KUSKURE

005

by @takwalam

KUSKURE

005

✍️ Ayshakwalam

Nayi murnar zuwan Hajiyan Atawami, da sauri na shiga gidan haka parlon ma, tana zaune Saman carpet su Safar duk sun baibaye ta, Maman su ma na zaune gefe tana dama fura, da sallama na shiga a Baki na, ta dago da murmushi Saman fuskar ta, na karaso da sauri na fada jikin ta nima tare da fadin

"Hajiya sannu da zuwa! Sannu da hanya"

Ta shafa Kai na tare da fadin

"Sannu Inaaya, ya makaranta?"

Na amsa da alhamdulillah kafin na matsa gefen Maman Safar nace mata na dawo, ta amsa to sannan naje daki na na shirya har da alwala kafin Kuma na fito na dawo na zauna cikin Yan uwana, bayan mun idar da sallar maghrib Baban Safar ya dawo daga aiki, duka su hudun suka fara rige rigen me karbo masa jaka da Kuma rungume shi, karshe Fahad yayi wannan nasarar Dan haka yayi musu gwalo ya kama staircase dan ya Kai, ina ta kallon su, duk lokacin da na gansu sun sake da mahaifin su ko mahaifiyar su se naji wani iri cikin zuciya ta, se na ayyana inama dai nima haka nake da nawa iyayen, inama ni ma nawa uban da tawa uwar suna nan nima da haka zan dinga yi da su. Karasowa inda muke Abban yayi, ya durkusa gwiwoyin shi a kasa ya gaishe da mahaifiyar shi, ta amsa da kulawa kafin ya gyara zaman shi wanda yasa na masa sannu da zuwa ban ma Jira ya amsa ba na koma daki dan su samu suyi hira. Sallah nayi sannan na kwanta na lumshe idanuna, se can Kuma nayi firgigit na tashi na zauna, na janyo jaka ta Dan dakko assignment din da aka bamu na physics, to amma Banga littafin ba, Hakan ya tabbatar min na bar shi a makaranta, na lumshe idanuna ina hasaso yadda zanyi goben idan naje, crap! Se kuwa na tuna guy din dazun, na danyi pouting kadan tuna yadda yasan komai akai na Amma ni ko sunan shi bansani ba, na dan sake tsaki se kuma na mike na fito parlor har lokacin Hajiyan Atawami da Abba suna ta Hira, na wuce su na zubo abinci Dan kadan zan wuce, Hajiya tace

"Inaaya, wannan Dan abincin zaki ci? Shiyasa ba Kya kiba kuwa"

Na danyi murmushi kadan tare da satar kallon Abba da ya zuba min idanun shi, nace

"Ya ishe ni, bana Jin yunwa"

Se ta gyada min Kai, na koma daki Abu na, ta dubi Abba tace

"Tana dai zuwa wajen dangin uwar ko?"

Ya dan shafa Kai yace

"A'a gaskiya Bata zuwa?"

Hajiya tace

"To saboda me? Akan wanne dalilin?"

"Hajiya ai zai zama kamar ana raba mata hankali, Amma ni fa ban hana su zuwa su ganta ba"

Hajiya tayi ta kallon shi da mamaki, tace

"Wanne irin tunani ne wannan? Raba mata hankali kace? Su wadannan da kake bari suke tafiya har Gusau ba kai tunanin zaa raba musu hankali ba? Se ita? Yar marainiyar yarinya ka raba ta da dangin uwar ta, to aikuwa gobe zanje na Kai ta su ganta ta gansu!"

Haka kuwa akai washegari bayan sallar jumaa, ni da Hajiya muka shirya Dan zuwa Rijiyar Zaki, Safar da taji labarin tace ai kuwa itama zata bimu, a gaban Hajiyan Atawami Maman su Safar tace

"A'a ba zaki je ba, kinsan ai kitso zaki je yau ko?"

Hajiya ta kalla Maman su Safar tace

"Ki barta mana muje tare , acan ma se ayi mata kitson kawai"

Ba yadda zatayi haka ta barmu muka tafi, gidan babban gida ne, like bakwai number of mutanen da suke cikin gidan ba, a'a girman ginin gidan, tun da muka shiga ake ce mana sannun mu da zuwa, har aka kaimu parlor, itama hajiyar tana zaune tana cin gujiya wadda muka fi sani da banbara nut, ni dai idan nace muku nayi shekara biyar kafafuna Basu taka gidan ba banyi karya ba, suma Kuma sun jima Basu zo ba, se kayan sallah da ake kawo min duk azumi da Wani lokacin suyi min shopping su kawo, Amma baa taba bani ba a bakin iya nake ji. Hana rantsuwa sukan je islamiyya su ganni Wani lokacin Kuma har makarantar boko suke zuwa gani na. Dan akwai lokacin da akai irin haka suka je gani na a islamiyya, suka bani kudi da su chocolate, ni Kuma na kawowa Maman Safar gida na fada mata Uncle Hafiz da Hajiya suka kaimin, kunsan me akai? Cire ni akai daga islamiyyar Baki Daya, se yanzun nake fahimtar ko dai basa son Muna mu'amula da su ne? To Allah ma sani!

"Lale!lale! Maraba da zuwa hajja Nafi, barka da zuwa. Ke da Inaaya? Ga Kuma safara'u"

Na kalla Safar da tuni ta cuno Baki, na danyi murmushi because I know how much she hate to be called Safara'u, ita dai tafi son ace mata Safar, se da muka Jira suka gama gaisawa kafin muka gaishe ta, dattijuwar nan har da kuka tana fadawa Hajiyan Atawami abinnda Abban su Safar yayi mata akai na, ni da Safar Muna ta kallon Wani Indian film da ake nunawa, ni hankali na kacokam yana kan film din, ita Safar ce dai hankalin ta ya rabu gida biyu, half wajen kallo dayan Kuma tana sauraran abin da suke fada. Kunsan Wani Abu da ni ? bani da wayo, duk wannan abun da akeyi Yana damuna quite sure, Kuma ina rikewa cikin zuciya ta, amma Kuma bana tsayar da hankali na na fahimci what's really happening, na sakawa zuciya ta bani da gata, bani da kowa, Abba da yake ubana na jima da cire zuciya ta akan shi, saboda na sakawa Rai na baya sona baya kaunata so I Don't even yearn for him, ita Kuma Safar she's clever, komai da ake a gidannan she's current, bincike a gurin Safar kamar yar jarida, Babu Wani abu da ake a gidannan da baya wucewa ta idanun ta, she's very observant!

Kafin awa biyu tayi duk 'Ya'yan Hajiya se da suka zo da suke cikin garin Kano, aka kafa lallaba ni, aka tsefe mana Kai aka wanke aka mana kitso, akai mana kunshi a kafar mu sannan da zamu tafi kaya dai kamar me, Muna zuwa gida tun da Maman Safar ta ga wannan aiki ta bata Rai, fuskar ta a murtuke ga Babu damar fada ko masifa tun da kuwa hajiyar Atawami na Nan, Abban su Safar na dawowa ta same shi da maganar

"Kaga Abban Safar ni dai gaskiya bana son abin da yake faruwa a gidannan..."

Ya aje pen din hannun shi yace

"Me ya faru Kuma?"

Nan ta fara fada masa munje Rijiyar Zaki ita Bata son haka, ita tana ruko na tsakanin ta da Allah , ita Bata son a raba mata kan Yara, wasu su gane ba yaranta bane ba gaba daya, ita kaza, ita can ita dai... Haka tayi ta fama shi Kuma Yana ta kallon ta har ta gama, yace

"Kar ki damu ai ni nasan zuciyar ki nasan me kike nufi, ki Kara hakuri Inaaya ba zata Kara barin gidan ki da sunan zuwa Wani gurin ba se makaranta"

Taji dadi kuwa kamar yadda take so, ko da yaushe ya dinga goya mata baya akan kudirin da take da shi akai na. Kwanan Hajiyan Atawami goma kafin ta tafi, a wannan kwanakin da take gidan mu, komai Yana tafiya daidai dan ko kwana a daki na take kwana, tare muke komai haka ta tafi ta barmu da kewar ta.

***

Kunsan mata kala kala ne, kowacce mace akwai halin ta, akwai yadda take tafiyarr da rayuwat ta. Akwai matar da zata iya tashi kawai taci abinci taji ya kamata ta fara zargin mijin ta, ko da kuwa shi wannan Mijin bai yi abun da zata zarge shi din ba, akwai Kuma irin su Habiba Wanda tsabar yardar da tayi masa bata iya ganin abin da yake akwai, Bata iya ganin laifi shi, Bata iya sawa zuciyar ta yayi Wani abun, a kullum a idanun Habiba yallabai is perfect, shiyasa ko zama kukai da ita na mintina biyar zaku ji ance yallabai yace, yallabai yayi kaza, yallabai yallabai, sunan yallabai is unending a bkin ta.

Shirin biki ya cigaba da gudana tsakani na da Aliyu, ban sani ba bansan cewar matar shi Bata da masaniya akan auren ba, to koma na sani me zanyi? Wannan ra'ayin shi ne shi ya zaba ya boye mata kada ya fada mata, Amma nima a nawa bangaren se da na binciko matar shi, ina son nasan wacece zanyi zaman gidan aure da ita, dana dinga bincike se da na Nemo komai nata, yaushe sukai aure? Yaranta nawa? Yar ina ce? Makarantar da tayi? Inda take aiki duk se da na bincika. Bayan na kammallà Abu daya ne baiyi min ba shi ne yadda aka fada min akace mijin ta wato Aliyu Yana mugun son ta, wasu since min ma ba zai iya Kara aure ba, wasu suka ce ai ba haka ta barshi ba, saboda to them irin wannan son baya existing a duniya Amma ni Kuma da na sake bincike akan halayen ta se naga bana zata mata bin malamai ko bokaye, na fahimci tsantsar biyayya ce ta saka yake Jin zai iya gasa hantar sa ya Bata ta ci, se naji ance wai dangin mijin ta basa son ta ko kadan, se Yan tsiraru da suke sonta a bayan idanun surukar ta. To daga Nan nace bari ni na fara nawa yakin daga kansu, ba yadda zaayi naje na tarar ta gama kankane ko ina.

Safiyar lahadi na tashi na shirya nayi wanka, na shirya cikin abaya baka, ban wani yi kokarin kwaliyya ba kawai na shafa mai na wuce kitchen saboda ina son creating content dina na sati me zuwa, komai ba hada shi yadda ya kamata kafin na fara shooting videos dina, menu din farko da nayi shi ne farfesun Naman Kai, se nayi naan bread me taushin gaske, nazo nayi drink, Amma ina gamawa na gaji sosae I couldn't continue the shooting, dole na hakura na fara packaging abincin , bayan na kammallà na kira me delivery na bashi address din Hajiya wanda Aliyu ya turo min, cikin sa'a ana Kai abinci ita Kuma Habiba taje gidan gaida Hajiya, tun da aka aje basket din take kallon basket din komai da komai har yadda ake wrapping irin na Wanda yallabai din ta ya aika mata ne, tana zaune akan zuba mata farfesun cikin bowl, ta girgiza kai tace da Hajiya

"Na koshi alhamdulillah"

Baa sake mata tayi ba aka dauke daga gaban ta aka bawa yaran Lailah da suka zo, tayi shiru tana ta kallon yadda kowa ke rawar jiki akan abincin, se ta dubi Hajiya tace

"Zan koma Hajiya! Dama nace na biyo na gaishe ki"

Tayi murmushi tace

"Na kuwa gode!"

Daga haka ta dauki jakar ta ta tafi gida zuciyar ta na ta sake sake!

KUSKURE ba kyauta bane ba, ma'ana is not free.

Pay N1k to

3091721807

First Bank

Aisha kwalam Hassan

Send evidence of payment to

***

And get access to our telegram group or you can access it on Arewa books.

©Oum A'eesh