SHAFUKAN ƘADDARATA .

PAGE 07.

by @sumy6163

⚡ SHAFUKAN ƘADDARATA ⚡

_*(pages of my destiny).*_

STORY AND WRITTEN BY:

Sumaiya M Tukur (the Charismatic).

PAGE 07.

Hajjo tana fitowa ta yi kiciɓis da Baffajo a ƙofar gidan yana safa da marwa, don bai samu ɗan aika ba, kuma bai kyautu ya shiga gida haka na matan aure haka kai tsaye ba.

Kallon Hajjo da take ta tafasa ya yi ya girgiza kai ya ce, "Mariya an tuno baya ke nan, ashe ban haneki ba, ashe baki min alƙwarin har abada kin daina wannan halin na ki ba? To shige mu je gida, kinga nan hanya ne bai kamata mu tsaya muna magana a nan ba"

Bata ce masa komai ba saboda yanda take jin zuciyarta na ƙuna, ta san idan ta furta wani abin yanzu bazai musu kyau ba. Gaba Baffajo ya sakata shi kuma yana baya, don gani yake zata iya canza shawara ta koma. Sai da suka isa har cikin gida kafin hankalinsa ya kwanta.

Ina zaune cikin taraddadi da tashin hankali suka shigo, ganin yanayin Hajjo yasa na shiga taitayina, don yanayi ne da zance ban taɓa ganinta a ciki ba. Ina kallo Baffa ya ɗibo ruwa a randan sanyi ya zauna ya yi tofi ya miƙa mata. Ba musu ta karɓa ta shanye, ajiyar zuciya ta dinga sauƙewa a-kai-a-kai. Sai da ya fahimci zuciyarta ta yi sanyi tukun ya fara mata magana cikin kwantar da hankali.

"Haba Hajjo, har ga Allah banji daɗin abin da kika aikata ba, kin fita gida ba tare da izinin mijinki ba, kinje har gidan mutane kin tada musu hankali, kina magana kina ɗaga murya har mazan waje suna jinki, ina mutunci a cikin wannan? Ai da wannan abin da kika aikata gara da ace haƙuri ki ka yi kika barwa Allah sai yafi miki alkhairi.

Kuka Hajjo ta fashe da shi ta ce, "Haba malam, 'yar tawa guda ɗaya tallin tal ake aibatawa ka ce kuma inyi shiru, ka kuwa san yanda na ji a raina, mayya fa malam, mayya fa suke ce mata, ina bazai yiwu ba, wallahi wannan karon sai dai ka yi haƙuri, don sai na nunawa Zainaba bata isa ba, sai na nuna mata iyakarta, sai ta san tayi kuskuren aibata mini 'ya, daga ita har zuri'arta kuwa. Idan har banyi haka ba ka ce ba Mariya ba ce, ɗiyar Kulu jikar Baushe, ai sai ta san cewa ko kura ta faɗi tafi ƙarfin akuya.". Tana gama magana ta miƙe ta shiga ɗakinta.

Kallona na mayar inda Baffajo ke zaune dafe da kansa, ga dukkan alamu kalaman Hajjo ne suke karakaina a cikin ƙwaƙwalwarsa. Damuwa ne ta bayyana a fuskata, ban taɓa tunanin faɗa wa Hajjo wannan maganar zai kawo tashin hankali har haka ba, Allah dai ya kawo ƙarshen wannan lamarin.

Da dare Baffajo ne ya ƙira Hajjo turakarsa bayan ya tabbatar da Shatu ta yi bacci. Dubanta ya yi sosai yana tunanin ta inda zai fara saƙa maganar da ya ke son yi mata, don ya tabbatar idan abin ya kai gobe komai zai iya lalacewa, musanman ma idan ta kaiwa kakanta Baushe ziyara. Gyara zama ya yi ya ƙira sunanta, ta amsa ta na mai zuba masa ido. Ya sake gyara zama ya ce.

"Mariya uwar marayu, mariya ta malan Bashari, bada kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, Mariya sarauniya kuma tauraruwar Bashari, an buga da ke an barki, kowa nan ya barki inda ya ganki, Mariya ɗiyar Baaba Kulu amanar Baushe, wa yace da ke ba ke ba, Mariya matar rufin asiri, Mariya ƴar aljannah, Mariya sarautar zuciyar Bashari."

Tuni wani murmushi ya kaiwa fuskarta ziyara ba tare da tayi shirin tarbansa ba. Ta kalli malam ta ce, "Gaskiya malam ka gama sani na ciki da bai, ka san lagona, yanzu duk yanda na ke jin ɓacin rai, a sannu sai naji duk sun fece."

"To ai Mariya, dama fushi da ɓacin rai basu da muhalli a wurinki, murmushi da kwanciyar hankali kaɗai nake son gani a tattare da ke. Yanzu dai ki natsu don Allah muyi magana ta fahimta."

Ina jinka malam."Hajjo ta faɗa tana tattara hankalita wuri gudi.

Baffajo ya gyara zama ya dubi Hajjo ya ce"Yawwa, so nake don Allah, don son da kike wa annabi ki janye ƙudurinki a kan Zainaba, na san komai kika ce zaki iya, amma wani lokacin haƙuri da fawwalawa Ubangiji lamari shi ya fi komai, kar ki manta kin fa min alƙawari kin daina komai, me yasa yanzu a kan wannan ƙaramin abin zaki sake jefa kanki a halaka, sannan kuma ai faɗa ba naki bane, yanzu fa kin girma, kin wuce yin duk waɗannan abubuwan, don Allah, ina roƙonki a matsayina na mijinki, na san mace ce ke mai biyayya, baki taɓa saɓawa umarnina ba, kuma na tabbatar baza ki fara yanzu ba. Kiyi haƙuri, muyi haƙuri, komai da kika gani yana da ƙarshensa, idan tata ƙaddarar ne tazo a haka mu taya ta da addu'a, Allah ya bata ikon tsallake ta."

Wani gwauron numfashi Hajjo ta sauƙe, mai haɗe da wani irin hawaye masu zafi. Bai hana ta ba sai da tayi mai isarta ta ɗan ji sauƙi a zuciyarta kafin ya shiga rarrashinta, da ƙyar da suɗin goshi ta yarda ta bar maganar, amma a can pasan ranta kokawa take da zuciya da ruhinta.

Washegari ina jiran jin ta inda Hajjo zata faro sai naji shiru, sai da yamma da Hassan ya zo ta ce ina takardar sakina, a take zuciyata ta tsinke, saki! Na furta. Ban san me ya faɗa mata ba, sai ji nayi ta ce ya tafi kar ya sake taka ƙafarsa a gidan sai dai idan da takardar saki, ba irin magiya da ban haƙurin da bai mata ba amma tayi biris da shi, tun yana zuwa har dai ya ɗauke ƙafarsa ya daina zuwa. Rayuwa ta min ƙunci, na shiga matsanaicin damuwa wanda har ta kaini ga kwanciya ciwo.

Wasa wasa fa magana ta fara zagaya gari ana alaƙanta gidanmu da gidan mayu, ɗaliban da suke karatu a makarantar Baffa suka fara raguwa, don iyaye suna cire ƴaƴansu, wasa gaske duk ƙauyen mu ta ɗauki zancen ni mayya ce, wasu har gida suke zuwa su ci min mutunci, idan kuwa aka samu yaro yana ciwon da ba a gane kansa ba, sai a ɗauko a kawo min a ce ni na kama shi, har ma manyan, sai ya zamana duk wanda ya yi ciwo mai tsanani a ƙauyenmu to nice na kama shi, gashi wani iko na Ubangiji kuma a dai dai wannan lokacin ne annobar wata cuta ta shigo ƙauyen namu, wanda idan ka kamu da ita dai da wuya ka tsallake kwanaki uku, mace mace sai ya yi yawa, mutane kuma sai suka alakanta hakan da ni.

Nayi kuka mara adadi, baƙinciki da ƙuncin rayuwar da nake fuskanta a ƙauyenmu tayi yawa, ko ƙofar gida ban isa leƙowa ba. Abin ta kai har Mai Gari ya ƙirawo Baffa ya masa kashedi da barazanar korarsa da iyalinsa daga garinsa,rayuwa ta yi mana ƙunci a wannan gabar.

Yawan tunani da damuwar da nake ya sanya na rame nayi duhu, gabaɗaya na lalace kamar ba Shatun Hajjo ba, ga wani zazzabi da ciwon kai da ya sanya ni a gaba, bana ko iya cin abinci sai Hajjo ta matsa, tun tana mini faɗa har dai ta sauƙo ta shiga rarrashina da ban baki, shi kanshi Baffajo ba a barshi a baya ba, kullum faɗa da nasiha ya ke min, ga kewar mijina da ya addabi ruhina, ban tabbatar da irin son da nake wa Hassan ba sai a yanzu da ya nisanta kansa da ni. Lokaci lokaci yana zuwa amma sam Hajjo ta hana mu ko da haduwa ne.

Haule ƙawata, ƙawar arziƙi ce da bazan taɓa mancewa da ita ba, ita kaiai ce bata ƙyamaceni ba a wannan lokacin, kullum ko da yaushe tana tare da ni tana tausata, iyayenta sunyi yanda zasu yi su raba mu abin ya ci tura, har duka an mata da girmanta amma bata fasa zuwa wurina ba

Sannu a hankali nayi wata uku a gida, a wannan lokacin abun ya yi kamari, abunka da mutanen ƙauye da iya zuzuta abu, don har ta kai ga an daina bin Baffajo sallah, haka ya haƙura da limamci ya dawo mamu, sai ya zamana ba mai yarda ya haɗa sahu da shi. Haka nan ma Hajjo, bata isa ta shiga taron mata ba, a take za a dare a watse a barta, kowa tsoron mutanen gidanmu yake, mu kaɗai muka dawo muna rayuwa, sai almajirin Hajjo Musa da bai guje mu ba, sai kuma Haule.

Watarana haka na tashi da matsanaicin zazzaɓi, ga jiri, da ciwon kai, ko idanuna bana iya buɗewa, ga tashin zuciya komai na ci haka zan dawo dashi. Hankalin iyayen nawa ba ƙaramin tashi ya yi ba, ba shiri muka nufi asibiti. Gado aka bani bayan an yi mini wasu ƴan gwaje-gwaje, a nan aka gano cikin da nake da shi dan watanni huɗu. Ba kaɗan ba su Hajjo suka yi murna da farinciki da wannan ƙaruwa. Kwanana uku a asibiti kafin aka sallamoni muka dawo gida, kula na musanman Hajjo da Baffana ke ba ni.

Bayan dawowar mu da kwana biyu Baffajo ya tara mu yake faɗa mana dole za a sanar da Hassan maganar cikina, Hajjo ta haye ta dire ta ce sam ba za a faɗa ba, da ƙyar da suɗin goshi Baffa ya shawo kanta, tun da dai cikinnan yana da Uba, to kuwa dole a sanar musu, idan ma baida Uba to dole a sanar da waliyan uban.

GIDAN INNA.

Inna kam tun bayan tafiyar Shatu ta fara ganin anfaninta a gidan, aikin da ya kamata duk ita take yi, don Indo dai bata dawo ba, Huse ta riƙe ta, ita kuwa Mairo ba abun da ta iya sai son jiki da ƙazanta, sai dai duk da haka inna bata ji ko ɗar ba, ranta sawai ta rabu da alaƙaƙai a cewarta. Gefe kuma ga su Huse na ta ƙara zugata.

Zaune Inna take tana hutawa da yamma bayan ta kammala musu abincin dare, magana take wa Mairo tun ɗazu ta tashi ta share tsakar gidan ta ɗauraye musu ƴan kwanukansu, amma ko alamum zata tashi babu.

Hassan ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, ta amsa masa, ya zo ya zauna a kan tabarmar kafin ya ce, "Barka da gida Inna"

"Yawwa sannu Hassan, ya ya kasuwar, ince dai ko lafiya naga duk kayi wani iri"

"Ba komai Inna, bari na shiga na ɗan watsa ruwa."

"To shi kenan, idan ka watsa sai ka zo ka ci abinci ko"

"A'a Inna, bana ci, a ƙoshe nake."

Dubansa Inna tayi da kyau ta ce, "Yanzu Hassan ba za ka cire damuwar wannan mai gani har hanjin a ranka ba ko, ka bi ka tsagalgali kanka, abincin kirki ma baka ci, dubi yadda ka dawo fa, ƙashi da rai, duk ka lalace kayi duhu, anya kuwa Hassan?"

Hassan ya dubi Inna ya ce, "Inna kenan, damuwa kam ai yanzu na fara, Inna wallahi ina son Shatu."

Wani salati Inna ta sanya ta ce, " Ta tabbata dai wallahi yarinyar nan ta gama da kai, bayan maita ma harda yan tsubbace tsubbace?"

Hassan ya girgiza kai ya ce, "Wallahi Inna Shatu ba mayya ba ce, kuma ina mai tabbatar miki da koda ƙur'ani aka bani zan rantse a kan Shatu ba mayya ba ce, an dai samu wani akasi ne kawai."

Tsaki Inna ta ja ta ce, "Sai kayi kuma, ni dai ganau ce ba jiyau ba, saboda haka ba abin da zaka faɗa mini in yarda, tashi ka bani wuri, kuma ka tabbatar ka zo ka ci abinci, idan ba haka ba sai na ɓata maka rai. Sakarai."

Mikewa Hassan ya yi ya wuce ɗakinsu, yana nan yanda yake, kullum kuma sai ya gyara ya share kamar yanda Shatu take yi, haka zai zauna ya yi ta magana shi kaɗai kamar tana nan, wani lokacin kuma ya ci kukanshi ba mai rarrashinsa. Fita yayi daga ɗakin ya shiga bayi yayi wanka, yana fitowa ya je ya ɗauki abinci kamar yadda Inna ta ce, dawowa yayi ya ajiye, ya jima kafin ya fita lokacin ana ta ƙiraye ƙirayen sallar magariba, bashi ya dawo gidan ba sai dare.

A cikin watanni ukun da ƴan kai da suka shuɗe masa ba Shatu, rayuwa ta yi masa ƙunci, walwala tayi ƙaura daga kan fuskarsa, Yaya Salisu tare da amininsa Isa sunyi ƙoƙarin ganin ya kwantar da hankalinsa ko yaya ne, amma abin ya ci tura. Yaya Salisu ya je wurin Inna sau ba adadi a kan tayi haƙuri Shatu ta dawo ɗakinta, ko don halin da ɗan'uwansa yake ciki, amma sam Inna ta murje gashin bakinta ta ƙi, tun suna ɗaukan abun wasa har ta kai ga ya daina fita kasuwa, don ko ya je ma babu abin da yake taɓukawa, haka zai wuni ya dawo.

Ganin haka ya sa Yaya Salisu ya je ya samu Inna Zulai da maganar, ita ma da fari ta ƙi yarda, tace masa ai ba anfanin zama da maye, duk aminta da shaƙuwarku watarana zai cutar da kai.

Kallon Inna Zulai ɗin ya yi ya ce, "Wallahi Inna kar ki so ganin yadda Hassan ya dawo, ya rame ya lalace, ko aski baya yi, duk yayi wani iri, kuma ma ni Inna har yanzu ban ma yarda wai Shatu na maita ba, don da ta na yi da ta cinye kurwar waɗanda suka wulaƙantata."

"Hmmm kai dai kawai ka bar mutum a inda ka ganshi" cewar Inna Zulai.

Da ƙyar da suɗin goshi Yaya Salisu ya shawo kan Inna Zulai ta amince zata je tayi wa Inna magana.

A lokacin da ta je ne ta samu Inna tana ta sababi tana bala'in baza su yarda da wani ciki ba, su je can su nemi uban cikin, ko kuma su riƙe kayansu don ita dai ba za ta haɗa zuri'a da mayu ba.

Sai da Inna Zulai ta mata jan ido kafin aka samu tayi shiru ta shiga ɗaki. Sai dai duk faɗa da nasihar da Inna Zulai ta mata ba wanda ta ɗauka, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, waɗanda suka kawo labarin ma ba ƙaramar tijara ta zuba musu ba.

Shi kuwa Hassan yana can ɗakinsu daɗi da farinciki sun ziyarci rayuwarsa bayan lokaci mai tsayi, rabonsa da dariya tun ranarda Hajjo ta masa koran kare ta hana masa ganin Shatu, sai yau da wannan daddaɗan labari ya zo masa. Duk masifar da Inna take yi yana ciki yana ji, fitowa yaƙi yi.

Suna cikin haka, Inna bata daina ɗaga muryar tana bala'i daga can ɗakin ba suka jiyo sallama a tsakar gida, amsawa suka yi, tun kafin su fito suka tsinkayi muryar tsohon yana faɗin, "Waye ne ya laƙabawa jikata maita, wallahi maza ku fito da shi, don sai na nuna masa uban kuturu ma ya yi kaɗan, bare na makaho. Wihuhuuuuuu dawa dai mazaje........✍️