PAGE 16.
by @sumy6163
💫RASHIN SANI 💫💫
STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).
Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.
Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.
PAGE 16.
Shiri sosai Aimana take na fara zuwa makaranta, su Kamal kam dake ba sabbin student bane sun koma tun last week, gabadaya sai Aimana taji gidan ya daina mata dadi, Allah Allah take ita ma ta fara zuwa school, ko zata samu ganin Kamal.
Ranar da dare suna zaune da Abdul suna kallo a falo, Mama dake daki ta kwala mata Kira, ta amsa hadi da mikewa tayi dakin Mama, ta sameta tana zaune a kan coutch dake dakin tace, "Gani mama"
Nuni tayi mata da kusa da ita tace, "zo ki zauna a nan".
Zama Aimana tayi sannan Mama ta fuskanceta da kyau, kamo hannunta tayi ta rike a nata sannan ta fara magana..
"Aimana, ina son ki saurare ni da kunnen basira, kiji me zan fada miki kuma kiyi aiki dashi ba don ni ba don Allah".
"Insha'Allah Mama"
"Aimana, yanzu zaki fara zuwa makaranta, ba irin wanda kikayi a baya ba, wannan karon zaki shiga wuri ne da ya hada mata da maza, masu shekaru irin naki da wanda suka fiki, masu tarbiya da marasa tarbiya, yare da kabilu mabanbanta,kowa da yanayin tasa rayuwar", ta nisa kafin taci gaba..
"Aimana ina son ki saurare ni da kyau, duk wuya duk rintsi, duk inda zaki tsinci kanki, kar ki yadda ki sauka daga kan tarbiyar da muka daura ki a Kai, kullum ina fada miki kuma bazan gaji ba, Aimana ki kama kanki, ki rike mutuncin ki, ki tsare kimarki na ya mace, musulma kuma bafulatana, kisan irin mutanen da zaki zauna dasu, banda kawayen banza, banda kawance da maza, ke ba yarinya bace yanzu Aimana".
"Sannan abu na gaba da zan fada miki, ki kama kanki a gaban ko wani namijin, ciki kuwa harda Kamal da yanzu, zaman karatu ya hadaku wuri guda, Aimana kina zakewa dayawa a sha'anin Kamal, ki zama mace mai aji, ki bari shi da yake namiji ya biyoki, ba wai ki rika binsa ba, duk mace mai zakewa a kan namiji bata daraja a idonsa, kar ki yadda ki zama ballagazar mace, idan kikaje makaranta kiyi abunda ya kaiki ki dawo, Aimana kar inji, kar in gani, Allah ya taimaka ya bada sa'a".
Shiru Aimana tayi tana sauraren mama, tunani take ko Mama ta gano ta ne, don kalamanta sunyi kama da gargadi da jan kunne a kan Kamal.
Damke hannun Mama tayi sosai a cikin nata sannan tace, "Kar kiji komai Mama, indai nice ki kwantar da hankalinki, ba abunda zakiji sai alkhairi, kuma ba abunda zaki gani sai alkhairi, amma fa Mama sai kin tayani da addu'a".
"Addu'a kullum ina miki Aimana ke da dan'uwanki, kuma zanci gaba dayi insha'Allah, Allah ya tsare min ku daga sharrin zamani, ya kuma hada ku da abokan zama na gari".
Kwanciya kawai Aimana tayi a kafan Mama, ta sanya mata kuka, rarrashinta Mama ta shiga yi, saida tayi kuka sosai sannan ta dago ta kalli Mama tace...
Ki tayani da addu'a Mama, tabbas Allah ya jarabceni da wani al'amari mai girma, duk da kananun shekaruna, amma na fahimci hakan, kiyi ta min addu'a Mama, Allah ya rage min abunda nake ji a cikin zuciyata".
Na sani Aimana, kuma ina miki addu'ar zabin Allah a kullum, kuma nasan insha'Allah duk abunda ya kasance a gareki, to shine alkhairin, Allah ya miki albarka".
"Ameen Mama".
Haka Mama taci gaba da kwantar mata da hankali, ta kuma dada mata kwarin gwiwar tunkarar abunda yake gabanta.
Washegari Monday, ranar Aimana zata fara zuwa school, driver dinta tun six yazo, su Aimana zumudi, tunda tayi sallah ta fara shiri, ko kafin ya iso ta gama shiri, Abdul sai tsokanarta yakeyi, JJC, a dai kula banda kauyanci.
"Sai kayi kuma,ai naga JJC din muna da yawa", haka sukayi ta tsokanan juna,dayake shima next week zai tafi makaranta, shi an hadashi dasu Juniour ne, Daddy yaso Aimana ma ta tafi can, amma sam taki, tace ita nan takeso.
Koda seven tayi Aimana ta gama komai ta fito, ta sallami su Baba, suka mata addu'a da fatan alkhairi, sannan taje ta sallami Dada ma ta wuce, suka dau hanya.
Tafiya suke, amma Aimana gani take kamar basayi, ta zaku ta ganta a cikin makaranta,ta matsu tayi ido hudu da Kamal.
Bayan kamar tafiyar minti arba'in suka iso, har ciki ya kaita, ta sauka ta sallamesa akan idan ta gama zata kirashi.
Shiga tayi cikin department nasu, sai raba ido take,ta ma kasa gane ina zata nufa, tsayawa tayi tana karewa wurin kallo, wani murmushin ta saki tana tuna lokacinda tazo ganin Kamal, can tace, "Ho su Aimana a university, Allah mai iko".
Tana nan tsaye taji an dafa kafadarta, koda ta juyo, sai tayi arba da wata matashiyar budurwa, da alama zata girme mata kadan, hannu ra mika mata, hade da mata sallama, amsa mata tayi itama tana me mika mata hannu, "naga kamar sabuwar zuwa ce".
"Eh, kema sabuwar zuwar ce?"
"Eh, Aisha Usman".
"Aimana Tahir".
"Masha Allah, nice name, yanzu ina muka nufa?"
"Kinga tsayuwar da nayi a nan tunani nake, ta ina zan fara dosa,amma bari muyi tambayar".
"Ok to muje".
Tafiya suka fara, can suka hango wata tana zuwa, tsayawa sukayi har ta iso, sannan suka mata sallama, suka tambaye ta inda suke nema.
"Lah, kuma sabin zuwa ne?"
"Eh, ko kema cikin mu kike?".
"Ah sosai ma, ai nima yau na fara zuwa, kuzo muje, yanzu aka kwatanta min inda zani,ai kun baro hanyar a baya".
Juyawa sukayi suka koma baya, suka nufi hall dinda zasu fara daukan lectures nasu.
"Ni sunana Aina'u Sulaiman, kufa?".
Suma suka fada mata sunayensu, tafiya sukeyi suna taba hira kadan kadan, har suka iso hall din, dalibai kuwa sun taru dayawa, dake duk yau suka fara zuwa, kowa ya nemi wuri ya zauna.
Can kamar bayan minti talatin, wani lecturer ya shigo, ya gabatar da kansa, sannan ya fada musu abunda zai koyar dasu, daga haka suka shiga abunda ya kawosu, awa biyu yayi kafin ya fita, zuwa can wani ma yazo, shima yayi nasa ya tafi, a haka dai saida sukayi lecturers hudu suka shiga musu, kafin su tashi karfe biyar, basu samu kansu ba Sam, sallah kawai sukeyi su dawo, shine break dinda suka samu yau.
A gajiye suka fito, ta dannawa direbanta kira, sannan suka nemi wuri suka zauna, ita da sabbin kawayenta da tayi, suna tattaunawa akan abunda aka musu yau,zuwa can driver ya iso, ta musu sallama ta tafi,tsabar gajiya, ko inda Kamal yake bata nema ba, duk da kuwa tazo da zunudin ganinsa.
Washegari ma haka suka tafi da sassafe, dayake makarantan akwai dan tazara daga unguwar su, shiyasa dole take fita da wuri, takance duk Mama ce ta janyo Mata, da ta barta tayi zamanta a hostel, da duk wahalan jeka ka dawo, da tashi da wurin nan bazata yi ba.
Tana isa kuwa ta hango Aisha, tayi inda take, suka gaisa sannan ta tambaye ta ko Aina'u bata iso bane, tace mata eh, itama zama tayi suna hira suna dan duba littafinsu, can kuwa sai ga Aina'u ta iso, itama gaisawa sukayi, sannan Aisha tace musu..
"Kunga dama ku nake jira kuzo, sai muje mu dubo times table namu, tunda dai kunga yanzu ku na sani a nan".
Mikewa sukayi gabadaya suka nufi, inda allon sanarwansu yake, anan suka dubo times table din, Aina'u ce ta musu snapping nashi da wayarta, sannan suka duba sauran abubuwan da ya kamata su duba, suka bar wurin.
Yau basu da class sai shadaya, don haka suka nemi wuri suka zauna suna dan taba hiransu, can Aimana tace musu bari ta dubo yayanta a cikin makarantar.
"Dama kina da Yaya a cikin makarantar nan, shine jiya kika barmu muka wahala, amma dai baki kyauta ba", cewar Aina'u.
"Shine ai, kina ga fa har batan hanya mukayi, kafin mu isa hall nan jiya, ai da kin kira mana Shi, nasan har can zai kaimu".
"To duk kuyi hakuri, nima nan da kuka ganni, bansan inda zan samesa ba, amma dai bari na kira wayarsa, dayake shi a hostel yake shiyasa, ina tsammanin bai San ma na shigo ba, da zai neme ni shima".
Tana magana ne tana neman wayar tasa, saidai tana shiga amma ba'a dauka ba.
"Kunga ma tana ta ringing baya dauka, ko baya kusa da wayar ne watakila".
"Eh zai iya yiwuwa, ko kuma yana class, wani level yake?", Aisha ta tambaya.
"Eh zata iya yiwuwa, level 4 yake".
"Ah kice manyan mune kenan su Kam, kuma shima medicine yake karantawa?".
"Eh", kawai Aimana tace, don ta fara jin haushin tambayoyin da Aisha take yi a kan kamal.
"Kice gidanku zai zama gidan likitoci Kenan, sunan wani littafi, na Ameera Adam".
Aina'u tace, kema kina karanta novel Kenan"
"Eh ina tabawa gaskiya, don gaskiya ana karuwa sosai".
"Ai marubutannan suna kokari sosai wallahi", kallon Aimana sukayi da tayi shiru bata cewa komai, tuni ta Lula duniyar tunani, tabota Aisha tayi tace..
"Ya dai Aimana, muna ta magana kinyi shiru".
"Ba komai, kawai ina wani nazari ne, ku tashi mudan zaga mana muga makarantar kafin lokacin shiga class yayi ko".
Suka kuwa tashi suka fara dan takawa, suna hiransu, can Aina'u tace...
"Hanyoyin cikin makarantar nan iri daya suke, idan muka bata zamuyi bayanin, gashi da girma".
Carab kuwa Aisha tace, "Haba Aina'u, kin manta muna da yaya a makarantar ne, ta yaya za'ayi mu bata ke kuwa".
Wani haushinta Aimana ta fara ji, wai daga ce mata akwai yayanta a makarantan, shikenan tabi ta damu da zancensa, Aisha kuwa bata san me ma yake ran Aimana ba sai cewa tayi..
"Ko ba haka ba Aimana, ai kiransa kawai zakiyi idan muka bata hanya, nikam gashi ko sunansa baki fada mana ba, yayan namu".
Sosai Aimana tayi kokarin shanye haushin da take ji ta saki murmushi tace wa Aisha..
"Gaskiyar ki Aisha, ba za ma mu bata ba insha'Allah, ai duk hanyar da mukabi zamu fita in Allah ya yarda".
Haka ne kam, suna tafiya har suka isa cafeteria, nan suka zauna, suka sayi ruwa da juice, sannan suka kama hanyar komawa, sabida yanzu to 11.
Hall dinda zasuyi lecture yau daban ne da na jiya, basu wahala ba suka gane, suka shiga, basu wani dade ba lecturer ya shigo, suka fara abunda ya kawo su.
Yau kam basu suka tashi ba sai kusan six, driver ta samu yana jiranta, dama tun a class ta tura mishi text, sabida haka sallama kawai ta musu ta tafi.
Ba ita ta isa gida ba sai karfe bakwai, wanka kawai tayi ta tada sallah, tana idarwa aka kira Isha, mikewa tayi ta gabatar, yau ko shafa'i da witiri bata samu daman yi ba tsaban gajiya, so take kawai ta jita a kwance, don ko abincin bata nema ba
Mama ganin yanayinta yasa ta zubo mata abinci ta kawo mata, tana zaune ta sata a gaba saida taci sannan ta tashi, ta barta, ai ba'a dau lokaci mai tsayi ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.
Can cikin baccin ne taji wayarta na kuka, ta bude idonta ta jawo wayar, bata ma duba mai kiran ba don baccinda yake idonta, muryar da taji ne yasa ta wartsakewa.
Sake sallama yayi, sai a lokacin Aimana ta samu damar amsawa, Yana jin muryarta kuwa ya gane yace..
"Aimana kece, ya kike, ya su Mama".
"Lafiya qalau Yayana, tun safe nayita kiranka baka daga ba, kuma baka kirani ba sai yanzu".
"Ki bari kawai Aimana, yau nayi busy ne dayawa, don bana cikin school ma, mun shiga asibiti, munje ganin wani surgery, to bamu dawo ba sai la'asar, kuma ana bukatar mu rubuta report na surgery din, gobe da safe zamuyi submitting, shiyasa ko ta kan wayar banbi ba sai yanzu".
"Ayya sannu ya Kamal, ai kuna kokari wallahi".
"Kema ai zaki shigo ki gani ne, yaushe ma zaki fara zuwa,en level 1, sun fara lectures jiya naji?"
"Ai ya Kamal tun jiyan nima na fara zuwa, kawai ban samu time bane, shiyasa ban nemeka ba, shiyasa yau da safe da naga bamu da class na nemeka, kuma ashe kaima baka nan".
"Iyye, kice my Aima an fara danawa, yanzu zaki gane me nake fada, ko dayake ai level 1 ba takura sosai, kuma karatunsu da dan sauki".
"Hmmm ya Kamal, wani irin ba takura, yau fa sai six na bar makaranta, kafin na iso gida to seven, duk na gaji wallahi".
"Haba ke kuwa, me ma akayi, wannan ma duk nasan introduction ake muku yanzu, ba'a shiga karatu sosai ba".
"Hmmm, ya Kamal, a dai bar zancennan don bana ma son ji yanzu, wani irin surgery ne kukayi yau din?"
"Sukayi dai, don mu ai yan kallo ne, amma abun kam gwanin ban tausayi, wayar wa kika samu haka".
"Wayata ce ya Kamal, kasan yanzu na zama big girl".
"Yanmatan jami'a ba".
"Yesss, ok ya Kamal, baka bani labarin surgery din ba".
Haka Aimana ta canza musu hiran, sun kai kusan minti ashirin suna waya, shima kudinsa ne ya kare, aikuwa Aimana ta kirashi, dake ita Daddy ya cika mata kati a wayarta, kuma Junior ma saida ya sa mata kati kafin ya bata wayar, so ita bata da matsalaar kati, sun kai kusan 12 suna waya kafin su kashe, wani bacci ne ya dauki Aimana me dadi, me cike da mafarkin Kamal dinta, ko da asuba makara tayi, saida Mama ta tashe ta, sallah ta yi ta yi azkar nata, kafin ta tashi ta kimtsa dakinta ,ta share tayi wanka ta shirya, wayar ta ta dauko, ta duba times table nasu, taga 9 suke da class, don haka ta shirya a natse, har ta taya Mama aikin gida.
Karfe takwas ta bar gida, yau driver har kofar hall da zasuyi lectures ya ajiyeta, ta sauka ta shiga, gaisawa tayi da wadanda ta samu a ciki, kafin ta nemi wuri ta zauna, don su Aisha basu iso ba, ta dan jima da zama kafin suka iso, don har sunso makara, suna zuwa lecturer dinsu ya shigo, don haka ko gaisawa basu samu damar yi ba.
Saida yayi awa biyu da rabi kafin ya fita ya barsu, dake basu da wani class sai karfe biyu, yasa suka fita suka samu wuri suka zauna, suna nazarin abunda aka musu, don anyi sa'a dukansu himma ne dasu wurin karatunsu, da an musu darasi suke natsuwa su duba, suyi jotting inda basu gane ba, don idan akazo next class suyi tambaya.
Suna nan zaune, Aimana ta fito da wayarta ta dannawa Kamal kira, an kuwa yi sa'a ya daga, gaisawa sukayi sannan ta tambaye shi ko yana free ne yanzu.
"Eh gaskiya banda class yanzu, amma...."
"Amma me, ba wani amma, ya Kamal kawai ina jiranka".
Dariya kadan yayi sannan tace, "Ho Aimana rigima, to shikenan fada min inda kike, ko dayake ma kawai mu hadu a cafeteria".
"Ok, to gani nan zuwa", daga haka ta yanke wayar, ta juya ta dubi su Aina'u da suka saki baki suna ganin yanda take wani lumshe ido tana kashe murya, wai kuma da yayanta take waya.
Aisha ta tabota tace, "Anya kuma Aimana, wannan Yayan ne kuwa, kodai ya shiga rigar yayunne".
Murmushi kawai tayi tace, "sai kiyi kuma, idan ba Yayan bane to menene".
"Uhumm, maji ma gani"
"Ba abunda zaku ji bare gani, Yayana yace mu hadu a cafeteria, zamuje ne?"
"Zuwa kai, kinga daga nan sai muga wannan Yayan da ake mana rowarsa", cewar Aisha.
Gabadaya suka dunguma suka tafi, suna isa kuwa Aimana ta hangoshi, yasha kyau cikin kanan kayanta, bakin wando da blue shirt.
Tsayawa sukayi suna karewa juna kallon, gabadaya sun ma manta da wasu al'umma a wurin, Aisha ce ta tabo Aina'u tace, "Ke kinga abunda na gani kuwa?"
"Na gani mana yar'uwa, ga dukkan alamu dai wannan yafi karfin yaya"
Dariya sukayi, sannan Aisha ta tabo Aimana.......