MANARAH

11&12

by @meenatyandoma

MANARAH

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai maki a duk inda ki ke 🫶🥰

PG 11&12

... Hisham da ke bacci a rikice ya miƙe ya na rarraba ido sakamakon kukan jinjirin da ya yi wa kunnuwansa dirar mikiya.

"Lafiya kuwa? Ko jikin"

Umma ta jefa masa tambayoyin.

Shuru ya yi domin ji ya ke kamar a bayan dakin da ya ke ne jinjirin ke ta tsanyara kuka.

"Umma ba ki ji kukan jariri ba?"

Jin abinda ya fada da sauri Umma da Kaka suka kalli juna.

"Aa kunnuwanka ne ke maka gizo. Babu kukan jaririn da muka jiyo, a cikin tsakiyar daren nan wane kukan jinjirin za mu ji. Sai dai in jinjirin aljanu ne."

Umma ta karasa maganar cike da tsabar mamaki.

"Ku barni in fita in duba domin kukan da na ke ji ya tsananta yanzu haka suna na nake ji ana kira"

"Subhanallahi! Ka fita ina? Ɗannan ka yi hauka ne? Ka ga ka kiyayi kanka yanzu haka Jinnu ne ke so su yi maka wasa da hankali. Don haka babu inda za ka fita"

Kaka ta tarbe haryar.

"To kila ke in kika fada masa zai ji. Yanzu kai ko da kudi a ka ce ka fita a tsakiyar daren nan sai ka fita? Haba Hisham ka yi ma kanka karatun ta natsu mana"

"Na ji ba zan fita yanzu ba amma dole ne gobe a sallame ni, na warke babu inda ke mini ciwo ko ba a sallame ni ba zan sallami kaina"

Ya karasa maganar tare da juyawa ya kwanta.

Tun bayan da ya kwanta Umma ke tofa masa addu'a har sai da kowa ya yi bacci a dakin ya rage saura ita ɗaya.

Doguwar ajiyar zuciya ta sauke. Yaƙi take da zuciyarta akan kada ta gasgata mata abinda take zargi game da Hisham. Allah ya sani gani take tamkar akwai saka hannun Jinnu a wasu abubuwa, amma sanin halin Jinnu da tayi da zarar ka gasgata su to fa shi kenan sun samu malafa a jikin mutum.

Deena kuwa duk da mahaifinta ne tsaye a kanta ta kasa saurarena face kuka da take cizga tamkar ranta zai fita.

Daren da ya tsala ne ya hana ta fita ta bar gidan ko zata ragewa zuciyarta raɗaɗin da take yi mata.

"Deena!"

Ya Kira sunanta cikin murya me dauke da nuna rarrashin wanda aka ɓata mawa.

Ɗan tsagaita kukan ta yi ba tare da ta amsa ba ta kalli mahaifin nata.

"Me ya sa ba za ki fahimceni ba? Kin san dai kaf duniya ke daya nake yiwa wata irin mahaukaciyar soyayya. Ki saurareni mana"

"Daddy a baya ne kake so na. Amma tunda ka wulakanta ni a gaban waccan ƙaruwar na tabbatar ka daina so na. Ni ka kyaleni in fita in bar maka gidanka, tunda nake da kai baka taba ɗaya min hannu da sunan duka ba sai yau"

Murmushin da shi ɗaya ya san ma'anarsa ya yi.

"Haba Mamana. Kada ki bari zuciya ta rika zugaki mana, ke fa shaida ce a kan irin soyayyar da nake nuna miki taya zan so wata bayanke? Ki kyale wannan zancen domin Shukura da kike gani ita ce arzikina duk facakar da muke da duniya ki sani ta sanadin Shukura ne. Ki kwantar da hankalinki kada ki bata darenki da damuwar wadda ni na san moriyar ganga nake ci"

Ya na kaiwa nan ya fice daga dakin.

Hajiya da ke labe tunda suka fara maganar kuka ta fashe dashi tare da saka hannuwanta biyu ta toshe baki gudun ka da su ji ta nufi dakinta da gudu.

Deena kuwa Kukan da take ne ya tsaya tare da tunanin me mahaifinta ke nufi da Shukura ita ce sanadin arzikinsa? Wace ce ita in Banda wadda take matsiyaciya a cikin matsiyata. Ta ya zai yi arziki da faƙiriya?

Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai da garin Allah ya waye da rana gaɗe-gaɗe ta yi sallah.

Tunda ta fito falon gidan ta hade girar sama da ta ƙasa domin jikinta ya bata Dadynta ya jima da fita. Mikewa ta yi da sauri zata nufi dakinta.

"Dawo ki zauna"

Ta tsinkayo muryar Hajiya na fada.

Ba don ta so ba sai don bata da yadda zata yi ya saka ta koma ta zauna.

"Deena wace ce Mahaifiyarki?"

Da mamaki ta kalli Hajiya.

"Ki amsa mini tambaya ta"

Hajiya ta fada cikin hade rai.

"Hajiya ke ce mana"

"Ma sha Allah. Da kika fahimci ni ce Mahaifiyarki sai dai ko alama baki daukeni a matsayin uwa ba, shin kaiwa ne banyi ba ko tsabar baki gani na da daraja ne?"

"Haba Hajiya! Me kuma ya kawo duk wadannan maganganun?"

"ke kika kawo su Deena, muddun ba za ki shiryu ba ki nutsu ki kama kanki a matsayinki Na mace wallahi ba za ki ga daidai ba. Ba tun yau ba Allah ne shaida ta iyakar kokari ina fada miki gaskiya, amma kullum ginin da na yi ke da Mahaifinki rushesa kuke. Deena Baki tsoron mutuwa ta ɗauke ki a halin da kike Ciki? In kika je kicewa Allah me? Ke mace ce ko babu mutuwa akwai tsufa duk daren dadewa aure za kiyi ki haifi yara so kike yadda kike ƙunsa mini baƙin ciki ke ma yaranki su rika ƙunsa miki? Kin mayar da kanki karuwa jaki da doki kowa jikinki ya ke samu a arha?"

Kamar jira take Hajiyar ta numfasa ta cabe zancen.

"Ni fa Hajiya ki fahimce ni. Mutum ɗaya ne nake tarayya da shi wato Hisham! Kuma shi ma ai aurensa zanyi nan bada jimawa ba. Kuma ma ni kam ba Daddy ya hana kiyi min fada ba?"

Hajiya bata yi mamaki ba domin inda sabo ta saba, mijin nata ya gama lalata Deena sai dai fatan shiriyar Allah.

Tamkar ba ita takewa nasiha ba haka ta mike ta bar Hajiya zaune ba a dauki dogon lokaci ba ta fito cikin shigar banza ta fice.

Hawayen da suka gangaro kumatun ta ne ta share.

"Ya Allah baka manta da ni ba, Miji bin mata ɗiya bin maza. Ya Ubangiji kasan zan iya daukar wannan jarabawar shi ya sa ka jarabceni. Ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawar ba don halina ba ya Allah."

Kukan da ya ci karfinta ne ya tilasta mata yin shuru.

Hisham kuwa kasancewar daren jiya aka gama kara me jini a yau ya tayar da bore dole a sallamesu.

Da kyar likitan ya amince zai sallamesu da sharadin nan da mako daya su duka zasu dawo ganin likita. Bayan anyi sallama Kaka bata yarda ta bi su gida ba kai tsaye gidanta ta wuce domin ba zata iya da matsalar gidansu Hisham ba.

Tun daga farko falon suke zabga sallama amma shuru kamar babu mutane.

Hajiya ce da Farida sai Nana wato Auta zaune cikin falon suna kallo abinsu.

In da sabo Umma ta saba da halinsu don haka ba ta damu ba suka yi gaba ita da Hisham.

"Mtsww! Su balamu anyi asarar kunnuwa, Allah mun gode maka da ba mu zamewa mahaifinmu annoba ba a cikin gidan nan"

Nana ta ƙarasa Maganar ta na taunar cingam.

Kafin Umma ta ankara Hisham ya yi wuff ya wanka wa Nana mari.

Ihu da kururuwa ta fara tare da fadawa jikin Hajiya.

"Hisham me zan gani haka? Cin zalin yarinya karama me ta yi maka?"

Ta karasa maganar ta na firfita Nana

"Oow! Wai baki ma gane me ta yi mana ba ko? To isar da na yi ce na cika na batse, kin san gawurtaccen ɗan iska idan ya cika ya batse babu wanda ya ke ɗaga mawa"

Hisham ya karasa maganar tare da kokarin ciro belt.

"Allah ya isana ban yafe maka ba duniya da lahira. Lalatacce haihuwar asara"

Kafin ta ƙarasa aika masa da waɗan nan mugayen zagin ya hau jibgarta da belt tamkar Allah ya aikosa.

Duk yadda Umma ta so ta hanashi abu ya ci tura ta kasa kusantar inda ya ke.

Hajiya kuwa ganin zai kashe mata Auta tsakiya ta shiga. Hisham bai bata lokaci ba ya ci gaba da jibgarsu su biyu.

Jin ihu yayi yawa ya saka Alhaji fitowa a gigice. Farida dake tsaye ta rasa yadda zata yi ne ta nufesa tare da fashewa da kuka.

"Abba zai kashe su ka taimake mu"

A rikice ya shiga tsakiya ya na me daka masa tsawar data maidosa cikin hayyacinsa.

"Ashe baka da hankali, kai wane irin dabbane matata uwar gidana ita zaka yiwa wannan cin mutumcin?"

"Ni ba ita nake duka ba shiga tsakiya ta yi shi ne na gwada mata ma'anar ɗan iskan da ta jima ta na kiran.."

Marin da Mahaifinsa ya tsinka masa ne ya saka shi yin shuru.

"Na yi nadamar haihuwarka Hisham na tsaneka. Da na san kai za a haifa Mani da ban auri Mahaifiyarka ba. Ka fi ce min daga gida ko da wasa kada in sake ganin ƙafarka a cikin gidan nan" ya karasa maganar tare da nuna masa hanya

"Sai me in Ka koreni! Ko baka koreni ba zan bar maka gidanka ka kwaɗa ka cinye. Na tafi in na tsaya kome zai iya faruwa"

Ya karasa maganar cikin ƙaraji.

Ba Umma kadai ba hatta! Alhaji sai da gabansa ya yi wata irin mummunar faɗuwa, domin yau ce rana ta farko da suka fara ganinsa a cikin irin wannan yanayin.

Kafin su yi kwakkwaran motsi ya fada dakin mahaifiyarsa ya dauko key din motarsa.

Jin irin wutar da ya ba motar ya fice da matsiyacin gudu ya saka Umma durkushewa saman gwuiwoyinta tare da fashewa da kuka.

Hisham kuwa tun bayan fitarsa gudu ya ke kwalawa tamkar zai tashi sama. Duk inda ya kutsa a take motoci ke bashi hanya, saboda ba su raba daya biyu a tunaninsu wani abu ya sha ko kuma baya da cikakken hankali.

"Na tsaneka! Ka fita ka bar mini gida"

Maganganun mahaifinsa suka ci gaba da yi masa amsa kuwa cikin kai.

Gudu ya ke ba tare da sanin ainahin inda ya dosa ba, ganin ya bar cikin garin Kaduna parking din motar ya yi ya ci gaba da tafiya da ƙafafunsa ya na ƙara kutsa kansa cikin jejin ba tare da sanin inda ya dosa ba. Tafiya ya ke ba tare da ya san inda ƙafarsa ke sauka ba.

Tamkar an latsa masa remote tsayawa yayi cak! Ya na karewa kogon kukar kallo. Mafarkin da yayi ne ya dawo masa sabo fill, "wannan shi ne kogon da aka fizgoni na fada ciki a mafarki" kukan jaririn da ya ji ne ya yi nasarar katse duk wani tunani da ke a cikin ransa.

Tamkar wanda magana ɗisu ke ja haka ya afka cikin kogon. Duk da duhun dake akwai bai hana shi hango jinjirar da ke kwance ta na tsala kuka ba.

Tamkar wanda ake ingizawa haka ya dauki jinjirar. Tamkar anyi ruwa an dauke kukan da take haka ya tsaya, dariya aka kece da ita wadda ta haddasawa kogon amsa kuwwa. Ba shiri Hisham ya zube bisa guiwowinsa....

500 NE KUDIN WANNAN LITTAFIN, DAGA YAU ZUWA GOBE KADAI ZA KU BIYA 300 A WANNAN ACCOUNT NUMBER 8133562798 Opay

Amina Abubakar

JOIN this channel for more pages👇👇👇

***