7&8
MANARAH
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
DEDICATED TO
ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰
PG 7&8
... A gaggauce Nurse ta riko Deena da ke faman kururuwa ga jini ya wanke mata fuska.
Shukura kuwa ko a jikinta domin ta san duk rintsi Hisham ya na a tare da ita.
"Amma dai ku dabbobi ne ko? Ta ya mun aje mara lafiya za ku zo kuna yi mana fada har ku fara zubar da jinin junanku?"
Nurse ta karasa maganar cikin zallar ɓacin rai.
"Kada ki fada nuni ba daɗi ke ma yanzu goshin naki ya zubar da jini"
Ce war Shukura
"Sister ba wannan maganar ya kamata mu yi ba. Kamata ya yi mu ceci rayuwar wannan baiwar Allah. Kada mu barta ga shi sai rasa jininta take"
Ta karasa maganar tare da kamo Deena da ta fara ganin mutane na koma mata bibbiyu.
Alhaji ne ya zo zai shiga dakin da Umma take, taron mutane da ya hango kofar dakin da Hisham ya ke ga kuma hayaniya ana ta yi ne ya saka shi shiga dakin da sauri.
Fuskar Deena da ya gani ita ce ya shaida domin bai manta biyo Hisham gida da take yi ba.
Wani ƙululun bakin ciki ne ya tokare masa zuciya lokacin da Nurse ke kora masa bayanin abinda ya faru.
"Ka yi asarar sannan ka ji kunya. Kana a gadon jinya amma karuwanka sun cike maka daki. Tsabar baku da hankali fada hada zubar da jini, na yi nadamar kawoka wannan duniyar. Da na san kai za a haifa mini uwarka ma BA zan bari ta haifa ba"
Ya karasa maganar cikin zallar ɓacin rai.
"Daddy BA haka bane. Zuwa sukayi yi su duba shi shi ne wannan tsautsayin ya faru. "
"Rufe min baki. Ai duk jirgi ɗaya ne ya kwaso ku."
Ya na karasa maganar ya fice.
Hisham kuwa dannar zuciyarsa ya ke domin da an sake ya furta koda kalma ɗaya ce ba zata yi wa mahaifinsa dadi ba ko alama.
Bayan an fita da Deena Shukura ma tafiya ta yi da nufin gobe zata dawo. Sai dai abinda Hisham bai sani ba Shukura ta na cikin asibitin.
Alhaji kuwa cikin ɓacin rai ya shiga dakin da Mahaifiyar Hisham ke kwance, farkawar ta kenan ta ji sallamarsa. Bata ɗago ba bare ya saka ran zata kallesa har ya zauna gefen gadon.
Kasancewar Mahaifiyarta ta zo gaisawa suka yi da Alhaji. Ganinta da yayi shi ya dakatar da shi daga maganar da ya so yi wa Safiya.
"Safiya magana fa ake miki"
Mahaifiyarta ta fada.
"Mama ki kyale shi don Allah. Kome ya zo karshe Alhaji ya sakeni."
Salati mahaifiyarta ta hau nanatawa cike da tashin hankali. Shi kuwa Alhaji fiƙi-fiƙi ya yi da ido cike da rashin gaskiya.
"Ayi hakuri Mama. Kuskure ne dai anyi amma tuni na mayar da Safiya. Hisham ne duk wata matsala da muka samu shi ne sanadi. Yanzu haka ya cika dakinsa da karuwai ana fada har an fasawa daya daga cikinsu kai"
Mama mace ce me matukar kawaici saboda haka kasa magana ta yi. Umma kuwa jin abinda ya fada bata san lokacin da ta fizge karin ruwan da aka saka mata ba ta fice dakin da gudu.
Mama na kira amma ina sai da ta yi nasarar shigewa dakin.
Jingine da gado ta hango shi. Da sauri ta karasa kusa da shi tana masa sannu, "Mahaifinka ya ce ka cika daki da karuwa. Hisham kana so zuciyata ta buga in mutu ko"
Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa ya na girgiza kai.
Shigowar Mahaifinsa ta saka shi hade rai.
"Haba Hisham! Kai fa yanzu ba yaro bane ka wuce duk wadannan abubuwan. Ka dawo cikin hayyacinka mana, haba yaron albarka nan gaba fa kai ne matsayin uba ranar da Mahaifinka ya kauce"
Mama ta karasa maganar da sigar rarrashi.
Tsoki Alhaji ya ja ya fice daga dakin a matukar fusace.
Bangaren Deena Kuwa bayan ta dawo cikin hayyacinta wayarta ta lalubo.
Sai dai ƙasa yin komai tayi face kukan data fashe da shi.
"Hisham ni? Ni zaka yi ma haka a gaban wata banza wulakantacciya kake nuna ka fifitata fiye da Ni? Sai na janyo mata masifar da har ka mutu ba zaka taba mantawa da ni ba a cikin rayuwarta."
Ta na karasa maganar ta kira mahaifinta.
Zaune ya ke cikin katafaren falon gidansa dake shaƙar da kayan alatu.
Wayarsa da ya ji ta fara ruri ce ya kalla. Da sauri ya dauka ganin wanda ke kiran.
Tamkar wanda aka tsikara da allura haka ya mike tare da furta.
"Dan gidan waye a cikin kasar nan. Ita kuma da ta zubar miki da jini waye Ubanta a kasar nan?"
Jin an ambaci zubar da jini a rikice Momy ta mike ta na tambayar lafiya.
"Babu lafiya domin an taɓo ɗiya ɗaya tilo da na haifa. Babu yadda banyi da ita akan ta rabu da yaron can ba amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ce shi take so. Ni kuma duniya Indai ta na son abu hakika zanyi mata shi. Yanzu haka ta na asibiti wata me rabon wahala ta fasa mata kai."
"Dadyn Deena wallahi ko me Deena ta zama kai ne sanadi. Kana da hannu dumu-dumu babu yadda banyi da kai ba akan sakin ta da muka yi take abinda ranta ke so, amma ka nunamin ai duk cikin gatane. Kudi, gidaje, motoci sai wanda ta zaba a matsayinta Na mace wadda wata rana gidan wani zata tafi..."
Tsawar da ya daka mata ce ta sakata yin shuru.
"Ba don na san ke kika haifi yarinyar nan ba da sai In ce don ba diyarki ba ce kike mata haka. Kin sakawa yarinya ido bayan ita ɗaya muka haifa a kaf fadin wannan duniyar, in banyi Mata gata na riritata ba wa kuke so in riritata? A kan yarinyar nan zan mummunan saɓa miki"
"Allah ya huci zuciyarka in Shaa Allah BA zan sake saka maku baki ba"
Ta na karasa maganar ta shige daki tare da share guntun hawayen fuskarta.
"aikin banza. Har ni za ki kawo ma wargi a cikin al'amarina? In dai a kan Deena ne sai In karar da duniyata. Abinda ya saka nake ɗaya miki kafa don ke kika haifi yarinyar nan."
Yana kaiwa nan ya fi ce daga gidan tare da masu take mai baya.
Dpo ya kira ce War ya na son jami'an tsaro su iske shi asibitin gwamnati.
Deena da ke zaune ita ɗaya bayan an gama gyara mata goshinta an mannesa da bandeji. Jin shigowar mahaifinta ya sakata sake rushewa da kuka .
"Subhanallah! Mamata wa ye ya miki haka"
"Daddy kasheni suka so yi, ka taimaka ka bi min hakkina da kyar aka kwaceni a hannunsu.
Bai bata lokaci ba ya saka jami'an tsaron shigowa kai tsaye suka nufi dakin da Hisham ya ke kwance.
Sauran marasa lafiya kuwa ganin 'yan sanda kowa ya yi ta kansa kallo ya koma dakin.
Umma na zaune ta ji shigowar su a rikice ta mike ta na salati.
Mahaifin Deena kuwa cikin ɓacin rai ya fara magana.
"Fada mini wane ne daga cikinsu ya yi miki haka?"
Alhaji da shigowarsu kenan dakin da sauri domin labari ya kai masa ga jami'an tsaro nan.
Da mamaki ya ke kallon Hisham.
"Ga shi nan sai dai ku kamasa shi daya. In ya so ku ƙullesa har igiyar ta ruɓe"
Mahaifin Hisham ya karasa maganar cikin ƙunar zuciya.
"Daddy BA Shi ba ne mace ce fa. Kada ku kamashi."
Deena ta karasa maganar cikin tashin hankali.
"Alhaji ni ce fa limamiyar wannan aikin"
Suka tsinkayo muryar Shukura na fada. A ƙufule Alhaji ya juyo sai dai suna haɗa ido cike da mamaki ya furta "Shukura!"
"Yawwa Daddy ita CE tsinanniyar da ta fitar min da jini. Ka saka a kamata a kulleta ta gane ba irina wadda ta fita gata ake yiwa haka ba"
Falau! Mahaifin Deena ya tsinke Deena da lafiyayyan Marin da ya sakata ganin duhu ya mamaye mata ido...
👇👇👇👇👇👇
***