Our home
by @autum17
"we are going home" Amreesh ya faɗa tare da jingina kanshi a headrest ɗin kujerar throwing his head back wards tare da lumshe idanun da.
Da katawa Dr Ahmad yay daga igniting ɗin motar ya juyo ya kafe shi da ido, "Matar ka pa"?ya tambaya after a while
Kamar bazeyi magana ba can kuma se yace"zan yi tafiya ne, don't ask any further" yay maganar kamar anyi Mishi dole. Magana is one of the things he doesn't like unless necessary.
Dr Ahmad ya jinjina kanshi kawai batare da ya sake cewa komai ba yay igniting ɗin motar suka ɗau hanya"where are you traveling to?"
Ya tambaya after a long time of silence "China" he replied after a while still idanun sa a lumshe
"Kasan amarya won't be happy idan bata ga ango ba, it's your first night man" buɗe blue eyes ɗin sa yay and tilted his head towards Ahmad wanda yake tuƙin shi kamar ba shi yay maganar ba
"Me first night ya ke nufi"ya tambaya da ita kar gaskiyar shi! Burki Ahmad ya taka which threw them both forward cuz basu da seat belt ba
Ƙara tsuke fuska Amreesh yay se kuma ya ƙara maida kanshi back wards ya lumshe idanun sa jin yadda Ahmad ya kafe shi da ido.
Bayan kusan minti biyar "are you serious man? Bakasan abinda ake nufi da first night ba? Ƙin tan kashi yay hakan yasa Ahmad ya tada motar suna tafiya ya na yima shi tsiya SE ya kalleshi SE ya tuntsire da dariya
Haka har suka iso gidan parking yay suka fito tare suna tafiya " but seriously man, ya za'ay day amarya? And I have told her yau za ayi aure? Ahmad ya faɗa yana tura ƙofar palorn"kayi duk abinda ya dace" ya faɗa yana haye wa sama while Dr Ahmad ya zauna a saman sofa thinking about lots of things
Tunanin sa ya katse lokacin da ƙamshin turaren sa ya bugi hancinsa kafin foot steps ɗinsa ɗaga idanun sa yay ya zube su akan Amreesh that has changed into a black suit that perfectly complimented his white skin ya ɗaure gashin sa into a pony tail as usual his lips looked glossy and more reddish kamar ya shafa man baki fuskar sa expressionless as always SE zuba ƙamshi yake
Ga wani tsadadden wrist watch Black color da yasa. he looked absolutely perfect and sexy....mata da yawa Are dying to have his attention and yet... "Man wannan kyau haka? Kada ƙasa yan mata su zaune" Ahmad ya faɗa with a mischievous smirk on his face!girgiza kanshi kawai Amreesh yay this guy will never change. "Ina akwatin? " It's in the car" he replied walking out. Dama tun tuni ya shirya ma tafiyar at first he wasn't sure amma yanzu he had to.kashe komai Ahmad yay kafin ya fito daga ciki ya kulle ƙofar.ya isa motar shi ya ɗauka masu wayoyin su. Ko da yazo har Amreesh yay settling inside the G-wagon .he got into the driver seat kafin ya tada motar and he drove them away.
"Kwana nawa zakai"? Dr Ahmad ya faɗa his attention on the road "2weeks" he replied slowly looking out the window
Few minutes later SE GA su sun iso airport ɗin they came out together. Suna fitowa wasu jibga jibgan maza guda huɗu came over to welcome come them dukan su sanye suke da baƙaƙen suits hakan na nufin body guards ne
Atare suka yi musu sannu da zuwa,ɗaya daga cikin su kuma ya buɗe Boot ya ciro akwati yay gaba while the other three suka take ma su Amreesh baya.
Dr Ahmad be bar airport ɗin ba har sai da jirgin su ya tashi sannan ya shiga motar sa ya ɗau hanyar asibiti lokaci ɗaya his heart rate increased da yay tunanin Samha
****AURA PRIVATE HOSPITAL****
Sanda Salmah ta koma ward ɗin ta samu Samha tayi Bacci hakan yasa ta zauna a gefen gado holding onto her hand ta faɗa duniyar tunani
'A'a long as Samha will live happy and comfortable life then the sacrifice is worth it! It doesn't matter what she has to bear,she will do it with pleasure ' ta ayyana a ranta tana ƙara kallon fuskar Samha that looked so innocent while sleeping....
Ƙwanƙwasa ƙofar akai ta bada izinin shiga se ga doctor Ahmad ya kutso kai hannun sa riƙe da take away na abinci still cikin kayan daurin aure. Sallama yay ta amsa tana sadda kai,and she greeted him ya amsa tare da tambayar me jiki
Miƙamata take away ɗin hannun sa yay ta karɓa tanay Mishi Godiya . Ajewa tai a gefe cuz it has not been long da ta cinye kazar da ta kawo ma Samha. " An ɗaura auren" ya faɗa after a while,ƙasa yay da kanta Zuciyar ta na mata wani irin what's the future of her marriage? Who is she married to? Me yasa bata tambaya ba tunda farko? Many thoughts ran in her mind tana ƙoƙarin ƙarfa fama kanta guiwa 'as long as Samha tayi farin ciki it's all worth it ' ta raya a ranta
"Allah ya sa hakan shi yafi Zama alkhair" ta faɗa after a while "Ameen" ya amsa yana kai sunansa ga Samha that was sleeping peacefully ɗauke idon sa yay
Bayan ya jujjuya maganar cikin ransa yace"zaki tare ne idan an sallame ku daga asibiti" faɗuwa gaban ta yay da sauri ta kalle shi , shima ita yake kallo
Tana wasa da hannun Samha dake cikin nata tace"zan iya tafiya da Samha pls" ta tambaya tana marairaice fuska kamarzata fashe da kuka
Jin jina kanshi yay sannan ya miƙe ya fita daga ward ɗin
Tana fita Samha ta fisge hannun ta hakan yasa Salmah ta kalle ta with shock written all over her face. Tun lokacin da Dr Ahmad ya shigo ya farka ɗan haka she heard everything
"Mahmah aure ki kayi? Samha ta tambaya tana kafe ta da idanu
Jinjina kanta tayi kafin ta fara mata bayanin what led to it hawaye shsɓe shaɓe a fuskar ta.itama Samha kukan take "why would you sacrifice your life for me? Idan da wata rana na butulce miki? Do I even deserve your sacrifice?idan da na...." Da sauri Salmah ta rufe mata baki tana girgiza mata kai at the same cleaning her tears "insha Allah bazaki butulce min Sam" ta ƙarashe maganar tana rungumota
"Ina kaunar ki sosai anty na" nima ina kaunar ki sosai ƙanwata"
After a while they disengaged from the hug and began talking about something else to relieve the atmosphere.
Se bayan laasar Dr Ahmad ya dawo hannun sa riƙe da ledojin abinci da kuma kaya be wasn't sure idan kayan za su masu but they should manage. Bayan ya ƙwanƙwasa am bashi izinin shiga ya tura ƙofar ya shiga. Da Samha ya ci karo Wadda kallo guda ta mai ta ɗauke kai. Shi ko wane irin masifaffen bugu zuciyar shi keyi ba ƙaƙƙauta wa. Mazewa yay ya idasa shigowa ya ajiye kayan da ke hannun shi
" Ina yayar ki"
"Tana baye"
"Okay"
Wayar shi ya ciro ya fara latsawa amma he wasn't understanding anything hankalin shi bakan Samha wadda tunda ya shigo take cika tana batsewa for no reason
Salmah CE ta buɗe ƙofar toilet ɗin ward ɗin ta fito ganin Dr tayi mashi sannu da zuwa ya amsa yana nuna mata kayan da ya shigo dasu sosai tai Mishi Godiya.
Miƙewa yay ya fita daga ward ɗin da kuma asibitin gabaki ɗaya
Duba kayan suka shiga yi iya da samha abayas ne masu kyau of different colors and sizes.
Kayan sun yi masu kyau sosai
Acikin kwanakin da suka biyo baya kullum sai Dr Ahmad ya zo ya duba su har yau da yakasance ranar sallamar su
He was there, shima ya karɓar musu takardar sallama.at around 4 suka bar asibitin a tunda suka ɗau hanya ba wanda yayi magana samha na kwance ajikin Salmah while he was focused on the road tuƙin shi yake once in a while glancing at them ta madubi
Se da suka ɗan yi nisa da asibiti sannan Salmah ta faɗa Mishi tana so ta dauki wasu abubuwa from their house,ba musu ya kai su har bakin ƙofa ya dire samha zata fita tace mata ta zauna she will bring everything badan taso ba ta koma cikin motar. Kallon ta yaya ta cikin madubi daidai ta ɗago suka haɗa ido
Yar harara ta sakar Mishi tana murguɗa baki ɗan haushi yake bata he wants to snatch her sister from,ita a tunanin ta shine mijin
Shima kauda nashi idon yay to a different direction
Salmah na shiga cikin gidan ta tattara musu all they will need cikin akwati ɗaya sannan ta fito,yana ganin ta ya buɗe mata boot tasa akwatin sannan ta shiga makwabtan su tabada mu kulli don dama gidan haya ne. Sannan ta dawo tashi ga motar sannan ya tada and they left. They felt a bit emotional duk da basu wani daɗe a unguwar ba.
Da kusan ƙarfe shida da rabi suka iso residence ɗin. Sosai gidan ya burge su tun daga waje and it's a quiet neighborhood kamar dai irin na Turawa, sannan akwai ita ce ina the sides of the road ga soke of the leaves sun fara canja color from green to orange signifying autumn
Me gadi Ya buɗe musu gare suka shiga nan ma dai sai kalle kalle suke Bayan ya parkar shi da kanshi ya buɗe musu ƙofa and they stepped down hannun su riƙe dana juna yana gaba suna biye dashi
Buɗe ƙofar Apartment ɗin yayi ya kunna wuta ya shiga sannan ya musu izinin shiga cire takalman su sukayi suka aje inda ya ake nashi
Ga wani daddaɗan ƙamshin daya bugi hancin su bayan haɗuwar wurin they were impressed.
Upstairs yay leading ɗin su to the left hand side ya shigar da su ɗakin dake bayan nashi
The room was spacious and beautifully decorated. Bayan nan ya fita ya basu wuri to freshen up
Kulle ƙofar sukayi sannan Samha tayi tsalle se gata saman gado Salmah also joined their joy knew no bound "I can't believe it, this is our home" Salmah ta faɗa the two of them facing ɗin ceiling "me too" samha ta faɗa kallon juna sukai suka sakar ma juna murmushi!