PAGE 15
by @sumy6163
💫💫 RASHIN SANI 💫💫
STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).
Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.
Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.
PAGE 15.
Tsayawa tayi ta ƙare musu kallo, sannan ta koma ciki tace wa Abdul yaje ya ƙira mata Aimana, shi ma yana fita kuwa ya hangosu, zuwa yanzu shima ya fara fuskantar akwai abu a ƙasa tsakanin Kamal da Aimana, cikin basarwa ya nufi wurinsu yace..
"Ah ya Kamal, ashe dai ka shigo, tun dazu Mama take jiran shigowarka, ashe da mutuniyar ka haÉ—u"
Sai yanzu da Abdul ya anbaci Mama tukun ya tuna ashe ita ya shigo gaisarwa, cewa yayi, "wallahi kuwa Abdul, kasan an daÉ—e ba'a ga juna ba, shine na tsaya muÉ—an gaisa kafin nan"
"Aikuwa dai kam ya Kamal, na gane, amma dai shigo ka gaida Mama tukun sai ka dawo ku cigaba da ƙarewa juna kallon", Abdul ya fada cikin zolaya, dukansu dariya suka masa, kafin Kamal ya wuce falon Mama.
Da sallama ya shiga, ya durkusa ya gaisheta, kafin ya zauna da kyau, hira suka ɗan taɓa kadan, ta kuwa tambaye shi ya makaranta, anan yake faɗa mata ai sunyi hutu, yanxu sun kammala 300 level, idan sun koma dai sai 400 insha'Allah, ta mishi addu'a tare da fatan alkhairi, sannan ya mata sallama ya tafi.
Yana fita tsakar gida kuwa ya rika baza ido ko zaiga Aimana, amma bai ganta ba, anan ya yanke shawaran bari ya shiga yagaida dada, don yasan bazata wuce nan ba, ilai kuwa yana shiga ya sameta a zaune tana dannawa Dada ƙafa, ya nemi wuri ya zauna shima, ya gaida Dada sannan ya kamo ɗayan ƙafar shi ma ya fara matsa mata a hankali.
"Kai É—an nan Allah ya maka albarka, kaga ja'iran nan saida ta gama min iya shege kafin take matsa min sawun nan, gashi dama ba wani iyawa tayi ba"
"To ai shikenan Dada, sai ya yi ta miki tunda ni ban iyaba, kuma dai zai tafi ya barni ne dake a gidannan, zanga mai matsa miki idan baya nan"
"Rabu da ita hajiya Dadanmu, idan kina so kullum ma zanzo in matsa miki sawunki".
"Yawwa kamalu, Allah yi albarka"
"Ameen Dadanmu"
Cuna baki Aimana tayi ta bar matsawa Dada ƙafar, tace, "Bari na bar waɗanda ake sawa albarka suyi, mu kuma ma tara a gaba".
"Haba ke kuwa, so kike yau a jimu ne, dawo maza mutuniyar ai kinsan tsakanin mu ba haka, taho yar jikalleta".
"Ba wani daÉ—in baki da zaki min Dada, ai nasan me zanyi, zamu gamu ne anjima".
Haka suka kasance a wurin Dada har na tsawon lokaci, sai jan Aimana Kamal yake da magana, ƙiran sallah da akayi yasa shi tafiya ba don yaso ba, haka kawai yake jin wani irin nishaɗi.
Koda yayi sallah ya koma gida, tunanin Aimana kawai yakeyi, sai ji yayi kamar ya koma su cigaba da hiransu, saidai yasan yanzu baida wannan hurumin, duba da cewa, yanzu dashi da Aimana ba yara bane, kuma ba muharramai ba.
A ɓangaren Aimana ma hakan ta kasance, bata so tafiyar Kamal ba, ina ma yayi ta zama kar ya tafi tayita kallonsa.
Washegari kuwa tana gama abunda zatayi, tayi wanka tayi ɗan yi light makeup nata tayi kyau abunta, ta fesa turare, ta fito falo, sai zuba ƙamshi takeyi, tana zuwa tace wa Mama zata je gidan su Hamida.
"Bazaki ba Aimana, akwai abunda zaki min".
"To Mama, amma ba daÉ—ewa zan yi ba, sai inzo in miki aikin".
"Ba inda zakije, kije ki jirani, yanzu zanzo na baki aikin".
"Don Allah Mama, yanzu zan dawo".
"Yaushe muka fara jayayya dake Aimana, to baza kije ba nace, ko kin gama aikin, and that is final".
"Kiyi haƙuri Mama".
Tana faÉ—in haka ta koma É—aki ta naÉ—e mayafinta ta ajiye sannan ta fito falo, Mama ta samu a falon, taje kusa da ita ta zauna, sannan tace..
To Mama me zanyi?"
"Ki shiga É—aki, wardrobe na nake son ki gyara min, ki fitar da kayan ciki, ki goge cikin sai ki mayar"
Tace to, tare da tashi ta nufi É—akin Mama.
Tana aikin ne kawai amma tunanin ta na wurin Kamal, ko me yakeyi yanzu, ko shima yana can yana tunanin ta, Oho, ta É—auki kusan awa É—aya da rabi kafin ta gama gyaran, ta fito ta faÉ—awa Mama ta gama.
"To yayi kyau, Allah yi albarka".
"To Mama yanzu naje ni?"
"Yanzu ƙarfe nawa ne Aimana, kusan shabiyu, me zakije kiyi a gidan mutane?"
"Allah Mama bazan daÉ—e ba".
"To naji ki bari rana tayi sanyi ko zuwa la'asar sai kije, amma da wannan rana tsago tsago ai bakya je gidan mutane ba".
Aimana ba yanda ta iya, haka ta haƙura da zuwan, amma hankalinta duk na can.
Tare suka shiga kitchen da Mama suka haÉ—a abincin rana, suna gamawa ta É—auki na Dada ta kai mata, sannan ta dawo ta shige É—akinta, wani wankan tayi ta gabatar da sallanta sannan ta fito, ta É—ebi abinci taci.
Idonta na kan agogo, ta ƙagu ayi la'asar, don ta samu ta fice, ai kuwa ana fara kiran sallah, ko idarwa ba'ayi ba ta tashi ta kabbara nata, Mama dai na ganin ikon Allah, tana idarwa tace wa Mama ta tafi, don yanzu kam ko neman izinin bata tsaya yi ba.
Tana fita kuwa bata tsaya ko ina ba sai gidansu Kamal, sallama tayi, Ummah dake tsakar gida ta amsa mata, ta shiga ta rusuna ta gaishe ta, haka kawai take jin nauyin Ummah yanzu.
Gashi mutanen naki basa nan, sunje duba umaru baiji dadi ba (kanin Kamal idan baku manta ba) a can gidan kakan su.
"Ayya Umaruru baiji daÉ—i bane, ni na daÉ—e ban ganshi bama, tun kafin tafiya ta makaranta".
"Ah lallai kun daɗe kam, anya ma zaki gane shi kuwa yanzu, don ya miƙe har yafi Kamalu tsayi yanzu, jiya ne ɗan zazzabi ya bugeshi, amma da sauƙi".
"Ayya to Allah ya ƙara sauƙi, ai dama shi yafi ya Kamal jiki tun da"
"Ai kuwa dai Umaru akwai saurin girma kamar mace".
Haka suka cigaba da hiransu, zuwa can kuwa sai ga Kamal ya shigo da sallamarsa, amsa masa sukayi a tare, bayan ya shigo yawa Ummah sannu da gida, sannan suka gaisa da Aimana.
"Ina ka shiga ne Kamalu, yau tun safe ka fita sai yanzu".
"Wallahi kuwa Ummah, naje wurin wani aboki nane, mun ɗanyi wani research kaan, kin san karatun namu bai buƙatar hutu, kullum a bincike muke".
"To Masha Allah, Allah dai ya taimaka, ga abincinka can".
"To sannu Ummah nagode, ya jikin Umar É—in, ko basu dawo bane yan dubiyan".
"Ina kuwa suka dawo, ai sunje gidan Hajja kam sai an gansu kuma, Aimana miko wa Yayan naki abincinsa gashi can"
"To Ummah", Aimana ta faɗa haɗi da miƙewa ta ɗauko masa, ta kai masa har inda yake zaune, sannan taje ta ɗauko masa ruwa mai sanyi a firij, tunda taga haka ƙannensa suke masa tun da.
"Sannu Aimana nagode, zauna muci".
"Kai ya Kamal, nikam a ƙoshe nake".
Daga murya yayi yace, "Ummah kinji wai baza taci girkin ki ba".
"Wallahi Ummah sharri yake mun, ce masa fa kawai nayi na ƙoshi".
"To idan baki faÉ—i haka ba ai sai kisa hannu kici, shikenan", ya faÉ—i yana mata wata kalar dariya da ta kasa gane ta mecece.
Wani harara ta maka masa sannan tace, "sharri dai ba kyau.
Ummah tana jinsu, murmushi kawai takeyi, ita dai har ga Allah tana fatan wannan tarayya tasu ta kasance har abada, saboda kalar tarbiyar Mama, ko wace uwa zata so haÉ—a iri da jininta.
Tashi tayi ta wanko hannunta, tazo suka fara cin abincin, dama cikin da sauran space, tunda ko abincin kirki ta kasa zama taci, tunani Aimana ta shiga yi, watarana haka zasuci abinci tare a gidansu, a matsayin miji da mata,haka sukaci iya cinsu, Aimana ita ta fara cire hannu, tace ta ƙoshi, shima kaɗan ya ƙara ci ya cire hannu, ruwa Aimana ta kawo masa ya wanke hannun, sannan ta tattara wurin, ta kai sauran abincin kitchen.
Hmm Ummah fa tana daga ciki take hango duk abunda sukeyi, abun ya burgeta ainun, ta kuwa yabawa Mama, don tasan ita ta koya mata duk wannan, lallai wanda yayi dace da samun Aimana ya dace da Mata, Allah ya bawa Kamal dinta.
Suko suna can,basu ma san Ummah tana kallonsu ba, sha'aninsu kawai sukeyi, bayan gama cin abinci, wani sabon hira suka kafa, Aimana ina zatasa ranta yau don dadi, gata ga Kamal, suna zaune suna hira, irin wanda suka dade basuyi ba, can tace masa..
"Ya Kamal, shekara kusan uku rabona dakai, duk lokacinda nazo hutu, bama haduwa, har in gama hutuna in tafi, kuma Humaida ta tabbatar min kana sanin duk lokacinda nazo, to amma meyasa baka zuwa?"
Wani numfashi yaja kafin yace, "Aimana bazaki gane bane, shi karatun medicine baida sauki, daga zaran kasa wasa sai kaga wasa kaima, gabadaya banda lokacin kaina Aimana, yau muna wannan practical din, gobe wani research ta can jibi wannan, gata wancan, sam banida zama, safe karatu, rana karatu, ke har tsakar dare karatu mukeyi, akwai semester da har aka gama banzo gida ba, saida nazo hutu,to kinji dalili, kina raina Aima, yanda zanyi squeezing time inzo ne yake min wahala".
"Ya Kamal kenan ba wani ina ranka, ai da haka ne zaka bar komai, ka sadaukar da yini guda kawai don kazo mu gaisa , musamman idan ka tuna inna koma fa sai bayan shekara zan dawo, kuma baka taba ko zuwa min visiting ba".
"To shikenan my Aima, kiyi hakuri nayi laifi, ban kyauta ba, ayiwa ya Kamal afuwa".
"Gaskiya in fada maka ya Kamal, nayi fushi dakai, sabida ga dukkan alamu wannan ya Kamal din bai damu da Aimana ba".
"Ayi hakuri dai a dena fushi da Kamal dinnan, don Kamal bazai juri fushin Aimana ba".
"Allah sarki Aimana, ya ta iya da ya Kamal dinnan, tun tuni ta yafe masa, saboda Aimana bata iya fushi da Kamal".
Rana ta farko da Kamal yaji Aimana ta Kira sunansa ba tare da ta hada da yaya ba, sai yaji wani iri,amma kuma abun sai ya burgesa,yace..
"Ah lallai Kamal ya kuwa gode,tunda an karbi uzurinsa".
"Eh an karbi uzurinsa, amma da sharasdin bazai maimaita abunda yayi ba".
"Insha'Allah ma Kamal bazai kara ba, a dai yi hakuri", ya fada harda kama kunne.
"To ai shikenan, ya Kamal ka bani labarin school naku, ya yake ya kake rayuwa a makaranta da sauran su".
"To gyara zama kisha labarin"
FUGUS, babban jami'a ne dake cikin jihar Zamfara a Gusau, LGA, inda ake koyar da fanni daban daban, a ciki akwai faculty of science, wanda shima ya kasu kashi daban daban, daga ciki akwai department na medicine, inda anan kamal yake.
Ya kasance department nasu ba su da wani yawa, kasancewar ba kowa yake sa'an samun gurbi a wannan fannin ba.
Kamal ya kasance daga cikin dalibai masu kokari sosai, tunda yake bai taba samun CO ba, saboda kokarinsa yasa mates nasa suke kiransa da guru, kai hatta lecturers nasu sun sanshi, duk da wahalan course nasu, haka yake samun kusan 5points a GP dinsa, ba ruwansa da shiga shirgin yan mata, duk da suna yawan shige masa kasancewarsa kyakkyawan saurayi mai jini a jika, kuma ga kansa na ja, kowacce so take taga ta samu shiga a wurinsa, bama yan mata ba, hatta mazan ma so suke su rabeshi, kodan sanin zasu karu dashi.
Su uku ne a dakinsu, dashi da Saif da Nabil, wadanda kuma sune kadai abokansa a makaranta, akwai shakuwa da amana sosai a tsakanin su, ta yanda duk sunsan labrin juna, kuma suna iya sharing damuwar su a tsakanin su, sunsan labarin Aimana sosai a wurin Kamal, don har sun dauka budurwarsa ce, koda yace musu wai kanwarsa ce jinsa kawai sukayi, don su dai sun san da wata a kasa, da suka fada masa kuwa ya musa daga nan suka rabu dashi.
Yarinya daya ce yake kulawa, itama sai da kyar ta samu ta shawo kanshi yake dan kulata, ita har ga Allah sonsa takeyi, amma shi yace mata baida lokacin soyayya a yanzu.
Ba abinda Kamal yakeyi a makaranta, sai abinda ya kaishi, da ya samu sarari kuma, ko anyi hutu ya dawo gida.
Rayuwar makaranta akwai wahala Aimana, komai sai kayiwa kanka, kaje ka gama daukan karatu, ka dawo kayi wanki ka wanke kwanonika sannan kayiwa kanka girki, komai fa kai zakayi,ba kamar kana gida ba.
Aimana shiru tayi tana sauraronsa, saida taji ya kai aya tukun, taja wani gwauron numfashi kafin tace..
"Kana kokari ma ya Kamal, amma idan aka jure watarana sai labarin, yanzu ya Kamal, kana nufin duk yanmata jami'a, baka da budurwa?"
"To ina zan kai budurwa yanzu Aima, babu soyayya a tsarina yanzu, me nake dashi da zan fara neman yar mutane".
"To ai ya Kamal zaka nema ne, kafin lokacin da Allah zai hore maka, kaga sai kawai ayi a wuce wurin"
"Aimana kenan, bazan yaudari yar kowa ba, saboda ina da kanne mata, kuma baznso wani ya yaudare su ba, ni nasan matata tana nan, a very special one, when the time comes..." ya yanke maganar yana aika mata wani shu'umin murmushi.
Wani irin sanyi Aimana taji a ranta, kenan ya Kamal ma yana jin abunda take ji a kansa, kenan ba ita kadai take kidinta take rawanta ba, itama wani kalan murmushi ta saki masa, suna nan zaune basu ankara ba sai Kiran sallah suka ji, ai da hanzari Aimana ta mike taje ta sallami Ummah ta wuce gida, ta kuwa sha fada a wurin Mama, ita dai hakuri ta bata ta wuce dakinta don gabatar da sallah.
Haka rayuwarsu ta kasance, kullum sai Aimana tasan yanda tayi ta tafi ganin Kamal, koda kuwa da sunan zuwa aika ne, bata taba tunanin me yasa shi baya nemanta ba sai ita ke zuwa gidansu, sabida abunda tasa a ranta kawai yanzu baida dalilin zuwa gidansu wurinta, ita kuma zata iya zuwa gidansu ko da sunan taje wurin su Hamida ne.
Ana cikin haka Daddy yazo da maganar makarantan ta, don ta samu admission, kuma sun bata course da take so, wato medicine, ta zabi course dinne kawai saboda Kamal, don tasan yanzu ba abunda zai sa suyi nisa da juna, tunda makarantan su daya, course nasu daya, kenan department nasu ma dole zai zama daya.
Mama kam har ga Allah bata so haka ba, don sarai ta karanci Aimana sosai, duk wani abunda take tana sane, ta bar tane na dan wani lokaci kafin tayiwa tufkar hanci, sai ga abunda ya bullo kuma, Aimana da Kamal a makaranta daya a wuri daya ba taso haka ba, sabida ta lura Aimana tana wuce makadi da rawa.
Haka tanaji tana gani, akayiwa Aimana registration da komai,sai dai tace bata yarda da zaman hostel ba, saidai a san yadda za'ayi, Daddy bai ki ba, ya bada mota daya da driver, wanda aikinsa kai Aimana makaranta ne kawai da dauko ta.
Aimana ba karamin farinciki tayi ba, game da wannan al'amarin, gata ga Kamal.
Saura sati ta fara attending lectures, Daddy yazo ya dauketa sukaje shopping, tare da adda Nana da tazo, ita ta taya ta zaban kayakin, kama daga takalma, jukunkuna, hijabs, don Mama tace bata yadda da mayafi ba, har sababin kaya masu kyau, turarika, kai da duk wani tarkace da ya mace budurwa zata bukata.
Koda Baba yaga wannan siyayya fada ya dinga yi wai ai yayi yawa, Daddy kuwa yace ba ruwanshi, kar yace zai shiga tsakaninsa da yarsa, washegari kuwa sai ga sabuwar waya dal a leda, wannan kuma sakon ya Junior ne, yace shine gift nashi na tafiya jami'a.
Aimana fa Shar abinta, ba karamin dadin wannan al'amarin taji ba, bugu da kari gata ga Kamal, kullum a wuri daya, ai bata da sauran matsala kuma.....
Hmmm ga Aimana ga Kamal a jami'a, a wuri daya 🤔🤔🤔