MR.BELLO

04

by @jamilaumarjanafty

MR BELLO..!

(The young Teacher)

Mallakar:Janaftyđź’ž

            🅿️4

#FLASH BACK...

  🌟 ALHAJI MUHAMMED HASHIM JIKAMSHI Shine asalin sunan mahaifin Bello da Muktar wanda ya kasance haifaffan garin jiĆ™amshi dake Ć™aramar hukumar É—an Musa a cikin babbar jihar katsina.

   Alhaji Hashim mahaifin Muhammed ya kasance ma'aikacin hukumar wutar lantarki na garin JiĆ™amshi yana da rufin Asiri daidai Gwargado, Matarsa ta farko Hajiya Maryam ta kasance 'yar dangi ce Auren Zumunci aka yi musu Ita 'yar nan garin JiĆ™amshi ne, Wata tara nayi da aure su ta haifo kyakkyawan É—anta namiji, aka sanya masa suna Kabiru, Sai haihuwar ta ta biyu ta Ć™ara yin Abubakar suna kiranshi Garba, wanda tsakaninsu shekara É—aya ne.

Tana da cikin na uku Hashim ya kara Aure da wata 'yar Malumfashi mai suna Aisha, Auren da ya sha maganganu sosai har sai da maryam tayi yaji zuwa gida sabo da yadda ta tayar da hankalinta kan Hashim ba zai ƙara Aure ba shi kuma yace sai yayi, toh iyayensu mata ba wanda ya goyi bayan shi saboda Maryam, Iyayensu maza ne suka shiga maganar har Maryam ta koma gidan Hashim aka yi biki lafiya, yayin da Aisha amarya ta tare a gidan Mijinta.

Tun Zuwan Aisha gidan bata taba jin daɗin zama da Maryam da 'ya'yanta ba Saboda yadda take nuna mata tsana ƙiri-ƙiri haka ma dangin Hashim ɗin sun koma bayan Maryam, Aisha ta zama bata da wani gata a garin Jiƙamshi T tun da Ita iyayenta sun yi nisa, tana shan wahala wajen Maryam da dangin Hashim Amma ko sau ɗaya bata taɓa furta wa Hashim ba, sai ma ƙoƙarin faranta masa cikin hanyoyi da dama wannan shi ya taimaka wajen bata matsayi mai girma a cikin zuciyar Hashim, uwa uba ga haƙuri da kawaici da kuma sanin ya kamata.

Wannan kulawar da Hashim ke nuna wa kan Aisha har sai da Maryam ta kai ƙararshi gida, wai yana fifita Aisha a kanta wanda dangi suka yi masa chaaa nan aka tara su dukkansu aka yi musu faɗa, ba kaɗan abin ya bashi mamaki amma kuma baya jin zai fasa nuna soyayyarsa ga Aisha, watan Aisha uku da zuwa gidan ta samu ciki mai azabar laulayi, sosai yake bata wahala sai ya kasance ko wanka sai Hashim yayi mata yake fita wajen aiki, hakan shi ne ya ƙara ma Maryam wutar ƙiyayyar Aishan da kishinta, shikuma Hashim ya ce ba zai fasa ba.

Cikin Aisha na wata biyar Maryam ta haifi 'yarta mace wacce ta ci sunan Mahaifiyar Hashim wato Ruƙayya Ita kuma Aisha sai da cikinta ya kai Wata Goma kana aka mata Operation ta haifi ƙaton ɗanta namiji ya ci sunan MUHAMMED Wanda dangi Sukayi ta ceceku game da Haihuwar saboda yadda Hashim ya kashe Kuɗi Sosai ga Hidimar Aisha Tundaga na Asibiti har zuwa na hidimar Suna, Duk da haka bai kulabsu ba kuma Itama Aisha bata mayar da kai ba, Duk ko da maganganun da Maryam ɗin Ke jifanta da shi.

  Watan Muhammed goma sha tara Aisha ta Ć™ara samun wani cikin wanda yazo da Sauye Sauye da dama domin an Sallami Hashim Daga Wajen Aikinshi batare da ya san laifin da ya aikata ba kuma sallama babu biya ko wani Ć™arin bayani abun da ya matuĆ™ar tayar masa da hankali shi da iyalanshi gaba É—aya gashi lokacin Kabiru da Garba An sanya su a makaranta har da Rukayyah,Muhmmed ne kaÉ—ai ba'a saka shi ba, Abun da yafi É—aga mai hankali shine lokacin da zai Auri Aisha yana gidan gado ne, To Shine ya ci bashin Banki,ya Siya Fili ya gina gida Duk Wata yana Cire Wani Abu Daga Cikin Albashinshi yana Biya To gashi An Sallameshi Kuma Banki bata Jira Dole ka a Biyata Kudinta.

Lokacin da dangin Hashim suka ji wannan labarin shikenan sai Aisha ta ƙara shiga gararin rayuwa na cewa Itace mai farar ƙafa, Ita ce Tunda Hashim ya auro ta karayar arziƙi ta kama shi Sai dai Ta Shige Daki Tayi ta Kuka Tana rumgume da Muhmmed ga Cikinta ya Tsufa Alokacin ne kuma banki Suka Nema Kudinsa Shine Dalilin Saida Duka kaddarorinsa da Motocinsa Harda Gidan Da Suke Ciki Suka Tattara Suka koma gidan Gado.

Aisha ta Shiga matsi da gararin Rayuwa Domin ba Inda Takejin Dadi Sai Ta bangaren Hashim Kuma Koda yan"uwanta Sunzo bata Nuna Musu Wani Abu Sai Dai Su Tafi Suna Zencen Ramarta Acikin Wannan Halin Ta Haifi yarta Mace mai Suna HIDIYA wanda Tunda Lokacin Da Aisha Ta Haifeta bata kara Lafiya ba Harta Koma ga Mallicinta ta bar Marayin ya"yanta Hannun Matar Hashim Wato Maryama.

Hashim yayi kukan Rashin Aisha Sosai ga Talauci ga Kewar Aisha Sai Suka Taru Suka Sanyamai Hawan Jini,Dangin Aisha Kuwa Sukayi ta Kokarin ko Hidiyan Hashim ya basu Su Tafi da Ita Ammh yan"Uwanshi Suka Hana Wanda ba Kowa bane ya Kitsamusu Haka sai Maryam Domin bataso  Adauke ya"yan Tafison Abarsu Tayi ta gana Musu Azaba Domin bata taba Son Uwarsu ba Suma bazata Taba Sonsu ba

Haka ko Akayi Dangin Aisha Sunaji Suna gani Suka Tafi Suka bar Muhammed Dan Shekara Uku da Wani Abu yayinda Hidiya Keda Shekara Daya da Rabi Abun Tsausayi Ammh Sun Sanar Dasu Cewa Lokaci bayan Lokaci Zasu Dinga Zuwa Dubasu Suka Amince,Bayan sun Tafi Aka Dauki Amanar su Muhammed Aka Damkama Maryam Wacce Ta karbesu kamar Gaske nan ko Cikin Ranta Mugun Nufi ne

Tun kafin Rasuwar Aishan Dama Ta Dade da Karantama Duka ya"yaanta Cewa Su Muhammed ba yan"uwansu bane Abokan Gabansu ne Saboda Babansu yana Fifitasu Fiye dasu Tayi ta saka musu Mugun Nufi acikin Zuciya Abunga ga yara nan da Nan Suka Haddace Karatun Nata Shiyaasa Muhammed Da Hidiya Suke Shan Wuya Ahannuta Ita da ya"yanta In Hashim yayi mgana ta Fashe da Kuka tace ya Raina Kokarinta,Data Fahimci Yana Damuwa da Halin da Suke Ciki Sai Koma yi musu Mgunta Aboye Abinci ma Kanzo Take basu,Ga Wahala Akasa Suke Kwana Cikin Sanyin Kasa Kafin Arufe Shekara Daya Yara sun Chanza Kamanni Tun balle ma Hidiya Wacce Bata da Lafiya Saboda Kwanan Kasa Nomomiya ta kamata Hashim baidata Cewa Domin Da yayi mgana yan Uwashi Zasu Tasomai da Fadin Uban me yake Tsinanawa Banda Zaman Banza,Yanaji yana gani sai dai yayita Kuka Shikadai Saboda Tsausayin Muhammed da Hidiya.

Amkrantar Gwannati Aka Sanyasu Sakamakon Kabiru da garba Dasuke na Kudi Tunda yan"uwan Hashim Sunfi Son So,Muhammed Tun yana Yaro yasan Gwagwamaryan Rayuwar Duniya,Sau biyu Dangin Mamansu na Zuwa Dubasu Suna Komawa da Kuka Saboda Tausayin Halin da Suke Ciki Tun Bama Muhammed ba Wanda Ke Karami Ammh Wahala ta Zama Cikin Jikinsa.

Tun yana Aji biyar yasan In An Tashi Mkranta ya Kama Hannu kanwarsa Su Shiga Cikin Kasuwa Yaringa Dako yasamu Abunda Zai Siya musu Abinci Domin Ko Sun Koma Gida Mama maryam bazata basu ba,Toh Ahakan ma basu Tsira ba In Suka Dawo sai ta kamasu Ta Masu Duka Hidiya Kuwa Kullum Cikin Kuka Take garba ya Daketa Kabiru ma Haka Rukayyah ma Sai dai in Muhammesd ya Ramata Mama ta kamashi Tayi mai Dukan Tsiya basu da Wajen da Suke Jin Sanyi sai Wajen Abbansu Wanda Shima Hawan Jini ya Kwantar Dashi.

Muhammed Dana Shekara Goma Aduniya Ita Kuma Hidiya Bakwai Allah yayima Hashim Rasuwar Mutuwar Data Raunana  Zukata Dadama Babu Uwa ba Uba Maraici ya Lullubesu Dama Ganin Abban Nasu ba"a musu Wani Abun Ammh yana Fadi ya Mutu Shikenan Wahalansu ya Karu Hidiya ta zama Jakar Aiki Itace debo Ruwa,Share Share,aike aike ,Wanki ne da Guga Ammh Rukayyah na Zaune Jangal batayi Muhammed Kuma Fita yake Tun Safe yana yawon Dakonsa Sai dare yake Dawowa Ya Siyoma Hidiya Abunda zataci Domin yasan Duk Wunin Aikin Da Zatayi bazata Bata Abinci ba.

Da Farko Adaki Suke Kwana Tare da Su kabiru Ammh Sai Mama ta Kullama Muhammed Sharri Akan ta Kamashi yana Turama Rukayyah Ahannu Awando Wanda Iyalan gidansu Suka Hadu basu Duba kankantar Shakarun Muhammed ba Sukamai Dukan Mutuwa Suka kuma Koreshi Agidan,Haka yafita yana Kuka Itama Hidiya tana Kuka Wannan Shine Silan barin Muhammed gidansu Ya bar Hidiya Cikin gararin Rayuwa Bai yi Nisa da garin Jikamshi ba,Cikin kasuwa yake Wuninshi Sai Dare ya Tafi Tasha ya Kwana yana Tara Kudinshi Kuma kullum Daddare zai Siyan ma Hidiya Doya da Kwai yazo Zauren Gidan ya Tsaya ta Sadado ta Fito ya Bata bayan ya Zaunar da Ita taci Tasha Ruwa Haka Zasu Rumgume Juna Kukan Tsausayin Kansu Hidiya tasha cemai Su gudu Wajen Dangin mamansu Ammh Muhammed yaki Saboda Shi kanshi bazai iya gane Gidansu Maman nasu ba Don yana Karami Sosai Lokacin Da ake Zuwa Dashi.

  Muhammed bai bar Zuwa Mkranta ba Hidiyace dai Mama ta Kashe mata mkranta Bashi da yarda Zai yi yanaji yana gani Rayuwar Kanwarsa Tana lalacewa Su kabiru ko Suna Haduwa Dashi suda Abokansu Haka zasu dingamai Dariya Suna Tofamai Miyau Shiyasa ko ya gansu yake Saurin Chanza Hanya Hidiya Kuwa Tagama Wahalan Amfanin da Ruwa da Rana Daddare kuma ta Kwana Akasa nan da Nan Ciwon Nomoniya Takaramata Yawa Sosai Kullum Cikin Mura take Kwana da Sanyi Ammh ko Muhammed yazo bata Sanar mai Saboda Karta Tadamai da Hankali Koda yaushe yazo Jikinta yayi Zafi sai ya Tambayeta tace bakomai.

Adaddafe Muhammed ya kamallah Jss3 sai ya Ijiye Karatun ya Maida Hankalinshi kan Dakonshi hade kuma da Jari Bola Kwata Kwata Zuciyarsa ta Kekahe Neman na Kanshi yake ba Domin Shi ba Sai Domin Tilon Kanwarsa Hidiya,yayi kwana Biyu yana Zuwa Baya ganin Hidiya na Fitowa sai Hankalinshi yatashi Ranar dayazo na Uku Azauren Gidan ya kwana yana Jiranta Ammh batazo ba,Tundaganan Jikinsa ya bashi ba Lafiya Gudun kada Wani ya ganshi ne ya sanya ya Koma kasuwa Hankalinsa Duk Atashe Wajen Karfe 1 na Rana yana Kasuwa yana Sana"ar Dakonsa Wani yaron Kawun Abbansu yazo yake Sanar Dashi Wai yazo Hidiya zata Mutu Cikin Fitan Hayyaci ya Watsar da Abunda Ke Hannunshi Suka Rumtuma Zuwa Gidansu.

Sai dai Suka ganshi Kwatsam ya Shigo Har Shashensu Alokacin Wajen Shekara Biyar Bai kara Shigowa Gidan ba,Hidiya tana Kwance Akasa Siminti Hancinta ya Toshe da majina Numfashinta baya Fita Ta Rame ta lalace Kasa ya Zube gabanta yana Kuka Hannu Ta Mikamai Tana Fitar Da Hawaye Daidai Lokacin kuma Kawun nan  nasu Suka zo Dama mama ganin Hidiyan ta Kusa Mutuwa ne Shine taje ta Kirasu Wai Suzo Su gani Ita bama tasan Bata da Lafiya ba Alhalin Tana sane Itama kema Kara Saka Ciwon Tashi Domin Wanka take Zuwa tamata Da Ruwan Sanyi Kuma Ta Hanata Sauya kaya Har sai Sun Bushe Ajikinta.

Muhammed ya Rude da ganin Halin da Hidiya ke Ciki ko Ta kan Kawunsu Dake mgana baiji ba ya Ciccibi Hidiya yana Kuka Ya Fita Da Ita Waje,yana Ihun Mutane su Taimakamai Ana Cikin Wannan Halin ne Allah ya jeho Alhaji lawal Acikin Motarsa Zai Wuce Katsina Alokaciin ganin Muhammed Dauke da Hidiya yana Kuka ya sanya ya Faka Motarsa ya Fito baima Tsaya Tambayan Muhammed ba ganin Halin da suke ciiki ya sanya ya karbi Hidiya ya sakata Abayan Mota ya Umarci Muhammed Daya Shiga Su Tafi Agaban Idon Dangin Mahaifnsa Suka Tafi Asibti da Hidiya ammh ba Wanda yayi Tunanin Binsu.

Babban Asibtin Garin Sukaje sai dai Suna Shigowa Get din Asibtin Hidiya tafara Wani kakari Muhammed ya Rude ya Rumgumeta yana Kuka yana Kiran Sunanta ganin Idanuwanta na Kafeewa ne ya sanya ya Kuramata ido hawaye na Fita Daga Cikin Idanuwanshi Yana ji yana Gani Agaban Idanuwansa Aka Zare Ran Hidiya Abunda ya kasa barin Zuciyarsa Kenan Har Shima ya koma ga mahallincinsa.

Muhammed yayi kuka Tamkar zai Zauce Saboda Mutuwar Hidiya basu Juya ba sai da Suka Shiga da Ita Cikin Asibitin Aka Tabbatar da Mutuwar Hidiya Kafin Alhaji Lawal ya Daukosu Zuwa Gida ganin Kukan da Muhammed Ke Yine yasa ya Tambayesu ina Mahaifinsu nan Muhammed yana Kuka yana bashi Lbrinsu Wanda ya Matukar bama Alhaji lawal Tsausauyi.

Abun Mamaki da Suka Dawo da gawan Hidiya ba Wanda ya Nuna Jimami ko Damuwa,Taruwa kawai Sukayi,Abun Takaichi Muhammed Shi yayima Hidiya Wanka Gawa Yanayi yana kallon Cikin Idanuwanta yana Kuka Ahaka Har Aka kaita gidanta na gaskiya A makabartan Aka Watse Aka barshi Alhaji lawal shi ya rikoshi Suka Fito ya Sanyasa Cikin Mota bai Zarce dashi ko"ina ba sai Katsina.

Alhaji lawal shi da Matarshi Hadiza basu Taba Haihuwa ba Gashi yana da Tarin Dukiya Ta Dalilin Kamfanonin Dayake Dashi kama daga na Robobi kanfanin Sarrafa Atamafa,na Takalma ne da Sauransu. ya Tara Kudi masu yawa Tunda yazo da Muhammed yabata lbrinshi Shikenan Tsausayi ya kamata ta kama Muhammed Ta Rumgume tana Kuka Kuma Sukaci Alwashi Zasu Rike Muhammed Tsakani ga Allah.

  Bayan Rasuwar Hidiya ba Dadewa Dangin Aisha Suka zo ganinsu suka Iske bakin lbrin Rasuwar Hidiya da Lbrin wai Muhammed ya Gudu ya Shiga Duniya Haka Suka Koma Malumfashi Suna Kuka Sosai na yadda Rayuwar ya"yan Aisha suka lalace Acikin Duniya,Shikuma Muhammed ya samu Chanjin Rayuwa ya koma mkranta,bayan ya gama Secondry Sch Suka Tafi Dangin Alhaji Lawal A malumfashi Alokacin ne kuma Aka gano Ashe Shi Alhaji lawal Abokin Wasa yake ga Marigayiya Aisha Mahaifiyar su Muhammed nan fa Sabon Kuka ya Tashi Ana Ta Rumgume Muhammed,Wanda koda da Rana Daya Mutuwar kanwarsa Hidiya bai Taba Bacemai ba.

   

Akasar England ya Hado Digree dinsa na Farko Akan Harkan Kasuwanci Haka kuma ya Wuce Kasar Calponia ya Hado Master dinsa Akan Accouting da Hada Hadar Kasuwanci Koda ya Dawo Nageria sai Ragamar Dukiyar Alhaji lawal Ta Dawo Hannun Muhammed,Shi kuma Alokacin A England yayi Aiki da Wani Kamfanin Turawa na Sarrafa Takalmam Maza so sai Suka Hada Huldar Kasuwanci da Kamfanin Alhaji lawal Dake Nageria kuma Alhamdulillah Lokaci Kadan Huldar ta kawo musu Kudi Sosai Suka Cigaba,.

Muhammed ya Wuce Duk Tunanin Mai Tunanin jin haushinshi ko Hassda Daga Danginshi Kuwa Suna da Lbrinshi Domin Alhaji lawal na Matsamai Lokaci bayan Lokaci Yana Zuwa Dubasu Rukayyah Tayi Aure Akano Su Kabiru kuma Angama karatun Ana Zaune ba Aikin Mama maryam kuma girma ya Kara kamata da Kuma Hakkin Hidiya da Muhammed Domin Taga yarda Allah yake Maida bawanshi Lokaci Daya.

Kafin Rasuwar Alhaji lawal Sai da Tabbatar  ya mallakama Muhammed Duka Dukiyarsa bayan Ancire na yan"uwansa,Wannan Abun yabama Mutane mamaki da kuma Girmama Soyayyar da Alhaji lawal Kema Muhammed Su Kabiru kuwa Hasaada da kyashi bai bar Zuciyarsu ba,Sai Sukayi lambo Suna Shigema Muhammed Harda Rokonsa Gafara Saboda Suma Su Shiga Jikinsa Su Samu Arziki Sun kuma yi Nasara Domin Daga Kabiru Har Garba ya Daukesu Aiki A kamfanonin Alhajin lawal Duk da Abun da Suka Aikata gareshi bai Taba bacemai ba Ammh in yayi Duba ga Yadda Allah ya Daga Darajansa sai ya Godema Allah.

   Mutuwar Alhaji lawal Da Matarsa Sakamakon Hadarin Mota Shiyakara Fito Da Sunan Muhammed Aduniya Domin ya Samu Dukiya mai yawa Yawancin Kamfoninin Alhaji Lawal Shi ya mallakesu Gashi Shima yasan Kan Kasuwanci Kafin Ya Rufe Shekara Daya ya Mallaki Jikamshi shopping mall Jikamshi Store* Jikamshi And Sons Nageria Limited..* Lokaci Daya Sunanshi yayi Suna A nageria Gefe Daya ya jawo Yan Uwansa Da Dangin Mahaifinsa yamusu Gata duk da Abunda Suka Aikata garesa Dangin Mahaifiyarsa kuwa Dama Sune Ahalinsa.

Tuni ya Tattara Kabiru da Garba da Mama Suka koma Katon Gidan Daya gina A Katsina Komawarsu Wannan Gidan Mai kama da Aljannar Duniya Shiya kara Saka Zuciyoyin Su Kabiru Gudirtan Cewa Ko Ta Halin kakane sai Sunga bayan Muhammed Sun mallake Duka Dukiyanshi Ita ko Mama Maryam ta Saduda Ance magaji mafiyi Domin Su Kabiru ya"yanta ne Ammh Sun Fita iya Kulla Makirci da Sharri Duk da Muhammed na Kanninsu Haka Suke Sadda kai Suna mai Biyayyah Duk Don ya Saki Jiki Dasu.

Cikin Shekara Uku ya Siya Musu gidaje da Motoci ya kaisu Makka Kuma yayi Musu Aure Kabiru Akaduna ya auro Karima sai Garba dayayi Aure a Kankara Ya Auro Sahura Dukkansu Sukazo Suna Cin Arziki da Dukiyar Muhammed Wanda Suka Wulakanta Rayuwarsa da Farko Mama maryam bata Rasu ba Sai bayan Auren Muhammed,ta rasu ta kukan Neman Gafaransa kan Abunda ta aikata garesa Shida kanwarsa,muhammed anso a tusamai auran Dangi A Ammh yaki Domin Allah ya Hadashi da Hassatu Wata Bafullata ne Daga Jahar Yola

Hassatu marainiya ce Bata da Uba sai Mahaifiyarta Data ke cema Daada Farar Bafullatana ce Kyakyawa da Ita Dangin Mamansa Suka yi komai na Auran Cikin Lokaci Hassatu Ta tare Agidan Mijinta Dake Katsina,Tun kuma Daga Lokacin Sai Abubuwa Sukayi ta Cigaba Arayuwar Muhammed gefe Daya Kuma su Kabiru da Matansu Suna ta Ta Hada Tuggunsu A boye Ita kanta Hassatu ta sani Domin ba kyashin Da basu Nuna mata Ammh bata taba Nuna ma Muhammed Ba bataso ta Rabashi da yan"uwanshi.

  Karima matar kabiru wabi Takeyi In ta Haihu sai anyi Suna Su koma ga Allah Ita kuma Sahura matar garba Shuru Haihuwan, Itama Din Shuru Kwatsam Hassatu ta samu Ciki Su kabiru ba Kulle kullen da basuyi ba kar Hassatu Ta haihu Ai kuwa hakansu bai Cimma Ruwa ba Domin A Babban Birnin India Delhi Hassatu Ta Haifi Kyakyawan Danta Namiji Wanda yaci Sunan muktar basu dawo ba sai da sukayi wata biyu suna dawowa kuma ya kaita yola wajen Daada tayi wata Daya kana Ta koma Katsina.

Lokacin da Muktar yazo Duniya yazo Cikin gatan Rayuwa sosai saboda Mahaifinshi na kan Samu Hassatu Ta Fahimci komai shiyasa take ta kaffa-kaffa da É—anta bayan tana sanar da Daada duk abun da ke faruwa Ita ta Haneta da kar ta sanar ma Muhammed Amma dai ta kiyayi kanta ta kuma dinga Lura Saboda Hakama Dukkansu Suka baro Gidajensu Suka dawo gidan Muhammed ke zaune shida Hassatu katon Gidane mai Dauke da part part da Zuwan Wai Sunfi Jin Dadin Zama tare Dashi Shi kuma bai kawo komai ya Amince Suka Tattaro Suka Dawo nan da Zama.

Inna Rukayyah ma Dake Kano Babu Abunda Muhammed baya Mata tana Kuma Zuwa Akai Akai Sai dai ita Tunda Tayi Aure Allah bai bata Haihuwa ba Sai da Muktar ya Shekara Bakwai Aduniya kana Karima matar Kabiru Ta Haifi Danta Namiji yaci Sunan kakansu Hashim Lokacin Tuni Ansaka Muktar A mkranta International Community School Abuja, Cikin Gata da Soyayyah mai Tsanani Wanda Ke Kara Wutar Kiyayya Azuciyarsu Kabiru Suna Tunanin in Suka Kauda Muhammed ya Zasuyi da Muktar Dansa na matarsa mai Sauki ne.

Hassatu bata kara Haihuwa ba Sai da Muktar ya Shekara 15 aduniya Ta samu Cikin MUHAMMED BELLO Wanda Ikon Allah ne da Kuma Rabo ya kawoshi Duniya Domin har maganin hana É—aukan Ciki kabiru yake bama karima tana Sanya ma Hassatu a cikin lemo tana Sha sai dai kuma abun da Allah ya riga ya yanke bawa bai isa ya kauce musu ba.

  Wannan karon ma a Ć™asar India Hassatu Ta sake haihuwar É—anta namiji mai kama da Mahaifinta sak shine Dalilin Da ya ci Sunan BELLO, Haihuwan da ta zoma Muhammed da Sauye Sauyen Arziki dadama Acikin Rayuwarsa Haihuwarsa da Shekara Suka Tattara Muhammed Zuwa Kasar Chicago Domin ya hado Digree dinsa na Farko Tunda yana da Kokari Sosai Shiyasa yagama Karatu Yana da Kananan Shekaru.

Akabar Bello a gidan

Shi da Iyayensa suna cigaba da kula da shi Shima yana Shekara 4 aka Kaishi Nagerian Turkish Acadmy, inda aka kai Hashim Din Wajen Kabiru, Tun Bello na Karaminsa Kowa ya Fahimci sadauki ne ga Zuciya ga Riko ga Kuma Kulafuci ga Saurin Fushi,kuma Iyayenshi na Matukar Sonshi kar ma Daada Taji lbri.

Lokacin da Muktar ya dawo Nageria yana da Shekara 22 cif ya haÉ—a Digree É—inshi na farko dayake yana Sha'awar Aikin Soja sai Muhammed ya kaisa NDA Nageria Defency Acadmy Domin karban Horan Sojoji Lokacin Shima Bello na jss1 misalin É—an Shekara 8 saboda kokarinsa ya saka akayitamai Jumping ,Kuma Sannan ne Haihuwa ta Budema Abba Kabiru da Abba Garba Bayan Hashim yayi Kasim Wanda Tsakaninsu da Bello Wata goma Sha Daya ne,,Sai kuma Wasu da Sukayi ta Mutuwa basa Tsayawa Dakyar ta Karshen Ta Tsaya Zubaida sai Sahura matar Garba Keda Zulfa,Ummu salma,Hamdiya Duka mata Suna Sun Taso Cikin Gata ne Sosai na Rayuwa Daga Dukiyar Muhammed Wanda baya kyashin yi musu komai na Jin Dadin Rayuwa

Abunda yakara ɓata ran Abba Kabiru Shine Muhammed ya ɗauki Hashim yakai shi University Of lagos bai kaishi Kasar Waje ba Shiya kara Fito da Wutar Kiyayyah Hakan Acikin Ranshi yana ganin Muhammed na Fifita matanshi da yayanshi Akan nasu Matan da yayansu Batare da Sanin Kowa bq Sukayi Shawara Shida Garba Sukayi Hayan Wani mutum ya K'wance Birkin Motar Muhammed Din Wanda Suka Shiga shida Hassatu Zuwa Yola Lokacin Bello na Makranta Hakama Muktar yana NDA, kuma Muhammed yaso suyi tafiyar a jirgi Amma da yake sun San Abun da suka shirya sai suka hana shi tafiya a jirgi, Garba ne dama mai cukun-cukun tiket ɗin tafiye-tafiyen Muhammed din, nan ya ce masa babu jirgi mai zuwa yola hakan ya sa dole suka tafi ,A mota tun da tafiyar ta dole ce, Daada ce ba Lafiya tafiyar da basu dawo ba Kenan Har abada sai dai Duka Iyalan suka ji saƙon Mutuwar su nan take...

Allahu Akbar.