BA NI DA IKO...

BABI NA TARA

by @fareedaabdallah

BA NI DA IKO...

©Fareeda Abdallah

***

Wannan littafin na kuɗi ne, 1k. A yanzu zan bada Free pages na book 1 a nan Whatsapp in sha Allah. Masu son littafin su saka kuɗinsu ta wannan account ɗin. 5407827015, FCMB, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar *** domin samun damar shiga group ɗin da zan dinga posting na labarin a Telegram da Arewa books.

In dai matsalar haihuwa ce ɓangaren mace ko namiji, muna bada saiwoyin maganin gargajiya da za a sha a samu biyan buƙata da yaddar Allah, kuɗin maganin 5k. Maganin Infection, Cancer, Ulcer, Suger, Hawan jini, duk muna bada magungunansu da yaddar Allah. ***.

9)

Sallamar da ake ta dokawa a ƙofar ɗakinta yasa ta miƙe zaune tana mitsittsika idanu. Barci har ya fara ɗaukanta, ƙasa-ƙasa ta ja tsaki, kanta ciwo yake yi sosai. Shi yasa ta so ta yi barci ko na awa biyu ne, tunda Hajiya ta tafi unguwa da Humaira tun misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe.

"Waye a nan?"

Ta tambaya da murya mai kauri, jin da tayi an sake yin sallama.

"Anty Binta ni ne, Isma'il na gidan Mai Unguwa."

Muryar wani matashin yaro ya amsa mata daga can waje.

Kafin tayi magana ya sake cewa

"Dama Malam ne ya aiko ni in kawo miki saƙo..."

"Saƙo?"

Ta katse shi da mamaki a muryarta.

"Kuma ni ya ce ka kawo ma saƙon?"

Ta sake tambayarsa.

Sai kuma tayi hanzarin sauka daga kan gadon, ta ɗauki hijabin sallarta ta zumbula akan rigar shan iska da yake jikinta ta fita zuwa falo.

Tana buɗe labulen sai tayi arba da Isma'il yaron maƙwafcinsu, riƙe da wata ƙatuwar leda yellow mai zane-zane, duk da bata karɓi ledar ba, ta hango kayan miya a ciki, sannan ta hango kamar ƙwai kamar dankalin turawa a wani ɓangare na cikin ledar. Domin sake tabbatarwa sai ta saka hannu ta taɓo ƙasan ledar, a nan ne kuma ta ji tuɓu-tuɓun ɗanyen nama mai yawa, ta ɗaya gefen kuma ƙwai ne da dankalin turawa.

Nan take ƙwaƙwalwarta ta haɗa ɗaya bisa biyu ta fahimci abinda ke shirin faruwa. Bata san sa'adda wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce a fuskarta ba. Hankali kwance ta ce

"Ai kam dai Isma'il ka yi ɓatan kai, wannan cefanen ba ni ya ce ka kawo ma ba, Innarsu Zakiyya za ka kaima..."

"Wallahi Anty Binta ke ya ce in kawo ma."

Isma'il ya katse ta

"Har sai da ya ƙara jaddada min ma ke zan kawo ma ba Innarsu Zakiyya ba."

Ya sake faɗa da tabbaci.

"To shi kenan! Na fahimta. Amma duk da haka dai je ka kai mata cefanen, ina ga kuskuren daga gurin Malam ne, ya manta ni tun jiya na fita girki. Idan ya shigo zanyi masa bayani, yi sauri ka kai mata ka ji Isma'il?"

Ɗan jim yaron yayi a tsaye. Kamar bazai kai ma Ramatu ba, saboda yadda Malam yayi ta jaddada masa lallai Binta zai kai ma cefanen. Amma kuma da ya tuna da Ramatu da Binta duk matan Malam ɗin ne, sai kawai ya juya zuwa ɗakin Ramatu yayi sallama, dama tana can cikin ƙuryar ɗakinta da Aminiyarta ta ƙud da ƙut suna hira, shi yasa bata san Malam ya aiko ma da Binta cefane ba.

Washe bakinta tayi kamar gonar auduga bayan ta karɓi ledar ta buɗe ta ga kayan daɗin da ke ciki. Jikinta na rawa ta ce ma yaron

"Na gode Ma'ila. Ka ce ma Innarka ina gaishe ta."

Bata jira ya amsa ba ta shige ɗaki da sauri tana nuna ma Aminiyarta Safiya rikitiɓar arzikin da Malam ya aiko mata da shi.

Safiya ta kama haɓa cikin mamaki take jinjinawa.

"Ah lallai Ramatu. Gaskiya na ƙara yarda kin gama da Malam Balarabe. Yanzu duk wannan uban nama da ƙwai da dankalin turawan da ya aiko da shi a girkin yamma ne kawai? Yau ba ranar alhamis ba, kuma ba ranar juma'a ba?"

Ƙaƙƙarfan dariya Ramatu ta fashe da shi, kanta sai kumbura yake yi jin yadda ƙawarta ke zuzuta irin hidimar da Malam ke mata.

"Ai Wallahi wannan ma kaɗan kika gani Safiya. Ina faɗa miki duk gidan da kika ga ba'a canjin abinci sai ranar alhamis da ta kasance kasuwar garinnan, ko kuma juma'a to fa lallai rufin asirin bai kai yadda ake zuzutawa ba. Malam fa ko da yayi asarar nan yana da kadarori, kinga kuwa ko da goma ta lalace ai ta fi biyar albarka."

Ta ƙarasa maganar tana dariya.

"Kuma idan baki manta ba na faɗa miki tun kafin waccan banzar ta haihu ya aje ta a kwandon shara. Har yau ɗinnan ni ce dai matar so a gidannan, kuma kullum irin cefanen da yake aiko min da shi kenan. (Ta yanko ƙarya ta zabga ma Safiya.)"

Ta cigaba da magana da salon cika baki. Tana ji a ranta a yanzu babu wata mace a idanu da zuciyar Malam sai ita ɗaya.

"Binta zaman banza ca-kuri cici cikon benci take yi a gidannan. Kin ga ba ta da kwana da miji, sannan ba ta da girki, duk wannan cefanen kayan daɗin da kika gani sai dai duk abinda na dafa in ɗan sammata abinda na ga dama, saboda fita hakki. Ke watarana ma Wallahi idan na tuno irin cin kashin da tayi min a baya, da gangar nake ƙin zuba mata abinci. Amma da yake mayya ce ko ƙorafi bata taɓa yi ma Malam ba, kuma har yau ta ƙi yin zuciya ta tafi gidan ubanta."

Ta ƙarasa maganar da baƙin cikin rashin tafiyar Binta a zuciyarta.

Tayi ƙwafa, sannan ta cigaba da cewa,

"Ko da yake ki bari kawai, kwanannan za ki ji labarin fashewar Bom ɗin da zan ɗana mata. Na san matakin da zan ɗauka. Mummunan ƙulli zanyi mata a gurin Malam, ƙullin da duk nacinta sai ta bar gidannan da ƙafafunta tun da ba na ubanta bane."

Suka yi dariya a tare, sannan suka tafa irinna aminai.

Safiya bata ƙara daɗewa ba tayi ma Ramatu sallama za ta tafi, har sun kai ƙofa Ramatu na mata rakiya, sai kuma ta juyo da dariya a fuskarta ta ce

"Aminiyas ina fatan dai wannan kayan daɗi da idona ya gani akwai kasona a ciki?"

"In don wannan ne kar ki damu Safiya. Anjima idan na gama girki zan aiko Hadiza ta kawo miki. Amma fa ki tabbatar kin juye ki bata kwanon ta dawo min da shi, domin gidanku kwano idan ya shiga rububi ba kasafai ya cika dawowa ta daɗin rai ba."

Suka sake yin dariya a tare. Suka rabu Safiya na ta zuba godiyar yau ɗaya dai za ta huta da cin tuwon dawan da suke yi duk dare, sai dai kullum ayi canjin miya, yau kuka gobe kuɓewa, ko ɗazu da ta fito ta ji kishiyarta na aiken a siyo mata garin busasshiyar kuɓewa.

******

Maimakon ta cigaba da kwanciyar kawai sai taje tayi wanka. Tana shafa mai take mamakin Malam da ya iya aiko mata da cefane yau da rana tsaka.

"Lallai da gaske namiji bai da kunya."

Ta faɗa a fili tana dariya.

Yau kwananta casa'in da uku da haihuwar Nana Aisha, wacce take yi ma inkiya da Humaira. Tun da tayi arba'in ta saka ran za'a bata girki, amma sai taga daga Malam ɗin har Binta ba su da niyyar yin haka.

Akwai ranar da tana tsakar gida Malam ya dawo da cefane, ko da tayi yunƙurin karɓa ba ƙaramin cin mutunci da gori Ramatu tai mata ba, kuma abu mafi baƙin ciki da takaicin shi ne Malam yana ji bai ce komai ba, a madadin yayi magana ma sai kaɗa kanshi yayi ya shige ɗakinsa.

Saboda baƙin ciki da ta koma ɗakinta sai da tayi kuka. Sannan ta sha alwashin in Allah ya yarda daga wannan ranar baza ta ƙara nuna tana so ta karɓi girki ba. Za ta zuba musu idanu, suk yadda suka dama haka za ta sha da haƙuri.

Bayan kwanaki da taga zaman haka bazaiyi mata ba sai tayi tunanin fara taɓa kasuwanci daga cikin gida. Taimakon da Allah yayi mata shi ne kullen unguwa da Malam ya daina mata, saboda ba ta ita yake yi ba. Duk sadda ta tambaye shi zuwa unguwa hannu kawai yake ɗaga mata alamun ya lamunce mata.

Da wannan damar tayi amfani tayi yawon arba'in hankalinta kwance. Duk wasu ƴan'uwanta na nesa da na kusa da suke yawan yi mata ƙorafin ba ta son zumunci sai da ta leƙa ta gaishe su.

Wata ranar asabar da safe tayi sammakon tafiya Kaduna. Sadda tayi auren farko a cikin Kaduna akwai matan arziki da tayi zaman maƙwaftaka da su, suka riƙe ta kamar ƴar'uwa.

Ɗaya daga cikinsu ita ce Aunty Shafa'atu, suna yi mata inkiya da Maman Fati, saboda ba yarinya ƙarama bace. Kamar ƴa haka ta riƙe Binta, saboda takwarar babbar ƴarta ce. Kai tsaye gidan Maman Fati tayi ma dirar mikiya.

Ta samu tarbar girma kamar yadda ta zata. Maman Fati ta ji daɗin ganin Binta fiye da yadda tayi tsammani, bayan dogon ƙorafin tunda aurenta ya mutu bata ƙara waiwayarsu ba ta yi mamakin ganinta da goyon kyakkyawar jaririya, saboda basu san Binta ta yi aure bayan barinta unguwar ba.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta cika gaban Binta da kayan ciye-ciye da ababen sha masu daɗi.

Babban abinda ya fi yima Binta daɗi a wannan ziyara da ta kai shi ne ganin ƴaƴanta da tayi, direba ya fito da su a mota an shirya su tsaf-tsaf za a kaisu Tahfeez, Maman Fati ita ta kira direban ta dakatar da shi, sannan ta shiga mata da yaran.

Da farko cak suka tsaya guri ɗaya, saboda ganin Ummeen tasu a wannan lokacin abu ne da basu taɓa tsammani ba. Sai kuma suka ruga a guje suka rungumeta, Abdallah da Yusuf suka fashe da kuka. Shi dai Al'amin da ya kasance ƙarami baiyi kuka ba sai naniƙe mata da yai tayi, saboda ya gane ta, akwai hotonta da Abdallah yake nuna musu da cewa ita ce Ummeensu.

A gurguje suka gaisa, haka sukai ta rungume ƙanwarsu kamar a basu ita su tafi da ita gidansu. Ta kawo ƴan kuɗaɗe masu yawa ta basu duk da ta san kuɗi ba matsalarsu bace, bata san za su haɗu ba shi yasa bata yi musu tsaraba ba. Ko da tace su tafi haka suka sake fashewa da kuka, ita kanta sai da tayi ƙwallah. Tuna ba yadda ta iya da ƙaddarar Allah yasa ta rarrashi kanta ta rarrashe su, ta raka su har jikin mota sannan suka tafi. Bayan ta yi musu ƙwaƙƙwaran gargaɗi kar su kuskura su faɗa ma mahaifinsu ko matar Babansu ta zo unguwar.

Bayan sun gama hirar yaushe gamo ne ta faɗa ma Maman Fati abinda yake tafe da ita. Shinkafar Hausa mai kyau take so ta dinga sarowa daga Kasuwar Magani tana aike ma Maman Fati tana siyar mata, tunda ita Maman Fati ƴar kasuwa ce, babu abinda ba ta siyarwa.

A wancan lokacin da Binta ke aure a unguwar Maman Fati ta sha bata saƙon shinkafa ƴar hausa a Kasuwar magani duk sadda za ta je ganin gida, saboda duk ranar alhamis ana samun shinkafar hausa mai kyau sosai a gurin Gwarawa.

Sosai Maman Fati taji daɗin wannan kasuwanci da Binta tazo mata da tayinshi. Domin ƙara ƙarfafa mata gwuiwa ma kafin su rabu sai da ta bata kuɗin buhu ɗaya. Ta kuma jaddada mata lallai ta lissafa ta fitar da kuɗin mota ta ɗora ribarta, sai su ga nawa kuɗin ko wane kwano zai kama, kuma nawa kuɗin buhu?

Wasu kyawawan dogayen riguna na ɗinki na yara da manya da Binta ta gani Maman Fatin tana siyarwa tayi shahaɗar ɗiban dozen biyu ta ce za ta je ta gwada siyarwa a Kasuwar Magani. Kuma cikin hukuncin Allah sai ta fara a sa'a, cikin kwanaki biyu rigunan suka ƙare tas!

Yanzu haka kasuwancin da take yi kenan, kuma Allah ya saka mata albarka a ciki. Tana samun kuɗi fiye da yadda ta zata a farko, babban asusu ta siya tana zuba kaso biyu bisa uku na ribar da take samu. Duk sati za ta aike ma Maman Fati shinkafa buhu uku, idan direba ya kai sai a bashi dogayen riguna ya kawo mata.

Bata taɓa samun matsalar rashin haɗuwar kuɗi akan lokaci ba, har ƴan ƙauyen kusa da su suna zuwa sarin dogayen riguna a wajenta.

Wannan kasuwancin da take yi shi ya ɗauke mata kaso tamanin cikin ɗari na damuwar Malam da Ramatu. Ta cigaba da rainon Humaira cikin nutsuwa, yarinyar ta ƙara ɓul-ɓul tubarakallah, kamar ba ƴar wata uku ba. Har yanzu farin fatarta na nan kaman ƴar larabawa in ji Hajiya. Ga ta da haƙuri, idan ba zazzaɓi take yi ba ana jimawa ba a ji kukanta a cikin gidan ba.

******

Bayan sallar Isha'i, tana zaune a kan kujera, ta yi kwalliya cikin riga da wandon karan miski masu kyawun gaske. Daga Kaduna Maman Fati ta aiko mata da kayan, bata taɓa sakawa ba sai yau. Ta daɗe tana kallon kanta a madubi, ita da kanta ta san ta yi kyau sosai.

Babu wanda zai kalleta ya ce ta haifi yara har huɗu saboda irin kyan jikin da Allah yayi mata. Da yake ita fara ce, sai ta haska sosai a cikin kayan.

Farar taliya ce a gabanta take ci, ga miyar tarugu da albasa da ta soya da manja, ta zuba kifi sosai a ciki. Ba yau Ramatu ta fara hana ta abinci ba, shi yasa ko da taga irin cefanen da aka kawo bata saka ran za a bata ba. Girkinta tayi a cikin kicin ɗinta kamar yadda ta saba, Hajiya kawai ta ɗiba ma, ta sake sauran a kula ta shige da shi ɗakinta.

Humaira na kwance a gefenta kan kujerar, idanunta biyu, tana ta watsal-watsal da ƙafafunta tana wasa. Ta kai lomar taliya bakinta ta ji sallamar Malam a bakin ƙofa, ko kafin ta haɗiye abincin ta amsa mishi har ya yaye labulen ɗakin ya shiga ciki.

Kamar baza ta amsa mishi ba, sai kuma ta danne zuciyarta ta amsa sallamarsa. Idanunta na kan abincin da take ci, da yanayin rashin kulawa ta ce

"Barka da dare Malam."

Tsaye yayi a tsakar ɗakin yana kallon abinda take ci.

"Yauwa Binta."

Ya amsa.

"Ya gidan?"

Ya tambayeta da sassaucin ɗaurewar da yake yi sosai a fuskarsa.

"Gida lafiya lau."

Ta amsa a taƙaice. Sai kuma ta ba iska ajiyarsa ta cigaba da cin taliyarta cikin kwanciyar hankali, kamar ma bata san da mutum a tsakar ɗakin ba .

Tun daga sama har ƙasa yake kallon irin kyawun da tayi. Haka kawai ya samu kansa da gode ma Allah da ya mallaka masa Binta a matsayin matarsa. Bai san yayi kewarta da yawa ba, sai yanzu da ya ganshi tsaye a kusa da ita. Ƙamshin daddaɗan humran jikinta da yake shaƙa tun daga nesa shi yake ƙara birkita mishi lissafi. Kamar ya janyo ta ya rungumeta tsam a ƙirjinsa yake ji, amma irin yadda ta game fuskarta guri ɗaya yasa shi ƙoƙarin dannewa ya kame kansa.

Sai ma ya rasa ta inda zai kamo ya cigaba da yi mata magana. A daburce ya ce

"Ya kuma na ga kina cin taliya Binta?"

"Ya bazan ci taliya ba Malam?"

Ta mayar mishi da tambayar tana watsa mishi wani irin kallo da dara-daran fararen idanunta.

Da baya da baya ya tafi a hankali ya zauna daɓas a ɗaya daga cikin kujerunta, hankalinsa ne ke ƙoƙarin tashi jin yadda ta amsa mishi, amma kuma yana ta iya ƙoƙarin dannewa kar ya bada kanshi a gabanta.

"Wai daman gani nayi ɗazu na aiko miki da cefane... Na zaci shi zan dawo in tarar kina ci?"

"Cefane?"

Sai kuma tayi wata siririyar dariya da ta ƙara ma fuskarta kyawu.

"Ka aiko ma da Matarka Ramatu cefane dai Malam! Tabbas yaro ya kawo min leda, amma sai na faɗa mishi ɓatan kai yayi, Ramatu zai miƙa ma don ita ce matar gidannan. Ni tuntuni ai ba ni da kason abincin da kake kawowa, ko ka manta ne? Ba ni da girki... Ba ni da kwana... tunda kuwa zaman kaina nake yi ai ka ga dole in nema ma cikina abinda zan ci... Musamman ma da nake da ɗanyen goyo, sai na ci, sannan ƴar laɓuɓuwata za ta samu abinda za ta ci a jikina. Don haka je can gurin matarka kabi kadin cefanen da ka aiko da shi ba gurina ba..."