BA NI DA IKO...

BABI NA BAKWAI

by @fareedaabdallah

***

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

7)

Sannu a hankali ya ɗaga idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur kamar an watsa barkono ya zuba su akan Hajiya, tsawon daƙiƙu goma. Sai kuma ya kawar da idanun ya kalli gefe ɗaya, ko kallon jaririyar da take miƙa mishi baiyi ba. Yaraf! Ya tafi da baya ya zube akan kujera.

Kanshi da yaji yana barazanar fashewa ya dafe da hannu bibiyu. Da ƙyar ya iya haɗiye wani dunƙulallen miyau da ya tsaya mishi a maƙogwaro, ya buɗe bakinsa a hankali ya ce

"Hajiya... Don girman Allah ki fice min da yarinyar nan. Wallahi Tallahi ba na ko ƙaunar ganinta a kusa da ni..."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Hajiya ta katse shi da faɗin haka hankalinta a tashe. Duk da ta tsammaci ganin haka, saboda ta san ya matuƙar saka rai kuma ya sakankance da cewar Binta za ta haifa mishi magajinsa.

To amma ya suka iya da abinda ya gagari wuta? Likitoci ko ita kanta Binta ba su da ikon da za su saka ta haifi Namiji. Da wannan dalilin kuwa za tayi iya ƙoƙarinta na ganin ta hana shi furtawa ko aikata abinda zai janyo mishi fushin Ubangiji, akan abinda hatta shi da yake uban cikin ba shi da iko.

Hajiya ta ɓata fuska, ranta a ɓace ta kira sunanshi.

"Balarabe?"

Kafin ya amsa ta sake cewa

"Kana cikin hankalinka kuwa? Wai me yake faruwa ne? Me yake damunka? Babbar kyautar da Allah yayi maka ba tare da ka biya ko sisin kwabo ba kake ce wa ba ka ko ƙaunar ganinta a kusa da kai?"

Hajiya ta jero mishi tambayoyin hankalinta a tashe.

Sai kuma ta mayar da idanunta kan kyakkyawar jaririyar da take riƙe a hannunta, yarinyar da sai bayan anyi mata wanka ne ma kyawunta ya ƙara bayyana. Kamar ɗiyan larabawa, fara tas da ita.

Ga hancinta mai tsawo, bakinta ɗan cut! ɗazu da ta buɗe idanunta gurin wanka manyan idanu gare ta dara-dara kuma farare tas! Anyi mata kwalliya cikin sababbin fararen kayan sanyi na saƙa, sun amshi jikinta sosai. Ta yi luf a cikinsu tana barci cikin nutsuwa ba tare da ta san abinda ke faruwa ba.

A karo na biyu Malam ya sake buɗe baki daƙyar ya ce

"Hajiya..."

Maganarsa tsayawa yayi sanadiyyar ƙaƙƙarfan kururuwan ihun Ramatu da suka jiyo ya karaɗe tsakar gida.

A tare su biyun ƙirjinsu ya buga daram! Malam Balarabe ya yunƙura zai fita sai kuma ya dakata sanadiyyar maganganun da ya ji suna fita daga bakin Ramatu cikin kuka.

"Wayyo Allah na mun bani mun lalace... Shi kenan! Binta ta kassara mu ta kassaraka Malam.. ta haifo maka annoba da alkaba'i a ranar Larabgana... ga shi tun yau ka fara karɓan ɗaya daga cikin baƙaƙen masifun da za su biyo bayan haihuwar baƙar kadara a gidanka."

Ta sake kwantsama ihu a karo na biyu, muryarta cikin kuka ya cigaba da kusanto turakar Malam tana cewa

"Malam! Malam!! Wai kana ina ne Malam? Ka fito ka ji saƙon da maƙwafcinka na Babbar gonarka ta hayin Kogi ya iso da mummunar saƙon yadda Ƙudan Ƙasa suka yanyame gonarka... Duk yadda suka so korarsu sun kasa... ya rantse da girman Allah ko kafin ya baro gonar zuwa nan Ƙudan sun yi mummunar illah ga masarar, wata kila yanzu ma sun gama lalata amfanin gonar gaba ɗaya..."

Hajiya na ɗaga ƙafa da niyyar fita ta tari Ramatu Malam ya riga ta ficewa a saba'in, Ramatu tana ƙoƙarin riƙo gefen rigarshi ya fisge ya fice da gudu hankalinsa a matuƙar tashe. Ko da ya isa ƙofar gida sai yaga ashe har maƙwafta sun san abinda yake faruwa, sun lulluɓe Malam Amadu yana kora musu bayanin yadda abin ya faru, kamar aikin asiri.

Domin kuwa duk da ɗaiɗaiku daga cikin ƙwarin sun shiga wasu gonaki da suke kusa da gurin, Miliyoyin ƙwarin sun tattara ne a gonar Malam Balarabe. Gonar da ta nunka ko wace gona girma a faɗin kewayen gurin.

Da yake akan mashin yake tafe, yana ganin fitowar Mal Balarabe yayi gaggawar tayar da mashin ɗin yana cewa

"Hau mu je ka gani Malam Balarabe. Al'amarin ya yi munin da muka rasa ta inda za mu ɓullo masa. Wannan bala'i ne kawai Allah ya aiko, sai dai muyi fatan Allah ya taƙaita."

Bai iya cewa komai ba ya hau mashin ɗin, a guje Malam Amadu ya fige ta kamar ba dattijo ba suka bar ƙofar gidan.

Nan take wasu daga cikin maƙwaftan da suke da babura suka yi goyon-goyo suka rufa musu baya. Hankalin kowa a tashe. Zukatansu cike da tausayin Malam Balarabe. Domin duk cikin gonakinsa wannan ta fi ko wacce girma, a gonar kaɗai yana noma amfanin gonar da sai ɗaiɗaikun manyan manoma a ƙauyen ke iya noma kwatankwacin yawansa idan sun haɗa noman gonakinsu gaba ɗaya.

Ko da suka isa, aikin gama ya riga ya gama. Duk girman gonar da amfanin cikinta ƙwarin sun lalata gaba ɗaya, kuma cikin ƙanƙanin lokaci. Ƙwarin sun ɗan taɓa wasu gonakin, amma basu lalata gaba ɗaya kamar yadda suka yi ma gonar Malam Balarabe ba.

Ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak! Ya ma rasa wane irin tunani ya kamata yayi. Yana tsaye kamar mutum-mutumi, yana sauraren bayanin da waɗanda mummunar al'amarin ya faru a gabansu suke yi.

Wani Markus da ya kasance gwari amma ya ji hausa shi ne yayi cikakken bayanin yadda komai ya faru tun daga farko har ƙarshe.

"Da farko sama ne ta fara yin duhu kamar hadari zai zubo ruwa...Daga baya kuma sai muka ɗauka gajimare ne, amma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci muka gane ba gajimare ba ne... Ƙudan ƙasa ne, Miliyoyinsu, suna shawagi a cikin samaniya. Ƙarar fikafikansu ya cika kunne, kamar waɗanda aka yi ma aika sai suka mamaye gonar Malam Balarabe.

Suka sauka kamar tsuntsaye, kowanne ƙuda na kama ciyawa da masara. Cikin ƙanƙanin lokaci reshen ko wane masara suka fara faɗuwa ƙasa kamar an zuba musu wuta... Da farko mun yi ƙoƙarin koransu da tsintsiya, amma da kaɗan sun tashi sai dubunnai su sake yanyame ko wace reshe.

Mutanenmu na hayin kogi sun kawo ɗaukin garwashi, suna ta dukansu da tsintsiyoyi, amma ƙwarin sun yi musu yawan da basa jin duka basa jin garwashi... Sai da suka gama lalata komai, kamar za su cigaba da ɓata wasu gonakin, sai kuma suka yi layi a cure suka nufi gabas ta inda suka fito..."

Yuuuu... jiri ya kwashi Malam Balarabe zai kife a ƙasa da saurin gaske waɗanda ke kusa da shi suka tare shi.

"Subhanallahi! Assha! Sai haƙuri Malam Balarabe. Abu baiyi daɗi ba amma ya za muyi da ikon Allah? Kayi haƙuri... Allah ya mayar maka da mafi alkhairi."

Ire-iren kalaman da jama'a suka yi ta furta mishi kenan cikin kwantar da murya. Bai iya ce ma kowa komai ba sai numfarfashi da yake ja sama-sama kamar mai cutar Asma.

Daga ƙarshe Malam Amadu da ya ɗaukosa ne ya sake goya shi a mashin, Malam Iliya ya hau bayansu ya tare Malam Balarabe, suka bar gurin cikin tashin hankali.

Har za su nufi gida da shi, amma duba da yadda numfashinshi ya cigaba da yin sama-sama, ga wani irin zafi da jikinsa ya ɗauka yasa suka wuce da shi asibiti. Babban asibitin Gwamnati da yake ƙauyen.

Sai da aka kwantar da shi aka ɗaura mishi ƙarin ruwa sannan Malam Amadu ya tafi, da cewar kafin ya koma gona zai je ya sanar ma da iyalan Malam Balarabe abinda yake faruwa.

*****

Kwananshi biyar a asibiti ya matsa aka sallame shi, ba don ya gama jin sauƙi gaba ɗaya ba. A cewarsa zai ƙarasa warkewa a gida.

Wannan mummunar asara da yayi, asarar da ko maƙiyinsa in dai yana da zuciyar imani sai ya tausaya mishi, shi ya dakushe farin cikin haihuwar Binta gaba ɗaya.

Sai ya zama da yawan masu zuwa gidan dubiyar jikinsa da jajen asarar da yayi kawai suke yi mishi da iyalansa. Ita kuwa Ramatu sai tayi amfani da wannan dama ta ƙara ruruta zancen ai haifar jaririya da Binta tayi a daren wayewar Larabgana shi ne silar afkuwar wannan babban bala'i a gare su.

Abinku da mutanen ƙauye, da jahilan cikinsu suka fi masu ilimi yawa. Duk yadda Hajiya ke ta kore zancen da nuna girman tawakkali da yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau maganganun Ramatu ya fi nata karɓuwa.

Kaso biyu bisa uku na mutanen ƙauyen sun yi amanna da cewar haihuwar wannan jaririya ko ba don a ranar Larabgana aka haife ta ba to tabbas bata zo da sa'a ba, ba ta kasance sila ta alkhairi ga mahaifinta ba.

Ƴan'uwa da ƙawayen Ramatu kuma, waɗanda suke da labarin irin romon wulaƙancin da ta sharɓa sanadiyyar Binta da cikin jikinta, cikin da aka gama fata da ɗora burin a haifi namiji, sai aka haifi mace, ga mummunar asara ta biyo baya. Sai suke ƙara ma zancen gishiri da cewa har da alhakin Ramatu a faruwar wannan al'amari.

"Ai Allah ba azzalumin sarki bane... Zalunci da cin amanar da Balarabe yayi ma Sadiya sanadiyyar Binta ni dama na san komai daren daɗewa sai Allah yayi mata sakayya. Ai ga shi nan, idan ma bai roƙe ta gafara sannan ya gyara zamantakewarsa da ita ba kaɗan ya fara gani."

Cewar Yayarta Hadiza.

A ɓangaren Binta kuwa, baiwar Allah. Gaba ɗaya ta tsangwami kanta, farin ciki da godiya ga Allah da ya kamata tayi saboda ya raba ta da cikin jikinta lafiya sam ba ta yi ba. Sai take ji a ranta kamar dai maganganun da Ramatu take yi gaskiya ne, ko dai jaririyarta mummunar ƙaddara ce ga Malam da ita kanta?

Idan ta zo nan a tunaninta kuma sai tayi saurin yin Istigfari, domin ita ba jahila bace. Tana da iliminta na addini daidai gwargwado. Ta sani babu wata rana da za'a ce don an haifi yaro a cikinta zai kasance silar afkuwar bala'i ga iyayensa. Kawai dai wannan asara tun tale-tale Allah ya riga ya ƙaddara zai faru da Malam a ranar da ta haihu, shi kenan.

Sai dai kuma hankalinta yana ƙara tashi idan ta shiga turakar Malam gaishe sa taga yadda yake amsa ta, kamar wata baƙuwa... ko kuma wacce bai sani ba balle har wani sabo ya shiga tsakaninsu.

Ba ma ya ko son kallonta. Kuma daga amsa gaisuwa sau ɗaya baya ko ƙara amsawa. Haka za ta gaji da tsugunno ta tashi ta fice daga ɗakin. Tana daɗewa a ɗakin ne kawai idan Hajiya tana ciki, saboda ita za tayi ta jan ta da hira a fakaice tana kwantar mata da hankali.

Idan kuwa tayi rashin sa'ar tarar da Ramatu a ciki... Wohoho! Ai ko mintuna biyu cikakku ba ta yi za ta fice saboda tsabar habaici da gori, da baƙaƙen maganganun da za tayi ta caccaɓa mata.

Abubuwa biyu ke faranta ran Binta, har yasa ta ji sanyi kaɗan da nutsuwa a zuciyarta. Na farko shi ne idan ta ɗauki kyakkyawar jaririyarta, ta ƙura mata idanu, kamar maganaɗisu sai ta ji wani sanyi a ranta. Har ma ta sakar ma ƴar wani lallausan murmushi.

Abu na biyu kuma shi ne idan taga yadda Mahaifinta Alhaji Habu, Kawunta Bala, matar Kawunta da take kira Anty Halima da sauran danginta na kusa suke tarairayarta. Har gidanta Mahaifinta da Kawunta suka je, bayan sun duba jikin Malam suka yi mishi jaje, har ɗakinta suka shiga ganin jaririya.

Sun yi mata nasiha sosai da kalaman kwantar da hankali, domin suna da labarin duk irin maganganun da ke zagayawa a ƙauyen. Sannan suka kawo kuɗaɗe masu yawa suka damƙa mata, musamman mahaifinta da ya kasance mai rufin asiri sosai, tunda har Makka ya je a shekarun baya kafin rasuwar Innarta.

Bayan tafiyarsu kuma kullum sai sun tura mata matayensu don taya ta zaman bakwai. Ita kuwa Aunty Halima bayan zuwa gidan safe da yamma tayi ma jaririya da ita kanta Binta wanka. Kusan kullum da rana sai ta dafa ma Binta nama mai ruwa-ruwa da lafiyayyen kunu ta aike mata da shi.

Tana zuwa nan a tunaninta ta ja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Ta kalli fuskar jaririyarta da har yau da ta kwana shida a duniya bata san wani suna za'a saka mata ba. Tayi murmushi, ta ce a fili

"Wannan ma zai wuce."

*****

Misalin ƙarfe tara na daren ranar, Binta ta gyare jikinta tsaf! Tayi kwalliya sosai cikin ɗinkin leshinta riga da zani. Ta fesa turare, ta kafa ɗaurin ture kaga tsiya. Sannan ta saɓa ƴar jaririyarta da itama take ta ƙamshi ta nufi turakar Malam.

A zuciyarta take jan duk addu'ar da ta zo bakinta, saboda magana ce take so suyi ta fahimta, tana fatan ya saurare ta da kunnen basira. Shi yasa ta je a sadda take da tabbacin Ramatu ba ta ɗakin, domin ta ji hayaniyarta da yaranta mintuna kaɗan da suka wuce.

Cikin nutsuwa, da siririyar muryarta tayi sallama a ƙofar ɗakin har sau biyu a ƙofar ɗakin. Jin da tayi ba'a amsa mata ba sai tayi tunanin ko har Malam ɗin ya kwanta.

Ta yi kamar za ta juya, sai kuma wata zuciyar ta ce mata

'Ki leƙa ki gani mana, kila bai fara barci ba.'

Kawai sai ta yaye labulen ta cusa kanta cikin ɗakin.

Turus! Tayi a bakin ƙofa, ganin Malam zaune a kan kujera, idanunsa biyu, yana kallonta tana kallonsa. Suka yi musayar kallo na wasu daƙiƙu sai kuma ya matse fuska ya kawar gefe ɗaya.

Jikinta ne ya ɗanyi sanyi, cikin raunin murya ta ce

"Yanzu saboda Allah Malam fushin da kake yi da ni akan abinda ba ni da iko har ya kai kana jin muryata ina sallama kayi banza da ni?"

Kamar da dutse take magana, idan ya tanka, kujerar da yake zaune akai ta tanka.

"Uhmmm"

Ta ja numfashi cikin ɓacin rai. Kamar za ta fita saboda fushi, sai kuma ta daure ta ƙarasa kan kujera ta zauna tana fuskantarsa.

"Gobe idan Allah ya kaimu kwanaki bakwai kenan da na haifi wannan ƴar taka. Zuwa nayi ka faɗa min wane suna ka zaɓa mata? Tunda dai ɓoye sunan sai ranar bakwai ba addini bane. Idan kuma baka zaɓa mata ba sai muyi shawara a tsakaninmu mu fitar da sunan da ya dace da ita..."

Buff! Ramatu ta banko labulen ɗakin ta shigo dagaje-dagaje da ita kamar an koro ta. Daga ita sai ɗaurin ƙirji, hannunta duk miyar ɗanyen kuɓewa. Tuwo take ci, amma tunda Zakiyya ta ce mata ta je giftawa ta turakar Babansu ta ji muryar Binta a ciki bata tsaya wani wanke hannu ba kawai ta fito zuwa turakar a fusace...