26
by @oumfatima33
💓MATAR MANYA💓
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 26
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
Bana ganin gabana sosai na nufi ɗakin Mama har ina cin tuntuɓe da butar Baba Mari wacce ta samu abin yi ta fara halin nata tana zuba tujara, bana cikin natsuwa don haka ko haƙuri ban iya bata ba na shige ɗakin Mama na zube a tsakar ɗakin ina sauke ajiyar zuciya a jere a jere. "Ke lafiyarki kuwa?." Mama ce ta jefo min wannan tambayar ganin yanda na faɗo mata ɗaki babu ko sallama, sai da na samu natsuwa sannan nace "Babu komai Mama."
Kallona tayi tace "In dai akan maganar da Babanku ya maki ce ki kwantar da hankalinki kiyi addu'a Allah yasa haka shi yafi alkairi, ya fiye maki wannan damuwar tunda kin san dai ba za'a zuba maki ido ki dauwama babu aure ba." Mama ta faÉ—a tana kallona.
"Ba komai Mama in sha Allah zan yiwa Baba biyayya a wannan karon koda kuwa almajiri ne zai bani."
"Madallah Allah ya maki albarka." Mama ta faÉ—a.
"Ameen." Na amsa da ita sannan na miƙe nayi mata sallama na wuce gida.
"Koda na isa gida nayiwa Mamay bayani sai naga tana murmushi tace "Ai abbanku ya min maganar Allah yasa alkairi, abinda muke ta jira gashi yazo. "Amma Mamy kwata kwata bani da tsarin aure a yanzu sai dai ba yanda zan yi tunda Baba ya riga ya bada ni nan da sati ɗaya ne ɗaurin auren." Na ƙare maganar a matuƙar sanyaye.
"Ki kwantar da hankalinki kinji daughter komai zai wuce in sha Allah."
"To Mamy ina fatan Allah ya bani ikon cinye jarabawowina."
"Ameen ya Allah." Daga haka muka bar maganar na shige É—akina na kwanta, kosu Ameerah da suka shigo zasu dame ni kora su nayi suka fita suna kuka. Ina jin Mamy na tambayar su sukace Aunty ce ta koro su. Ina nan a kwance na kasa tsinana komai na aikin dana taho dashi gida zan yi kiran Kairiyya ya shigo min, É—auka nayi muka gaisa take sanar dani cewa Salis É—inta ya kai kuÉ—in aure gidansu.
Zaune na tashi ina tayata murna saboda na san Salis mutumin kirki ne sannan suna tsananin son juna tsakaninsu. "Allah yasa alkairi Bestie ya nuna mana lokacin."
"Ameen ya Allah, saura ke ki maida hankali ki fito da Mijin mu shige daga cikin tare." Ta faÉ—a tana murmushi.
"Hm ki bari kawai Besty ban daÉ—e da dawowa daga kiran da Baba ya min ba."
"Me ya faru Allah yasa dai lafiya?." Ta tambaye ni.
"Cewa yayi ya bada aurena nan da sati ɗaya za'a ɗaura auren." Na ƙare maganar a sanyaye.
"Ya bada aurenki kuma, amma wa zaki aura?". Tayi min tambayar cike da mamaki.
"Ban sani ba Besty kawai na amince zan yi masa biyayya saboda na san ba zai taɓa cutar dani ba."
"Haka ne amma ke yanzu ba yarinya bace kina da right ɗin da zaki zaɓawa kanki abokin rayuwa, addinin Musulunci ne ya baki wannan damar."
"Kwarai na san da haka, amma ki tuna a wancan lokacin dana bijire nabi zaɓin nawa me hakan ya haifar min banda tarin nadama, nifa yanzu Bestie na sauwaƙa ma kaina na zubar da duk wani sha-shanci da buri duk abinda Allah ya ƙaddara min zan amshe shi da hannu biyu, ke dai ki tayani addu'a kawai Allah ya bani ikon cinye jarabawowina."
Ajiyar zuciya Kairiyya ta sauke tace. "To shike nan Allah ya zaɓa abinda yafi alkairi."
"Ameen." Kawai nace mata mukayi shiru, sai can kuma Kairiyya tace "Kin canza sosai Besty kamar na Bestyta ba da na sani mai azabar kafiya da taurin kai, ga jan ajin tsiya, kinda.gwara kawun rijalu!". Ta ƙare maganar cike da zaulaya.
Murmushi nayi nima nace mata "Rayuwa ce ta koya min darussa Besty amma dai Alhamdulillah tunda na dawo hanya da wuri."
"Hakane kam sai dai muce Alhamdulillah." Daga haka hirar ta ƙare muka yi sallama.
★★★
Washe gari weekend Alhaji yazo har gida ya nemi alfarmar tafiya da yara suyi weekend. Abba bai hana ba yace Mamy ta shirya su, duk da cewa ban so hakan ba sai dai ba zan iya musu da Abba ba shi yasa nayi shiru kawai na shige ɗaki. Fahimtar hakan da Abba yayi ne saboda duk lokacin da Alhaji Murtala dala yazo wurin yaran sai na ɓata rai idan ma bance komai ba, hakan yasa ya zauna yayi min nasiha sosai. "Ko kinƙi ko kinso baki isa ki cire jinin Mahaifin yaran nan daga jikinsu ba, sannan duk inda akaje aka dawo shine dai Mahaifinsu na ainihi ba zaki canza hakan ba. Saboda haka dole ki sakawa zuciyarki haƙuri ki bar yara su saba da Mahaifinsu da sauran ƴan'uwansu." Abba ya faɗa yana son fahimtar dani.
"Kayi haƙuri Abba in sha Allah ba zan ƙara ba." Na faɗa ina jin kunyar abinda nayi.
"Masha Allah, Allah yayi maki albarka."
"Ameen Abba na gode sosai." Daga haka na koma ɗakina Abba kuma ya fice da yaran da ƴar ƙaramar jakar da aka zuba musu kaya, su kuma dai murna suke saboda sun san zai kaisu yawo su shawo zaƙi.
****** A cikin satin gaba ɗaya Mamy ta hana ni fita aiki tasa Abba ya amso min hutun aure, gyaran jiki ta fara min mai inganci tamkar yanda ta saba. Abin ba wani a kaina na saka shi ba don haka gyaran ya gundureni don ba yanda zan yi ne kawai, ai kuwa na canza sosai matuƙar canzawa saboda fatata na saurin ɗaukar gyara gashi dama can ba haka kawai muke zaune ba duk bayan kwana biyu sai aunty tayi mana don tace cikakkiyar mace itace mai kula da jikinta da tsaftar kanta.
Gyaran ciki kuwa abubuwa take bani masu inganci naci dana sha har sun ishe ni, in na faki idonta nake zubar da wani, don lokaci ɗaya naji jikina ya wani irin sauyawa tamkar ba ni ba. Duk wannan budurin da ake fargaba da tunanin wane Mijin ne zan aura bai bar ni ba, sai dai ina matuƙar ƙoƙarin dannewa bana nunawa ko a fuska.
Shirye-shirye a can gidanmu Baba keyi wanda hakan ya azabar ɗagawa Baba Mari hankali ganin zan ƙara yin wani auren ita kuma ga nata ƴaƴan bazawara da budurwa a zube ba mashinshini, banda azabar masifa tamkar su cinye junansu ba abinda suke yi.
Kasa haƙuri tayi ta barwa Allah ta dage musu da addu'a ta kuma gyara munanan halayenta, ta gyara tsakaninta da Ubangijinta ta kuma gyara tsakaninta da Mijinta da abokiyar zamanta sai Allah ya dubeta ya bata mafita. A maimakon hakan sai ta shiga Malamai da ɗan jarin da bai taka kara ya karya ba wanda Karima ta samu da ƙyar ta haɗa mata domin ta koma sana'arta ko zata rufawa kanta asiri, duk da cewa Alhamdulillah yanzu Baba yana ciyar dasu safe rana da kuma dare sannan ya musu sutura da magani in basu da lafiya. Domin kuwa sana'arsa ta amfane shi Alhamdulillah, ga shi duk watan duniya idan aka yi albashi sai Salma tayo sayayyar kayan abinci ta kawo masa, sannan tayiwa Mahaifiyarta da ƙannenta har da ƴa'ƴana Baba Marin take haɗawa.
******
A banza suka cinye mata kuɗi domin kuwa an ɗaura auren Salma ranar da aka saka shi, sannan yaran nata kuma har yanzu shiru ba wanda yazo koda wasa yace hana son su. Tamkar tayi hauka haka ta koma lokacin da aka riƙa shigowa da saitin akwatina na lefen Salma guda goma sha biyu tamkar ba auren bazawara ba.
Har yanzu da aka ɗaura auren Salma dake can gidan Aunty Zali bata san Mijin data aura ba don haka take cikin damuwa, yaƙe kawai take a cikin ƙawayenta. Sai bayan sallar magrib ana shirin miƙata gidan Mijinta Iyayenta na yi mata nasiha ne suke sanar da ita cewar ai ba ita kaɗai bace yana da mata sannan kuma su biyu ya aura a yau ɗin.
Wani irin hantsilowa zuciyata tayi tamkar zata faso ƙirjina ta fito zabar yanda abin ya dake ni, wai mijin da aka aura min yana da mata sannan mu biyu ya aura yau ɗin wato ukku kenan. 'to waye wannan mi yasa ya aure mu mu biyu bayan yana da wata matar a gida, shin wai ma shi ya ganni yace yana so ko kuwa kyautata aka bashi.' waɗannan tambayoyin suke min kai-kawo a zuciyata.
'to dama me kike son gani saurayi wanda bai taɓa aure ba, bayan ke ɗin bazawara ce harda yara biyu kika haifa.' wata zuciyar ce ta ankarar dani abinda na manta don haka nayi ƙoƙari ina danne kaina har suka gama aka fita dani don miƙa ni gidan aurena a karo na uku wanda nake fatan ya zama shine na ƙarshe......