MR.BELLO

09

by @jamilaumarjanafty

🅿️9

"Washegari Wajen Misalin Karfe 12:00pm na Rana Sai ga Wayar Security Din bakin Get Zuwa Cikin gida Suna Tambayan Shin Aneesa Tasan Da Zuwan Wata Bakuwa Wai Bilkisu Kabir kaita?Alheri ce Ta Daga wayar bata Basu Amsa ba,Sai da Ta Shiga Dakin Daada nan Ta Iske Aneesa Cikin girmamawa Take Sanar da Ita ko tana da Wata bakuwa..? Ko Sauraranta Aneesa batayi ba Ta Fice da Sauri Cike da Murna Akan Fuskarta Daada na Mata Dariya.

Tana Fitowa Haraban Gidan Cikin Daga Murya tace"Plz Open d Get..."Tafada Cikin bada Umarni,Jiki na Rawa Securitys Din bakin Katon get Din Suka Wangalema Direban daya kawo B.kaita get Motar su kirar prado Baka ta samu Damar Sulalowa Cikin Gidan.

Bello da Uncle Aminu Dake Zaune saman Wasu Fararen Kujeru,Daidai Wajen Saman Mension Din Bello Suna Hango Duk Abunda ke Wakana Aharabn Gidan,Bello yana sanye da Riga da Wando Duka White ammh Rigar bata Da Hannu hakama Wandonsa 3quater ne,Karamin Tebur ne Agabansu Dauke da Madaran Hollandian sai Farantin kayan lambu da Ruwa,Gefe Daya Kuma Kafafun bello ne Farare Harde Saman Teburin ya maida kanshi baya bisa Kujeran Dayake zaune Magzine ne ahanunshi yana Karantawa Ayayinda Shima Aminu ke sanye da Irin Shigarshi Sai dai Shi Wayarsa ce Ahannunsa yana Faman latsawa Shiyasa Yafi Bello Lura da Filin Haraban Gidan Wando Sojoji ke ma Safa da marwa.

  Uncle Aminu Idonshi na kai Sanda Aneesa Ta isa da Sauri Ta Budema B.kaita bayan Mota ta Fito Tana Sanye da Shadda Ruwan kasa Tayi Dinkin Riga da Sikat an mata Stone Work karamin Gyale ne Akanta Sai Flat Shoe dinta kalan Kayanta Cike da Ihun da Suka Saba Suka Rumgume Juna Harda Tsalle kamar Wasu yara,Mallam Inuwa Dake Kofar Barayinsu Daya ke Dakunansu na Kwana yana Ta baya da Sauri ya kariso Wurin Yana Washe baki yake Fadin"A,"ah Maraba Hajiya Bilkisu.."

B.kaita ta saki Aneesa Tana Fadin"Yauwa Baba Inuwa Kwana biyu..? Yana Dariya yace"Wlh kuwa anzo lafiya..? Tace"Lafiya lau Alhamdulillah.."Aneesa Tace"Baba,Hira baza Tayi Dadi ba ba S.jibiya.."Mallam Inuwa ya kada kai kafin yace"Ayyah Sai dai in kun Hadu Amkaranta,."Da Sauri Aneesa Tace"In sun Hadu zaka ce Baba ka manta ni Na bar Mkrantan nan Kenan.."Tafada Tana Mirmishi gefe Daya Hannuwansu Sarke da Juna Ita da B.kaita.

Yar Dariya Mallam Lawal yayi kafin yace"Au hakane fa,Toh sai dai kuyi mgana ta Waya ."Yafada yana Kunshe Dariyanshi Shida B.kaita Cikin Farinciki Aneesa Tace"Insha Allahu Baba Bari mu karisa Ciki.."Mallam Inuwa yace"Madallah Nima yanzu Zan Fita zan kai Motarku Wanki ne.."Aneesa bata jishi ba Shiyasa bata bashi amsa ba.

Uncle Aminu Dake Zaune yana Kallonsu yace"Bello kalli kaga kamar Dalibarmu Bilkisu Kabir kaita nake gani Tare Da Aneesa..?

Bai Dago ba Cikin Rashin kulawa yace"Tunda ka ganeta Ita din ce.."Daga Haka ya Cigaba da Abunda yake batare Dayabama mganar Aminun muhimmanci ba balle harma ya kai Duba Zuwa ga Inda yake Nuna mai.

Cikin Saurin Uncle Aminu ya Mike ya Isa Jikin karfen Daya ma Wajen Kwanya Cikin Kaushin Murya ya Furta.."Bilkisu kaita.."Yafada da Dan karfi,Aneesa da B.kaita Dake Shirin Shigowa Kofar da Zata Sadasu da Babban Falon Gidan Suka Dago a Tare  cike da Mamaki B.kaita tace"La Uncle Aminu Gud Afternoon.."Tafada Fuskarta na bayyana Fara"a Domin Daga Inda Suke Tana Hango Uncle Bello Zaune Duk da Jaridar Dake Hannunsa Ta kare Fuskarsa,Aneesa Ko cin mgani ta Fara Tana Kauda kai Aminu na Lura da Ita Cikin Ranshi yana Fadin"Dis gal kamar Wata majanunuwa.."

Cikin Sakin Fuska yace"Afteernoon Too Bilkisu How are u.? Ya Hutu..? Fatan zaku Dawo mana Ku Dora Daga Inda Kuka Tsaya ko .? Cikin Jin Dadi B.kaita tace"Insha Allahu Sir Nida Salamatu Jibiya nan zamu Kareta,Anee ce dai tace Tabarmu Uncle.."yar Dariya yayi kafin yace"Haka tace muku..?karya Take Itama Kwatar-kwashi Dolenta ne.."

Yafada yana Kallon Aneesan Wacce Ta Dago Tana Hararanshi Ta kasan Ido Jin Abunda yace,ganin Haka yasa yace"Ke Uban Wa kike Harara..? Baki da Kunya ko.? Bar ganin Ina Gidanku Kina ganin Sojoji na yawo har yanzu ina Mtsayin malaminki ne sai na Sakko na Chasaki yanzu nan.."Yafada yana Nuna ta baki Ta Tura gaba Tana Kunkuni Baki ya Rike kafin yace"Oy Say Srry Uncle.."

"Bakaken Idanuwanta Ta Dago Tana kallonshi Lokaci Daya Tana Wani bata Fuska Fara Saukowa yayi Daga Step din yana Fadin"Dont let me to come Down Aneesa u will be In Troble.."Yafada Cikin Kakkausan Murya Bikisu ce Tayi Saurin Damke Hannun Aneesa Tana kallonta ganin ya kusa karisowa ne ya sanyata Rankwafa Tana Fadin"Srry Sir..."

Tafada Idanuwanta Sun kawo Kwallah Tsayawa yayi kafin yace"Bacemin Daga gani Bush gal kawai.."Jin Haka yasa Aneesa Ta Fizgi Hannun B.kaita Sukayi gaba bakin nan yayi gaba Sai Allah ya isa Take Durama Uncle Aminu B.kaita na Dariya Kasa Kasa,Bello Dake zaune gefe Ya Dago da kansa Daga Karatun Jaridar Dayake yana Fadin"Kana Son saka ma kanka Damuwa Wani Lokacin.."Yafada yana Kallom Aminun wanda ke kokarin zama Kan Kujeran Daya Tashi.

Tabe Baki Aminu yayi kafin yace"Name fa Sarkin Tsari..? Mirmishin Rainin Wayau Bello yayi mai kafin yace"Eh mana banda Jama kai Rainin Ina Ruwanka da Aneesa da kawarta Look nan fa ba Kwatar-kwashi bane Sakaci kadan zakayi yarinya ta zageka ballatana Dat Nonsees Aneesa bata ganin Girman Kowa.."Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Cikin Kufuluwa Uncle Aminu yace"Ina Ruwanka..It only I know ina da Barkwanci da Sakin Fuska Kuma yarinya Ta kawomin Raini Wlh Na zaneta,Nafi dai Wanda ko Agida bai Da Dadin Sha"ani.."Waigowa Bello yayi yana Kallon U.Aminu kafin yace"Aoh..Better.."Daga Haka ya Shige Ciki ya barshi nan yana Binshi da Harara

Acikin gida Kuwa B.kaita yau Taga Anty Rahila,Hibba da Daadan Da Aneesa Ke basu Lbri Dayake Wannan ne Zuwanta na Farko gwara S.jibiya tazo Sau Daya Itako Aneesa Gidan su B.kaita Tataba Zuwa A katsina sanda Sukaje Gidan Abba Kabiru Ita da Anty Rahila da ya Muktar sai Ta Rokeshi ya saka Direba ya kaita,B.kaita ta Jinjinama Daular da Aneesa Ke Ciki Duk da Kowa yasan Matsayin Muktar din Afalin kasan nan Ammh Acikin Ranta Tana mamakin Mr.Bello yadda bai Dauki Duniya Abakin komai ba.

Kafin kace kwabo Ancika B.kaita da Kayan Makuleshi da Abinci Agabanta sai da Sukaci Sukayi Nak Ita da Aneesa kana Suka Koma Dakin Aneesan Suka Dasa Sabuwar Hira,sallah kawai ke Tadasu Har Dare,lokacin da Suka Fito Har Ya Muktar ya Dawo nan Aneesa Taje ta gaisheshi Ita da B.kaita har yana Zolayan Aneesa Da cewa ko Zata koma Zamfara ne..? Da Sauri Tace"Ta yafe..Akasa Dariya Gabadaya,B.kaita nan ta Kwana Saboda Ta Kira Ummanta Ta Fadamata So Direbansu shi kadai ya koma Sai Washegari Ranar Biki Anty Rahila tace Aneesa ta Shirya Ita da Hibba Su Raka B.kaita gidan Biki Haka ko Akayi Su Aneesa Yan mata aka Chaba Ado,Aka Wuce Mallam Inuwa ya kaisu chan Maitaman bayan Anty Rahila da Daada Sun Cika B.kaita da Kayan Arziki Tatafi Tana Murna Da Kuma yabon karamcinsu.

Haka Itama B.kaita achan Gidan Sha"anin sai Nuna Aneesa Take Amatsayin Kawarta Ummanta sai Ita zata saka Dasu Take,nan Suka Wuni sai Yamma kana Mallam Inuwa yazo ya Daukesu Suka Koma gida suma bayan anciko Musu kayan Biki niki niki,nan Sukayi Sallam Da B.kaita Domin Washegari da Safe zasu koma Suka Rabu Akan sai Sunyi yawa bayan B.kaita tace agaida mata da Uncle Aminu da Kuma Mr.Bello bata Rai Aneesa Tayi kafin tace In kin matsu kizo da kanki Haka Suka Rabu Cike da Kewa Tun bare ma Aneesa Ta Datakejin kadaice bata da abokin Hira sai Hibba ko Daada.

****

KATSINA

Area:Kofar Laura

ABBA KABIRU HOUSE*

  Cikin Fada Abba Kabiru yace"Rufemin Baki Sakarya Kedai kice baki da Dubara Irin ta Yan matan Wannan Zamanin ammh Har ace Wani karamin Halitta bello ya gagareki..?

Yafada cikin kufuluwa da Jin Haushi Baki Zubaida Ta Tura kafin tace"wlh Abba nayi iya bakin kokarina Ranar fa Kusan Targadi yayi min fa,yace mudaina Kusantoshi shi ba dan"uwan mu bane Bamu Hada komai Dashi ba.."

Hajiya karima Dake Zaune gefen Zubaida bisa Daya Daga cikin Lumtsuma lumtsuman Royal Chairs din Dake Falon Ta tabe baki tace"Wai Alhaji Tsoron yaron kake ji ne hala..?Kake ta wannan Kumfar bakin..? Yarinyar nan tana iya bakin kokarinta ammh ko yabawa bai Tabayi ba,Hakuri zakayi ku kyaleshi Tunda Bakar Zuciyarsa Haryanzu batajin zata iya yafe muku.."

Abba Kabiru ya mike yana Saba Babban Rigan sa yana Fadin"Lalle baki da Hankali Karima Taya zan kyaleshi ai Mafita Daya na samu Sa"ar da zai zama Suruki na,Shine kadai zai sa ya yafemana laifinmu na baya kamar yadda Dan"uwansa bai Rikemu ba,Kina ganin yanayin Yaron nan Wlh sai ya iya Makamu Kotu nida garba kuma Tsaf za"a Daure mu Tunda Mun Aikata..",

Hajiya karima Ta Mika hannu t Kwantar da Zubaida kan Cinyarta Tana Fadin"Kaima kasan Bazai yi Haka ba,Ai dolensa ne ku nashi ne,Kuma Muktar bazai barshi yayi Haka ba.."Zubaida tayi Saurin Cewa"Umma Toh Shima Daddy Tsoron Uncle Bellon yakeji,Duka gidanan Suna Sonshi bamai Dauremin gindi Sai Daada,Kiga fa Ko Fadama bamai son yi mai Umma gaskiya suna Sonshi Sosai.."

  Abba Kabiru ya Tsaki yana Fadin"Nasani Shi nake gudu ammh ke karima baki ganewa,wannan Tsohuwar Bufullatanan nan Dama Tun Farko ni batamin ba Inama Tunanin Ita ke Zuga Bellon ba Wani ba,ke ko Zyciyarsa kaf bana Zuru"armu bane chan ya kwasoshi Wajen Dangin Fulani,kinsan su da bakar Zuciya da Mugun Abu.."ya karishe Fada yana Rike kugu Cike da Jin Haushi bata samu Zarafin Mgana ba,Abba kabiru ya Cigaba da Fadin

"umh nifa Abun Daya Nake gudu karima,Kada Wannan Shegiyar Zulfa kinsan Ita da Uwarta makirai ne Suje su karkatar da Hankalinshi ya Aure ta Ai ni na Kade Haduwa zasuyi da Garba su yakeni na Shiga Uku.."

Hajiya karima tace"Haba Alhaji yama za"ayi Haka ta Faru Ai Alhaji garba in bai Taimake ka ba, bazai yake ka ba Sai dai Ita Hajiya Sahuran don bata da Kirki kuma indai bai Auri Zubaida ba sai dai kowa ya Rasa.."Jinjina kai yayi yana Fadin",Shine mgana gaskiya..."

Kasim Dake Kofar Falon Tundazu ya Kariso yana Fadin"Abba nifa bana ganin laifin Bello kune masu laifi Tsakani ga Allah baku kyauta ba kuma ko nine irin matakin da zan Dauka kenan ."Yafada yana zama kujeran Datake Kusa data Inda Hajiya karima take zaune ita da Zubaida.

Harara Abba kabiru ya Laftamai kafin yace"Dillah rufemin baki Sakarai kawai,Ai Hashim yafika kirki Yana Kokarin Zuwa Gidan Muktar din yana Tusa kanshi Duk Domin Asirinmu ya Rufu Ammh kai baka ma Zuwa balle ma na saka ka alissafi.."Kasim dake Sanye da Riga da Wando Navy blue  Na kamfanin Armani,yace"Ai ina Kiran Ya Muktar ta Waya kuma Abba bana samun lokci ne kaima ka sani.."

Hannu ya Yarfa yana Fadin"Matsa chan ka bani Waje kaima baka da amfani ko Abota sai ku kulla Dashi Bellon mana Tunda Dama da kadan ya Girmeka mu samu Asirinmu ya Rufu kada yaron nan Yace zai yi Shari"a Damu Watarana.."Yamutsa Fuska Kasim yayi kafin yace"Nifa Abba bana son Raini ni,kaga yadda gayen nan yake wani cin mgani da Isa Wani Lokacin fa bai ma kaunar Hada Iska Dakai fa,Ni kuma Zuciya gareni ban Iya Juran Wulakancinsa Tun Kwanaki Dana Taba Kiransa Ya Tambaya ni wanene Inafa cemai nine kasim Dan Wajen Abba kabiru ammh Gayen nan yace bai sanni ba Kuma kada nakara Kiransa ya yanke Kiran.."Yafada Cikin Zafin Zuciya.

Shuru Abba kabiru yayi Kafin yayi Mgana Hajiya karima ta Rigashi da Cewa"Sai fa Hakuri Alhaji Ammh kam kunbi son Ronku,Tsakani ga Allah Ko bakomai Muhammed Dan"uwanku ne Da Kuke

Uba Daya kowa yaji Aikin Da Kuka yi sai yayi Tir daku.."Wata Uwar Harara ya zabga mata kafin yace"Rufemin baki Munafuka Ina ce Lokacin bada Shawarki nake amfani ba.."cikin Daga Hannu tace"A"a Wlh ni Haihuwa nace Ku Hana Hassatu bance ku kashe Rayu ka ba.."

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Shedan ne,Da kuma Kaddara Kuma duk Garba ne yaja Shi ya kawo Shawaran Gashi mun cika burin mu na Kauda Muhammed Da matarshi,Munkuma yi Nasaran Kwatan Dukiyan Ammh Sai gashi komai ya lalace Karshenta ma Namu ya"yan ne ke Ci karkashin nashi ya"yan da Muka Tozarta Allah kenan.."Yake Fada yana Sauke Numfashi.

Kasim yace"Abba Tunda kun Tuba Shikenan,Shima Ya Muktar din ai ya yafe muku Shima kuma Bellon komai zai Wuce Nan da Lokaci kadan.."Zubaida tace"Allah yaya Daada nan ce ke Bala"in Sonshi Shida Aneesa ko Guda bata kaunar ya Tabasu.."

Cikin Mamaki Hajiya karima tace"Wata Aneesa kuma...? Tafada Tana Wasa da gashin kanta Gyara kwanciya Zubaida Tayi kafin tace"Kanwar Anty Rahila ce Daddy muktar ya Daukota Daga Borno Shegiyar yarinya ce Ta nan sai Zuba iskancinta take Ko Ballon bata Shakka,Mkrantar Dayake koyarwa ma Take ,Tare suke Tafiya kuma in sun samu Hutu su komo Tare.."

Baki Abba kabiru ya Rike kafin yace"Kaji ko... ? Itama Matar nashi So Take ya Auri kanwar nata Kinsan Yan Bornon nan ba Kyau Tuni zasu ja Hankalinsa.."Kasim Dake zaune yayi Dariya kafin yace"Kai Abba Daga mgana sai kace zai Aureta.."zubaida tace",Anya Abba basa ga maciji fa yadda kasan Annabi da kafurai Shi kadai ke iya mata Hukunci agidanan Daada Tayi Shuru ko Anty Rahila bata iyawa da Fitinar Aneesa kamar Mai Bugun Aljanu.."Dariya ta kara Kama Kasim Cikin Nishadi yace"Niko har naji ina Sonta Domin ina son mace mai Tsiwa.."

Hararansa Hajiya karima Tayi kafin tace"Toh mara kunya.."Mikewa yayi yana Sosa keya yace"Umma,Abba ni zan Fita zan Shiga Cikin garin Wajen Abokina Shamo.."Hajiya karima ce Kadai Tace mai adawo lafiya Shiko Abba kabiru komawa yayi ya Zauna yana Wani Nazari Acikin Ranshi.

****

GRA-Katsina

ABBA GARBA HAUSE

  

Suma Duka iyalan gidan Suna Zaune A kayatattacen Falon na Gidan Abba garba,Harda su Hamdiya da Ummu salma da Inna Rukayyah Wacce Suka zo garin Jiya,kuma Sunfi Dasawa da Abba garban Shiyasa Take Sauka agidanshi kuma Matar Shi Sahura Wacce Suke Kira Mama Sahura,Makiran Macece Ta iya Duniyanci Tasan yadda Take Hillatan Mutum Shiyasa Kaf yan"uwan Mijinsu sunfi yabonta Fiye da Karima Umma kenan,Shiyasa basa zama Waje Daya Duk da Abaya sunyi Amintakan Munafunci Tunda Rabuwan Mazajensu yazo kowacce Ta Koma Tsagin Mijinta Shiyasa Inna Rukayyah ke Sauka gidan Abba Garba kuma ko Taje gidan Abba kabirun Umma bata mata Wani karban Mutumci.

Zulfa ce ke Basu lbrin Irin Wulakancin da Bello yayima Zubaida sai Dariya Suke Sha Tun barema Mama Sahura Dake Mirmishi Cikin Kissa Tace"Kash..Banji Dadi ba.."Tafada Tana kallon Inna Rukayyah Wacce Ta kada kai Tana Fadin"Ai ni Wlh naji Dadin Hakan,Duk da Muma bamu Tsira ba Wajen Ja'irin yaron nan ammh gwara yayi mata Haka din,ko ba komai ni Nafison In ma Auren Bellon zaiyi ya Auri Zulfa Saboda Daga Kariman har yarta basu da Kunya sam."

Cikin Kissa Mama Sahura tace"Ah inna ba komai Ai Duk Dayane da Zubaidan da Zulfan Duka Namu ne,Fatanmu Dai Shine ya zabi Daya Cikinsu yadda bazai Auro na Waje Balle har tazo Taji Abunda ya Faru ta Zugashi ya Dauki Mataki bq.."Inna Rukayya ta Girgiza kai Tana Fadin"Hakane...Ammh ni nafi son ya Daidaita da Ita Zulfan,Ai mganar Gaskiya Su kabiru sunyi kuskure Babba,Rudin Shedann Dana Zuciya ya Debesu Kuma Tunkafin Su Fada da bakinsu mutane Su ke Zargi Saboda yadda Suka Hau Dukiyar Marayun,Kinga fa Haryanzu chan Jikamshi Gulmar Dake Tashi kenan.."

Mama Sahura tace"Umh Inna Wlh Alhaji baida Tunanin Kashe Rai,Duk Yaya kabiru ne Yaja Shine mugun Shi ya Dinga Forcing Dinshi har ya amince,Ammh Haryau kukan Nadama yake Yana kuma ganin Laifin Yaya kabirun Daya Dorashi kan Wannan Kuskuran.."

Inna Rukayya tace"Hakane Ai Shi kabiru akwai Hange Hange ne,Allah dai ya kyauta don ma Mun Samu Shi Babban bai Dauki Abun da Zafi ba Shidai Bellon Shine Naga kamar Yana da Wani Shiri ne.."Mama Sahura ta gyara zama Tana Fadin"Shine ai Inna Mukesi mu Jawoshi ajikinmu yadda ko Yana da Niyyar Wani Abu Sanadin Hada Surukanta damu Dole zai Hakura,Ko Zulfan ko Zubaida Duk Wacce ya Aura Insha Allahu Shima zai Manta komai.."

Jinjina kai Inna Rukayyah Tayi kafin tace"Hakane kam..Toh Allah ya bada Sa"a Kafin na Koma zanje Abujan Insha Allahu..."Da Sauri Hamdiya tace"Inna zan biki Banta ba zuwa ba.."Ummu Salma tace"kin ma isa Wlh Dani za"a Je.."Tafada Tana Hararan Hamdiyan Dariya Inna Rukayyah Tayi kafin tace"toh duk naji Gabadayanku Zamu Tafi Ba Dadewa zamuyi ba bai Wuce mu kwana biyu ba Dagachan zamu koma kano Saboda Hutu ya kare.."Jin Haka yasa Suka kama Murna Zulfa na gefe tana latsawa waya cikin Mirmishi tace"Daddy bai da Mtsala Uncle Bello ne Mai Damuwar Inna Shifa bai kaunar ganin Wani Daga Cikinmu Agidanman Saboda mu Har yaji yakema Abuja Mutum kamar Zuciyar kafiran Farko.."

Inna Rukayyah tace"Nagani Zuwana na Farko Diban Albarka da Yaron nan yamin kamar nayi kwallah ,muktar din na mai mgana ya gaisheni Wlh ko Waigowa baiyi ba ya Fice Da Hanzari kamar yaga kashi.."Tafada tana Rike baki Mama Sahura tace"Hmm Haka fa yakema Kowa Ko Su Alhajin basu Tsira ba baya gaishesu..."

Inna Rukayya tace"Gadon Zuciyar Bakaken Fulanin nan ne na Dangin Uwarsu.."Mama Sahura tace"Wlh Haka Alhaji yace.

Daga haka suka Cigaba da Hiransu Sama sama Duk dai Akan Bello ne da Irin Rashin Mutuncin Dayake ma Duk Wanda ya Fito Daga Tsatson Abba kabiru ko Abba garba.

*******

Kwanci Tashi babu Wuya Awajen Allah gashi Har Hutu ya kare,Tuni Daliban GGUSS kwatar-kwashi Sun koma Harda Wasu Daga Cikin yan Jss3 sun Dawo SS1 ciki Harda B.kaita Ita da S.jibiya Tun kwana uku da Yin Resume Suka Dawo Mkrantan Amatsayin Senoirs.

Aneesa ko bata da Masaniyar Komai,Duka gidan ba Wanda Yama Bello Mgnar Aneesa,ganin Tun Satin da Wuce Mallam Inuwa ya maida sa Sch Din sai Kowa ya sakankace kan,Bello ya Bar Aneesa Ta cigaba da Jeka ka Dawo,ko da Su B.kaita suka ga Me bello Jikamshi ya Dawo Shi kadai sai Suka Cire rai kan Aneesa baza ta Dawo ba jidda madaki da Suka Dawo suka Iske Suna Neco sun kusa gamawa Har Dakinsu Tazo Neman Aneesa suka Sanar da Ita Aneesa bazata Dawo ba,Hakika Yan Ajinsu Sun Dawo Da yawa yayinda Wasu kuma Basu Dawo ba,Dalibai dadama in Sukaga B.kaita da S.jibiya Sai sun Tambayesu Aneesa Su kuma Cikin kewa Suce Anee bazata Dawo ba Wasu Dayawa Sunji Dadi wasu kuma basu Ji Dadi Ba Domin Aneesa Ta zama Cele by Force Ackin mktantar Sabida bakinta da Kuma Tana kanwar Da Handsome man Mr.Bello jikamshi.

Aneesa Har party Ta Hada Bayan Komawar Bello Makranta Ita Da Hibba Suka chashe,Ashe Tungunne bata kare ba Duka Duka Satin Bello Daya Da Tafiya yama Ya Muktar Waya kan Ashiryama Aneesa kayan provisin da Abun Bukata Ranar Monday zai zo su koma Tare,Ya Muktar Cikin mamaki yace mai"Na zata zaka barta ta Fara Jeka ka Dawo anan Abuja.."

Cikin Gimtse Fuska Bello yace"No...Nan zata Cigaba Har ta Kamallah.."Daga Haka ya Datse Kiran,Ya Muktar Kuwa kai ya girgiza kafin yace"There is a War In Aneesa Taji Lbri ."Bai gayama Kowa ba sai Anty Rahila Wacce Ta nuna Taji Dadin Haka Ita ke Fadama Daada,Wacce Har Awaya Ta Kira Bellon Yana Jin Mganar Aneesa ne yace"Wlh Tallahi Daada...Mgana Daya bazan Chanza ba Aneesa Bazata bar Kwatar-kwashi ba sai ta kamallah Secondry Duka Tukunnah.."Tunda Daada Taji Haka batama bata ma kanta Lokaci ba Ta Kashe Wayarta.

Anty Rahila da Aneesan Direba ya Daukesu Suka Shiga Mall Suka mata Siyayyah ammh Data Tambayeta sai tace Borno Zata Tura ta ta musu kwana Biyu,Aneesa bata wani soZuwa barno ba Saboda Takuran ya Ali,gashi ita kuma bata wani Shaku da mama Falmata ba Tamafi Shakuwa da Hajiya yana,Ga dai Wanda Tafi Shakuwa Dashi Sosai nan Marigayi Alhaji Bukar Bulama...

Haka dai Suka Dawo Gida Aneesa na Kuncin Zuwa Borno,Daada da Anty Rahila ba Wanda yace mata Kanzil,Ranar Lahadi kuwa sai ga Bello ya Diro Abuja Shida Uncle Aminu Wanda Ita Aneesan bata ma san Zuwansu ba sai Wajen yamma Tana Falon Daada Suka Shigo Tunda Ta gansu sai Jikinta bai Bata ba,Tana gaishesu Aminu ne kadai ya amsa Bello Cikin Tsare gida ya kalleta kafin yace"Ki Tsefe kanki kiyi Kitso ki kuma Shirya Abubuwanki masu amfani gobe zamu Wuce Dake.."

Aneesa Ta zaro Ido Waje kafin tace"Zuwa ina kuma...?

Harara ya sakarmata kafin yace"Zuwa Makranta.."Wani Zabura Aneesa Tayi kafin ta Dora Hannu Akai ta Zumduma Ihu,Wanda Sai da Suka Toshe Kunnuwansu Daada Dake Daki Ta Fito da Sauri Tana Fadin"Lafiya...?

Tasamu Amsan Tambayanta ganin Aneesa malale Akasa Tana Kuka da Birgima Tana Fadin Ita babu Inda Zata Tafi sai dai Akasheta.."Uncle Aminu gefe yaja Aranshi yana Fadin"Yarinyar nan Yar bala'i ce.."Shiko Bello Belt din Kungunshi ya Fara Warwarewa yana Fadin"sai dai ki Mutu ko..? Lalle ko zaki mutu da duka,kinga sai na Dauki gawanki na kai makarantan Bushi girl kawai.."