💔NAUYIN BAKI👄💔 Na Uwar Batoorl
Page 7 _ 8
💔NAUYIN BAKI....👄💔
Na
Uwar Batoorl.
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍
🅿️ 7 _ 8
⭐️
Kwana ɗaya, kwana biyu.... har aka ci kwanaki shida masu kyau, Sadeeq na a kwance maƙale da oxygen, ba abinda ya sauya kuma ba wani ci-gaba da aka samu, duk da kuwa likitoci na matuƙar ƙoƙarinsu, wajan kula da shi da ba shi duk wata taimako da ta kamata, kuma Umar na nan a tare da shi a ko da yaushe, sai Abba sun zo da dare sannan yake tafiya gida ya je yayi wanka yayi uzurinsa ya dawo, su kuma sai su tafi, dan shi yake kwana da Sadeeq ɗin, watarana Sa'ad ya taya shi, watarana kuma Khalid ke taya shi.
A gefen ma'aikatarsu kuma, Khalid ke ƙoƙarin zuwa yana duba duk abinda ya kamata, Umar kuma daga asibitin yake duk abinda zai iya yi a waya ne, ko ko a system, don shi ne MD na companyn nasu dama.
Ɓangaren su Umma kuwa suna iya ƙoƙarinsu wajan addu'oi, sadaka da sauransu, kuma daga ita har Mama suna kan gyara Sadiya wacce a yanzu bikin ke matsowa, ya rage sati biyu, sai dai a kwanakin kaf Sadiya bata da kuzari, duk fushi take, fama take da damuwa a kan rashin zuwa ta gano Yaya Sadeeq nata, Umma da Mama sun zuba mata ido ba wanda ya ce ta shirya a je da ita, hakan ba ƙaramin ƙara ƙona mata zuciya yake ba.
Haidar ma yana amsan nashi rigiman, domin duk ta birkice mishi akan zuwa ta dubo Yaya Sadeeq, ya ƙoƙarta wajan ƙiran Yaya Umar a waya ya tambayi asibitin da suke zai zo dubiya, amma Yaya Umar bai sanar mishi ba dan Mama ta hana shi, sarai sun sani muddin aka sanar mishi to zai kwashi Sadiya ne su je asibitin, kuma ita da asibiti ba shiri suke yi ba sam-sam.
Sadiya banda kuka da damuwa ba abinda ta sanya wa ranta, kuma fushinta da Mama ya fi yawa shiyasa ma ta tattara ta koma wajan Umma, duk da a can ɗin ma ko da yaushe tana ɗaki ba fitowa take yi ba, yau da ya kama Lahadi zai cika sati guda ciff da kai Sadeeq asibiti, Sadiya tana jin fitan Abba da Umma zuwa asibiti, ta fito palourn jiki ba ƙwari, a sanyaye take tafiya tana son ta tafi gidan Mama ne ta kulle kanta a ɗaki, ko in aka ga tana shirin mutuwa za a barta ta gano Yaya Sadeeq nata, tana ƙoƙarin ficewa a palourn ta tsinkayo muryan Khalid, dan shi yau bai je asibitin ba saboda a gajiye matuƙa ya dawo daga company jiya, wuni yayu hutawa yau, yana ganin Sadiya cikin zolaya ya ce, "Sady amarya sai ina? Kinsan dai Yaya Sadeeq ya hana ki sintiri da darennan ko? To a kunnenshi kuwa."
Sadiya tana jin abinda Khalid ya faɗa sai ta fashe da kuka, kuka take na kewan Yaya Sadeeq da hanata zuwa ganinshi da aka yi, kuka take na kewan duk wasu kulawa da yake bata da dokoki da sauransu, a kwanciyansa ciwon nan ba za ta iya tuna dokarsa nawa ta take ba, ya hana ta fita daga zaran magrib tayi, amma kuwa tana fita daga gidan Umma zuwa na Mama, ya hana ta zama ba ɗan kwali amma haka take zama yanzu abinta tunda ba idonsa, ya hana ta yawan waya-waya da danne-danne, amma yanzu sai su raba dare suna waya da Haidar, maganan karatun Ƙur'ani kuwa ta kwana biyu bata taɓa ba ma, Islamiya kuma daman su Umma ne suka ɗaure mata wajan zama; a kan ba za ta je ba tunda suna gyaran jiki, duk da kuwa ya ce ta dinga sanya hijabi da hula p-cap ta je, dan p-cap ɗin zai tare mata ranan da ba'a so ya daki fiskanta, dokokin Yaya Sadeeq ba za su irgu ba, domin ya zame ne kaman uwa da uba a gare ta, yana shagwaɓa ta amma yana tarbiyartar da ita, babban yaya madadin uba.
Khalid jin Sadiya bata bashi amsa ba sai kukanta da ya tsananta, da sauri ya ce, "Allah ya huci zuciyarki ƙanwar Yaya Sadeeq, ni a ta ya ma zan faɗa mishi bayan har yanzu bai farfaɗo ba."
Sadiya ƙara kukan ta yi, tare da juyowa ta dawo ciki, a kan kujera ta zauna tana cigaba da kukanta, Khalid da ya ga kukan ba mai ƙarewa bane, sai ya ce, "Sady wai kukan me kike yi ne haka?"
Sadiya cikin kuka ta ce, "Yaya Khalid su Mama sun hanani naje na kalli Yaya Sadeeqna."
Numfashi Khalid ya sauƙe domin ya ɗauka ko wani abun ne ya faru, duk da ya san wannan wani abu ne ga Sadiya ko Yaya Sadeeq, saboda shaƙuwansu da yanda suka damu da juna, a kan Sadiya sai Yaya Sadeeq ya ɓata da kowa, sai dai kuma zuwan Sadiya asibiti ai ba mai yiwuwa bane, tunda ita ba ƙaunar asibiti take ba, dan akwai lokacin da Yaya Umar yayi hatsari, yanda ya jikkata ma an ɗauka ba zai rayu ba, domin motar da yayi hatsari da ita bata sake moruwa ba, ko da aka sanar da gida cikin tashin hankali da ɗimauta duk aka ɗugunzuma aka tafi FMC PLATEU har da Sadiya, amma da yardan Allah ana shiga asibitin tun ba a isa ɓangaren da Yaya Umar yake ba, Sadiya ta kama rawan jiki tana abu kaman wacce za ta shiɗe, sai da aka fice da ita a asibitin sannan ta dawo dai-dai, ita haka halittarta yake tana matuƙar tsoron asibiti sam-sam bata son asibiti, domin da farko an ɗauka ma ko aljanune gare ta, amma anmata ruƙiya ba komai, kawai bata son abu da asibiti ne ita, maimakon ta dubo mara lafiya sai ita ma ta kama yin cutar, dan muddin ta shiga cikin asibiti ta fito to sai tayi ciwo a gida, duk tsananin ciwonta kuma bata wuce chemist, ko me zai same ta to a gida ake jinyarta, har a gama treatment ta warke.
Khalid bayan ya gama dogon tunaninsa, cikin sigar lallashi ya ce, "Sadiya kiyi addu'a kawai Yaya Sadeeq ya farfaɗo da wuri ya dawo gida, kin ga zuwanki asibiti wata matsalarce babba ma kuwa, kuma yanzu ke da kuke ganiyar shirye-shiryen biki in ba Allah ya aiko ba ya kama dole ai ba abinda ake so ya same ki, mutane sukan ce waɗanda suka kusa aure tsautsayi na bibiyarsu."
Girgiza kai Sadiya tayi cikin kuka ta ce, "In sha Allah ba abinda zai faru Yaya Khalid, dan Allah ni ka kaini, ko ka faɗa mini inda aka kai shi sai Haidar ya kai ni, ko kuma ma naje da kaina na dawo lafiya."
"A'a Sadiya, ni ba ruwana, idan wani abu ya faru ai Umma kaɗai sai ta cinye ni ɗanye, idan Yaya Sadeeq kuma ya ji labari kinsan zai iya ball da ni a kan haka, kwanaki da kika sa na taimaka miki kika je gidan su ƙawarki har kika kai bayan Magrib, kina sane ai sarai marina Yaya Sadeeq yayi a kan haka, to ba ruwana."
Sadiya kuka ta cigaba da yi tana roƙon Khalid, shi kuma ya dage ba ruwansa, daga ƙarshe cewa yayi, "Kinga kiyi maza ki tashi ki tafi gidan Mama, idan su Abba sun je to Yaya Umar yana dawowa gida yin wanka, dan haka sai ki mishi kukan ko zai tausaya miki ya barki ki je."
Da sauri Sadiya ta miƙe tare da gode wa Khalid da dabaran da ya bata, ficewa tayi dai-dai tana isa ƙofan gidansu, dai-dai Umar ya fito a mota ya kulle zai shiga gida, da mamaki ya juya yana kallonta jin yanda take kuka kaman an mata mutuwa, ba tare da ya ce mata ƙala ba ya juya ya shige gidan, ita kuma ta mara masa baya tana kan kukanta, duk da a zuciyarta addu'a take Allah ya ɗaurata a kan Yaya Umar ya ce zai tafi da ita, dan ta fi kowa sanin halin Yaya Umar na zafi, sam-sam baya raga mata, idan ya raga mata to ta ci albarkacin Sadeeq ne, amma shi sam baya ɗaukan rigimarta da shiriritarta, shi da Mama, Umma da Yaya Sadeeq ne daman suka shwagaɓa ta, Yaya Umar bai sha mishi kai ba yanzu yayi ball da ita.
Umar na shiga palourn, Sadiya ma ta shigo da kukanta, har zai wuce hanyan ɗakinsa sai kuma ya tsaya ya dakata, fiska a haɗe ya ce, "Ke kukan me kike wa mutane? Uban wa naki ya mutu?"
Sadiya cikin ɗan tsoro-tsoro da shagwaɓa-shagwaɓa ta ce, "Ya..yayyy...Yaya Umar ina..ina..inaso ne naje na kalla Yaya Sadeeq, kuma..kuma..kuma sai Um..Umma da Mamaa suke ƙi, kuma wallahi inason na ganshi, inban ganshi ba zuciyata kuma zan mutu", ta ƙarishe faɗa cikin rawar murya, ga hawaye masu rauni da ke zubo mata.
Umar kallon baki da hankali ya yiwa Sadiya, sannan ya wuce ɗakinsa, ya watsa ruwa ya sanya jallabiyansa ya feshe turaruka masu daɗin ƙamshi sannan ya fito, Umar ma ba baya ba wajan haɗewa da kyau da suffar jarumta, hasken fatan Umar irin na Sadiya, hatta da wushiryasu iri ɗaya dan wajan marigayin mahaifinsu suka gado, sai dai shi Umar bai da dimple, wannan kuma a wajan Mama Sadiya ta gado, Umar dogo ne mai tsayi da ƙaƙƙarfan jiki ga faɗin ƙirji, yana da ƙira matuƙa mai kyau da ɗaukan hankali, suna ɗan kama da yanayi na jini da Sadiya, amma dai kaman ba sosai ba, Umar yana da zafi sosai, kuma bai cika haƙuri ba, amma yana da biyayya, kuma yana da kiyayewa yayi abinda ya kamata, yana da magana sosai amma banda da Sadiya, domin a wajan Sadiya ganinsa take kaman dodonta, dan tana yin gar-gar zai make ta baya kuma son reni, albarkacin Sadeeq kawai take ci, amma duk da haka idan tayi wani abun idan ya aika mata da wani irin kallon za mu haɗu ne, a take za ta sha ruwan jikinta ta nitsu, sam-sam shi da Mama basa ɗaga mata ƙafa.
Sadiya tana zaune a palourn tana kuka da kuma ƙarfi, dan ya jiyo, har ya fito tana kukan, bai bi ta kanta ba ya juya ya nufi fita, sai da ya kusa fita a palourn sannan ya dakata ya ce, "Ki rufe wa mutane baki kamun na ɓaɓɓallaki, in asibitin kike son zuwa to ki shirya maza gobe za a kawo ki, kuma idan kika yi halinki da kika saba a asibiti, ina mai tabbatar miki da sai na yi ƙuli-ƙulin kubura da ke, tun da ance miki zaman daɗi ake a asibitin da muke fama", yana gama faɗa ya fice, cikkn jin haushin iyayinta, akan me simple and short ta buɗe baki ta roƙa za ta asibiti, sai ta kama kuka kuma akan me? Me aka mata? Uban wa ya mutu? Yarinya kawai ta zama kaman wata goyon gauro.
Sadiya hamdala tayi tare da saurin haɗiye kukanta, farinciki take gobe za ta je ta gano Yaya Sadeeq nata da yardan Allah, da haka ta miƙe ta wuce ɗaki, bata jima ba da shiga ɗakin ba ta jiyo sallaman Mama, fitowa tayi tare da mata sannu da dawowa, Mama da ido take binta da kallo har ta fice, sannan ta girgiza kai tana addu'an shiriya ga tilon ƴar tata, tare da fatan Allah ya sa idan ta shiga gidan aurenta ta gyaru kuma ta shiga ne sai mutuwa.
Sadiya tana shiga palourn ta samu Abba da Umma a zaune, Sa'ad na daga gefe, don yau shi ne a gida, Khalid sun koma tare da Yaya Umar za su kwana can.
Sadiya kanta a duƙe ta shigo da sallama, duk suka amsa mata, ɗan rusunawa tayi tare da faɗin, "Sannunku da dawowa Abba da Umma da Yaya Sa'ad."
Amsawa duk suka yi suna murmushi, ita kuma ta miƙe ta cigaba da tafiya za ta haura saman bene, Abba ne ya dakatar da ita, yana murmushi ya ce, "Auta zo nan abinki."
Idanuwanta cikowa suka yi da ƙwalla, sannan ta juyo a sanyaye kanta a ƙasa har ta ƙaraso gaban Abba, tsugunawa tayi tana ƙoƙarin mai da hawayenta, amma sai da suka gangaro.
Abba ɗagota yayi tare da zaunar da ita a gefensa, yana faɗin, "Share hawayenki Auta, faɗa mini wa ya taɓa ki, dan anga Yayanki ba lafiya za a ke cin zalinki ko, to Abbanki yana nan."
Sadiya fashewa tayi da kuka, tana kuka ta ce, "An hana ni naje na ga Yaya Sadeeq Abba."
Shafa kanta Abba yayi, tare da cewa, "Kwantar da hankalinki Auta, ai baki sanar da Abba ba shiyasa, amma kinga yanzun da magana ta iske Abba, ai zuwa ya zama dole, babu kuma mai hana ki, kije ki kwanta kiyi bacci hankali kwance, gobe in sha Allah ni da kaina zan kai ki, ki gano Yayanki, wa ya isa ma ya hana Sadiya zuwa ga Sadeeq."
Ɗiff! Haka kukan nata ya ɗauke ta ja ajiyan zuciya, tare da sakin murmushi, da siririyar muryanta da kukan da ta kwashe kwanaki tana yi ya cinye, ta ce, "Nagode Abba, Allah ƙara rufin asiri da arziƙi."
"Amin Auta, Allah ya muku albarka."
Da amin duk suka amsa, sannan Umma tana murmushi ta ce, "Shikkenan fushi da ƙunci sun ƙare, Abba ya kashe case ko?"
Sa'ad dariya yayi ya ce, "Ai kuwa dai Umma, dan tun da Yaya Sadeeq ya kwanta a asibiti, Sady ke fushi da ƙunci, ƴar dariyarnan tata da tsokana duk babu, ƴar rawan kai irin ta amaren da suka kusa aure duk babu, wa zai kalli Sady ya ce aurenta nan da 2 week's?"
Abba danƙwalon Sa'ad yayi tare da cewa, "Mai anguwan garinku Sa'adu, ka ƙyale mini Auta da zolayarka, kuma Abbanta yana kallonta ya hangi ƙyalƙyalin alaman da ke nuna ta kusa aure."
Sadiya hannayenta ta sa ta rufe fiska cikin jin kunya, sannan ta miƙe ta haura sama tana ƴar murmushi, ga farin cikin za ta je ta gano Yaya Sadeeq, ga batun aurenta da Haidar nata, da idan mutum yayi sai taji kaman ta mishi kyauta.
Sa'ad ma miƙewa yayi ya shige ciki yana dariya, dan ya kwana biyu bai ga Sadiya a irin shauƙin ba.
Umma dubanta ta mayar ga Abba, cikin magana da ladabi ta ce, "Abban Sadeeq, kana ganin ba wata matsala a zuwan nata?"
"To matsalar da rashin zuwan nata yake haifarwa ai ya fi na zuwanta, dubi yanda yarinya duk ta zama kaman ba ita ba, damuwa duk ya lalatar da kumarinta da kuzarinta, kawai ta je koma menene Allah ya kawo da sauƙi, balle ma a jikina nake jin in sha Allah ba abinda zai faru sai alkairi."
Umma jinjina kai tayi ta ce, "Allah ya sa haka."
"Amin Ya Rabbi Halimatu", faɗin Abba yana sauƙe numfashi.
Daga haka duk suka yi shiru na mintuna, sannan Abba ya miƙe ya nufi haurawa sama, Umma ta tashuwan tayi ta rufa masa baya, suka wuce ɗakinsa kai tsaye.
Sadiya cikin tsananin shauƙi da farinciki tayi waya da Haidar yau, kuma ya fahimci hakan a yanayinta, hakan ya sanya bai yi ƙasa a guiwa ba wajan tambayan dalilin farin cikin, ta sanar mishi Abba da Yaya Umar sun amince za ta asibiti, shi ma ya taya ta murna matuƙa, duk da gefe guda na zuciyarsa tunani ne na Allah ya sa kar komai ya same ta, dan shi ma ya san lalurarta ta zuwa asibiti, haka dai suka ƙarishe wayansu cikin ƙaunar juna, suka yi sallama, Sadiya ta kwanta cikin farinciki matuƙa, har mafarki tayi Yaya Sadeeq ya farka ya dawo gida.
***MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA ***.**
⭐️
PLATEU SPECIALIST HOSPITAL
ABUBAKAR SADEEQ POV
***
Umar dama tun da safiya Sa'ad ya sanar da shi batun Sadiya, hakan ya sanya da ya koma ta yi rigimarta ya ce ta shirya, dan daman ko bata yi rigimar ba zai ce ta shirya ɗin.
Bayan dawowansa su Abba sun tafi, shi da Khalid ne zaune a ɗakin da aka kwantar da Sadeeq, Khalid ya ce, "Yaya Umar."
"Na'am Khalid", Umar ya amsa idanuwansa na kan system da ke gabansa yana dudduba ayyukan company.
Khalid ɗan sosa kanshi yayi sannan ya ce, "Yaya Umar please a bar Sady ta zo ta duba Yaya Sadeeq, baka ga ba yanda ta koma ba, duk ta zama abin tausayi har Yaya Sadeeq da ke kwance jinya ma ya fi ta kyan gani, kuma ita da ake shirye-shiryen aurenta ai ya kamata a kalleta da kumari ta yi ɓul-ɓul, ba damuwa ya ramar da ita ba, dan Allah Yaya Umar ka yiwa su Mama magana su barta ta zo, na san idan kai kayi magana za su amince."
Umar kallon Khalid yayi fiisha, sannan ya ce, "Da alama dai daman kai ka turo mini ita ta dinga yi mini halinta na kukan banzan nan ko?"
Girgiza kai Khalid yayi da sauri yana faɗin, "Ba ni bane Yaya Umar, ni banma san ta fice a gidan ba, dan ko komawana daga wajan aiki na jiyo motsinta ne daga kitchen za ta wuce sama, amma ko magana ba muyi ba."
"Ya yi kyau to, gobe kamun ka wuce wajan aiki za ku taho tare ka aje ta, ka amshi saƙonnan sai ka wuce", Umar ya faɗa har sannan idanuwansa na kan system da ke gabansa.
Khalid washe baki yayi cikin murnan hankalin Sadiya zai kwanta, ya ce, "Allah ya kai mu goben Yaya, Allah ya bai wa Yaya Sadeeq lafiya wadatacciya."
"Amin", Umar ya amsa a taƙaice ya cigaba da aikinsa.
Khalid sosai ya ji daɗi, dan a duniya suna ji da Sadiya suna sonta, kwatankwacin yanda Yaya Sadeeq ke son ta da kulawa da ita, a cikin Abba su huɗu ne kawai, Yaya Sadeeq, Aunty Khausar, Yaya Sa'ad sai kuma shi Khalid, sam basu da ƙaramar ƙanwa mace, shiyasa shigowan su Sadiya rayuwansu, ya sa duk suke ji da ita suke ƙaunarta.
Har kaman zai ƙira Sadiya ya mata albishir, sai kuma ya fasa ya cigaba da danna wayarsa kawai.
Washe-gari da wuri Khalid ya tattara abinda zai tafi gida da su, ya tafi, yana zuwa ya samu har an kusa kammala abun karyawa, kasancewan yana son shiryawa da wuri, bai tsaya bi ta yiwa Sadiya albishir ɗin ba tukunna ya wuce yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya, Khalid mai kyau ne, matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da huɗu.
Khalid ya kammala ya fito kenan, ya samu Abba, Sa'ad da Sadiya har Umma su ma sun fito a shirye tsaf, gaishe da Abba da Umma yayi, sannan Sa'ad, sai ya dubi Sadiya yana faɗin, "Ke kuma irin wannan gayu haka sai ina haka? ƙanwar Yaya Sadeeq Amaryan Haidar."
Sadiya washe baki tayi tare da ɗaga ma Khalid babban yatsanta, alaman jinjina shawaransa ta jiya tayi, tana murmushi mai kyau ta ce, "Sai wajan Yaya Sadeeqna."
"Au! Wa ya riga ni yi miki albishir ɗin Yaya Umar ya amince ki je, ya ce ma na kai ki."
Sadiya murmusawa tayi, tare da yi masa nuni da Abba amma da ido, kamun Khalid ya ce wani abu sai Abba ya ce, "To wannan dai zuwan Abbanta ne ba na Umar ba."
Khalid ƴar dariya yayi tare da cewa, "Congrats ƙanwar Yaya Sadeeq."
Daga haka Sadiya ta ɗauki basket, Umma ta miƙa wa Khalid flask Sa'ad ya riƙe sauran abubuwan suka fice.
Umma da Abba da Sadiya mota guda suka shiga direba ya ja su, Sa'ad da Khalid kowannensu ya shiga tashi motar dan daga asibiti duk wajajan aikinsu za su wuce, shi Sa'ad shi ne ke kula da gidan man Abba, shi kuma Khalid a companyn Sadeeq yake aiki.
Umma da Abba hira suke a kan Khausar da ta ƙira tana shirin zuwa biki, kuma tana tambayan Yayanta Sadeeq dan tana ƙiransa baya tafiya, Abba ya ce lallai shi ma ta ƙira shi akan haka, amma daman ya kwaɓi su Sa'ad har Umar, akan kar wanda ya sanar mata Sadeeq ba lafiya, a barta kawai sai ta zo bikin, in zuwa lokacin ya ji sauƙi shikkenan, idan bai ji ba kuma to ta zo ta gani, Umma ta jinjina kai dan ita ma daman hakan ta tsara.
Sadiya tana lafe a jikin kujera, tana jin hiran su Abba sama-sama, tana addu'an samun nitsuwa a zuciyarta har bacci yayi gaba da ita, har suka isa asibitin tana bacci, sai da direba ya parker a gefen ward da Sadeeq yake, sannan Umma ta dubi Abba, tare da cewa, "Auta fa bacci take yi."
"Ki ƙira sunanta da bismillah da addu'a sannan ki taɓa ta, ta taso mu shiga ciki", Abba ya faɗa yana ficewa a motan, tare da zagayawa ɓangaren da Sadiya take ya buɗe ƙofan.
Umma bismillah ta yi, murya a tausashe sosai ta ƙira sunan Sadiya, sannan ta ɗan taɓa kumatunta tana maimaita sunanta, "Auta³, tashi mu shiga ciki ki kalli Yaya Sadeeq ɗin naki."
Sadiya cikin bacci ta soma jin tsikan jikanta na tashi, kamun ta nisa a hakan ta tsinkayi muryan Umma na ƙiran sunanta, bismillahn da Umma ta yi shi ya dirar mata a kunnenta, ya ankarar da ita yin bismillah tare da addu'an farkawa a bacci, a nitse ta wara idanuwanta suka sauƙa kan Abba da ya zuba musu ido yana murmushi, motsawa tayi tana ƙoƙarin yaƙar tashuwar tsikan jikinta da rawan da jikinta ke ƙoƙarin ɗauka, a haka ta lallaɓa ta fito a motan, tana arba da haraban asibitin a take wani juwa ya ɗibeta, tayi baya za ta faɗi, da sauri Umma ta tallafota jikinta tana faɗin, "Ki yi addu'a Auta, za ki samu nitsuwa da ƙwarin guiwa."
Jikin Sadiya rawa yake da gaske idanuwanta na ƙoƙarin tara ƙwalla, taku ɗaya biyu kawai hawayen suka fara gangarowa jikin ya kama mazari sosai, Umma kiɗimewa tayi ta juya ga Abba tana faɗin, "Abban Sadeeq ko za a haƙura ta koma motan direba ya maida ta gida kawai?", Umma ta faɗa idanuwanta na tara ƙwalla, dan rawan da jikin Sadiya yake ya yi yawa.
Abba kamo kafaɗan Sadiya yayi daga jikin Umma, a nitse ya ce, "Halimatus-Sadiya, wajan Yaya Sadeeq naki za ki je fa, maza ki daure kinji yarinyar kirki ƴar albarka, ki ta maimaita Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un."
Sadiya jikinta na rawa ta gyaɗa wa Abba kai, sannan ta koma jikin Umma ta lafe, duk da har lokacin jikinta na rawa, a haka suka cigaba da takawa har suka shige ciki, ruwa lokacin Sadiya ta kusa ficewa a hayyacinta, kuka take mara sauti, har wani jajjan numfashi take kaman za ta shiɗe, Umma a gigice ta ce, "Dan Allah a maida ta Abban Sadeeq, wallahi yarinyar nan tausayi take bani."
Abba jinjina kai yayi alaman su juya, da sauri Sadiya ta girgiza kai, tana buɗe baki da nufin magana sai sautin kukanta ya fito, cikin kukan take faɗin a barta dan Allah, suna cikin haka sai ga Umar, tana ganinshi ta soma miƙa mishi hannu, cikin kuka take cewa, "Yaya dan Allah ka kai ni wajan Yaya Sadeeqna, dan Allah."
Umar amsanta yayi a hannun Umma, a haka jikinta na rawa ya riƙeta a jikinsa har suka ƙarasa cikin ɗakin da Sadeeq yake, tana kuka tana a kai ta wajan Yaya Sadeeq.
Har gaban gadon Umar ya kai ta, a dake ya ce, "Za ki iya tsayuwa?"
Da sauri Sadiya ta jinjina kai alaman za ta iya, sai Umar ya sake ta yana faɗin, "To maza ki rufe wa mutane baki......", maganan bakinsa ne ya maƙale sakamakon na'urar da ke saƙale a jikin Sadeeq da ta ba da sauti, da sauri Umar ya juya, idan ba gizo idanuwansa ke masa ba yatsun Sadeeq ke motsi, ai da sauri ya hanzarta ya fice dan ƙiran likita, Umma da Abba da su Khalid da suke tsaye a waje, ganin Umar ya fito a hanzarce, da sauri hankali tashe suke tambayansa lafiya?
Umar yana tafiya yake faɗin, "Idan ba gizo idanuwana suka mini ba to Sadeeq ya motsa."
Bai gama rufe baki ba, Khalid da Sa'ad suka rufa masa baya dan ƙiran likita, Umma da Abba kuma suka shige ɗakin da sauri suka yi wajan gadon da Sadeeq ke kwance.
Sadiya dama Umar yana sake ta, ta riƙe ƙarfen gadon tare da runtse idanuwanta dan ta tattaro iya ƙarfin guiwanta, idanuwanta a kulle take faɗin, "Yaayaa nah, dan Allah ka tashi, Yaayaana ka daina wannan zaman asibitin bana so bazan iya jure abinda nake ji ba", cikin matuƙar karaya da gajiya da sarewa tayi maganan, tare da fashewa da matsanancin kuka ta ɗaura kanta a saman ƙirjinsa tana kuka jikinta na kan rawa har ƙafafuwanta suna ƙoƙarin gaza ɗaukanta.
Umma da Abba a haka suka shigo suka samu Sadiya, ga Sadeeq nan har ya wara idanuwansa, amma wani irin kai da da kawowa alaman da ke a jikin na'urarsa ke yi da mugun sauri, wanda hakan ke dai-dai da bugun zuciyarsa, da sauri Umma ta kamo Sadiya da niyan ɗago ta, amma Sadiya ƙam-ƙam ta ƙanƙame Sadeeq, Abba na ƙoƙarin kai hannu, sai ga shigowan likitoci da su Umar, da sauri likitan ya ce a ɗaga Sadiya a fice da ita cikin faɗa, saboda barinta da aka yi har ta kwanta a ƙirjin mara lafiyan, kuma a saitin da zuciyarsa take, sam hakan bai yi ba.
Umar ne ya ƙaraso, caɗak ya ɗage Sadiya ya nufi waje da ita, wacce zuwa lokacin ta sume, su Umma duk suka rufa musu baya, bisa umurnin likitoci a kan duk su fita, dan tun kan a ɗage Sadiya ma suka fara bai wa Sadeeq taimakon da ya kamata.
Sadeeq da tun da muryan sautin kukan Sadiya ya dirar masa a ƙwaƙwalwa da zuciya, a take ya motsa yana jinta a jikinsa kuma ya ƙoƙarta ya buɗe idanuwansa, wani irin gudu da ƙarfi zuciyarsa ke masa kaman za ta faso ƙirjinsa ta fito, ji yake Sadiya da ta kwanta a ƙirjinsa saitin zuciyarsa to taimakonsa ta yi da zuciyar ta fito, duk kuka da maganganun Sadiya yana jin su sarai, amma ba zai iya motsa komai nasa ba bayan idanuwansa da ya ƙoƙarta ya buɗe ko zai kalli kyakkyawar fiskarta, da Umar ya ɗage Sadiya a jikinshi, cikin rauni da nauyin da hannunsa ya masa ya motsa da niyan ya kamo Sadiya, amma sai hannun ya saki ya ɓingire, idanuwansa ya karkata ya bi su Umar da kallo har suka fice, amma bai samu ganin fiskanta, idannuwansa ya maida ya lumshe, ciki-ciki murya ba sauti ya buɗe tsadadden bakinshi ya ƙira sunanta, "Saa..dii..yaaaa", a rarrabe ya ƙira sunanta kuma ƙasa-ƙasa sosai, domin indai ba kunnenka ka kai wajan bakinsa ba, to ba za ka ji sautin ba, sannan in idanuwanka ba sa ganin bakinsa ba za ka gane me ya faɗa ba, daga haka sunanta na ɗaukewa a bakinsa, bugun zuciyarsa ya tsaya, numfashinsa ya ɗauke ɗiff.
***
Za ku iya samun littafin a wannan manhajoji.
BAKANDAMIYA HIKAYA.
AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
***
a kan Naira #500.
Idan littafi ya zama completel 1k yake in sha Allah.
# Hareeyh
# ***
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚