MANARAH

5&6

by @meenatyandoma

MANARAH

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰

PG 5&6

...Ƙasurgumin jeji ne wanda a iya kallonsa ba zaka taba tsammanin mutum zai iya ratsawa ta cikinsa ba. Dogayen bishiyoyin da ke jejin kallo daya zaka yi masu sai gabanka ya faɗi. Sakamakon wani irin tsayi da lankwasawa da suka yi.

Deena da babbar amiyarta Afra ne ke ratsa jejin ba tare da tsoro ko farbaba.

"Deena amma kin tabbatar kin yanki gashin Hisham? Kinsan fa yadda muka yi da Boka"

Afra ta karasa maganar tare da haurawa saman wani dutse da ya tare gabansu.

"Hauka ake in Taho BA tare da gashin nan ba. Ai ko zanyi yawo tsirara sai na mallaki Hisham na rabashi da kowa na da, tunda dama can ba jituwa suke da mahaifinsa ba. Ko kinsan jiya ma sai da ya mareni muka dambatu wannan sawun fa duk shi ya yi mini shi"

Ƙatotuwar ashar Afta ta zabga tare da dakatawa da tafiyar da take.

"Wallahi Deena kina bada mata. Yanzu har kinyi lalacewar da Hisham zai kamaki ya rika duka tamkar wata baiwarsa? Ni kam me kika gani a jikinsa da ba zaki iya rabuwa da shi ba. Farin kawai ne da kuma kyawu da ke gare shi amma kin fi shi kudi gata galihu"

"Hmm! Ba za ki gane ba. Kawai dai mu karasa gaban Cinyedu"

Banza Afra ta yi da ita domin ta kawo ta wuya.

tafiya kadan ta kawo su wurin bukkar cinyedu.

Bukka ce da aka zagayeta da jajayen kyallaye ga kuma wasu daka-dakan kawunan kwarangwal da ke rataye a kusa da ita. Kallo ɗaya za ka yi wa cinyedu sai hantar cikinka ta kada sannan ka fahimci sunyi hannun riga da imani.

Tsoho ne wanda ya ga jiya ya ga yau. Fatar jikinsa duk ta yamushe, ilahirin jikinsa gashi ne tamkar jikin dabba.

Tsafaffen buzun da ke shimfiɗe suka hau tare da dubarsa.

Kallonsu ya yi tare da kwashewa da dariya.

"Ka ga ɓatattu ahalin ɓatacce. Miƙo mini gashin"

Ba musu ta saka hannu ta fito da gashin ta mika masa.

Wata ƙatuwar kwarya ya dauko me cike da ruwa ya juye gashin. Wasu layu guda biyu ya dauko ya watsa cikin ruwan.

Hannunsa na hagu ya dauka ya saka cikin ruwan tare da rufe idanunsa ya na karanto wasu ɗalasiman tsafi.

Ya dauki daƙiƙu kafin ya buɗe idanunsa.

Tamkar wanda ya hango ranar mutuwarsa haka ya zabura tare da murza idanunsa, da gaske ne ba gizo bane bare ya saka ran ko bacci ya fara daga zaune har ya lula duniyar mafarki.

Halin da suka ga Cinyedu ya fada shi ya saka su jin gabansu ya fadi. Kallon da suka ga ya na masu ne ya saka sauran nutsuwar data rage Masu tserewa.

"Lafiya kuwa? Ko wani abu ne ya faru"

Deena ta tambaya murya na rawa tamkar me shirin fashewa da kuka.

Bai ce mata uffan ba fa ce nuni da yayi mata akan ta leƙo cikin kwaryar. Hisham ne tsaye ya juya hannunsa rike da jariri ya na dariya.

Kururuwar da Deena ta kwala ce ta saka Afra firgita bata san lokacin da ta leƙo ba.

A firgice ita ma ta juya ta na me kallon kwaryar.

"Boka me nake gani? Ina Hisham ya samu jariri. Don girman tsafinka ka fada mini ainahin abinda ke faruwa"

A maimakon ya bata amsa sai gani suka yi ya turbune fuska.

"Hakika wannan ce rana ta farko da na ci karo da abinda ya girgizani. Rana ta farko da na gabatar da bincike a maimakon in ga sakamakon abinda nake nema sai wani bakon lamari ya sake Kunno Kai. Ku sani yau ta kasance rana ce ta rashin sa a domin na rasa gane me Jinjirar nan ke nufi. Amma tabbas ke da Hisham kuna cikin gagarumar matsalar da sai nan da mako biyu in ta yiwu zan gane ainahin abinda nake son ganewa."

Ya karasa maganar tare da kallon Deena.

"Shi kenan! Ta faru ta kare. Da ma akwai matsalar da zata gagareka? Ni kam na shiga ukuna"

Tsawar da ya daka mata ce ta sakata hadiye sauran maganar.

"Ba don kin kasance kin jima kina zuwa wurina ba da yanzu ba wannan maganar ake ba. Ki bace min da gani kada ki kuskura in GA kafarku sai nan da mako ɗaya"

Rufe bakinsa a rikice suka mike da gudu-gudu suka baro wurin.

...Alhaji kuwa tun bayan da suka kawo su Hisham asibiti jikinsa ya yi wani irin sanyi musamman ga Safiyarsa. Me ya kai shi ya furta kalmar saki, ba shakka ya yanka babban kuskure. Tun kafin ta farka ma ya mayar da ita.

Yau ita ce rana ta farko da ya ji tamkar ana sarrafa jikinsa, da gaske shi ne yayi wannan aika-aika?.

Nurse ce ta isar masa da sakon likita na nemansa a office.

Bai bata lokaci ba ya iske sa a office din.

Farin glass din da ke fuskarsa ya sauke tare da kallon Alhaji Mukhtar.

"Alhaji munyi nasarar tsayar da jinin da yaronka ya zubar. Yanzu haka wani jinin muke kara masa. Amma mahaifiyarsa yanzu haka sai dai mu dage da addu'a domin zuciyarta ce ta so samun matsala. Wani abu da ta ji ko ta gani shi ya karasa rikita lafiyar jikinta. Amma In Shaa Allah Zata farka a ko wane lokaci, sai dai a kiyaye fada mata duk wani abu da zai zamto yana tayar mata da hankali"

Godiya Alhaji ya yi ya fice daga office din. Kasancewar Hajiya na wurin Umma ɗan abokinsa wanda ya kasance abokin Hisham ne ya kira wato Yazid. Domin har a zuciyarsa in dai ya na cikin dakin ya na kallon Hisham da ke kwance bai san wanda ke kansa ba. Wata zuciyar ayyana masa take ya saka fulo ya danne kan Hisham har sai ya mutu.

Don haka Yazid na karasowa Alhaji ya fice daga dakin.

Ba karamar firgita Yazid ya yi ba ganin aminin nasa kwance ga uban bandeji a kai. Wayar Hisham ce ta hau ruri, sunan Deena da ya gani ne ya saka shi dauka ya sanar da ita halin da ake ciki. Kamar jira ake yana katse kiran sai ga na Shukura ya shigo.

Wata Ashar ya danna tare da kara wayar a kunnensa. Ita ma bai boye mata komai ba.

Sai da ya katse kiran ya gane ya tafka babban kuskure domin su duka sunce ga su nan zuwa kuma ya san kamar wuta da ruwa haka suke ba su jituwa.

Motsin da Hisham ya fara ne ya saka Yazid zaunawa a kusa da shi ya na masa sannu.

Kansa da ya ji ya masa nauyi ne ya saka shi dafe goshinsa wanda aka nannaɗe da bandeji. Ɗaya bayan ɗaya abinda ya faru ya shiga dawo masa.

Dogon tsokin da ya ja ne ya saka Yazid tambayarsa lafiya.

"Ina Umma take"

"Ta na dayan dakin in ji Alhaji"

Sunan Alhaji da Hisham ya ji an ambata ya saka duk wani annuri da ke fuskarsa daukewa.

Yazid bai yi mamaki ba domin ya san takun sakar da ke tsakaninsa da mahaifinsa.

Flat ya dauko ya zuba masa fruits ya miko masa.

Sai dai ko da wasa ya ki ya ci bukatarsa daya a zo a cire masa wannan jinin ya kama gabansa.

Kofar da suka ji an turo ce ta sakasu kallon wurin.

Deena ce a gigice ba ta ɓata lokaci ba ta haye Saman gadon ta na jero masa sannu.

A yanzu kam ya saki jiki da ita sosai tamkar ba su bane suka gama ci ma juna mutumci ba.

Turo kofar da aka sake yi ce ta saka gaban Yazid faɗuwa. Shi kenan! Ta faru ta ƙare a yiwa me zane ɗaya sata.

Deena kuwa girar sama data kasa ta hade ganin wadda ta tsana fiye da kowa a rayuwarta wato Shukura.

Shukura kuwa ko a jikinta domin ta fi Deena boye kishi da kuma iya bariki.

"Sannu dolena! Ubangiji ya baka lafiya, ya kake ji"

Murmushi ya yi domin har ga Allah ya na kaunar Shukurah ba kaɗan ba.

Zagin da Deen ta laftawa Shukura be ya saka Hisham haɗe rai. Domin tun bayan shigowar Shukurah ya ma manta da Deena ta na wurin.

"A gidan uban wa ya zama dolenki? Ke asuwa In ana babbakar Giwa a tunaninki ana jiyo ƙaurin Zomo ne?"

Murmushin da ke kara tafiya da imanin Hisham Shukurah ta yi.

"Haba 'yar uwa. A tunanina yanzu ba lokacin fada ba ne mu nemi lafiyar masoyinmu koma me ye zsi a yi daga baya. Haka ne ko dole na?"

Ta karasa maganar tare da kallon Hisham.

Tsatss! Deena ta dauke Shukurah da lafiyayyun mari.

A maimakon Shukura ta yi yunƙurin ramawa kumci ta dage ta na murmushi ta kalli. Deena

"Mari karamin abu ne da zan iya shanyewa Indai a kan Dolena ne wato Hisham"

Wannan magana da Shukurah ta yi Deena ji ta yi tamkar an watsa mata tafasasshen ruwan zafi a zuciya.

Hisham da ya kai makurar ƙurewa a fusace ya fara magana.

"A kan me za ki tsaya ta marar mini ke. In dai na isa da ke bance ki ɗaga mata kafa ba "

Jin abinda ya fada ya saka Shukura jefawa wani irin kallon me dauke da na fiki iya bariki.

Yazid kam wasu yawu ya haɗiye ƙut! Domin ya san tabbas shi ɗaya ya yi kaɗan ya iya kashe wannan wutar da ke shirin kunnuwa.

Deena kuwa cikin rufewa ido ta tunkari Shukura. Sai dai kafin ta karasa tuni Shukura ta watsar da fruits din dake cikin flat ɗin ta saukewa Deena Shi a goshi. Fashewarsa ta yi daidai kwala ihun Deena lokaci ɗaya jini ya biyo baya.

Ihun da Nurse ta ji shi ya saka su shigowa ɗakin da gudu. Mutuwar tsaye suka yi ganin abinda na mujiyarsu suka hasko masu....

Meenat A 'Yandoma

***

DON ALLAH MASU TAMBAYAR GROUP KU SHIGA WANNAN👇👇

***