PAGE 9
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa
FREE-BOOK
PAGE 9
Muna tafe a hanya muna ƙara tattauna rayuwa ni da Ammie har muka iso garin Gusau. A wannan karon Ammie ta samu horo iri-iri daga ƙungiyoyi daban-daban ma su kula da masu kalar ciwonta wanda a yanzu in sha Allahu duk abinda zai zo mata muna da yaƙini da saka rai cewa za ta iya adopting dai-dai gwargwado.
Kalle-kalle na fara bayan mun sauka a motar wai ko zan ga Yaya Ashiru a tawa wautar, amma har muka samu Napep muka hawo ban ga ko mai kama da shi ba.
Muna isowa ƙofar gida muka sauke kayanmu na shiga gaba na tura gidan sai dai kuma ga mamakina a rufe yake ta ciki.
Cike da mamaki na ƙara tura ƙofar amma kuma a rufe take. Idan zan tuna ranar da zamu tafi wani igiya na samu na zarge ƙofar kawai muka yi ta tafiyarmu.
Kallona Ammie ta yi ta ce.
"Beenafah lafiya?"
"Ammie gidan kamar a rufe yake."
"To ki ƙwan-ƙwasa mu ji."
Zuciyata cike da fargaba na hau ƙwanƙwasawa kamar yanda Ammie ta ce. Sai da muka yi kusan minti biyar muna jira sannan sai ga wani mutum ya buɗe ƙofar ya fito.
Kallon mu ya yi cikin nuna rashin sani ya ce.
"Malamai daga ina?"
Shiru mukayi, daga ni har Ammie ba'a samu mai tanka masa ba tsabar mamaki wanda sai Bahrain ne daga ƙarshe ya ce.
"Gidanmu ne mana, mun dawo daga asibiti, ka buÉ—e mu shiga."
Kallon Bahrain ya yi yana wani murmushi ya jinjina kansa ya ce.
"Gidan ku ne ko Yaro?"
Bakin gaskiyar Bahrain ya ce.
"Eh mana."
"To, ni dai gadi aka ɗauke ni kuma masu ainahin gidan suna Abuja, sai ƙanin matar mai gidan da yake ciki wanda ya yi aure wata ɗaya da suka wuce, bayan su ban san wasu ma su zama a nan ba..."
A gigice na É—ora hannuna a kai na buga wani irin gigitaccen ihu na ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mun shiga Uku Ammie mun lalace...Yanzu mu ina zamu nufa,..."
Itama Ammie dafe gefen zuciyarta ta yi tare da runtse idanuwanta gam a hankali ta shiga furta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahuma ajirni fiy-musibati wa Akhlufni khairan minha...."
Addu'ar da ta yi ta nanatawa kenan har sai da ta ji nutsuwa sosai a ranta, kanta na wani irin sara mata ta janyoni zuwa jikinta ta na faÉ—in.
"Ya isa Beenafah.. Ya isa. Kema ki maimaita wannan addu'ar da nayi in sha Allahu Ubangiji zai musanya mana da mafi alheri.."
Tana kan faÉ—ar haka sai ga wani ya buÉ—e gidan ya fito.
Cikin mamaki na kalle shi na ce.
"Uncle Isma'il?"
Uncle Isma'il ƙanin Mummy Zaliha ne uwar su ɗaya uban su ɗaya. Tun da suka koma Abuja shi kuma ya shiga neman alfarma cewa dan Allah su bashi gidan ya saka amaryar sa idan lokacin auren sa ya yi. Da farko har Daddy ya amince amma mummy ta ce ita sam bata amince ba domin watarana idan sun shigo garin ai dole suna da buƙatar wurin zama saboda haka bata amince ba. Yana na nan yana ta neman mafita sai gashi ya zo gidan wata ranar Alhamis ya tarar gidan buɗe babu kowa duk an bi an cire AC ɗinda suke gidan, an sace kayan babban generator dama duk wa su sauran kayan da suke waje. Hakan yasa ba shiri ya ɗauki waya ya kira Mummy Zaliha, nan take suka yi meeting daga ƙarshe suka kira Isma'il ɗin suka ce ya gyara ɓangarensu Beenafah ya saka amaryar tasa a ciki. Part ne mai ɗauke da Babban parlour wanda yake da dining area ɗan matsakaici da kitchen, sai ɗakin bacci ɗaya sai toilet a ciki. Idan ka fito akwai verander kewayayya da kuma toilet ɗin waje sai aka zagaye Part ɗin aka saka babbar ƙofa wacce ake iya rufe gidan idan an so. Bayan an yi bikin ne Daddy ya turo musu sabon mai gadi domin tsaron gidansa.
Wani irin ɓata rai ya yi tamkar bai taɓa sanin yan da ake dariya ba ya ce.
"Ya akayi?"
Haɓa na rawa na ce.
"Uncle Isma'il ba ka ganemu ba ne? Mu ne familyn Dr. Bello Wazeer ƙanin mijin Mummy Zaliha.."
Wani kallon sama ƙasa ya yi mana sannan ya ce.
"Na gane mana, Mulaifa ce da Beenafah da kuma Bahrain...."
Cikin jin wani sanyi a raina na nuna mutumin da ya tare mana ƙofar na ce.
"Wannan mutumin ne ya ce wai ba zamu shiga ba. Dan Allah ka ce ya barmu mu shiga..."
Girgiza kan shi ya yi ya ce.
"Ba zaku shiga wannan gidan ba domin ba ku da matsugunni a ciki?"
Cikin wani irin kuka jikina na wata irin tsuma na ce.
"Dan Allah Uncle Isma'il ka rufa mana asiri dan Allah ka barmu mu shiga, gidanmu ne fa. Gidan Daddy ne Yayan Mahaifinmu wanda bamu da wani bayan shi a duniyar nan..."
"To ni ina ruwana, ai ba Laifina ba ne ni..."
"Don Allah Uncle Isma'il, don darajar iyayen ka kada ka kore mu daga nan..."
Hannu na ga ya saka cikin aljihu ya ciro waya ya lallatsa ya kara a kunnen sa wanda ba ɓata lokaci naji yana magana daga ƙarshe ya miƙo mini wayar, hannu na rawa na karɓa na joganata a kunnen tare da fashewa da wani irin sabon kuka mai tsuma zuciya na ce.
" Daddyyy! dan Allah kada ka kore mu daddy, daddy Idan ka koremu ina zamu nufa?"
Daga can ɓangaren Daddyn cikin masifa ya fara magana da cewa.
"Zama zan yi ku riƙa yi mini wasa da dukiya ina kallon ku? Kun tafi kun bar gida a buɗe sakaka saboda bakusan zafin kuɗi ba duk an shiga an yi mini sata sannan ki ce kuma in bar gida ku ci gaba da yin yanda kuka ga dama? To na rantse da Allah hakan ba zai yi yu ba, nasan yau da gobe tun ana ɗaukar abun da yake waje watarana cikin gidan za'a shiga a yayeni. saboda haka na rantse da Allah zamanku a gidan nan ya ƙare har abada..."
A hankali Mummy ta miƙo hannu ta karɓi wayar daga hannuna ta kara a kunnenta tana zubar da hawayen baƙin ciki domin duk abinda yake faɗa tana jin sa daman wayar a hands free take ta ce.
" Ka ji tsoron Allah Alhaji Mudassir! Ka ji tsoron Allah. Ka tuna waÉ—annan yaran ba su da wani wanda za su kira na su bayan kai.... "
" Ke dan Allah ni bana magana da mahaukaciya,sai dai ina miki addu'ar Allah ya baki lafiya...Isma'ila ka amshi wayar ka ji mi zan gayamaka."
Durƙushewa na yi zuwa ƙasa ina wani irin kuka tamkar wacce akace uwarta ta mutu.
Ammie ma haka ta ja Bahrain ta rungumesa jikinta tana ta addu'a wacce ita ce makami a gareta, ga kanta sai ciwo yake tamkar zai tsage gida biyu.
Bayan ya gama wayarsa ya juyo ya kallemu ya ce.
"Ku shiga ku tattara kayanku ku saka a mota ina jiranku."
Tamkar wata mai koyon tata haka na daddafa na shiga ni kaɗai yayin da Ammie ta togace bakin gate. Sai da na gama bincika ko'ina ban samu kayan ba sai daga ƙarshe na tarar dasu ɗakinda Generator yake, an rabke su wuri ɗaya tamkar wasu kayan bola-bola.
Ganin ina neman ɓata masa lokaci ya saka mai gadin ya kwashe kayan ya saka a cikin Hilux ɗinda na gani nan a harabar gidan da alama ita ce motar tasa domin ni can baya dana san shi ban san shi da mota ba.
Wani babban wulaƙanci ma da ba zan taɓa mantawa da shi ba shine wai mu shiga baya tare da kayan, shi ba zamu shigar masa gaban mota ba. Hmm! Duniya kenan.
A hankali yake tafiya har muka baro GRA ɗin zuwa wata unguwa da bamu taɓa sanin tana Existing ba a rayuwa.
Yara ne gasu nan suna ta wasa abin su, mutane gasu nan ko ta ina.
A bakin wani matsakaicin gida ya yi parking ya fito ya buɗe ƙofar gidan. Yara ya kira suka saukar mana da kayan sannan ya ciro makullai guda uku na kubaka ya damƙa mini a hannuna tare da faɗin.
"Ku gode Allah ma saida na gama gyara gidan sannan akace na baku ku zauna. Kuma wallahi ku saurara ku ji gargaɗina; ko da wasa kada na sake ganin ƙafarku a ƙofar gidan can , koda wasa kada na ji wai kunje neman wani abu wallahi rashin mutunci zan yi muku wanda ko kare ba zai ci ba. Kuma shima kunga wannan gidan? Zamanku a ciki temporary ne, kada ku yarda ku ɓata mini gidana kunji na gaya muku."
Har ya ƙarasa maganar sa ya tattara ya tafi daga ni har Ammie babu wanda ya ce masa uffan. Muna nan a tsaye ina ta kuka da ni da Bahrain Ammie ta kira wani yaro cikin yaranda suka tsaya suna kallon mu ta ce.
" Ya sunan wannan unguwar ne?"
" Nan Shi ne Hayin Malam Ibrahim."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Na gode."
Kallona tayi ta ce.
"Ku zo muyi addu'a mu shiga. Ba komai kuyi haƙuri, duk yanda rayuwa ta zo wa bawa to dole ya yi haƙuri ya godewa Allah..."
Ganin ta dafe gefen kanta tana neman zubewa ƙasa yasa na ƙwallara wata irin razananninyar ƙara da gudu na je gareta na ce.
"Ammie mine ne? Miye ya same ki?"
Murmushi ta yi ta ce.
"Bakomai Beenafah, kai na nike jin yana ciwo sosai.."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..Ammie muje ciki kisha magani, lokacin shan maganin ki ya yi ma tun ɗazu. Mummy dan Allah ki ƙwarara kanki kin ji Ammie na."
Cikin gidan muka shiga da bismillah É—auke a bakinmu. Na samu wuri na zaunar da ita cikin verander.
Gidan a gyare yake fes kamar yanda yace, ko'ina an fenteshi da kalar zuma, ga breaking tiles an baza ko ina a filin gidan har bakin ƙofar fita.
Ɗakunan nabi na leƙa. Ciki da parlour ne guda ɗaya, sai ɗaki ɗaya daban a waje, kitchen da kuma toilet, sai kuma rijiya da aka yi ta da ɗan tsayi sannan aka rufe bakinta da murfi itama a jikinta duk tiles ne har sama. Gidan gwanin sha'awa, da hakan Ammie sai ta ji hankalinta ya ɗan kwanta kaɗan.
"Beenafah zo ki bani maganin nasha mana."
Da sauri na zo na É—auko mata tasha da kanta sannan na mayar.
"Ammie ni ina jin yunwa."
Kulolin da muka zo da su ne tun daga gidan Dr. Basheer wanda ya saka aka shirya mana abinci kafin mu gama shiryawa. Wai shi yasan idan muka iso ba zamu samu damar ɗora girki ba domin akwai gajiya da kuma buƙatar shirya wuri.
Plate na É—auko na zuba masa,lafiyayyar shinkafa da miya ne da nama. zaunawa ya yi yaci, bayan ya kambala ya É—ora kansa akan cinyar Ammie dake zaune murya cike da rauni yana hawaye kaÉ—an-kaÉ—an ya ce.
"Bana son Daddy Ammie... I hate him, I hate Mummy Zaliha har Humaida ma.."
Da sauri ta sanya hannunta ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce.
"Kul! Kada na ƙara ji kaji ko Bahrain..Komai na duniya haƙuri ake. Tashi ka yi sallah ka ɗauki ga tabarma can ka shimfiɗa daga can ka kwanta ka yi bacci."
Lokaci É—aya muka tashi muka yi sallar sannan ta ce mini.
"Beenafah mu ci abincin nan mu zo mu shirya kayan nan da wuri."
GyaÉ—a kaina na yi na ce.
"To Ammie."
Abincin na É—auko na zuba mana a tare muka zauna muna ci. Ganin yanda nake ta juya cokalin yasa ta kalleni a hankali ta ce.
"Ki yi haƙuri da duk yanda rayuwa ta zo miki."
Komai bance ba har muka kambala sannan na ce ta kwanta ta huta ni zan gyara komai da kaina tunda lokacin hutawarta ya yi. Daman ba wani kaya ba ne. Katifa ce wacce muke kwanciya ni da Ammie sai katifar Bahrain. Single room ɗinda ke wajen kawai na gyara mana domin shi ma yana da faɗi sosai,kuma ya ishe mu bama buƙatar ciki da parlourn. Sai kayan tarkacen kayan aiki su ma da ba wasu masu yawa bane na saka a kitchen ɗin. Sai kayan sawarmu dana kai parlourn na jere a lungu ɗaya da kayan siyayyar abincin da muka zo da shi daga can.
****
Tun da Mummy ta ji Daddy yana waya da su Beenafah ta zo ta tsaya a kan shi bayan ya kammala ta kalle shi ta ce.
"Yanzu kai saya musu gidan za ka yi ko ya ya?"
Ɗan taɓe baki ya yi ya ce.
"Eh to. Idan Shi Isma'ilan ya ce zai siyar sai a saya musu..."
Cike da mamaki ta ce.
"Ka siya musu Alhaji? A'a, ni gaskiya ban yarda ba. Idan kace ka siya musu kuɗi ne zaka kashe ma su yawa, sannan shi kan shi Isma'il ɗin idan ka siye gidansa zai ɗauke shi matsayin hujjar da zai ci gaba da zama gidanmu wanda ko da watarana muna so ya tashi ba zai tashi ba. Saboda haka ka barshi a haka dai, su zauna, duk ranar da wata buƙata ta so kowa zai iya kama abinda yake da shi."
Jinjina kai Daddy ya yi cike da gamsuwa da maganarta ya ce.
" Kuma fa zancen ki haka yake wallahi..."
" Ah to! Ni da ka yi shawara dani ma tun farko ai wallahi ba gidanda za'a basu sai dai su je can susan yanda za su yi,da shikenan mun huta da gaibu."
"Eh to, banƙi ta taki ba, amma dai kinsan ko ya ya ne su ɗin jinina ne tunda ƙanina ne ya haife su. Da ace kin amince kamar yanda na ce tun farko da sai mu zo nan da su, idan yaso ita ɗin sai a barta a can..."
Da sauri ta É—aga hannunta ta ce.
"A'a wallahi. Rabani da gayyar tsiya gayyar na ayye. Su tsaya can inda yafi dacewa da su"
****
Zaune nake na buga uban tagumi a bakin wurin da na ajiye kwanonin wanke-wanke ina ta karanta wasiƙar jaki tsawon lokaci.
Muryar Ammie na ji a kaina tana faÉ—in.
"Beenafah...!Beenafah Lafiya kuwa?"
Kukan da nake riƙewa ne ya ƙwace mini ina kallonta na ce.
"Ammie Yaya Ashiru! Ina matuƙar jin kewar sa a rayuwata, shikenan Ammie, Shikenan mun rasa Yaya Ashiru da gaske? Mutumin kirki wanda ya ɗaukemu tamkar en uwansa."
Cike da tausayawa ta dafani ta ce.
"Ki yi haƙuri, In Sha Allahu watarana zamu sake haɗuwa tun da muna a gari ɗaya..."
"To Ammie shikenan? Shikenan da gaske rayuwarda zamu ci gaba da ita kenan? Da gaske Daddy ya rabu damu tamkar bai san su waye mu a wajen sa ba?"
Kujerar tsugunno ta janyo ta zauna a kusa dani a hankali ta ce.
"Beenafah! Ki daina cewa haka domin babu wanda yasan gobe. Ki ci gaba da kyautatawa Allah za to, ki yi haƙuri, lokaci ya yi da ya kamata mu manta da bayanmu mu fuskanci gaba. Kinga cikin wata ukun nan, mun ci kuɗi sun yi dubu dari biyu, kuma idan bamu yi wani shiri ba sauran kuɗin nan suma haka za su ƙare. Ko million kake da shi matuƙar baka riƙa juya su ba kace za ka riƙa zara watarana sai an wayi gari ba ko biyar...."
Jiki a sanyaye na ce.
" To ko yanzu Ammie miye ya rage? Dubu ɗari da saba'in mi za su ce mana? wacce sana'a zamu tsira da su har ta iya riƙemu har kuma muci abinci a ciki Ammie? Ga Bahrain dole ya kamata ya koma school Ammie...."
Miƙewa ta yi ta shiga ɗaki ta ɗauko wata jaka ta buɗe tare da fitowa da wani tsumma dake dunƙule. Kwance ƙullin tayi, sai dai kuma wayam! ba komai a ciki.
Cike da tashin hankali ta shiga faÉ—in.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! "
" Lafiya Ammie? Miye kike nema haka?"
Na faÉ—a nima hankalina a tashe ina mai tsatstsareta da ido.
ĆŠakin ta sake komawa ba tare da ta tankani ba ta hau birkita kayan dake É—akin wanda tana yi tana hawaye a hankali tana kiran sunan Allah.
Sai da ta yiwa komai namu kaca-kaca amma kuma da alama ba ta yi nasarar samun abin da take nema ba.
Cike da damuwa na ce.
"Ammie wai miye kike nema haka?"
Lumshe idanunta ta yi a hankali sannan ta buÉ—e tana mai share hawaye ta ce.
"Ba komai Beenafah. Yanzu miye abin yi?"
Ɗan Jim! Na yi ina nazari tsawon lokaci sannan daga ƙarshe na ce.
"Muje a kai Bahrain makaranta kada kuɗin nan ya iyarda salwancewa, gashi shikenan tallafinmu ya ƙare na wurin Dr. Basheer."
***
Islamiyyar Ummul-Qura dake Muslim foundation muka kai shi inda muka masa registeration dubu goma sha ɗaya komai da komai. A nan suka yi mana tayin makarantar bokon su domin har boko ake a wurin, amma sai muka ƙi amincewa saboda yanayin rayuwa. Bayan naga jadawalin su sai na ji makarantar ta burgeni sosai, hakan yasa na ja Ammie gefe na ce.
"Ammie mu biya masa nan É—in kawai, makaranta ce mai kyau.."
"Amma Beenafah.."
"Ammie karki damu. Ina da plan, in sha Allah zamu iya. Ki ƙarfafani Ammie in cika mafarkina akan Bahrain, Daga term sai term ne fa.."
Cikin shakku ta ce.
"Beenafah.."
"Mu je Ammie in sha Allah zamu iya."
Bayan mun kambala tun a hanya Ammie take mita har muka iso gida.
Bayan ta zauna na É—auko mata abinci da ruwa da magani sannan na zauna a kusa da ita.
"Ni fa Beenafah duk ba wannan ba,yanzu ke dan Allah kina ganin ba mu ɗauko abin da yafi ƙarfinmu ba? Dubu tamanin da shida fa muka bayar zama ɗaya! Kin san fa har yanzu ina kan zuwa follow-up. Don ma Allah ya taƙaita mana yanzu an rage magungunan ba kamar can baya ba, amma kuma har yanzu bamu daina saye ba. Ga abinci, ga buƙatocin rayuwa..."
Hannunta na riƙo ina murmushi na ce.
"Ammie...Dole mu yi aiki tuƙuru domin goben Bahrain. Saboda haka mu samu wata sana'a da zamu riƙa yinta a cikin gida ko kuma ni na riƙa fita da tallar..."
Da sauri ta girgiza kanta ta ce.
"Har abada, komai zai faru Beenafah ba za ki yi tallah ba. Mu siyo kayan ƙulle-ƙulle mu riƙa saidawa a gida."
Da wannan shawarar na amince mata na karɓi kuɗi na tafi kasuwa na yo mana sarin kayayyaki muka zauna muka ƙulla sannan na shiga maƙotan da muke da su zagaye damu na tallata musu.
****
Haka rayuwa taci gabar mana da tafiya wanda yau da gobe bata bar komai ba, gashi mun wayi gari sana'ar da muke ta cikin gida kaɗai ta tabbatar mana ba zata iya riƙe mu ba.
Da ƙyar muka samu mu kayi masa registeration ɗin third term satin nan da ya gabata. Gashi komai ya yi mana tsaye sai godiyar Allah.
Yau ma Ammie na zaune waje akan sallaya misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe ta buga uban tagumi na fito cikin shirina na zauna dab da ita na ce.
"Ammie kina tunani ne akan abin da zamu ci gobe ko? Ai na duba na gani, shinkafar kwata-kwata iyakacinta yau, ga shi ba kuɗi kuma ba wani dogon ciniki.. Ni ina ga Ammie, ki ɗauki shawarar Maman Fakiha ki yarda na riƙa soya Awara da dankali a ƙofar gidannan, zama a haka bai zai yi ba..."
Da sauri ta girgiza kanta tana mai tsiyayar da ruwan hawaye ta ce.
" A'a Beenafah! Kowa da ra'ayinsa, Maman Fakiha tana iya É—orawa 'Ć´ar ta talla, ni ba zan iya ba."
"Ammie ki yi mini izini na tafi gidan matar nan da na yi miki bayaninta wacce Biba ta kaini wurinta. Kinga aikin ba na kwana bane iyaka naje da safe daga zaran na gama mata aikinta sai na dawo gida abina. Zan ce mata bana buƙatar komai kawai idan wata ya yi ta biyani kuɗina, hakan zai taimaka sosai... "
" Beena... "
" Ammie dan Allah kada ki ce a'a. Wannan ita kaÉ—ai ce hanya tunda bakya son na yi talla....."
Ganin still kamar tana kan doubting yasa na kama hannayenta tare da rausayar da kaina murya a ƙasa sosai na ce.
"Ammie! Idan ma kina wani tunani a kaina ne please ki daina. Kinfi kowa sanin wace ce ni,abinda zan iya da wanda ba zan iya ba...in sha Allah zan yi iya yina Ammie....."
✍️ OUM-AMEER ✍️