MANARAH

9&10

by @meenatyandoma

MANARAH

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰

PG 9&10

....Zafin marin na gama sakinta a fusace ta juya domin ganin wane isasshen ne. Domin a tunaninta Hisham ne, sai dai abin ya zo mata a bazata domin mahaifinta ta gani a cikin wani irin yanayi wanda ba ta taɓa ganinsa ba.

Kafin ta furta wata magana ya karbe zancen.

"Ashe baki da hankali! A gabana kike fada mata irin waɗannan maganganun. Da na san ita ce ta yi miki haka ko da wasa ba zan kwaso kasa inzo wurin nan ba da sunan daukar mataki"

Ya karasa maganar tamkar ya fizgo Deena ya ci gaba da jibga.

Ita kuwa Deena mutuwar tsaye ta yi domin ta fi tunanin wannan mafarki ne take yi. "Kai aa, mahaifina da nake so da kauna shi ne zai yi mini haka. "

Ta karasa maganar a ƙasan zuciyarta.

Duk wanda ke cikin dakin matukar mamaki ne ya kama shi. Musamman Hisham da ya san irin kaunar da mahaifanta ke mata.

Ganin mamaki ya ki sakinta ɗauke da murmushin da ita kadai ta san ma'anarsa ta karasa a gaban Deena.

"Hayaniya ko hayagaga ba su bane ke nuna kin kai ƙwarya a bariki. Ko a haka aka tsaya ina me tabbatar miki na gwada miki na miki zarra fintin kau a bariki. Ina tare da Mahaifinki sannan tare nake da Saurayinki, a kaina Ubanki zai iya sakin wannan tsohuwar da kika bari a gida."

Shukura ta karasa maganar tare da dafa kafadar Deena.

"Karya kike. Ni ba sa'arki ba ce, ke matsiyaciya na nasan ba haka kika barsu ba "

Deena ta karasa maganar cikin ƙaraji ta na me kokarin shaƙe Shukura.

A karo na biyu ya sake tsinketa da marin.

"Na fuskanci ba ki san wacece tsaye a gabanki ba. To a kanta zan iya yin komai duk son da nake miki."

Ya karasa maganar tare da fizgo Deena suka bar cikin ɗakin.

Kaka da duk tsoro ya gama kamawa ganin anzo tafiya da jikanta. Ajiyar zuciya ta sauke.

Mahaifinsa kuwa ba haka ya so ba don haka a fusace ya bar dakin.

"Hisham! Wace ce wannan?"

Shuru ya yi ba tare da ya ce uffan ba.

"Hisham Mahaifiyarka fa ke tambayarka"

Kaka ta karasa maganar cikin sigar rarrashi.

"Beb ɗina ce. Umma kin dai san komai bana son tambayoyi, Umma ya kike so ke ma ki zama irin sauran ke kadai fa kike kaunata kaf a cikin gidan can"

"Na sani Hisham! Suma sauran su na kaunarka halinka ne ba su so. Ita rayuwar nan da kake gani takaitacciya ce yau ina raye gobe fa? Abinda ke faruwa tsakaninka da Mahaifinka ko alama bana jin dadinsa. Mace fa ce nan tsaye macen ma ga dukkan alamu karuwa. Ina kula da addininka ina ilimin ka, ina nutsuwarka? Hisham me kake so ka zama?"

Kallon Shuruka ya yi mata alama da ta fice, ba musu tabar ɗakin.

"Umma addu'a za ki yi min wata rana duk zai mana tarihi"

Inda sabo ta saba da jin irin maganganun nan a bakin Hisham. Ta na rokon Allah wata rana duk su zama tarihi.

Hajiya kuwa tun bayar zuwan Mahaifiyar Safiya asibitin ta koma gida. Babbar ɗiyarta Zainab ta Kira.

Duk tambayar da su Nana ke mata taki sanar da su haƙiƙanin abinda take shiryawa.

Farida CE ta Kula ran Mahaifiyar tasu a bace ya ke. Don haka su shuru suka yi suna jiran zuwan Zainab.

Ba a dauki dogon lokaci ba sai ga ta ta iso.

Bayan sun gaisa take tambayar ina dayar munafukar da ɗan ta suke. Kaf abinda ya faru mahaifiyarta ta kwashe ta fada mata.

"Wallahi Hajiya so na yi a ce yadda ta yanke jiki ta fadi ta zarce har lahira"

Zainab ta karasa maganar tana laluben jikkarta.

"Me kuke ci na baka na zuba? Daga ita har shi lokaci suke jira. Ɗaya bayan ɗaya za su rika tafiya har shi Alhajin. Yanzu dai bani maganin da Boka ya baki"

Wasu tarkace ne ta fiddo tare da tsube su a gaban mahaifiyarta.

"Wannan maganin ki zubawa Daddy a cikin abin sha. Ki tabbatar ya gama shanye shi tas kada ya bar koda kadan ne. Ita kuma wannan ɗiyar me kama da Aljana boka ya ce ki samu wani lungu a cikin ɗakinta ki boye muddun Daddy ya tunkari ɗakin zai ji tsabar tashin hankali da damuwa firgita zai rika yi ba zai kara shiga cikin ɗakinta ba."

"Yawwa Boka haka nake so. A yanzu kam ko babu raina nasan ba za ku sauka a kan turbar da na ɗoraku ba."

"Amma Hajiya a kwai dai sauran rina a kaba. Boka ya ce lamarin Hisham a wannan karon wani haske ya rufe masa ido."

"Ban gane ba Zainabuna. Wane haske kuma, sanar da ni abinda ke faruwa"

"Hajiya ni ma bai yi mini bayani ba. Kawai dai ya ce mini ki yi gaggawar zuwa gobe."

"Dole na kuwa. Ya boka zai min haka"

"Yanzu dai ku tashi mu je in samu inda zan maƙala wannan ɗiya. Kafin waccan baƙar jaɓar ta dawo"

"Ni Hajiya bakin cikina har gobe Daddy ya ƙi yi ma Hisham korar kare daga cikin gidan nan. Har yau fa bai datse kudin dake shiga Account din sa ba"

Nana ta karasa maganar ta na cuno baki.

"Haba Auta. Kara hakuri kadan ba kudi ba dukiyar duka ma kun kusa mallaketa"

Ta na karasa maganar suka nufi ɗakin Umma.

Bincike suka yi ba kadan ba. Can bayan Tvstand suka saka diyar robar da kallo ɗaya zaka yi mata ka sai gabanka ya fadi.

"Munafuka. Sai gidan nan ya gagareki zama sai kinyi nadamar haihuwar ɗa namiji"

"Faɗi ki ƙara Hajiya. Ni ce babba a gidan nan amma haka Daddy ya ɗauki Hisham ya kai ƙasar waje, ni kuma ya barni cikin kasar nan kamar baya so na"

"Ki daina tuna mini Zainab. Na kunshi bakin ciki ba kadan ba amma yanzu su ke ƙunsar nasu, nan da lokaci kadan zamu bataya a cikin gidan nan"

Cike da jin dadi suka fito daga cikin ɗakin suna zagin Safiya.

Zainab bata bar gidan ba sai da duhun magriba ya fara....

Tafiya take yi a galabaice hannuwanta dafe da ƙaton cikin da ke gabanta.

Kallo daya za ka yi mata ka gane a galabaice take yadda suturar jikinta ta jigata da datti wani sashenta kuma ya barke.

Gashin kanta a kwance ya ke ya baje a tsakiyar fuskarta duk datti ko alama ba zaka iya shaida fuskarta ba. A bisa tsautsayin kafarta ta goce ta fada wani rami. Ta saman cikinta ta faɗa, wata irin ƙara da kururuwa ta saki.

Cikinta ne yayi wata irin murɗawa lokaci daya jini ya ɓalle. Matar da ta gani tsaye a kanta ya sakata yunkurin miƙewa sai dai lokaci ɗaya komai ya tsaya mata, a sama-sama ta riƙa jiyo kukan jariri kafin wani bakin duhu ya mamaye idanunta...

FREE PAGES SUN KUSA KAREWA. KU TURO 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 8133562798 OPay Amina Abubakar

MASU TAMBAYAR GROUP KU SHIGA NAN 👇👇👇👇

***