29
by @oumfatima33
💓MATAR MANYA💓
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 29
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
Haka naci gaba da kasancewa a gidan Suhail tsawon kwana uku babu wani sauyi, tsakaninmu gaisuwa ce kawai idan ya shigo da safe duba ni haka ma da dare. Abin yana damuna sosai saboda ina fassara hakan da tsanar da yayi min ne, ko kuma ya kasa yafe min har yanzu.
Matarsa kuwa tunda nazo gidan ban ganta ba tamkar ma bata gidan ne, yau daya shigo da safe dubani bayan na gaishe shi kamar yanda na saba ya tmbaye ni in da abinda nake buƙata sai nace masa "Zan shiga mu gaisa da Matar gidan." Ɗagowa yayi ya zuba mata ido yana mamakinta. Wato in zasu shekara a haka ita ko a jikinta ko, tunda dama ba sonsa take ba, ƙila yanzun ma takura mata aka yi ta amince da komen.
"Cikin jin zafinta yace "Allah ya kiyaye." Yana gama faɗa yayi gaba fuuu ya barni ba baki buɗe ina mamakin abinda nayi masa daya fusata shi. Baki na taɓe sanin ba abinda nayi masa na haye sama domin ɗauko mayafi in fita saboda zaman wuri ɗayan ya ishe ni dama so nake in ɗan miƙe ƙafafuna.
Part ɗin dake ɓangaren hagu na nufa wanda na tabbatar da cewa shine na Matar gidan domin kuwa iri ɗaya ne da wanda nake ciki. Knocking nayi a hankali na tsaya jiran a buɗe min, wata yarinya ce tazo ta buɗe min ta bani hanya na shiga parlon. Tsarin ginin irin wanda nake ciki ne komai da komai sai banbancin kayan da aka zuba ma ko wanne kawai. "Aunty tana sama bara na kira maki ita." Yarinyar ta faɗa tana haurawa saman.
Kamannin yarinyar dana gani a fuskar wacce ke saukowa daga saman ya shaida min cewa itace Auntyn tata kuma Matar gidan, baƙace ba laifi tana da kyau dai-dai gwargwado don ba za'a kirata mummuna ba, ba kuma za'a kirata mai tsananin kyau ba, tana tsaka tsaki ne. Sannu nayi mata na fara gaisheta a matsayin wacce nazo na sameta, wani irin mugun kallo na wulaƙanci da take jifana da shi ne yasa naji raina ya fara ɓaci don gaskiya bana son raini da wulaƙanci a rayiwata.
"Me kike yi min a gida, munafuka algunguma mara tsoron Allah, ko an faɗa maki ban san irin shaiɗancin da kika yi ba ne? Amma da yake baki da kunya shine kika ƙara dawowa saboda anga yayi kuɗi shine aka ƙaƙaba masa baya so don aci banza ko?, makwaɗaitan banza daga ke har Iyayen naki." Ta ƙare maganar tana riƙe ƙugu cike da rashin kunya.
Bamu san lokacin daya shigo ba har yaji abinda take faɗa ba sai ji muka yi ya daka mata wata razananniyar tsawar data saka mu firgita baki ɗaya. "Ashe baki da hankali, Iyayenta sa'o'inki ne da zaki zagesu? To bari kiji, wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara furta irin wannan maganar ko ki shiga abinda bai shafe ba, in ba haka ba kuma ranki zai yi mummunan ɓaci!." Ya ƙare maganar furiously cike kuma da gargaɗi.
Hannun Salma data daskare a wurin magan-ganun Aliya na ratsa ƙwaƙwalwarta yaja suka fice a ɗakin yayinda Aliya ta rushe da kuka, baƙin ciki tamkar ya kashe ta. Tsabar an raina mata wayo kishiyoyi har biyu a lokaci ɗaya ba tare data gama ko sanin Mijin ba. Abinda yafi ƙona mata rai shine maido wannan tsinanniyar yarinyar da kowa ya san irin son da Suhail ke mata, sannan ita waccen ɗayar da bata tare ba ƴar masu kuɗice da zata zo ta riƙa taka mutane son ranta domin ƴar mai gidansa ce.
****** Suhail kuwa bai tsaya ko ina ba sai da ya kaita har ɓangarent ya zaunar da ita cikin ɓacin ran da yake ciki yace "Why Salma? Why? Me yasa kika yi abinda kowa yake goranta mana a kansa haba don Allah, ya ishe ni haka bana son tunawa!". Ya ƙare maganar tamkar zai fashe da kuka.
Tuni kuka yaci ƙarfina don tun a can dannewa kawai nake sai yanzu na samu damar yinsa son raina, cikin muryar kukan nace "Ƙaddara ce da kuma sharrin zuciya, amma na daɗe da gane kuskurena don Allah kayi haƙuri ka yafe min tun ba yau ba nake son neman gafararka sai dai ban samu dama ba!". Na ƙare maganar ina ƙara fashewa da kuka, ido ya zuba mata yana kallon yanda take kuka wanda ba ƙaramin taɓa zuciyarsa kukan ke yi ba.
Ganin ba zata daina kukan ba shi kuma azabtuwa yake da hakan yasa ya riƙo hannunta abinda bai taɓa kwatanta yiba tunda tazo gidan sai yau. "Ya isa haka kukan." Ya faɗa mata cikin sanyin murya da son tayi shirun. A hankali kukan nawa yake tsayawa har ya tsaya gaba ɗaya na share fuskata sai faman ajiyar zuciya nake saukewa.
Sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya fice don yin shirin fita Office.
★ Yau satina ɗaya a gidan Mamy tazo min dasu Ameerah dake ta rigima suna neman Auntynsu shine yau ta tambayi Abba ya basu izinin zuwa su dubani tunda dama yaran basu taɓa zuwa ba. Ba kaɗan ba nayi farin ciki da zuwan masu domin har yanzu ina cikin damuwa duk da cewa Suhail baya min wani abu na rashin kyautawa amma dai har yanzu babu sakewa a tsakaninmu.
Bayan na cika gatansu da abinci da abin sha harda su chocolate na É—aukowa yaran suna ta murna, ganin hankalin yara ya tafi kan ciye-ciyensu yasa Mamy ta fuskanci Salma tace.
"Meke damunki ne daughter? Fuskarki ta nuna damuwa kar ma kice min babu komai." Tayi hakan don ta san zan iya cewa babu komai É—in innbar damuwar a raina tayi ta damuna.
Ajiyar zuciya na sauke na shiga zayyanewa Mamy duk abinda ke faruwa tunda nazo gidan saboda munyi shaƙuwar da bana iya ɓoye mata komai. Ajiyar zuciyar itama ta sauke sannan tace "Kar ki damu in sha Allah komai zai yi dai-dai domin kuwa har yanzu Suhail na sonki, ko a wancan lokacin takuraasa akayi ya rabu dake amma ina mai tabbatar maki da cewar har yanke kece a zuciyarsa. Kawai dai abinda ya faru ne ya kasa mantawa har yanzu kuma kece zakiyi ƙoƙari ki mantar dashi."
"Taya zan mantar da shi Mamy?." Nayi mata tambayar cike da son jin amsar da zata bani. Kallona tayi tana murmushi tace"Oh ni su daughter ashe dai ana son bawan Allah aka bashi wahala." Ta ƙare maganar cike da son ta zaulaye ni. Kaina na duƙar ƙasa ina murmushi kunya na kama ni.
"Kina ji ko? Ki bani hankalinki nan in maki bayanin abinda zakiyi ki ƙwaci kanki."
"To Mamy." Na faÉ—a ina mayar da hankalina gaba É—aya gareta saboda da gasken so nake mu shirya da Suhailuna komai wuce tamkar bai faru ba.
"Abu na farko da zakiyi shine: da farko ki kwantar da hankalinki ki nuna masa cewar kin sauya sannan a shirye kike da ki kyautata masa ki basa duk kulawar data dace, na biyu ki dage da tsafta da gyara jikinki wanda na san bani da matsala dake ta wannan fannin. Sai kuma girki, wai tsaya ma kina masa girki kuwa anya?." Mamy tayi min tambayar tana tsareni da kallo.
Kaina na duƙar sannan nace "Ina yi Mamy shine baya zuwa yaci, kullum fa in ya shigo da safe ya duba ni bana ƙara ganinsa sai dare in yazo min sallama!". Na ƙare maganar cike da damuwa.
"Laifinki ne daughter, kece kika hore shi da haka a zamanku na farko. Abinda baki sani ba shine, shi Namiji tamkar ƙaramin yaro yake duk yanda kika tarbiyanceshi tofa haka zai miƙe ko shekara ɗari zaku yi a tare. Shi yasa duk Macen data auri Mijin wata take shan wahala da shi saboda hanyar da Uwar gida ta ɗora shi a kai a haka zai miƙe sai kiga ana ta samun saɓani saboda da banbancin ra'ayi, sai tayi da gaske zata iya canza wasu abubuwan."
"Haka ne Aunty na fahimta na kuma gane kuskurena." Na faÉ—a ina jin ba daÉ—i har cikin raina akan abinda nayi a baya.
"Ki zama gwana wajen iya tsara girki, wannan ma na san baki da matsala sai dai ki ƙara dagewa. In na fita zan shiga Kasuwa in sayo maki kayan ɗanɗanon girki da kamsasa shi, ki riƙe Thyme leaves da kyau domin kuwa kat ne wurin fitar da daddaɗan ƙamshin girki harma da ɗanɗano. So nake in kika ɗaura girki ya tashi hankalin gidan nan gaba ɗaya da ƙamshi har ma da masu wucewa ta waje."
"In sha Allah Mamay." Na faÉ—a ina murmushin maganar tata.
"Abu na gaba shine, kiyi masa biyayya ki girmama Iyayensa ki mutunta ƴan uwansa, sannan ki zama mai haƙuri dashi ako wane hali, k zama mai ɓoye sirrinsa. Ki zama mai sauƙi a mu'amala dashi. Ina fata kina fahimta?."
"Sosai nake fahimta Mamy." Na bata amsa.
"Yauwa haka nake son ji." Ta ƙare maganar tana gyara zamanta ta sake fuskanta da kyau da alamar abinda zata faɗa yana da mahimmanci sosai.
"Abu na karshe da zan faɗa maki shine ki iya kula dashi a shimfiɗa, ki san duk yanda zakiyi ki faranta masa ta hanyar bashi gamsashshiyar natsuwar da yake buƙata." Da sauri na duƙar da kaina saboda nauyin zancen da naji duk da cewa ba wani buɗe maganar tayi ba.
"Ba abin duƙar da kai bane gaskiya nake faɗa maki, matuƙar kika riƙe waɗannan abubuwan da kyau tofa kin gama da Rijalu a zaman duniya sai kuma fatan shiga aljanna ranar gobe ƙiyama." Dariya na sanya saboda maganar tata ta ƙarshe ta bani dariya, itama taya ni tayi muka shiga yi tare.
Mun daɗe muna hira don sai bayan sallar la'asar suka yi min sallama suka tafi suka barni da kewar su tamkar in bisu. Bayan wucewarsu na fara tsara yanda zan gudanar da shawarar da Aunty ta bani, don haka haɗin dilkar da tazo min dashi na fitar na kwaɓa sannan na shiga kiching na ɗaura girki mai sauƙin nauyi saboda na dare ne.
Cikin ƙankanin lokaci na kammala sannan na shafe jikina da haɗin dilkar nan na shiga gyara inda ya ɓaci a gidan, sai da na gama tsaf sannan na saka ƙamshi a ko ina na shiga wanka.....