24
by @oumfatima33
*💓MATAR MANYA💓*
*By*
*OUM FATIMA*
*GAJEREN LABARI*
*PAGE 24*
*BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM*
"Assalamu alaikum." Kairiyya ta faɗa daga can ɓangaren lokacin data ɗauki wayar.
"Bestie!". Na kira sunanta muryata na bayyana halin da nake ciki.
"Bestie kina lafiya kuwa? Meya faru kuma?." Tayi min tambayoyin duka a lokaci ɗaya cikin damuwa. Zayyane mata duk abinda ke faruwa nayi a ƙarshe nace "Ya kike ganin zan iya aiki a ƙarƙashinsa bayan duk abinda ya faru a tsakaninmu".
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Kin bani tsoro Bestie, nayi tunanin wani mummunan abu ne ya same ki ko yara." Kairiyya ta ƙare maganar cikin samun natsuwar jin cewar ba wani mummunan abu bane ya samu aminiyar tata ba
"Kawai ina cikin damuwa ne Bestie amma ba abinda ya same mu."
"Na fahimta, amma ki sani cewa wannan wata damace kika samu wacce kika daɗe kina burin samunta, kada ki bari wani personal issue ya hanaki cika burinki na taimakon Iyayenki, abinda zakiyi kawai shine ki kama kanki kiyi abinda ya kaiki ba ruwanki da shishi-shigi ko nuna cewa wata alaƙa ta taɓa shiga tsakinku dashi tunda shima bai nuna hakan ba, idan kikayi haka shike nan kin ja mutuncinki zakiyi aikin ki cikin kwanciyar hankali domin gina rayuwarki ta gaba daya iyalanki." Kairiyya ta ƙare maganar cikin bata ƙwarin gwiwa.
"Na gode sosai Bestie zanyi hakan in sha Allah." Na faɗa mata ina jin ƙwarin gwiwar yin amfani da shawar da suka bani.
******* Washe cike da ƙwarin gwiwa na tashi tun da safe nayi duk abinda na san inayi sannan nayi wanka na shirya tsaf cikin doguwar rigar leshi ɗinkin T bubu, dai-daita ɗaurina nayi na soke ya zauna ɗas tamkar ɗauka akayi aka ɗora shi.
A gur-guje mukayi breakfay Abba ya wuce damu ya sauke yara a makaranta nima ya ajeni wurin aikin sannan shima ya wuce nasa wurin aikin.
Ofishin marketing manager na fara zuwa shine yayi min jagora har Office ɗin da zan yi aiki a cikinsa wanda bani kaɗai bace mu biyar ne Maza uku Mace ɗaya ni cikon ta biyun.
Gabatar dani yayi a garesu a matsayin sabuwar ma'aikaciyarsu da zamuyi aiki tare, suma gabatar da kansu sukayi a gareni sannan aka nuna min sit ɗina da zan maye gurbin kaishi da Allah yayi mata rasuwa sannan aka gabatar min da fayil fayil na ayyukan da zan fara. Zama nayi da Bismillah bakina ɗauke da addu'ar neman taimako a wurin Allah na fara dubawa ɗaya bayan ɗaya.
Ranar haka na yini aiki na ba wasa don so nake na dai-daita abubuwa, Sallah kawai naje masallaci nayi ko ta kan abinci da abokiyar aikina mai suna Raihana tayi min tayin zuwa ban bita ba nayi mata godiya na koma Office naci gaba da aikina.
Koda lokacin tashi yayi nice ƙarshen fita saboda sai da na tsaya na tattare wasu takardun ina son ƙarasa su a gida. A ƙafa na riƙa takawa har na fita daga Companyn gaba ɗaya na tsaya don neman abin hawa saboda nace Abba ba sai ya dawo ɗaukata ba ba zan dawo da kaina.
Dai-dai lokacin da nake ƙoƙarin tsayar da adai-daita sahu motarsa ta fito daga Companyn, yana hakimce a baya direbansa na tuƙashi shi kuma yana duba wani aiki a cikin laptop ɗinsa. Kamar ance ya ɗago kansa sai kwai idanuna a cikin nasa, sarƙe idanunsa yayi a nawa yana min wani irin kallon da sai da nayi da ƙyar na fisge idanuna na faɗa adai-daita sahun ina ce masa "muje."
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki lokacin da mai adai-daitar yaja suka bar wurin, yau tunda safe da yazo yake zuba idon ganinta amma ko mai kama da ita bai gani ba. Har ya fara tunanin ko dai bata zoba ta fasa amsar aikin, sai kuma ya ganta dai-dai lokacin daya fito shima zai tafi gida.
Rufe laptop ɗin yayi ya ture komai ya kwantar da bayansa saman makarin kujerar motar ya lumshe ido yana kokawa da abinda ke neman fin ƙarfinsa, yana a wannan yanayin har suka isa gida wanda yana zuwa ya haye sama kota kan Aliya dake can ɗakinta ana faman kwalliya don tarbar miji bai biba ya shige ɗakinsa ya kulle.
Fitowarta kenan cikin sauri don ta tare shi ta samu har ya shige ya rufe ƙofar, sororo tayi tana tunanin abinda ya same shi saboda duk da cewa ba sonta yake ba amma yana ƙoƙarin sauke haƙƙin aure dake wuyansa.
Harta ɗaga ƙafa zata masa knocking sai kuma ta fasa ta sauka ƙasa don haɗa masa abinci kafin yayi wanka ya sauko, sai da ta gama haɗa komai ta zauna jiransa. Jin shirun yayi yawa yasa ta haura saman tayi masa knocking. Sai data jima a bakin ƙofar kafin yazo ya buɗe mata, ɗaure yake da towel jikinsa na raɓar ruwa alamar daga wanka ya fito.
"Am dama naga ka dawo baka yi min magana bane." Tayi maganar tana zuba masa ido.
"Bana jin daɗi ne." Ya bata amsa a taƙaice.
"Ayya sorry Allah ya sauwaƙa, ko in kawo maka abincin nan?."
"No kije zan sauko." Ya faɗa yana maida ƙofar ya rufe. Ajiyar zuciya Aliya ta sauke ta juya ta tafi tana addu'a da fatan ganin ranar da zata samu gurbi ko yaya yake a zuciyar bawan Allahn nan.
******** Naci gaba da gudanar da aikina cikin kulawa da taka tsan-tsan, duk wata hanyar da zata sani yawan haɗuwa da Suhail ko keɓewa da shi bana binta. Idan har mun haɗu to aiki ne ya haɗamu, ko ana general meeting ko kuma zan kai wasu takardu Office ɗinsa kuma shima bana yarda in tsaya daga gaisuwa ba abinda nake ƙarawa zan fice.
Haka zai bini da kallon takaici wanda nake fassara shi da cewar kallon tsana ne yake min, wanda ba kaɗan ba hakan ke kayar min da gaba
Albashina na farko kamar yanda nayi alƙawari da zuciyata haka na kaisu na dire a gaban Abba da Mamy nace "Gashi nan albashina ne na farko, ku saka min albarka."
"Masha Allah, Allah ya sanya albarka ya ƙara maki ƙwarin gwiwa." Abba da Mamy suka faɗa.
"Ameen." Na amsa cike da jin daɗi na miƙe zan tafi Abba ya kirawo ni. "Ina kuma zaki je? Dawo ki ɗauki haƙƙinki mana." Abba ya faɗa yana nuna min kuɗin dana aje.
"A'a Abba wannan naku ne, dama nayi alƙawarin cewa albashina na farko na kune ka'ida Mamy, kuyi min addu'a kawai ita nake buƙata." Na faɗa ina duƙar da kaina.
"A'a ina ba za'ayi hakan ba, ya za'a yi kiyi aiki tuƙuru kuma sannan ki bamu kuɗin duka, haba dai." Abba ya faɗa.
"Ai kuwa dai Abbansu, Nima abinda ke raina kenan nake son faɗa." Cewar Mamy itama.
" Kun can-canci fiye da haka Abba domin duk wata nasara dana samu kune tushenta, don Allah kar kuce a'a." Na faɗa ina jin abinda nayi dai-dai ne har cikin zuciyata.
"To shike nan tunda kin dage bari mu ɗauki wani abu daga ciki sai musa albarka sauran kuma ki ɗauka kiyi abinda ya dace dasu wannan hukunci na yanke." Abba ya ƙare maganar yana dibar kaɗan daga ciki ya miƙa wa Aunty Zali.
Tunda Abba yace hukuncin daya yanke kenan ba yanda na iya nasa hannu na ɗauki kuɗin na fice daga ɗakin. Da yamma na nemi izinin zuwa gida wurin Abba da Mamy basu hanani ba, har su Ameerah na nemi alfarmar tafiya tare dasu ta barmu da sharaɗin mu dawo da wuri.
Wanka nayi musu na shirya su tsaf gwanin sha'awa suna ta murnar Auntynsu zata fita unguwa dasu. Nima shiryawa nayi tsaf cikin doguwar rigar wani material mai kyau nayi rolling mahaifinsa na ɗauki jaka da takalmi wanda suka hau da wankan nawa muka yiwa Mamy sallama muka fice.
Duk inda muka bi sai an kallemu domin kuwa ba ƙaramin kyau muka yiba Masha Allah, ga yaran kyawawa suma ƴan kuɓul-kuɓul dasu sai surutu suke min har muka isa bakin titi inda zamu sami abin hawa. Wata haɗaɗɗiyar motace ta wuce ta gabanmu har ta wuce sai kuma ta dawo da baya.
A hankali ya sauke gilashin motar ya leƙo kansa yana cewa. "Sannunki dai ƴanmata." Ɗauke kaina nayi tamkar ban ganshiba na kama hannun yaran ina ƙokarin wucewa ya buɗe motar ya fito ya sha gabana yana cewa.
"Am baki jiba, magana fa nake maki." Ya faɗa yana zuba min ido tamkar zai cinyeni dasu.
"Au dani kake wai ai naji kace ƴanmata ne ni kuma kaga babar ƴanmata ce." Na faɗa ina nuna masa Ameerah. Murmushi yayi yana cewa "You are jocking ba, nace in ba damuwa ku shigo na sauke ku."
"Akwai damuwa to, don haka bama buƙata!." Na faɗa a fusace saboda ya fara hasalani. Hannun yarana na kama na kauce da nufin muyi gaba mu samu abin hawa ya ƙara shan gabana. A matuƙar fusace na ɗago ina watsa masa wani mugun kallo nace.
"Malam wai miye kake yi haka, nace Bama buƙata kabi ka isheni sai kace dole haba don Allah." Na ƙare maganar a masife ina komawa ainahin Salmata ta baya. Magana zai ƙara yi na ɗaga masa hannu nace. "Bani wuri in wuce kona maka rashin mutunci." Na ƙare maganar ina zaro masa manyan idanuna da suka sha kwalli.
Hannu ya ɗaga alamar saranda yana kaucewa a hanyar. Tsoki na saki na figi hannunsu muka yi gaba ina mita a raina, tamkar wani soko haka ya saki baki ya bita da kallo yana mamakin masifarta.
Ajiyar zuciya Suhail dake zaune a cikin mota yana kallon duk abinda ke faruwa tsakaninta da saurayin ya sauke. "Azababbiyar yarinya." Ya furta a ƙasan makoshinsa yana lumshe ido da tunanin cewa ashe har masu kuɗinma yanzu sauke musu masifar take saboda kallo ɗaya yayiwa saurayin da suturar jikinsa da motar da yake tuƙawa ya san ba daga ƙaramin gida ya fitoba.
Da wannan tunanin a zuciyarsa yaja motarta da yake tuƙawa da kansa ya nufi unguwarsu saboda yana son ganawa da Babansa ne.......