RUWA CIKIN COKALI

chapter 6

by @mamanafrah3028

***




*RUWA CIKIN COKALI* 
(Ya ishi mai hankali wanka)
 
                  
                NA


         MAMAN AFRAH

 
.        *Daga marubuciyar* 
  *Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu* 
      *****

           BOOK 1

         PAGE 6️⃣


             *SADIYA*

   Ranta ne ya mata ƙuna tana jin wani zafi da raɗaɗi a zuciyarta, ta fara tunanin shin mai Nasir yake nufi da ita ne? Ta yaya za a yi mace ki dawo gidanki ki haɗu da mijin ki amma ko kallo baki ishe shi ba bare ki sa ran zai miki magana ko ya yi wa ɗan da kika haifa masa.

   Kallon ƙaton kwaɗon da ya datse ƙofar ta yi a karo na biyu, tana jimami a zuciyarta ta ce

'Ya san ya sauyawa gidan mukulli amma bai bani ba to mene ne nufinsa? ' Ta faɗa a zuciyarta tana saka hannu ta riƙe kwaɗon tana tunanin yadda za a yi ta buɗe ta shiga gidan, tun da babu gidan wanda take shiga a umguwar bare yanzu gidan wa ma za ka je da tsakar ranar nan, to idan ka je ma ka ce mai?. Ɗan sakin kwaɗon ta yi ya bugu jikin ƙofar yana sakin wani ɗan ƙara, kanta ta jingina a jikin bangon ƙofar daga gefe tana jin ita daj bata dace sa miji ba a gefe ɗaya zuciyarta tana faɗa mata hatta mahaifin ma bata yi dace da shi ba.

   Ta jima a haka tana jin irin yadda gumi yake sartu a jikinta saboda zafin ranar da ake gabaɗaya ranar a buɗe take. Motsin da Kalifa ya yi ne ya dawo da ita daga duniyar saƙa da warwarar da take yi a zuciyarta. Ɗagowa ta yi tana ƙarewa layin nasu kallo babu kowa sai mutane da suke ficewa jefi-jefi idanu ta mayar hanyar da ta biyu ko za ta hango mashin ɗin da Nasir suka wuce amma ko alamarsa, ta daɗe a tsaye ko za ta ga ya dawo amma shiru tamkar  maye ya ci shirwa!.

  Zafin rana ga goyo shi kansa Kalifa so yake ta sakko shi, ganin abin ba na ƙare ba ne, don a ƙalla ta yi kusan minti talatin a wajen a tsaye amma babu alamar Nasir zai kawo mukullin.  A hankali ta sakko daga matakalar gaban gidan tana jan ƙafa ga yunwa ga baƙin ciki da takaicin ɗa namiji da yake ƙunsa mata, ga rashin adalcin da iyayenta suke mata, na rashin jin damuwarta da kuma magance mata ita.

    Gidan da yake kallon gidan ta, nan ta hangi inuwa da ɗan dakali a wajen, haka ta cira ƙafafu tamkar iska za ta ɗauke ta, suna zuwa inuwar ta zauna har lokacin bata sauke Kalifa daga bayanta ba. Bayan ta zauna sai ta kifa kanta a gwiwarta tana jin babu daɗi ganin duk wanda zai wuce sai ya kalle ta, har ta fara zargin ko daj sun zata mahaukaciya ce. Maganar Kalifa ta katse mata tunani jin ya ce

"Mom a sakko ni" Ya faɗa cikin maganrsa ta gwaranci da bata fiye fitowa raɗau ba, hannu ta kai ta sakko shi, sai lokacin ta lura da hannunsa da ba a wanke masa ba lokacin da ya ci tuwo. Tana sakko shi ya fara ɗaga hannu yana nuna hanyar da suka baro yana faɗin

",Abba" Wani iri ta ji a zuciyarta don wannan maganar da ya yi hakan yana nuni da cewa ya ga mahaifinsa lokacin da suka wuce, baki ta buɗe cikin sanyin murya ta ce

"Abbanka yana zuwa ya ke siyo maka alewa ne, kana son shan alewa?" Kai kawai ya gyara mata.

  Zuwa can tana zaune Kalifa a cinyarta jakarta ƙarama a gefenta a ajiye, ganin yara suna wucewa da uniform a jikinsu ta tabbatar yanzu ƙarfe uku ta yi.

  Wani yaro ɗan maƙotanta daga can gefe ya fito sanye da unifort riga pink me ɗigo-ɗigo yayin da wandon yake purple, tun da ya hange ta yake dariya har ya ƙaraso ya ce

",Auty Sadiya" Ya faɗa yana cike da fara'a amsa masa ta yi ya shiga gaishe ta sai kuma ya ce

"Aunty ya kike zaune a waje?" Ya tambaya yana kallon ta da yake da ɗan wayonsa don zai yi shekara tara zuwa goma, rasa ma mai za ta ce masa ta yi duk ta ɗan diririce sai kuma can dabara ta faɗo mata sai ta ce


"Tare da Abban Kalifa muke to mukullin ne ya faɗi shi ne ya koma ya dubo?" Ta samu kanta da sharara masa ƙarya. Dariya ya yi bai ce komai ba don shi ko kaɗan ba ya son wannan mutumin bashi da kyawun hali ya yi ta korarsu idan suka je gidansa. Wasa ya yi wa Kalifa ya fito da alewa a jakar makarantarsa ya bashi yana ɗaga masa hannu yana masa bye-bye shi ma Kalifan bye-bye ya masa. 

    Alewar ya miƙa mata ta karɓa ta ɓare masa ya fara sha, shiru babu amo ba labarin Nasir har aka fara kiran la'asar abin ya ɗaure mata kai don ta san ko ma ina zai je ya ci a ce ya dawo tun da dai ta san ba kasuwa ya tafi ba tun da gashi nan da kasuwa zai je da wuri zai fita. Abin ya fara bata tsoro tana zaune babu sallar azahar babu ta la'asar gashi tana tsoron shiga gidajen maƙota cibi ya zama ƙari don matsawar ta shiga ya zo ya ganta tabbas akwai gagarumar matsala. Kalifa sauka ya yi daga cinyarta saboda ya gaji da zaman waje ɗaya, ya shiga kewaya wajen, yana ɗan wasa.

  Ta buga uban tagumi ta yi nisa cikin tunanin lamuran gidan aurenta, tana tuna irin wulaƙanci da tozarcin da Nasir yake mata, ƙaran wani birki da mai mashin ya ja shi ne ya dawo da ita hayyacinsa, a kiɗime ta tashi ta je gaban mashin ɗin da ta hangi Kalifa kwance a wajen, mai mashin ɗin wanda yake ɗauke da ƴan makarantar islamiya da ya ɗakko, kanta a take ya shiga juyawa ta yi kan Kalifan da gudu ƙirjinta yana bugu tamkar zuciyarta za ta fasa ƙirjin ta fito tana faɗin

 "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"


                *JIDDA* 


    Idanunta cike da hawaye ya cigaba da magana don don duk abin da take faɗa iya gaskiyarta take faɗa komai daga ƙasan zuciyarta yake ta ci gaba da faɗin

  "Ni ba damuwata rashin mijin ba damuwata ɗaya yadda Umma za ta takura min idan aka yi auren Aliya ba a haɗa da nawa ba, kuma kin ga Abba ba zaman gidan yake ba, sai na gwammace kiɗa da karatu in ma bata kore ni ba, don ba gori ba har goriba sai ta min a kan rashin auren"

   Shiru Salama ta yi tana nazari da tunanin maganganun ƙawar tata a lokaci guda tausayin Jidda yana mamaye mata zuciya da ruhi.

   Ibrahim wanda ya cika da zufa tun furucin Jidda na farko wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwa, kuma shi har ga Allah a yadda yake jin Jidda ta gama bin jijiyoyin da jinin jikinsa ba zai iya rayuwa ba sai dai ita sai dai furucin ta ya nuna masa da sauran rina a kaba, domin kuwa da wuya wai gurguwa da auren ne, shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa tana tuno masa haɗe da dawo masa da tunanin abin da ta furta wanda shi ne ya saka shi a ɗimuwar da yake ganin dab yake da ya rasa Jidda wanda hakan kuma babban ƙalubale ne a rayuwarsa.

'Salama damuwar yawancin ƴanmtan yanzu shi ne auren namiji mai kuɗi kuma kyakyawa, yawancin kowacce burinta ne wannan, ni kuma inda muka sha bamban da saura kenan tunanina burina haɗe da ƙudurina basa kan namiji kyakkyawa kuma ba wai don hakan ya haɗa nasaba da munin da nake da shi ba, uwa uba dukiya basa gabana don ni a ra'ayina in auri talaka kuma mummuna in da zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta yadda kyawunsa ba zai ruɗi ruɗaɗɗun ƴanmata ba, sannan dukiyarsa ma ba za ta tsone musu idanu ba, kin ga burin Aliya ne wannan ni kuma bani da ra,ayi a kan hakan, amma zan ci gaba da addu'a Allah ya bani miji na gari daidai ni' Wannan su ne furucin da ya hargitsa tunanin Ibrahim da sauri ya saita madubin motarsa ƙan ƙarami na ciki wanda yake maƙale fuskarsa ya kalla a ciki, ganin irin kyawun da Allah ya yi masa sai da ya ƙara jin gabansa ya faɗi tamkar dai a yau ne ya taɓa ganin kyawun fuskarsa.

   Zuwa yanzu duk ba ya fahimtar maganganun da suke tattunawa, hankalinsa ya yi bala'in tashi yana ta tunanin ya zai yi ya mallaki Jidda, tun da gashi ba ya ma cikin mazan da take da burin aurr, na farko dai shi yana da kuɗi sannan uwa uba Allah ya hore masa kyau shi kyakkyawa ne ajin ƙarshe, zai iya tabbatarwa ya cika dukkan abin da ta lissafa zai samar mata na kwanciyar hankali a gidan aure sai dai kash! Bai sani ba ko za ta karɓe shi a matsayin kyakkyawa kuma mai kuɗi don ya tabbata shi dai sai dai a saka shi cikin masu kuɗi pan ajin farko ba ma ajin ƙarshe ba.

   A fili ya furta

"Ya zan yi?" Ya jefawa kansa tambayar  da bashi da amsar ta bare kuma mafita. Yana cikin wannan tunanin kamar an ce ya ɗago sai ya ga wayam babu kowa a jikin motar, dama ya ji ba ya jin maganarsu kasancewar a ruɗe yake bai yi tunanin dajna jin muryarsu da ya yi ba. Idanu ya hanga sai kuwa ya ga Jiddan za ta shige gida ta juyo tana yin bye-bye kasancewar ita yake kallo sai ya ga tamkar shi take ɗagowa hannun bai san lokacin da ya ɗaga nasa hannun ba yana mata bye-bye tamkar wani soko. Ganin ta shige gidan ya dawo hayyacinsa sai a lokacin ya yi tunanin ashe ma bata ganinsa kasancewar baƙin gilashin motar, sannan ma shi da ba saninsa ta yi ba shi kaɗai ne ya san ta ya san matsayinta a zuciyarsa. Can da ya hanga sai ya ga ashe Salama ƙawarta ta ɗagawa hannun, huci ya busar mai zafi daga bakinsa ya ɗan kwantar da kujerar tare da mayar da bayansa ya kwanta ya rufe idanunsa kawai ita yake hangowa lokacin da take yi wa ƙawarta bayani, yadda take bayani cike da damuwa shi ne abin da ya fi tsaya masa a rai.

   Idanun ya runtse da ƙarfi a fili ya furta

  "Jiddaaaa" Yana mai jan harafin ƙarshe na sunan nata, ya jima a haka har sai da aka fara kiran sallar magriba ya tashi tare da gyara kujerar ya mayar da ita daidai ya mayar da hannunsa kan mukullin motar ya kunna tare da fara ƙoƙarin janta duk da yana jin tamkar jijiyoyin jikinsa sun daina aiki, kamar dai ba zai iya jan motar ba, yana ƙoƙarin yin kwana, sai ya ga  wani mai mashin da yake ɗauke da wani mutumi ya tsaya a take mutumin ya sauka yana sanya hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙawa mai mashin ɗin, yana bashi ya juya ya fara tafiya mai mashin ɗin yake miƙa masa canji amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya bar shi, haka ya shiga magana shi dai Ibrahim kasancewar ba a kusa yake ba bai ma san mai yake cewa ba sai dai ya san godiya yake masa.

   Mai mashin ya ja mashin ɗinsa ya yi gaba, a inda Ibrahim ya bi bayan Abba da kallo har ya shige cikin gidan da ya ga Jidda ta shiga.

  Sosai ya yaba da yanayin dattijon kuma daga gani ya san tabbas yana da dattako da tsayuwa a kan iyali.

  A zuciyarsa ya ce

'Wannan ne mahaifin Jidda kenan?'Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma yana ta tunanin wace ce Ummar da ya ji Jidda ta ambata tana maganar za ta mata gorin aure, in dai kuwa haka ne to tabbas ba mahaifiyar Jidda ce a gidan ba, ko dai mahaifiyarta ta mutu ko kuma bata gidan sun rabu da mahaifin ta, a take ya ji wani tausayinta haɗe da zazzafan son ta ya ƙara dirar masa, sosai yake jin son ta a jiki da ɓargonsa ya yadda yake jin tozalin da idanunsa suka yi da ita yau sai ta ƙara fasa masa wani sabon son don tamkar ta motsa masa mikin da yake cikin zuciyarsa ne.


   Haka ya baro unguwar ransa duk babu daɗi, gashi babu biyan buƙata sannan kuma ya yi wani mugun jin da zai hana zuciya da ruhinsa sakat. A daidai wani masallaci ya yi parking daga can gefe fitowa ya yi alwala ya yi ya bi jam'i sai da ya idar sannan ya shiga mota ya ƙarasa gida ransa duk wani iri, tabbas ya faɗa tarkon so son ma na wacce bata san yana yj ba, son da zai ringa saka shi fargaba tun da bashi da tabbacin mallakar wacce yake yi wa so ɗin.

   Yana shawo kwanar gidansu ya figi motar da mugun ƙarfi, don yanzu hatta motar ma haushin ta yake ji, a yau ne ya ji ya tsani kuɗi da kuma kyawun da yake da shi, yana ta tunanin cewa da shi mummuna ne kuma talaka babu abin da zai hana shi tunkarar Jidda a yau. Sai dai ta wani ɓangaren ya ji daɗin jin furucin ta ko ba komai zai yi amfani da damarsa wajen kaɓa zuciyarta sai dai ya san abin da zai yi.

   Horn yake da ƙarfi mai gadi da yake sallah bai zo ya buɗe ba, shi kuma bai fasa doka horn ɗin ba. Ya jima yana yi duk da ya san mai gadi ba zai ƙi buɗe ƙofa da gamgan ba, mai gadi ko da ya yi sallama daga sallah sai da ya karanta gabaɗaya azkar ɗin da ake yi bayan idar da sallah, sanna ya taso a nutse ya wangale ƙofar, ya ja baya Ibrahim ya shigo da motar da gudu yana yin wani parking a tsakiyar wajen. Fitowa ya yi daga motar mai gadi duk sai ya sha jinin jikinsa ya ɗauka ko shi ne ya ɓatawa Ibrahim ɗin rai da bai buɗe ƙofa da wuri ba, da sauri ya ƙarasa yana mai cewa.

"Afwan yallaɓai ina sallah ne" Hannu kawai ya ɗagawa mai gadin ya shige cikin gidan, bai bi ta kan part ɗin Mummy ba direct part ɗinsa ya nufa yana ta sauri shi kanshi bai san dalilin saurin nashi ba. 

  Yana shiga bai tsaya a falo ba ya shige bedroom wayoyinsa ya ɗora a kan madubi ya cire hula da rigar jikinsa ya cilla kan gado agogon hannunsa ya cire ya ajiyee yana hango shi a madubi sanye yake da farar singlet fara tass tamkar takarda sai wandon yadin da ya cire rigar, hasken fatarsa da kwantaccen gashin sa tamkar ba'indiye shi ya sa ya ji zuciyarsa ta tsinke saboda tunowa cewa masoyiyarsa bata son kyakkyawan namiji.

  Kan gadon ya koma yana ture hula da rigar da ya cire gefe don ba al'adarsa ce jefar da kayansa a kan gado ba shi mutumin ne mai tsafta. Amma yau yanayin da ya shiga ya sa yana abu wanda ba halayyarsa ba. Tashi ya yi ya kunna AC haɗe da ƙure mata gudu a take sanyi ya haɗe ɗakin duk a nufinsa ya samu sassaucin zafin zuciyarsa da yake azalzalarsa na rashin wacce yake so. Ya koma ya zauna wayarsa ta fara ƙara amma bai tashi daga zaunen ba, har kiran ya tsinke, wani ya shigo sai a karo na uku sannan ya tashi ya ɗakko wayar ganin suna Mummy ɓaro-ɓaro ya yi saurin ɗagawa tana tambayarsa rashin shigowarsa ɓangarenta ya sanar da ita wanka yake son yi sai lokacin ta ji ɗan dama a ranta don ta san da wuya Ibrahim ya shigo gida bai fara shiga part ɗinta ya ganta  ba. Suna gama wayar kiran Abeed ya shigo ɗagawa ya yi suka yi magana ya ajiye ya koma ya kwanta reran a kan gadon idanunsa a rufe yana ta nemawa kansa mafita.

  Zuwa can ya tashi zaune kamar an tsikare shi da sauri ya ɗakko wayarsa, sunan direbansa ya kamo hannunsa har rawa yake don yana ganin wannn hanyar ce zai bi ya samu mallakar Jidda don zai yi duk yadda zai yi ya samu soyayyarta ya kuɓuto ta daga gorin da ya ji tana furtawa da bakinta cewa za a yi mata idan bata samu miji mai auren ta ba. Bugu ɗaya biyu direba ya ɗaya ya ce

"Barka da dare yallaɓai" Ya faɗa cike da girmamawa. Amma maimakon Ibrahim ɗon ya amsa sai ya ce

"Ina za a samu kayan gwanjo?" Tambayar ta zo masa a ba za ta amma sanin kyauta irin ta yallaɓai ɗin sai ya yi tunanin ko kyauta zai yi da su, duk da ya san kaya sabbi dal yake bayarwa.
 
  "Za a samu wane iri?" Ya faɗa yana jiran jin amsar sa

  "Daidai ni?" Maganar ta zo masa a bazata amma sai ya ce

"Ana samu yallaɓai akwai wani abokina maƙocinmu ne ma yana buɗe dila ta kaya kuma masu kyau kamar sabbi... Kafin ya gama magana Ibrahim ya ce

"Bana son wanda suke kamar sabbi na fi son tsoffi wanda suka ji joki idan son samu ne ma wanda suka fara gashi" Shiru direban ya yi sai kuma ya ce

"To yallaɓai sai dai a karɓo ƙarshen dila irin wanda aka gama zaɓewa aka bari su ne wanda ake karyar da farashin su saboda tsufansu"

  Ibrahim ya ce

"Yawwa su zan saka maka kuɗi a account yanzu ka je ka samo min su" Amsa masa ya yi da 

"To" Ƙit ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya.

   Haka direbansa ya kawo masa kayan cikin wata bakko don kuɗin da ya tura masa ko rabi ba a ɗauka ba, part ɗinsa ya kai masa ya bashi umarnin tafiya tare da crwa ya riƙe sauran kuɗin. Direban yana fita ya buɗe kayan da sauri yana fito da su, sosai sun ji jiki ba ma wannan ba warin da kayan suke irin na gwanjo su ne suka sa ya kusa yin amai, waya ya ɗaga ya kira mai wanki ya bashi kayan ya ce a wanke amma kar a goge, don a ransa ya san ba zai iya saka su babu wanki ba, don ba don Jidda ba babu mai saka shi saka gwanjo.

   Yana ɗaukan kayan shi kuma ya fito ya nufi part ɗin Mummy don lokacin har ya yi wanka ya saka wani kayan sun je masallacin isha'i da Daddy, a falon ya same su yana shigowa cike da kulawa suka tashi suka nufo shi, kowa ya rungumi gefen ɗaya daga jikin Ibrahim ɗin suna matuƙar son ɗan nasu. A haka suka ƙarasa saman dining ɗin in da Mummy da Daddy suka kama shi cike da kulawa suka zaunar da shi a kujera, Mummy tana dariya cike da wasa ta ce

"Haba Daddyn Mu'azzam ya kake neman kayar min da ɗa bai gama zama ba fa ka janye hannunka" ,Ta faɗa tana kallon Ibrahim da yake ta murmushi kyawawan haƙoransa a waje. Daddy ma cike da wasa ya ce

"Wai kina nufin kin fini son shi ne?"

  Mummy ta ce

"Eh mana"
  
  Daddy ya ce

"To bari mu ji daga bakin Ibrahim ɗin, Mu'azzam tsakanin ni da Mummynka wa ya fi son ka kuma wa ka fi so?" Ya faɗa yana daga tsaye har da kama tsantsa shi ala dole yana jiran ya ji mai za a ce kar a je ba a zaɓe shi ba.

  Mummy kuma ta kasa tsayar da dariyar da take marar sauti, shi kuma Ibrahim yana ta kallonsu ɗaya bayan ɗaya yana tunanin ta inda zai ɓullowa wannan diramar tasu.

  Mummy ta ce

"Kai muke jira"

  Ibrahim ya ce

"Duk kuna sona na sani, ni kuma na fi son...

  Kowa ya yi saranda yana jiran kar a zaɓi ɗan uwansa ba zaɓe shi ba, kowa ya san idan ba a zaɓe shi ba za a masa dariya. Kamar daga sama suka ji Ibrahim ya ce

"Ni kuma ina ƙaunarku ku duka" Gabaɗaya sai aka kaure da dariya Mummy da Daddy suka nemi kujerarsu suka zauna, Mummy ta zubawa kowa abincin suka shiga ci cike da annashuwa.

  Bayan sun kammala suka koma tsakoyar falon suna tattaunawa, a nan mai aiki ta shigo ta kwashe kwanukan ta tsafta ce dining ɗin.


       Ibrahim ne ya musu sallama ya ce zai je ya kwanta, kasancewar dai yaƙe yake musu don kar su fahimci yana cikin damuwa, yana zuwa part ɗinsa ya shiga ya kulle, bai watsa ruwa ba kasancewar bai daɗe da yin wanka ba, jallabiyar jikinsa ya cire ya saka sleeping dress masu laushi ya kwanta tare da yin addu'a. Bayan ya shafa addu'ar ya shiga tunanin mafitar da yake a kan lamarin Jidda don a gobe ba sai jibi ba ya yi wa kansa alƙwarin sai ya je mata da kalmar so kuma son na aure!.

   Tunanin wani abu ne ya faɗo masa hakan ya sa ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran Abeed abokinsa bayan ya ɗauka yana ta masa surutu Ibrahim ya ce

"Dalla malam ka tsaya na faɗa maka abin da ya kawo ni, ka tsaya kana ta zuba kamar lalataccen famfo"

  Abeed ya ce

"To dama ai kamar jiran kiranka nake ka san maganata ni da kai bata ƙarewa" Banza ya masa akan abin da ya faɗa don ya san kawai surutu ne zai cika shi da shi kp ya ringa bashi labarin ball ɗin da aka ci shi kuma yanzu ba wannan ne a gabansa ba, don ba ya so ma ya faɗawa Abeed ƙudurinsa gudun ya masa dariya ko ma ya ce sai ya bishi wajen Jiddar.

  Cike da ƙosawa da kalaman Abeed Ibrahim ya ce

"Ni tambayarka zan yi ko ka san wani mai wanda mutum zai shafa ya yi baƙi kuma ya yi muni?" Ya faɗa hankalinsa kwance don shi ya shiryawa faɗawa komai a kan Jidda.

  Abeed  jin babu alamar wasa a furucin da abokin nasa ya yi sai ya ce

"Man da za a shafa a yi baƙi da muni ko dai mai da za a shafa a yi fari da kyau?" Shi ma ya tambaya babu alamar wasa a maganarsa kamar yadda Ibrahim ɗin ya yi.

   Shiru Ibrahim ya yi yana ɗan nazarin kamar ba zai ce komai ba har sai da maganar Abeed ta katse masa tunani jin ya ce

"Magana nake maka ka ƙyaleni?" Wani yawu ya haɗiye yana fatan dai ba cewa zai yi ba a samun man ba ya ce

"A,a kamar yadda na faɗa maka mai wanda zai saka baƙi da muni, ka san dai ai ni dai in ba zabiya zan komai ba mai zan yi da fari, kyau kuma ni da indiyawa da larabawa ko za a samu bambanci bainwuce a ce ni bahaushe ba ne su kuma larabawa da indiyawa, to mai zan yi da kyau?"

  Abeed ya ce

"Wai kana nufin kai ne kake neman wannan man da ka ambata mai za ka yi da shi?"

  Maimakon ya amsawa Abeed tambayarsa sai ya ce

"Tambaya za ka min ko amsa min tawa tambayar za ka yi" Ya faɗa yana jin tamkar ya janyo shi daga wayar ya yi ta bugu har sai ya huce.

 Abeed baki ya taɓe kamar Ibrahim ɗin yana ganinsa ya ce

"Kai malam ni ban san inda ake siyar da wannan man ba, to wai kai mai ya sa ma za ka shafa wannan man? Wane mai bada gurguwar shawarar ne ya baka shawarar nan, bayan kana da kyau wanda ƴanmata suke maka caaaa... Wani takaici ne ya cika Ibrahim jin abin da Abeed ya faɗa shi kuma a halinnda yake ciki yanzu gani yake ko wata mace aka alaƙanta shi da ita tamkar an ci amanar Jidda ne, wayar ya sauke daga kunne ya datse kiran haɗe da yin cilli da ita can gefe ya kwanta tare da juyawa wayar baya. Abeed kuwa dama ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, dama ya san hakan zai ta faru don ya san Ibrahim ya tsani maimaita tamabaya.

  Washe gari ko da ya tashi bayan ya yi shirin fita office, don yau shi kaɗai zai tafi kamfanin don Abba ya ce zai zauna ne ya yi wasu rubuce -rubuce a kan kayan da za a shigo da su daga waje na kasuwancinsa wanda duk manyan kasuwanni da shaguna yawanci wajensa suke sarar kayan. Yau ba kamfanin wajen gidan su Jidda zai je ba, ɗaya kamfanin yin shinkafa zai je, duk ransa ba daɗi don a ganinsa idan ya doshi hanyar wajen gidan su Jidda ma ai daɗi zai jia ransa. Bayan sun kammala break fast ya  fito riƙe da jakar wajen aikinsa da wayoyinsa, suna tsaye da Mummy tana jero masa addu'a mai wankin da ya ba wankin gwanjo jiya ya zo yana mai cewa

"Barka da safiya Hajiya" Ya gaishe da Mummy cike da girmamawa, bayan ta amsa ya juya ya ce

  "Barka da safiya yallaɓai" Ibrahim ya ce

"Alhamdulillah, mu je in buɗe maka part ɗin nawa ka saka min kayan, ya faɗa gudun kar ya bashi mukullin idan ya tafi kafin ya dawo Mummy ta tambaye shi kayan mene ne bakko guda a cike. 

  Bayan ya saka masa ya dawo ya mata sallama, kamar ya sani kuwa sai da ta tambaye shi kayan mene ne don Mummy tana da sanya ido a kan lamurinsa, duk da ya mallaki hankalin kansa amma tana lura da al'amuran da suka shafe sa.


        Sanar da ita yanyi cewa wasu kaya ne da ya saya,  yana mata sallama direbansa  ya buɗe masa mota bayan ya shiga ma'aikatan gidan wanda suke wajen suna ta kawo gaisuwa cike da bashi girma yana amsawa, rufe masa ƙofat aka yi direban ya shiga ya tada motar mai gadi ya buɗe suka fita ya mayar ya rufe yana musu fatan alkairi, ɗago masa hannu Ibrahim ya yi da yake yau motar da ya fita da ita mai farin glass ce ana gani.


    Kamar jiya ma yau ya shirya wajen ƙarfe biyar na yamma, bayan ya fito wanka bai shafa mai ko turare ba kawai wannan kayan ya ɗakko ya saka kala ɗaya riga da wando baƙaƙe, ya kalle shi a madubi, duk da tsuffin kaya ne kasancewarsu baƙaƙe sai suka ƙara haska fatarsa hakan ya sa ya ji gabansa ya faɗi don tamkar ma kyau aka ƙara masa, da sauri ya cire ya ɗauki wata jar riga wacce daga gwiwar hannun ma ta ɗan fashe, ya saka baƙin wando, duk da a cukwuikuye suke amma dai ya ga sun masa kyau. Kai ya dafe ya koma bakim gado ya zauna yana tunanin ko dai baƙin mai ko na gawayi zai samu ya dishi farin fatarsa amma sai ya yi tunanin zai koma kamar dodo kuma ba ya so ma Jiddar ta ɗauka ko mahaukaci ne ta ƙu kula shi. Wayar da ya sa direba ya siyo masa tsohuwa key pad ita ya saka sim ɗinsa guda biyu ya ajiye nasa wayoyin masu tsada a kan madubin, dakyar ya samu takalmi yana fatan kar ta gane takalmin me tsada ne, wata hular sanyi ya ɗauka duk da zafin da ake ya saka amma sai ya ga ta yi kyau, ya ajiye ya ɗauko hularsa da yake sakawa da yadi, ya ɓata karin jikin hular ya saka ya danna a kan ta rufe wannan lallausan gashin kan nasa, sannan ya fito da kunnuwan waje sai ya zama gashi nan dai kamar wani wanda ba wayayye ba amma dai in mutum yana da hankali to yana kallon fatarsa kaɗai zai gane ɗan hutu ne bai saba da wahala ba.


    Fitowa ya yi kasancewar Mummy yau ta fita gidana biki, bai san bikin waye ba amma ta ce masa ta tafi gidana biki, Daddy ma ya fita shi da wasu abokansa da suka zo wajensa.

  Part ɗinsa ya rufo ya fito ya saka mukullin a aljihu yana gama sakawa ya ga mukullin ya faɗo sai a lokacin ya lura, ashe ajjihun a yage yake, a ɗayan ya saka sai ya ga babu yaga.

  Tun da ya fito yake addu'ar Allah ya sa kar ya haɗu da wani daga ma'aikatan gidan, cikin ikon Allah har ya je bakin get bai haɗu da kowa ba, dama ko wajen ajiye motoci bai kalla ba kasancewar yau ba a ma managar mota. A hankali ya kama ƙaramar ƙofar ya buɗe amma sai da ƙofar ta yi ƙara ƙiiƙiii mai gadi da yake banɗakinsa ya ji ƙaran taɓa ƙofa dama yana shirin fitowa ne, hakan ya sa ya ƙara ƙaimi wajen sauri ya fito yana cewa

"Waye?" Lokacin har Ibrahim ya fita ya rufo ƙofar, yana fitowa ya fara sauri don ya san dole sai mai gadi ya leƙo, kuma baya son kowa ya ganshi, mai gadi kuwa da sauri ya ajiye butar hannunsa, ɗan taku ɗaya biyu ya yi yana leƙo hanyar cikin gidan ko zai ga wanda ya shiga amma bai hango kowa ba.

  Da ɗan sassarfa ya nufi get ɗin ya buɗe ƙaramar ƙofa domin leƙawa ya ga ko fita aka yi tun da ba shigowa aka yi ba, Ibrahim da yake ta sauri don ganin ya bar layin nasu jin an buɗe ƙofar don ƙaran ta ziyarci kunnuwansa, da sauri ya raɓe daba jikin wata katangar wani gida yana leƙo mai gadin har ya gama kalle-kallensa ya koma ya rufo ƙofar, Ibrahim ya fito daga maɓoyarsa ya cigaba da tafiya yana fatan Allah bashi nasara a kan abin da zai je nema, yana fatan ya samu Jidda ta amince masa don ko a gobe in ta amince ya yarda a ɗaura musu aure!.

  Tafiyar tashi bata je ko ina ba ya ji ya gaji kasancewar bai saba da wahala ba, napep ya tare ya shiga tare da faɗa masa inda zai kai shi, sai da suka kusa zuwa inda za a gangara ya ce mai napep ya samu wuri ya sauke shi, haka ya fito tare karɓar account no mai napep ya masa transper na kuɗinsa har da ƙari, mai napep sai godiya yake kamar ya ari baki, amma zuciyarsa cike da tambayoyi da wasi-wasi don ya tabbtar wannan ba ƙaramin mutum ba ne duba da yanayin maganarsa irim ta wayayye kuma mai ilimi, sanna kana kallonsa ka ga wanda yake zaune a hutu ba a wahala ba, sai dai yanayin kayan jikinsa ya sa kana iya jiyo warin abin gwanjo daga jikinsa.


   Shi dai bai ƙara bi takansa ba ya fara tafiya yana ta addu'ar dacewa, dacewar kuma ba ta komai ba sai ta sa'ar ganin Jidda tare da fallasa mata asirin zuciyarsa da fatan ta amince da shi....

   
   *Akwai abaya gwanjo masu kyau da imganci akwai dila, akwai rabin dila, akwai kwatar dila akwai sayen ɗaya* 

  *Sannan akwai zannuwan gado, labulaye, abaya mayafai* *kayan yara takalma lesuna atamfofi shaddodi hijabai amma su sabbi ne da sauransu* 

   *Sannan akwai magungunan mata, kama daga daka mai kyau da matsi ba wanda ake sanyawa ba wanda ake tafasawa a shiga, akwai maganin gyaran breast ga matan da nononsu ya zube ko ya yaƙune da wanda suke yi yaye da masu shirin yaye, akwai tsumi domin dawo da darajar ki wajen miji, akwai kuma sanyi wanda shi maganinsa dole ne don idan kina da sanyi ko kinnsha magani ba za ki ga kyansa ba.* 

   *Akwai mayuka na gyaran fata, kama daga wanda zai saka fari da wanda baya saka fari wanda shi iya fata zai gyara ya saki yi glowing, akwai shower gel, da sabulai da dai sauransu*

   *Mai buƙata ta min magana ga no ta nan a ƙasa* 

      MAMAN AFRAH
      ***