MATAR MANYA

27

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 27

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Kaina a lulluɓe yake cikin lafayar da Mamy ta naɗa min lokacin da take tayani shiryawa shi yasa ba zan ƙarda komai ba game da gidan da aka kawo ni. Ni dai naji lokacin da muka tsaya bakin ƙofa aka yi horn mai gadi ya buɗe muka shiga farfajiyar gidan da ban san ya take ba, a hankali Baba Lami ƴar'uwar Mama ta fito dani daga cikin motar ta kama hannuna muka nufi ɓangaren dama.

Sama naji mun fara haurawa wanda hakan ya tabbatar min da cewa upstairs ne, wata ƙofar aka tura muka shiga ta zaunar dani saman gado, nasiha suka ƙara yi min kafin sukayi min sallama suka tafi. Hawayen da suka zubo min na share sannan na buɗe fuskata ina ƙarewa ɗakin kallo, sosai ɗakin ya ƙawatu da tsadaddun furnitures da aka zuba a ɗakin sai ƙamshi yake yi masha Allah.

Ajiyar zuciya na sauke ina godewa Mamy da Abba saboda irin Namijin ƙoƙarin da suka yi wurin zuba min kayan ɗakin, bani da abinda zan iya saka musu dashi da ya wuce kullum in riƙa yi musu addu'a da fatan alkairi. Tashi nayi na ware lafayar na shiga toilet nayi alwala na fito na mayar da ita tsaf na tada sallar isha'i da aka kira, ina gamawa na ɗora da shafa'i da wuturi.

A nan inda na gama sallar ina lazumi bacci ya ɗauke ni ban sani ba, kusan ƙarfe 10:00pm naji alamar an buɗe ƙofar an shigo, a firgice na tashi zaune ina murza idona zuciyata cike da tsoron wanda zan gani a matsayin Mijina. Ba zata, firgici da kuma mamaki suka kamani a lokaci ɗaya saboda wanda na gani a matsayin Mijin nawa. Don haka na buɗe baki da nufin yin magana amma na kasa sai mui-mui nake da bakin ina nuna sa da yatsa.

"Rufe bakin ba mafarki kike ba, wanda kika tsana ɗinne dai a matsayin Mijinki a karo na biyu kuma ko zaki mutu tsabar ƙiyayyar da kike min sai dai ki mutu a ɗakin nan." Suhail ne mai wannan maganar, yana gama faɗa kuma ya aje laidojin daya shigo dasu ya fice abinsa ba tare daya ƙara cewa komai ba. Duk da cewa zuciyarsa ba haka take buƙata ba amma dole ne ya bata lokaci domin sanin meye a zuciyarta game da shi kafin komai.

Ɗakinsa dake ɓangaren ya shige ya maida ƙofa ya rufe yana rintse idonsa yana jin nauyin da yake dako a ƙirjinsa na tsawon shekaru yana zagwanyewa, "Alhamdulillah" ya furta a hankali sannan ya taka ya nufi cikin ɗakin da aka ƙawata shi da tsari mai kyau...

Abinda ya faru shine.....

Lokacin da Suhail ya dawo rayuwar Baba ya taimaka masa tsakaninsa da Allah ya cire shi daga cikin tsananin rayuwar da yake ciki ba tare daya duba abinda ya faru a baya ba, sosai hakan ya motsa zuciyar Baba ya ƙara tabbatar da nagarta da kuma mutuncin yaron.

Ya rasa ta wace hanya zai saka masa shine ya yanke wannan hukuncin saboda har cikin zuciyarsa yana son haɗa jini da yaron saboda nagartaccen mutum ne daya can-canci aso shi. Da ace yana da wata nagartacciyar ƴar bayan Salma to da tabbas ita zai bashi, sai dai kaf a cikin yaran babu wadda ta kama koda farcen Samar ne musamman yanzu da rayuwa ta koya mata darasi ta ƙara shiga hankalinta, tana kuma bakin ƙoƙarin ganin ta kyautata masa domin goge wancan tabon data dasa masa a zuciya. Alhamdulillah ta samu fiye da abinda take nema a gareshi domin kuwa a tsakaninsu in banda addu'a da fatan alkairi babu wani abu da zai ce tayi masa na rashin kyautawa tun bayan wancan.

Don haka ya nemi alfarmar zama da Suhail da Mahaifinsa. A gidan Malam Umaru Mahaifin Suhail suka haɗu, bayan sun gaisa kai tsaye yazo da buƙatarsa ta sake bawa Suhail ɗin auren Salma a karo na biyu bayan ya tabbatar musu da sauyin dabi'u data samu a halin yanzu.

Jim Malam Umaru yayi yana nazari kafin yace "Amma Malam Shehu mai yasa ka yanke wannan hukuncin? Baka gudun a mai-maita irin kuskuren da akayi a baya na yin auren ba tare da amincewar yarinya ba kuma mummunan abu yazo ya biyo baya?."

"Subhanallah Malam in sha Allah abu makamancin hakan ba zai faru ba sai dai alkairi, domin kuwa Salmar ta canza ta kuma gane kuskurenta. Wan can ma da ya faru ƙaddara ce amma tayi nadama sosai." Saurarawa yayi kafin yaci gaba da cewa "Dalilin da yasa na yanke wannan hukuncin shine ina son haɗa zuri'a da yaron nan saboda yaron kirkine mai nagartar da kowa zai so haɗa zuri'a da shi, dalili na biyu kuma shine ina son in masa wani abu wanda zan ji a raina cewar na kyautata masa, duk da cewa na san har abada ba zan iya biyansa alkairin da yayi a gare ni ba. To sai dai a kaf cikin yarana bani da mai nagartar da tafi Salmatu a halin yanzu, kamar yanda na faɗa abinda ya faru a baya ƙaddara ce da kuma ƙuruciya, amma yanzu komai ya sauya." Malam Shehu ya ƙare maganar zuciyarsa fes da kyakkyawar niyar kyautatawa wanda ya kyautata masa.

Sosai Malam Umaru ya amince da dalilan da Malam Shehu ya kawo, sannan kuma har zuciyarsa shima yana son Salmar kuma shi shaida ne akan sauyin data samu domin har gida tazo ta nemi gafarar abinda ta aikata musu, wanda Babar Suhail tayi mata korar kare a gidan. Shi kam ta ɓangarensa bashi da matsala ya amince sai dai ya san inda darun yake wurin Baba ne, amma duk da haka ya san yanda zai tanƙwara ta ta amince.

Sai dai ba zai yi gaggawar yanke hukunci ba dole sai an ji ta bakin yaro domin shine mai ikon zabar abinda ya dace da shi. Don haka Malam Umaru yace.

"Na gamsu da bayananka Malam Shehu sannan kuma a ɓangarena na amince, sai dai ba zan yanke hukunci ba har sai da amincewar yaron tunda rayuwarsa ce." Gaba ɗaya ido suka zuba wa Suhail da tunda suka fara maganar kansa ke ƙasa bai ce komai ba kuma ba wanda zai iya gane yanayin da zuciyarsa ke ciki.

"To Malam Suhailu kaji abinda muka tattauna a kai, shin zaka iya amsar kyautar da nayi maka a karo na biyu ko kuwa, kar kaji komai idan baka buƙatar hakan ka faɗa kanka tsaye ba abinda zai faru." Malam Shehu ya ƙare maganar yana kallon Suhail.

Shiru yayi kansa a ƙasa nauyin Malam Shehu na kamasa wanda har yaji cewar ba zai iya masa musu ba, domin ko a baya bai ƙishi ba. Hasalima shine ya tsaya masa har aka yi auren, idan duk aka ture wannan ma zuciyarsa ta amince da hakan domin har abada ba zai iya ƙin Salma ba ko me zata zama a rayuwa saboda soyayyarta ƙaddararsa ce ya san da hakan tun suna ƙuruciya. Shi yasa ko a wancan lokacin ya kasa rabuwa da ita har sai da aka tursasa masa.

Ganin shirun yayi yawa yasa Malam Umaru taɓa shi yace "Kai muke saurare kayi shiru." Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya buɗe baki zuciyarsa na shiga maban-bantan yanayi yace. "Na amsa Baba kuma na gode, ba zan taɓa ƙin amsar abinda ka bani ba." Wani irin farin ciki ya kulluɓe zuciyoyin Iyayen nasa suka shiga hamdala suna saka masa albarka, kafin suka tattauna yanda ɗaurin auren zai kasance......