushi. Ƙiris ya rage Umma ta saki fitsari a wando tsabar firgicin da ta shiga bata san sanda ta saki cup din hannunta ba, idanunta a waje ta furta “Zakiyya!” Gumi kuwa tuni ya jiƙe jikinta tas. Sauran ma duk waro ido suka yi suna kallon Zakiyya su ba abin su ruga da gudu ba yara su musu dariya. Kiyya kuwa kallonsu kawai take tana murmushi. Kafin ta ƙarasa cikin parlorn tana bin yanayin parlorn da kallo kaf memory ɗin rayuwarta yana dawo mata. “Ba mafarki kuke ba Umma, Zakiyya ce. Ina wuninku?” Ta furta tana zama saman kujera. Shigowar Jadda ce yasa duk suka ɗaga kai suna kallonta rawar da jikkunansu yake yi kuwa basu fasa ba. Jadda ta yi sallama, amma aka rasa me amsa mata, ita kanta murmushin kawai take ganin yarda idanuwansu suka bayyana tsoro da tashin hankali ƙarara. Ganin basu amsa ta ba sai kawai ta kama hannun Kiyya suka nufi ƙofa kafin ta furta “Ina buƙatar halartar dukkaninku zuwa taro a parlorna. Eh, Zakiyya ce Allah ya yi mata dawowa.” Wannan karan Umma tsabar juyin da cikinta ya yi, ji ta yi kamar hanjin cikinta suna tsitstsinkewa… Amma ce furta “Cabɗim jam! Wannan fa shine ana wata ga wata.”
“Me yasa kika fito baki tsaya kin ci abinci ba? Ko har yau kina nan da rashin son cin abincin naki?” Murmushi Kiyya ta yi kafin ta girgiza kai kaɗan, tana kallon sashen Mahaifiyarta amma ba dama ta ce zata je, saboda yarda Jadda ta matse hannun nata da kyau. “Mu je ki ci abinci tukunna, koma me ye sai ya biyo baya.”
Idanunta ta dinga shawagi da su, a tsakanin yaran da suka zagaye Abbanta. Zuciyarta na zillo ta buɗe musu hannayenta alamar su zo, soyayyar yaran tana sake hauhawa da samun matsuguni a zuciyarta. Su huɗu ne kansu guda, idan kuma ba idonta ne ya nuna mata ba, sai taga kamar akwai kamanceciniya tsakanin yaran. Zahir da ya ɗan fi su wayo ya ce “Abba, wacece wannan?” Murmushi Abba ya yi ya ce “Yayarku ce, Zakiyya baku santa ba ko?” “Mun santa tana yarinya a hoto Jadda tana bamu labarinta, amma ba an ce ta mutu ba.” Zuhaira ta furta tana kallon cikin idon Kiyyan. Kafin Abba ya ce komai sun runtuma sun fice da gudu basu tsaya ko ina ba sai parlorn Ammi. Tun daga ƙofa suke kwaɗa mata kira “Ammi come out, Sister Kiyya ta zo” Ammi ta ji wata irin faɗuwar gaba, da sauri kuma ta mayar da idonta kan Sharifat da bata gane abinda yaran suke nufi ba. Zahir ya ce “Ashe bata mutu ba Ammi, ashe tana da rai ta yi girma ta kai Yaa Yasmeen fa, ta ce mana My Name is Zakiyya Zawiyya….” Ya faɗa yana kwaikwayon yarda Kiyyan take magana. Mami Sharifat a razane take kallon yaran jin abinda suke furtawa da sauri ta mayar da kallonta kan Ammi da ta kasa yarda su haɗa ido. “Zakiyya na da rai?” Ta jefowa Ammi tambayar da ta kusa tarwatsa zuciyar Ammin shin da wani ido zata kalli Sharifat ta mata bayani? Anya ta kyauta kuwa?
JIKAR NASHE✍🏽