MANARAH

3&4

by @meenatyandoma

MANARAH

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai maki a duk inda ki ke 🫶🥰

PG 3&4

... "Ku dai kara dubawa da kyau. "

Hisham ya fada domin ya kara tabbatar da abinda ya ke son tabbatarwa.

"Haba me gida! Ai ko da muna shaye-shaye ba za mu rasa gabe ka ba. Domin kai mutum ne me matukar halacci addininka shi ya saka kowa ke kaunarka. Ka taimaka ka sanar da mu wane ɗan balaja'un ne ya yi sanadiyar zuwanka wannan wuri. Domin mu mun san tabbas ba a kan hakkinka ba sai dai ƙazafi ko sharri ne suka kawo ka wannan wuri"

Daya daga cikinsu ya karasa maganar ya na huci.

A yanzu kam Hisham ya tabbatar abinda suke fada da gaske ne. Saboda ga dukkan alamu daga cikin zuciyarsu ya ke fitowa. To amma waye suka gani shi dai ya tabbata ba shi ba ne, domin duk iskancinsa baya shan kayan maye bare ya yi tunanin ko ya sha ya bugu ne ya aikata haka ba tare da ya sani ba.

"In na fada muku gaskiya za ku yarda?"

"So sai ma Me gida. Domin ba ka yi kala da mutanen da za su yi mana karya ba"

"Ba ni ba ne kuka gani, hasalima ban taba zuwa garin da kuke fada ba. Babban abinda ya bani mamaki waye wannan kuke fadar kun gani daga ina ya ke me ya sa muke kama?"

Mamakin da ke fuskarsu kasa boyewa ya yi. Suna shirin magana wani daga cikin yan sandan ya bude kofa tare da fito da Hisham.

Wadda ya gani zaune saman kujerar ce ya saka shi hade girar sama da ta ƙasa.

Kasancewar duhun dare ya fara Dpo din da case din Hisham ke hannunsa ya je ya dawo. Ba a bata lokaci ba Deena ta yi masu barin kuɗi suka bata Hisham. Kasancewarta ɗiyar masu kuɗi kowa ya san waye mahaifinta. Cikin gaggawa suka bata shi.

Tamkar wanda aka aiko wa da mutuwa haka ya ci kunu. Ɗan juyowa ta yi ta kallesa, murmushi ta yi ta ci gaba da tuki.

"Ki tsayar da motar nan ki aje ni"

Yi ta yi kamar bata ji me ya ke fada ba ta ci gaba da tuki.

Tsawar da ya daka mata ce ta saka Sitiyarin ya kusa kubce mata. Ba shiri ta yi parking a bakin hanya.

"Hisham ka saurareni ka yi hakuri na ga dai ba yau muka fara irin wannan fadan ba. Kamata ya yi ka tsaya mu fuskanci juna"

"Ke har kin isa ki kayyade mini matan da zanyi tarayya da su. Mata tambar numfashi na ne. Ki bar ganin ina ɗaga miki kafa ba wata wahala ba ce in rabu da ke"

Rass! Gabanta ya yanke ya fadi.

"Za ka iya rabuwa da ni?"

"Ke uwara ce da bazan rabu da ke ba?"

Ta karasa maganar tare da jin kansa ya sara.

Murmushin muguntar Deena ta saki, ko ba komai a yanzu ta san ciwonsa ne ya tashi. Sai yadda ta yi da shi.

Juya kansa ya ke tare da saka hannuwans biyu ya dafe shi. Komai ya koma masa bibbiyu. Muryar da ko a gigin bacci ba zai taba mantawa da ita ba ya ji ta fara kiran sunansa.

So ya ke ya bude idanunsa amma ya kasa wani irin duhu ya gilma masa. Daga nan ya karasa kwanciya a kujerar motar.

Dariya ta kwashe da ita. Belt ta saka masa.

"Dadina da gobe saurin zuwa. Duk wulakantar da za mu yi ni da kai mutu ka raba. Ta ya ma zan yarda in rabu da Kai wa zai yarda ya aure ni karya kake Hisham yadda muka fara tare sai mun karasa tare."

Ta karasa maganar tare da fizgar motar.

Kai tsaye katafaren gidanta da mahaifinta ya mallaka mata ta nufa.

Me gadi bai bata lokaci ba ya bude mata kofa. Da taimakon me gadi ta shigar da Hisham ciki saman gado suka tasar da shi.

Saman Bedside ta zauna tana me kare masa kallo. Wata 'yar karamar Kwalba ta dauko almakashi ta saka ta yanki gashinsa ta mayar a jikka ta rufe.

Kai tsaye Toilet ta fada.

Mahaifiyar Hisham kuwa ta kasa bacci alwallah ta tashi ta yo ta tayar da sallah. Ta jima ta na kai kukanta ga Ubangiji kafin bacci ya dauke ta.

A tsakiyar ƙasurgumin jeji ya tsinci kansa. Siririyar Muryar da ta saba kiransa a wannan lokacin ma ita ce ta ci gaba da kiransa. Abinda ya kula da shi a karkashin wata bishiyar kuka ne sautin ke fitowa.

Duk da tsoron da ya kamashi haka ya yi ta maza ya karasa. Kogo ne wanda baka iya hango karkashinsa saboda tsabar hudu.

"Ka taimakeni, ka fito da ni"

Wata murya ta fada a daidai lokacin da ya hango wani hannu alamar ana neman taimako. Mika hannun da yayi da karfin tsiya aka fizge shi cikin kogon.

A gigice ya farka daga wannan mummunan mafarki tare da kallon inda ya ke.

Safiya ta yi har rana ta fito.

Deena da ya hango tsaye a gaban mirror ne ya saka shi hade girar sama data kasa.

"Ba dai za ki fita hanya ta ba ko?"

"In fita a hanyarka ai har abada. Ka fito kawai ka aureni duk da dai kasan na wuce ajinka. Kudin da mahaifina ya mallaka rabinsu naka mahaifin bai mallaka ba. Ko da ya ke ya zanyi kai ɗin kaddarata ne"

"Shi ya sa ba zan taba aurenki ba. Kina yar bariki sannan baki tauna magana ko alama. Ke tsaya kiji duk iskancina ba zan auri yar iska ba"

Wata ashar Deena ta watso tare da mikewa ta yi kan Hisham.

Tusa hali bare anci wake, mai hali baya barin halinsa. Fada suka kaure da shi ya sameta ya yi mata ruɗu-ruɗu, ba tare da kowa ya raba su ba suka koma gefe suna haki musamman Deena da ya haɗawa gajiya a jiki.

Bai ce mata uffan ba wanka ya yi ya fice.

Bata dauki dogon lokaci ba ta fizgi motarta ta bar gidan kai tsaye wurin boka ta nufa.

Kasancewar ba da mota ya fito ba napep ya tsaida.

Sai dai abinda ya faru a cell Shi ya Kara faruwa a napep.

"Oga kaine da kanka. Me gida tun daga ranar da ka yi mini kyautar kudin nan Mahaifiyata ta cika mini na siya napep din nan. Wallahi me gida na gode ka zama sanadiyyar canza rayuwata. Da ace kowa irin zuciyarka gareshi tabbas da an rage mabarata"

Da mamaki Hisham ke kallon me Napep din kasancewar yau ya fara ganinsa.

"Ka ga ba ni bane. Ka nemi wanda taimakesa"

Hisham ya karasa maganar cike da mamakin wannan lamari me kana da almara. Shi da ya ke dan iska ta ya ke da lokacin taimakon wasu al'umma.

Me Napep kuwa daukar haka yayi a matsayin abin nan da salihan bayi keyi, wato su yi kyauta su nuna ba su suka yi ba. Saboda ba su so ma ayi masu maganarta. Bayan ya dauke shi bai amsa kudinsa ba, haka ya bar Hisham cike da mamakin wannan bakon lamari.

Tunda gari ya waye Umma ke bin kan Alhaji a kan ya je ko abinci ne ya kaiwa Hisham. Keƙarshe kasa ya yi tare da kafa sharadin duk wanda ya yi kuskuren zuwa inda Hisham ya ke sun rabu har abada. Maganar Alhajin ce ta makale sakamakon ganin Hisham da yayi kamar daga sama.

Da sauri Umma ta mike cike da zallar mamaki.

"Kai! Wa ya fito da kai wane isasshen ne?"

Tamkar yayi magana da dutse haka Hisham ya yi banza da shi.

"Da kai nake magana! "

Ya daka masa tsawar data saka Umma rikicewa”

"Don Allah ka fada masa kada laifinka ya dawo kai na"

"Haba Umma a tunaninki zan kwana a cell ne. Yanzu ma abinda ya maidoni kayana na zo diba"

"Alhamdulillah! Safiya kin kyauta ina tufka ina warwarewa. Ai tunda na ga Hisham ya shigo gidan nan na san da da hannunki ciki. Kije na sakeki saki daya, ki tabbar kafin ki fita kin haɗa da wannan watsattsen yaron naki."

Ji da ganinta kai har ma da numfashinta tsayawa suka yi na wucin gadi. Ji take anya ba mafarki bane ta ke, Alhajin ne ya saketa.

Maganar Hisham ce ta dawo da ita cikin hayyacinta.

"Umma Kada ki wani damu! Allah ne ya iyakance miki zaman gidan nan. Me kike tsinta a ciki in Banda ɓacin rai da takaici. Kina gama idda akwai zawarawa sabbi fil Umma sai kin zaba kin dar..."

Sauran maganar ce ta kasa fitowa sakamakon lafiyayyun marin da mahaifinsa ya ɗauke shi da su. Bai bata lokaci ba ya ci gaba da jibgarsa tamkar Allah ya aikosa, cikin rufewar ido Alhaji ya buga Hisham saman daning table, Hisham da fasassun glass a tare suka kai ƙasa kafin ka ce me jini ya ɓalle ko motsi bai kara yi ba.

A gigice Umma ta yi kansa ta na kiran sunansa. Hannunsa ta ɗaya ta ga hannu ya koma ƙasa sharaf.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Hisham babu. Alhaji ka kashe Hisham"

Tana karasa maganar numfashinta ya tsaya cAk! A gefen Hisham ta sulale.

Dariyar mugunta Hajiya ta saki kafin ta fashe da kuka.

"mun shiga uku Alhaji hawa biyu a gabanmu wayyo Hisham ɗinmu....

MASU BUKATAR LITTAFIN KAI TSAYE SU SHIGA NAN👇👇👇👇

***